Gaba ɗaya kowani ahali daga cikin su haka suka wuni da fargaban a wani hali yaran nan suke a ciki, tun jiya da dare ba ci ba sha, ruwan tea din da suka sha lokacin da suka yi nafilfili ne kaɗai ya rage a cikin su..
Abu kamar wasa har dare ya yi, babu labari dangane da su.
Hajiya layla da Alhaji Ubaid da mare ce suka bar gidan Owais sakamakon kiran da Hajiya Sarah take tayi masu game da rashin dawowarsu gida, kuma sun bar su cikin fargaba.
Kusan gaba ɗayansu suna a falo cikin damuwa, kowa ka kalli fuskarshi babu annuri bacci su ke ji amma damuwa ta hana baccin ya ɗauke su, sun kasa sun tsare suna jiran dawowar ƴa'yan su, Sheikh imam ne ke tausarsu da nasiha mai ratsa zuciya, Taj ne kadai baya a falo bai jima da fita ba, ya je ya kwantar da baby Junaid da ya yi bacci, Benazir da Aisha da Anila Suna a zazzaune kan Sofas sun zabga tagumi suna sauraron Sheikh Imam, yayin da Dr shureim yake a gefen shi, shi kanshi Imam malik din ba ƙoshin lafiya ne da shi ba, sosai yake jin ɗacin abun da Musa ya yi mashi a ranshi, ya yi masa abun da har abada ba zai manta da baƙin cikin nan ba, amma ya ɗauki dangana, kuma baya son rauninsa yasa suma su shiga damuwa ko dan Saboda alƙawarin da ya ɗaukarwa Aisharsa.
TAJ🌹
Yana a zaune gefen gadonshi. Idanunshi akan baby Junaid dake ta sharar bacci, bakomai ne ya fado masa aran shi ba face wasu maganganun da suka ta6a yi da Uzair, Allah sarki ba rabon Uzair yaga gudan jininsa..
Tunawa ya yi da lokacin da Unaisah take yar jinjirarta, murmushi ya yi, yayin da hawaye suka cicciko idanunshi, baya jin zai iya rayuwa batare da ƴar shi Unaisah ba.
Shafa fuskar Junaid ya yi da tafin hannunsa, bai aune ba ya ji ya ka6e masa hannu cikin magagin bacci ya soma yin sambatu yana fadin, "Ni ka daina kallona, duk ka takura ni, ka tashi ka tafi tun da ka kwantar da ni."
baisan sa'adda ya yi dariya ba.
Ashe idanunshi buɗe suke, sun yi ja sai cika yake yana batsewa.
"Baby Junaid, Ni ne fa? Daddy Taj."
Zum6ura masa pink lips dinsa ya yi, "Ni ba wani nan, kawai ma ka takura ni, Allah saina faɗe mata abun da kake mini.."
ya faɗa yana kokarin miƙewa zaune da sauri Taj ya mayar da shi ya kwantar, ya janyo duvet ya lullu6e shi dukan shi.
"Pls ka yi hakuri ka yi bacci, ba zan ƙara damun ka ba"
"Toh ka tashi ka tafi." Murmushi ya yi tare da miƙewa cikin sanɗa ya fuce daga dakin.
Leƙowa Junaid ya yi daga cikin bargo, ganin babu Taj yasa shi mayar da kansa ciki ya ci gaba da yin baccinsa.
Unexpected wayar Taj ta soma ruri, a lokacin yana gab da zai shiga falo, cikin sauri ya zaro wayar, ko da ganin sunan my in-law ya bayyana yasa shi saurin picking yatsunsa har kerma suke saboda zumuɗin ya ji ya ake ciki, duk da yana fargaban me zai ji daga gare sa.
"In-law, Guess what? Muryar Chief ce ta katse shi.
Ɗan zaro idanunsa ya yi cikin rudu ya ce, "Chief, bangane me ka ke nufi ba? Kun samo su um?"
Sautin dariyar Chief Owais ya jiyo, "Ka fara yin sujudusshukr kafin in sanar da kai." Cikin sauri ya fuskanci alkibla ya yi sujjada, kafin ya miƙe yana tambayar shi meya faru?"
Nan take Chief ya zayyana mashi komai da ya faru a gidan Kurkukun kaddara! Ya Ilahi ji ya yi kamar a mafarki.
Ya ƙara da cewa, "Yanzu haka Elders suna a CSH ana yi masu treatment saboda raunukan da suka ji, Unaisah da Batool kuma suna a cikin asibitin Headquarter din mu, lafiyarsu kalou, amma ana ƙara bincika lafiyarsu, saboda kwakwalwar Unaisah ta ɗan ta6u sakamakon razanar da ta yi..."
Bai ƙare sauraran Chief Owais ba ya arta a guje ya nufi main door zai fuce.
Gaba daya suka bi shi da kallo, muryar Benazir ce ta katse shi, "Taj, meya faru? Ina zaka je?"
Ya juyo fuskarsa ɗauke da murmushin farin ciki ya ce, "Sun dawo. Sus.. Suna a headquarter ɗin mu! Unaisah da Batool..."
kusan a tare suka miƙe tsaye tare da bin bayan shi, tsabar ƙaguwa kamar zasu bangaje juna.
Sheikh Imam da Aisha motar Dr Shureim suka shiga., Benazir da Anila suka shiga motar Taj, tare da Motocin Securities gaba da bayan nasu motocin.
A lokaci ɗaya motocin suka fuce daga villa din sai baza gudu suke yi saman titi kamar zasu tashi sama..
*ISOD HEADQUARTER🔥*
Lokacin da motocin su suka ƙaraso Headquarter basu sha wahalar shiga ba, suna yin parking dinsu, cikin sauri suka fito daga ciki, Taj da Benazir ne a gaba, Ummi da Shureim suna a biye da bayansu, yayin da Sheikh Imam da Anila suke biye da su.
Isod Soldiers din dake zarya a tsakar headquarter din sai kallonsu suke yi, sai dai kwata kwata babu alamun sun ma san da zaman su saboda hankalinsu na akan abun da ke gaban su.
Da yake sun san da zuwansu kuma ga Taj a tare da su hakan yasa duk inda suka bi a hanzarce agents din dake a ciki suke darewa su basu hanya don su wuce.
Lokacin da suka karya kwanar da zata sada su da inda suke unexpected suka soma jiyo ihun Unaisah tana faɗin, "Acid na watsa mashi akan fuska! Na ƙona masa fuska, ya mutu! Bazai ƙyale ni ba, gayanan ina ganin shi, fatalwarsa ce, kashe ni zai yi..."
Tsantsar farin ciki da rudani ne akan fuskokinsu, cikin sauri suka faɗa Private room din, Doc suka gani a bakin gadon da take, Chief Owais yana a zaune daga gefen gadon ya rurruƙeta, sai ihu take tana firgita kamar mai aljanu.
"Babyna..." Benazir ce ta faɗa, da gudu ta nufi gadon, Chief Owais ya miƙe ya bata guri, zama ta yi tare da janyota ta rungumeta akan kirjinta, batasan sa'adda ta saki kukan farin ciki ba.
Ta dinga shafa bayanta tana fadin, "Unaisah ki daina kuka, mommyki tana a tare da ke! Ina fata basu cutar min da ke ba.."
Jajayen idanunta ta ɗaura akan benazir, tana magana yawu na fita ta bakinta ga majina dake zalalowa ta hancin ta, "Acid na watsa mashi a saman fuskar shi, na ƙona shi, ina ganin shi da idanuna yana a cikin ɗakin nan ya ce sai ya kashe ni, gashi nan zai ta6a ni...!"
da karfi ta faɗa a rikice, shatun jijiyoyin wuyanta sun fito rudu rudu.
Ƙanƙameta Benazir ta yi kamar zata mayar da ita cikin cikinta..
Babu wanda bai tausaya mata ba!
"A ina aka gan su? Ina Batool? Ina Musan? Bai cutar da su ba? Meke damun Unaisah ne?" Chief suke ma tambayoyin, Shureim sai baza idanunshi ya ke yi burinshi ya ga Batool dinsa haka itama Ummi ta kasa samun sukuni.
"Pls, ku kwantar da hankalinku, ba a cutar da su ba, Unaisah ta yi faɗa da Musa harta yi nasarar watsa mashi acid a saman fuskarshi, shiyasa ta razana, kamar gizau ya ke yi mata tun ɗazu muke ta kokarin mu shawo kanta mun kasa, ga docs nan ta ƙi bari su duba ta, kowa ya kawo hannu zai ta6a ta sai ta fashe da ihu tana faɗin gayanan zai kashe ta.."
Tsantsar mamaki ne da rudani akan fuskokinsu, akwai tambayoyi da dama da suke son yi mashi sai dai sun lura ba a cikin nutsuwar shi ya ke ba.
"Ina Batool? Itama hada ita kuka dawo?"
Dr Shureim ne ya tambaya cike da damuwa..
"Harda ita muka dawo, amma sai dai ku yi haƙuri..." Gaban su ne ya fadi, cikin rawar murya Ummi ta ce, "Pls ba sai ka fada ba, in dai ba alkhairi bane ka yi shiru, zuciyata zata iya bugawa in mutu!"
Fuskar Owais babu annuri ya ce, "Tun da baku buƙaci in fada ba ku biyo ni mu je ku gani da idanunku, amma pls komai zaku gani ku yi haƙuri."
gaba daya sun sha jinin jikinsu.
Bayan fitarsu daga ɗakin ya rage saura Unaisah dake rungume a kirjin mommynta, Taj yana a zaune kan kujerar dake fuskantar su, addu'oi suke ta tottofa mata akan ta.
Doctor din da ya zo duba ta yana a tsaye yana jira su kammala shawo kanta don ya samu ya yi mata allura.
A gaban dakin da take suka tsaitsaya cirko cirko, saboda zullumi da farbagan abun da zasu taras ya sa kowannan su yake jin tsoron ya shiga ciki.
"Bismilla, mu shiga daga Ciki."
Chief ne ya faɗa tare da bude masu ƙofar ɗakin.
"Dan Allah sir, ka fara faɗa mana a wani hali take ciki? Ina jin tsoron na ga abun da zai yi silar mutuwa ta!"
"Ummi, ke da kan ki kika ce inna san ba alkhairi bane kada na faɗa, why zaki canza magana, kawai ki shiga ciki." Yanayin yadda yayi mata magana da walwala akan fuskarsa kamar ba Chief Owais ba.
Sheikh Imam ne kadai hankalinsa bai tashi ba saboda yasan Chief Owais ba zai ta6a bari su zo ganinta ba in har wani mummunan abun ya faru da ita..
Tura kofar sheikh Imam ya yi, ya shiga da bismillah a bakinsa, yana dira ƙafarsa ya hango ta a kwance saman gado ta yi ɗai ɗai tana ta sharar baccin ta.
Wani irin annurin farin ciki ne ya lullu6esa da ƙarfi ya furta, "Alhamdulillah, ku shigo ku ga jikata da ranta da lafiyarta ba abun da ya sameta..."
A hanzarce suka bankaɗo cikin dakin, Ummi da Shureim suna ɗaura idanunsu akanta, wani irin daɗine mai tattare da farin ciki ya cika zukatansu, kamar wadanda aka yi wa albishiri da gidan Aljanna, bakinsu ya ƙi rufuwa, idanunsu sun cicciko tab da kwalla. Kewaye gadon suka yi, jikin Ummi na 6ari ta zauna daga gefe, ba zata iya jira ta farka ba, tallabo kanta ta yi tare da rungumeta a ƙirjinta, batasan sa'adda kukan farin ciki ya 6alle mata ba, wallahi sai ta ji gaba daya kamar an yaye mata baƙin cikin da ke a cikin Zuciyarta.
Cusa yatsun hannayenta ta yi a cikin gashin Batool ta na yamutsawa kamar tana yi mata susa ta ƙanƙameta, ta fara manna mata sumbata tun daga kan kuncinta har izuwa goshinta, kamar zata lashe ta, ta ma manta da sauran mutanan dake a ɗakin, kowan nan su murmushin farin ciki ne ɗauke akan fuskarshi, Dr Shureim sai washe baki ya ke yi, har sujudusshukr ya yi a dakin, lokacin da ya ɗago hawaye ne sharkaf akan kuncinsa, sai kallonsu ya ke yi kamar zai haɗiye su.
Matsewar da Ummi ta yi mata ne yasa ta farka daga bacci, tunkan ta buɗe idanunta hancinta suka shakar mata ƙamshin turaren Aunty Umminta wanda koda yaushe in kana a kusa da ita sai ka ji shi a jikin ta.
Cikin rawar murya ta shiga furta, "Aunty Ummi? Ke ce? Kece a kusa da ni? Aunty Ummi kamshin turarenki nake ji? Dan Allah in bacci nake yi kada ku farkar da ni, mommyna kawai nake so na kasance da ita har ƙarshen rayuwata, dan Allah kada ku bari ya raba ni da ita, ina so na rayu saboda ita, ina so na sanya ta farin ciki..."
Sambatun da ta ke yi ba karamin karya musu zuciya yayi ba.
Shiekh Imam a fakaice yake sharce ƙwalla, bakomai yake tunawa ba, fa ce ranar da ya kar6eta cikin tsumma daga hannun Aunty Laura, ya jinjina ta ya kira ta da sunan shegiya a gidansa, Ya Ilahi! Ya yi danasanin furta kalmar nan.
Tallabo fuskarta Ummi ta yi da tafukan hannayenta, hawayen dake zarya kan kuncinta kaitsaye suke sauka akan kuncin Batool hakan ya tuna mata da ranar da ta haifeta irin hakan ta faru.
"Batool, ki saka idanunki a cikin nawa, ni ce a tare da ke, ba abun da zai faru da ke, kuma babu wanda zai ƙara raba ni da ke, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba Batool, bazan ƙara tafiya na barki ba, ina sonki fiye da raina..."
A hankali ta soma buɗe idanunta da suka yi mata nauyi saboda baccin da ta sha, har yanzu allurar da doc sukai mata bata sake ta ba, wata irin malalaciyar kasala take ji.
Dakyar ta iya tsayar da idanunta a cikin na ummi.
Cikin disasshiyar murya ta furta, "Aunty ummi na.. "
jinjina mata kai ta yi da murmushi ta ce, "Daga yau ba sunana aunty ummi ba, ni ba gwaggonki bace, kuma ba yayyarki bace, Mahaifiyarki ce, ki kira ni da Mommy, ko kira ni da Ummi"
gaba daya suka saka dariya cikin raha.
Sam ta kasa kawar da idanunta daga kallon fuskarta, gani take kamar mafarki ne.
Cike da so da ƙauna suke kallon juna.
"Batool, ni baki ganni ba?" Dr shureim ne ya yi maganar cikin karyayyar murya, a hankali ta mayar da idanunta akan fuskar shi, lokaci ɗaya ta shiga tariyo maganganun Musa a cikin kunnanta, ta ji komai, ta ji irin baƙar izayar da mahaifinta ya sha saboda ita.
Fashewa ta yi da kuka kamar ranta zai fita, gaba daya hankalinsu ya tashi matuƙa, a tunaninsu wani abunne ya 6ata mata rai, lallashinta suka dinga yi, Dr Shureim har ya karaya, ya yi zaton saboda ta ji shine silar abun da ya faru da mommynta shiyasa ta ke kuka, kallon da take masa ya yi masa kama da kallon tsana.
Jiki a sanyaye ya juya zai bar ɗakin batare da kowa ya lura ba, baisan idanunta a kan shi suke ba, ƙwacewa ta yi daga jikin Ummi, duk da rashin kwarin jikinta a haka ta duro daga kan gadon, suna ta tambayarta ina zata je, Anila na kokari ruƙota ta ka6e hannunta, da gudu ta bi bayan shi, yana gab da zai fuce ya ji ta rungume shi ta baya ta zagayo da hannayenta kan cikin shi, sosai ta ƙanƙameshi, wani sanyi ne ya ratsa zuciyar shi kamar kamar me.
cikin shesshekar kuka ta furta, "Daddy, ina zaka tafi ka barni? Bakasan na fi bukatar ku akan komai ba? Daddy ina son ka wllh, kaine bugun zuciyata, jagoran rayuwata, wanda ya tsaya mini tsayin daka don ganin ban yi maraicin uwa a tare da ni ba, uban da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda ƴarsa ta rayu, idan babu kai babu ni daddy..."
Yayin da take furta masa kalaman nan, ji yayi kamar anyi mashi albishir da gidan Aljanna, farin ciki kamar zai kashe shi, gaba daya mutanan dake a dakin saida suka yaba da iya tsara kalaminta, ta burge su, ta kuma sace zuciyar su, especially Sheikh Imam da Chief Owais sun kasa dauke idanunsu daga kallon su.
A hankali ya ruƙo yatsun hannayenta, yayin da yake tunawa da ranar da ya fara ganinta tana jinjirarta, a lokacin da Ummi ta kawo mashi ita cikin tsummanta.
Janyota ya yi ya dawo da ita ta gabanshi, ya sanya hannayenshi biyu ya yi hugging dinta tighly kamar zai mayar da ita cikinsa, a hankali yake shafa sumar kanta har izuwa saman kanta, so yake ya yi magana shesshekar kuka ta hana shi.
"Kun ga yadda Allah ke ikonsa ko? An raba ku saboda zalunci, Allah kuma ya sake haɗaku ta yadda ku kanku baku ta6a tsammani ba, ribar hakuri da tawakkali kenan, mu runƙa hakuri da kowace kaddara ko jarabawa da ta same mu, duk abun da Allah ya yi a rayuwarmu mai kyau ne, amma sai mun yi hakuri zamu gane hakan, kawai mu yi hakuri mu ci gaba da addu'a, mu kuma yi masa biyayya kada mu sare ko mu butulce masa, mu dinga tunawa da ni'imomin da ya yi mana kafin jarabawarsa ta riske mu..."
Anila ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi, hawaye sun ciko idanunta abun ya ta6a zuciyarta.
"Zan iya cewa, yau ce rana ta huɗu da na yi farin ciki mara misaltuwa a rayuwata, ranar dana ga su Taj a raye, da ranar dana ga Aisha da Benazir da ransu da lafiyarsu, sai kuma yau da Allah ya nuna mini abun da ya fi komai faranta raina.."
murmushi suka yi gaba ɗayansu.
Miƙewa Aisha ta yi daga kan gadon ta je gaban Dr Shureim ta tsaya tana kallon su..
Ita shaida ce akan irin kaunar da yake ma Batool dinta.
Da kyar ya iya furta, "Ki yi hakuri Batool, bada son raina komai ya faru ba, bansan na binne ki ba, bana a hayyacina, kuma bansan kina a raye ba, da wlh har raina zan iya badawa don in ceto rayuwarki.."
Ɗagowa ta yi da fuskarta dake a jiƙe da hawaye, "Abba, zan roƙe ka alfarma ɗaya a duniyar nan."
Cikin sauri ya ce, "Zan yi maki, komai kike so ki faɗi." Kowa ya nutsu yana jiran ya ji me zata ce.
"Pls, mu manta da abun da ya wuce, bana ganin kowan nan ku da laifi, komai da ya faru na sani bayin ku bane, na ji komai da kunnena, idan kuna yin magana akan abun da ya faru a baya baku tunanin zai haifar min da damuwa?"
Batool ba karamin kashe su ta yi da dadi ba, tun yanzu sun san wacece yar tasu, yarinya mai tawakkali, mai hankali da tunani jikar Imam Malik kenan, ɗiya ga Ustatha Aisha bintu Imam da d
Dr.Shureim, lallai ta fito daga tushe mai daraja.
"Na yi maki wannan alfarmar Batool, mun daina, ba zamu ƙara ba." Ya fada yana share mata hawayenta.
Murmushi ta yi, "Nima yanzu ina da iyayen da zanyi alfahari da su, ina da gata, sannan daga yanzu za'a dinga kira na Batool Shureim kamar yadda ake kiran yar uwata da Unaisah Zaheer Tajudeen."
gaba ɗaya suka sanya tafi.
"Ina taya ku murna gaba ɗayan ku, Allah raya mana Batool dinmu Allah kuma ya kare mana ita."
Anila ce ta fada tana nufar su, janyo batool ta yi ta rungumeta sosai.
"Nima ina taya ku murnar ganin ƴar ku, kuma in sha Allah, ba za ku sake rabuwa da ita ba."
Chief Owais ne ya faɗa cikin sanyin murya.
Godiya suka yi ma shi, kafin ummi ta ja hannun Batool ta kaita gaban sheikh Imam malik, "Kin gane shi ko sai na yi maki bayani?" Murmushi ta yi, "Kakana ne, Baba Imam."
Rungumeta ya yi a kirjinshi ya fara saka mata albarka da yi mata addu'o'i yana jin sonta da ƙaunarta na ratsa shi, ita ce jikar shi ta farko kuma ɗaya ƙwallin ƙwal daga gurin ƴar sa abun alfaharin sa.
Allah kaɗai yasan ɗumbin farin cikin da Batool ta ji a yau, wallah baya misaltuwa.
A hankali ta raba jikin ta daga na sheikh Imam Malik, Ummi ta ruƙo hannunta ta kuma ruƙo hannun sheikh Imam, ta ja su har gaban Chief Owais, ta yi ma Shureim da Anila alamar su matso kusa da su, duk yana a tsaye yana kallonsu ya harɗe hannayen shi kan ƙirjin shi ya rasa gane me zata yi.
"Assalamu alaikum."
Muryar Taj ce ta katse hanzarin ta, kusan a tare suka juya baya suna kallonsu yayin da suke shigowa, shi da Benazir ne sun saka Unaisah tsakiyar su, jikinta lullu6e da bargo kamar wadda sanyi ya kama.
"Ku yi hakuri, kun ji mu shiru, Unaisah ta ƙi daina firgita, sai yanzu muka samu ta dawo daidai, tana ta neman ƴar uwarta..."
murmushi kowan nan su ya saki, da sauri Batool ta nufeta suka rungume juna, kamar zasu koma mutun ɗaya, yau dai ta zama ranar tunawa a rayuwar su.
(Ni boss hada ƴar ƙwallata 😥)
"Sis kina lafiya? Meke damun ki? Ya cutar da ke ne um?"
adabarbarce take tambayarta..
Da kyar ta iya buɗe baki muryarta ƙasa ƙasa ta ce, "Ba abun da ke damuna, lafiyana lou, bai yi mini komai, ina fata kema kina lafiya..."
jinjina mata kai Batool ta yi, "Nima ina lafiya sister, na ji dadi babu abun da ya faru da mu, Allah ya kare mu, bai cimma manufarsa ba." Ta fada tana dan sauke ajiyar zuciya.
"Sai dai ban iya tuna komai da ya faru ba."
"Batool, tunawar baida amfani, tun da ba alkhairi bane, idan ma akwai abun da ya kamata ki ji zaki ji, amma ba yanzu ba.."
Murmushi ta yi, "Na ji, amma kin yi min laifi, daga yanzu karki ƙara kira na Batool, ni ƴar uwarki ce, cousin dinki ce, kuma yayarki, sannan aminiyarki..."
Gaba ɗaya suka sanya dariyar farin ciki, musamman iyayensu farin ciki ne tsantsa tare da su .
"Kina nufin, ke ɗiyar Uncle ɗina ce Shureim? Jinin da ke yawo a jikina shine a jikin ki?" Ta tambaya kamar irin batasani ba..
Cike da jin dadi Batool ta jinjina mata kai,
"Ba mamaki, shiyasa farko da kika fara ganina a gidan kurkukun kaddara kika manne min kamar ciki ɗaya muka fito ashe jinina ce ke." Dariya suka yi..
"Ina taya ki murna Batool, Aunty Ummi, Uncle Shureim kuma ina taya ku murna, kamar yadda Batool ta yi dacen iyaye nagari, kuma haka kun yi dacen ƴa ta gari, saboda Batool ta dabance, samun irinta zai yi wuya, ni ta yi min hallacin da bazan iya biyanta ba, saboda ta ja ni a jiki a lokacin da sauran yan uwanmu suke guduna, a lokacin da nake tsaka da maraicin rashin wani nawa a kusa da ni, a kuma lokacin da na tsinci kaina a baƙon guri mai rikitarwa, duk yadda zan misalta maku ba lallai ku fahimta ba.."
ta fada tare da janyo Batool ta rungumeta.
kukan farin ciki suka kama yi.
gaba daya kowa dake a gurin saida ya zubda masu ƙwalla saboda sun ta6a zukatan su.
Saida suka gama koke koken farin cikin nasu, daga bisani Ummi ta janyo hannayensu, ta kawo su gaban Chief Owais wanda komai dake faruwa a kan idanun shi, ta kuma ruƙo hannun Benazir ta ce ma Taj ya matso kusa da ita, gaba daya suka kewaye Chief Owais.
"Bani da abun da zan iya saka maka da shi, bazan iya biyanka ba! illa iyaka in sanyaka a cikin addu'o'ina, Allah yasa silar kyautata mana da ka yi ya zama sanadin shigar ka Aljanna, Allah ya wanzar da farin ciki da lafiya mara yankewa a cikin rayuwarka, Allah ya yaye maka dukkan damuwarka, Allah ya lullu6eka da rahamominsa, Ya kare mana kai daga sharrin duk wani abun cutarwa da kai da ahalinka, Allah ya ci gaba da daukaku, Allah ya baku hakuri da juriyar cinye jarabawar da kuke fuskanta, Allah kuma ya baka mata tagari wadda zata zama cikamakon farin cikin rayuwarka..."
Tun da ta fara yi masa addu'oin ya lumshe idanunsa yana ɗan jinjina kanshi, gaba ɗayansu suke amsawa da Ameen Ameen, Chief ya yaba da addu'oin ta sun faranta ran shi.
"Abun da yasa na tara ku a gabansa, saboda ina so ku taya ni yi mashi godiya, saboda ba zan iya yi ni kadai ba."
ta fada tana duban kowan nansu, aikuwa gaba daya suka haɗu suna yi mashi godiya da addu'o'i duk da ya nuna basai sunyi ba, ya ce su gode ma Allah shine abun godiya, suka ce sun yi wannan amma yabon gwani ya zama dole.
Gaba ɗayan su suka fito daga headquarter din, suka nufi inda suka bar Motocin su, bayan kowan nan su ya shiga ciki, at same time motocin suka soma tafiya a hankali, har suka bar headquarter ɗin.
"Baby, ina kika samu waɗannan kayan na jikin ki? Tun dazu nake ta so in yi magana." Ummi ce ta faɗa tana kallon Batool, da sauri ta dubi kayan, shirt ce fara, da coat din da aka daure mata qugunta da shi, daga gaban rigar an rubuta Dg.
Zare idanu ta yi kafin ta yi magana Ummi ta riga ta cewa, "Kamar kayan Chief ne ko? Na ga sunan rank dinsa a jiki."
"Bansan lokacin da ya sanya min rigar ba, bazan iya tunawa ba.."
ta fada tana dan girgiza kan ta.
Dr shureim da ke driving dinsu, a hankali yake satar kallon su ta mirror, sai faman sakin murmushi ya ke yi yana kallon family ɗinsa.
"Wani kaya ne last a jikin ki?"
"Overroll ce, irin ta jikin Unaisah, sai coat da muka ɗaura a sama, bansan ya akai na rasa kayana ba." Kwanto mata da kai Ummi tayi kan kafadarta, ta lumshe idanunta tana sauke a jiyar zuciya..
Wow 😍😂
_______________________Ex-Prisoners🔥🔥🔥🔥🔥🔥
"Naufal! ! Haris! Javed! Mubeen! Ku tashi na samo mana hanyar da zamu fita" can cikin bacci suka tsinkayi muryar Sajeed dake ta kiran sunayensu cikin muryar raɗa.
Bubbuga kafafunsu ya yi, "Dalla ku tashi, idan ba haka ba zan tafi in barku."
At same time suka farka tare da yaye bargunan su, idanunsu biji biji suke ganin shi, sai miƙa suke yi da hamma alamar bacci bai ishe su ba, a saman wata ƙatuwar mattress suke a kwance lallausar gaske, mai tudu kamar gado.
Hasken dakin ya kunna hakan yasa suka samu damar ganin shi da kyau, yana a tsaye gaban katifar hannun shi ruƙe da nannaɗaɗɗiyar igiya mai kauri, zaro idanu waje suka yi a ruɗe har suna hada baki gurin furta, "Sajeed me zaka yi da igiya?"
Harara ya watsa masu, "Bana ce maku ina ta nema mana hanyar da zamu fita ba? Ko baku so ku koma sashen Chief?"
Haris da ya fi su hankali ya ce, "Sajeed kana da gajan hakuri, kuskure ne wannan mu yi gaban kanmu ba tare da izinin daddy Taj ko Chief ba! Ransu zai baci idan suka ji, tun da sun ce mu ƙara hakuri why ba zaka hakura ba?" Harara Sajeed Ya watsa mashi tare da tamke fuskarsa.
Naufal ya ce, "Ni abun da bangane ba, ta wani kofa ne zamu fitan? Me kuma zamu yi da igiya?"
"Haƙurina ya ƙare, ni bazan ci gaba da jira ba, wallahi babu wanda ya isa ya hanani in fita, na gaji na gaji, ku baku gaji bane da zama a kulle? Baku tunanin akwai wani abu da ya faru wanda ba aso mu sani shiyasa aka garƙame mu anan?"
Kallon juna suka yi, kowan nan su da wannan tunanin a ranshi.
"Idan nan zamu ci gaba da zama meyasa ba za a dawo da su Unaisah nan din ba? Me kuma yasa mu ba za a mayar damu can ba? Meye amfanin kulle mu?"
"Sajeed, amma ai muna yin waya da su Unaisah ko? Kuma sun faɗa mana komai lafiya lou, sun je farmaki sun dawo lafiya."
Javed ne ya fada fuskarsa a yamutse..
"Baku tunanin sun faɗa mana hakanne don su kwantar mana da hankali? Ku yi tunani mana! Wani abu yana faruwa! Har yanzu ban yarda Danish yana lafiya ba, kawai suna boye mana ne, ƙwara mu je mu gane ma idon mu." Kallon kallo suke jefawa junan su.
Tunzura su ya dinga yi har saida ya shawo kansu suka amince zasu bishi, saukowa suka yi daga kan latifar, gaba dayansu pyjamas ne a jikin su, kowa da kalar nasa.
Sajeed ne jagoran su wato Master Planner, yana a gaba suna a biye da bayan shi cikin sanɗa suke yin tafiya, kamar 6arayi duk don kar a kama su.
Cikin muryar raɗa Naufal ya ce, "Mu kadai zamu tafi? Su parveen fa? Idan suka farka suka ga babu mu zasu shiga damuwa."
"Ƙwara karmu tafi da su, kasan halin Jemimah tsiwarta kaɗai ta isa ta tona mana asiri, in aunty Danejo tasan me muke ƙullawa zata kira ne ta fada.." Javed ne ya fada.
"Ku daina ɗaga murya, ku yi shiru." A cewar Sajeed.
A hankali suke tafiya suna yan waige waige sun jera layi, sai da suka kusan ƙarasawa ga stairs unexpected suka ji muryar mutane a cikin kunnan su..
"Banza ki sha a hankali kada ki ƙware, matsalata dake kin cika haɗama, wlh zan tona mana asiri muna satar abinci uban kowa ya ji." "Wai ke ina ruwanki da ni, ba cewa ta yi mu ci komai muke so ba..." Gabansu ne ya faɗi kusan a tare suka kai dubansu gare su, suna a zaune kan matakalar benen da suke tunkara, su biyu ne, Praveen ta tasa plate din chicken pepper soup, da duka hannayenta biyu ta ke duma loma, bakinta duk maiƙon mai.
Jemimah tana zaune a gefenta, saman cinyoyinta gwangwanin madara ne daga gani sabo ne ta fasa, ta buɗe shi sai sha take yi, duk ta yi buɗu buɗu da kumatunta, har saman gaban rigar baccin ta madararce ta 6are kamar farar kura.
"Mun masu wayo sunata bacci, mu kuma kullum sai mun farka tsakar dare mun saci abinci, da safe aita neman wanda ya kwashe ragowar abinci, mu yi shiru da bakinmu, wai Aunty Danejo sai tace 6era ne batasan mune 6erayen ba.." Jemima ce ta fada.
Parveen ta ce, "Ai ran nan ina jin ta tana tambayar waya sace naman miya, nasan kece munafuka." ƙyalƙyacewa suka yi da dariya, su kadai a tsakar dare ko tsoro basa ji.
"Ya zamu yi? Haris ne ya tambaya.
"Wallahi idan suka ganmu ba zasu bari mu fita ba," Naufal ne ya faɗa..
"Ku yi shiru, a hankali zamu bi ta ɗayan benan, kada ku yi wani motsi da zaisa su lura da mu!"
Sajeed ne ya faɗa cikin raɗa..
Cikin sanɗa suka fara hawa stairs din, suna tafiya suna waiwayon su Parveen...
Sai da ya rage saura Mubeen dake a bayansu yana gab da zai haura second floor tari ya kubce mashi.
Aikuwa a rikice Parveen da Jemimah suka zabura tare da mikewa tsaye gaba ɗaya suka saki abun da ke hannunsu ya 6are ƙasa, kafin su kai idanunsu tuni Haris ya ja wuyan rigar Mubeen sun karya kwana.
Kallon juna Jemimah da Parveen suka yi idanunsu azazzare..
"Jemimah kinji sautin tari?"
Jinjina mata kai ta yi, "ƙwara mu koma ɗaki, ni tsoro ya kama ni, dama Aunty Danejo ta ta6a bamu labarin fatalwar dare dake zuwa ma mutun in bai yi bacci ba ta cinye kurwarshi..."
A tsorace ta faɗa tana zare green eyes din ta.
"Dallah ƙarya take maki, babu wani fatalwa, tatsuniya ba gaskiya bace ƙirƙirarran labari ne.."
bata ƙare maganar ba idanunta suka sauka akan warin takalmin dake akan ɗayan stairs din gefen su.
Cikin sauri ta nufi takalmin, Jamimah na gani ta gargaɗe ta akan kada ta ɗauka na ɗan aljani ne, ta yi banza da ita.
Daukar takalmin tayi ta jujjuya shi nan take ta gane warin slippers din yan uwansu maza ne.
"Wani ya wuce ta wurin nan, Jemimah ki jira ni, bari na je na leƙa."
Ruƙe rigarta Jemimah ta yi"Ai wallahi ƙafata kafarki, Yo kawai ki barni fatalwa ta cinye kurwata."
Dungurin goshinta Parveen ta yi, "Shashasha, mu je." Upstars suka hau, duk inda Parveen tayi Jemimah tana a biye da bayanta kamar bindi, har suka 6ullo ta hanyar da su Sajeed suka bi, suna ƙarasowa suka hango ƙatuwar glass window dake a buɗe, ta cikinta suka dira ta baya akan wani floor, anan suka hango igiyar da suka ƙulla jikin ƙarfen da ke a kewaye da gurin da tagar take.
"Hakan na nufin su Sajeed sun fita!" Ta fada tana dan jinjina kanta, murmushin gefen fuska ta saki..
Ta soma kiciniyar kama igiyar don ta dira, ruƙo ƙafar wandonta Jemimah ta yi a tsorace ta ce, "Dan Allah kada ki tafi ki barni, bazan iya hawa ba."
Harara Parveen ta watsa mata, "Ya zan yi dake? Karki kuskura ma ki ce zaki hau, faɗowa zaki yi kanki ya fashe ki mutu.."
Kuka ta saka mata, bata saurareta ba ta buge hannunta, ta ruƙe igiyar ta bi jikinta, ko leƙenta Jemimah bata iya yi saboda gajartarta.
Watsawa ta yi da gudu ta koma cikin gidan ta nufi dakin sauran yan uwan nasu.
A lokacin suna a kwance kan mattress dinsu kusan su shida sun kudundune cikin duvet ɗinsu.
Abun ka ga mai ƙarancin hankali tana shiga ta daka suka ta dira a samansu, aikuwa a firgice suka farka tare da yaye bargon, suna ganinta suka fasa ƙara saboda razanar da suka yi.
Ganin yadda suka ruɗe ne yasa ta yi saurin cewa, "Ni ne fa Jemimah.." Ta faɗa tana goge garin madarar dake akan fuskarta, lokaci ɗaya suka sauke ajiyar zuciya.
"Uban me ya kawo ki dakinmu?"
"Kawai muna baccinmu kin wani zo kin tada mu! Me ma ya farkar dake a irin wannan lokacin.."
Idanunta cike tab da ƙwalla ta ce, "Pravin ta fita, nayi nayi da ita ta tafi da ni ta ƙi."
waro idanu waje suka yi cike da mamaki jin abun da ta ce, "Ina ta je?"
"Ku zo in nuna maku, har takalmin su Mubeen muka tsinta suma sun fita, na je ɗakinsu ban gansu ba."
Da shagwa6a ta ƙare maganar,..
Kusan a tare suka sauko daga kan katifar, in ka cire mutun ɗaya da bata farka ba, saboda nauyin bacci ne da ita sai sharar baccinta ta ke yi.
Gaba Jemima ta yi suka bi bayanta, bayan da suka ƙarasa gaba ɗaya sun yi mamakin ganin igiyar da aka ɗaura.
"Abun da za'ai, tun da mun samu hanyar fita, mu bi su kawai." A cewar Sarah.
"Ɗaya bayan ɗaya zamu hau."
"Ni fa wa zai goya ni?"
Wani kallon rainin wayou su ka yi mata, "Ki koma ki kwanta, ba za ki iya hawa ba, zaki iya faɗuwa ki mutu." Fashewa ta yi da kuka, "Wlh saina tona maku asiri gurin aunty Danejo, tun da ba zaku hau da ni ba."
Da jin hakan suka fara lallashinta, Hawwa ta ce, "Abun da za'ai yanzu, Jemimah ki je ki kira Azeeza da Deeja, su zo mu tafi, kada mu barsu Su kadai," Amsawa tayi da toh, sai bayan da ta tafi Sarah ta ce, "Meyasa zaki aike ta ta kira su?"
"Saboda mu samu mu tafi, in ba haka ba ba zata ƙyale mu ba."
Hannah ta ce,"Deeja bata da hankali, akwai matsala idan Jemimah ta gaya mata, Azeeza kuma bazata iya fitowa ba saboda tsoro."
Hibba ta ce, "Yanzu ya zamu yi? Ga samu ga rashi, don wlh idan muka tafi risky ne su zo gurin nan," ta faɗa da damuwa..
Hanna ta ce, "Idan kuma muka dira muka je can, baku tunanin zamu ja ma kanmu wata matsalar?"
"Yanzu me kuke nufi mu hakura mu koma?" Yasmin ce ta fada tana dubansu..
Rubina ta ce, "Kun manta nauyin baccin Deeja? Wlh ba zata farka ba ko Jemimah zata watsa mata ruwa ne a jikinta, ita kuma Azeeza tsoro gareta, ba zata iya hawa igiya ba, dole su haƙura da bin mu..."
da jin wannan maganar ta Rubina nan fa suka samu kwarin gwiwar aiwatar da abun da ke ransu.
Sarah ce ta fara hawan igiyar saida ta dira ƙasa, sannan Hawwa ta haura itama..
Ɗaya bayan daya suka dira gaba daya.
Baiwar Allah Jemimah sun mata wayou, a gajiye ta koma dakin su ta je ta taso Deeja, ta dinga bubbuga kafadarta, cikin magagin bacci Deeja ta dinga zaginta, da ta saka naci aikuwa ta sanya ƙafa ta ingizata, gaba daya ta kundumo ƙasa daga kan katifar, cikin shesshekar kuka ta ce, "Allah Ya isa banza, don kin samu na zo tada ki, kuma wlh tafiya zamu yi mu barki, kuma saina rama." Ta faɗa tare da mikewa ta hau kan gadon, ta saita cinyar Deeja ta gartsa mata cizon da ya yi silar farkawarta ta fasa ƙara, kafin ta dawo hayyacin ta, Jemimah ta watsa a guje ta nufi ɗakin Danejo dake a upstairs, ta buɗe ƙofa ta shiga cike da zullumin kar Deeja ta biyo bayan ta.
Cikin sanɗa take tafiya, ɗan hasken bedside lamps ne kadai ya haskaka dakin.
Hawa ta yi kan gadon ta rarrafa ta nufi Azeeza dake a kwance gefen Danejo, saitin kunnanta takai bakinta, "Azeeza! Azeeza! Ki tashi ki ji wani abu." Takura mata ta yi da ƙyar ta farka, toshe mata baki Jemimah ta yi da tafinta, abun ka da matsoraciya ta zazzare eyes dinta kwata kwata bata iya ganin wanene ya toshe mata bakinta, saboda ƙarancin hasken ɗakin duk da ta samu lafiyar idanunta amma har yanzu in haske bai wadatu ba bata iya gani da kyau, sa6anin da ko da akwai haske sosai in dai dare ne bata gani.
"Ni ce fa, Jemimah, ki taso mu tafi, su Parveen sun samu wata kofa a baya sun fuce daga gidan nan..." Ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Jemimah dake mata raɗa.
Buge hannunta ta yi, "Ba inda zan je, ki kyale ni in ci gaba da yin baccina pls,"
"Dan Allah ki taso mu tafi, suna jiranmu, su suka ce in kira ki mu tafi." Da jin wannan maganar yasa ta miƙe, ruƙo hannunta Jemimah ta yi, ko mayafi babu akanta sai zallar sumar kanta da ta rufe bayanta.
da taimakon Jemimah take iya ganin hanya, cikin sanɗa suka fuce daga ɗakin.
~________________________________🌹💋~
A bangaren su Owais, bayan da suka fito daga motocin su suka nufi main falo, fuskokin su ɗauke da murmushi.
Officers suna ganin Unaisah da Batool suka fara sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah da ya dawo da su lafiya..
Chief yana jiyo muryar wani officer yana fadin, "Allah ya ku6utar da mu da ya dawo masa da hurul aininsa, don wlh ba raga mana zai yi ba, yadda yake ji da yaran nan kamar ransa akan su har kurkuku zai iya sawa a kulle mu."
Murmushi Chief Owais ya yi tare da ɗan girgiza kan shi.
Ummi da Shureim ne a gaba sun saka Batool a tsakiyarsu, yadda kasan wadanda suka ɗauko kwai a cokali sai tattalinta suke, ko tari ta yi sai sun tambayi is she okay.
Haka Unaisah ma tana a tsakiyar Taj da Benazir, sun saka ta tsakiya, hannayensu tallabe da bayanta, Anila tana a gefen su.
Sheikh Imam da Chief Owais suna a biye da bayan su.
A hankali Ƙofar falon ta zuge, suna shiga Unexpected suka yi arba da Chefs kewaye da ƙofar, a tare suka hada baki gurin furta, "Muna yi maku barka da dawowa gida lafiya, Unaisah and Batool, mun yi murnar ganinku gaba ɗaya, shiyasa ma muka shirya maku dinner, Please ku biyo mu mu je..." Kallon juna suka yi bakin su a buɗe da mamaki akan fuskokin su.
Basu yi ƙasa a gwiwa ba, suka bi bayan Chefs din, kaitsaye suka nufi garden din gidan.
Suna shiga suka fara yin arba da sparkling light din dake haskaka arean gurin, shimfiɗa aka yi masu ta alfarma, wata hadaddiyar carpet mai faɗi da laushi, daga saman ta kayan dinner ne..
Gaba daya farin Ciki ya hana su furta kalma, sai dai suka dinga bin Chief da kallo saboda sun san shine ya shirya komai don ya faranta masu.
"Chefs sun faɗa min tun safe baku ci komai ba, shiyasa na umarce su da su shirya maku dinner, tun da yanzu mun samu kwanciyar hankali, nasan akwai yunwa a tare da ku, Pls ku zauna ku ci..."
sun nuna farin cikinsu sun kuma yi mashi godiya, a zagaye da dinner din suka zazzauna.
Kowan nan su ya fara ɗaukar abunda ya ke son ci, a baki Ummi da Shureim suke ba Batool ta na ci, itama saita ɗebo ta sanya ma kowannansu a baki, sheikh Imam dake kallonsu ya rasa ina zaisa ranshi don farin ciki, Benazir ma a baki ta dinga ba Unaisah tana ci.
"Sir, kai ba zaka ci bane?" Aneelerh ce ta tambaya tana duban Owais da ya yi tsaye yana ɗan daddana wayarsa.
Da fara'a akan fuskarsa ya dago ya dubeta, kafin ya bata amsa wayarsa ta yi ringing, ganin kiran daga CSH ne yasa shi saurin ɗagawa yasan kira ne me muhimman ci.
Ji suka yi ya furta, "Alhamdulillah, Alhamdulillah! Meyasa tun da suka farfaɗo baku kira kun sanar da ni bane?"
"Okay, pls karku barshi ya taho, ku ruƙe min shi, nasan shi da kafiyar tsiya.." Ya fada yana dariya.
Bayan ya yi rejecting call din ya dube su, "Kira ne daga Combat Support Hospital, Omar da Salsalbeel sun farfado daga coma, sun samu lafiya tun jiya da daddare..
Hada baki suka yi gurin furta Alhamdulillah..
Juyawa ya yi da sauri ya nufi hanyar komawa parking space, yana 6ullowa ta gaba ya hango Security Officers sunyi gungu guda suna magana baisan me suke tattaunawa ba.
Nufar su yayi da ɗan saurin shi, suna ganin shi suka dare, a rude yake kallon yaran da yake ta ajiya a part ɗin Taj, daga kallon da yake yi masu yasa duk suka sha jinin jikin su.
"Tayaya akai kuka buɗe kofar kuka fito?" Tambayar da ya fara jefa masu kenan,
Da sauri suka nuna Sajeed da yatsan su, "Wallahi babu ruwanmu, Sajeed ne ya ƙulla mana igiya ta baya, da ita muka kama muka sauko ƙasa"
Abun da ya faru bayan da mazan suka gudo, suna ƙarasowa gaban kofar shiga falon Chief security Officers suka ritsa da su, suka fara tambayarsu daga ina suke? Waya buɗe masu kofa suka fito.
Suka yi shiru basu amsa masu ba, kwatsam suka jiyo takun tafiya suna juyawa suka hango ƴan matan dake 6ullowa ta bayan sashen Taj ɗayan bayan ɗaya, hankalin Officers din ya ɗan tashi a rude suke kallon su har suka ƙaraso, mazan na ganinsu suka ɗaura hannayensu a saman kansu alamar sun shiga uku, saboda rashin gaskiya sai suka rufe matan da faɗa akan don me za su biyo su.
Aikuwa Parveen ta tona masu asirin ta yadda suka samu hanyar fitowa daga part din Taj, ran officers din ya 6aci suka rufe su da faɗa kamar za su buge su, duk sun tsoratar da su.
Suna tsaka da korawa chief bayanin abun da ke faruwa suka jiyo ihu daga can nesa da su.
Gaban kowan nan su ne ya fadi, a ruɗe Sarah ta ce, "Mun shiga Uku, Azeeza ce, wallahi ita ce, Kuma bata gani sosai idan dare ya yi, kada ta faɗo ta ji rauni..."
bata ƙarashe maganar ba, da gudu suka dunguma izuwa bayan sashen, tunkan su isa suka hango Azeeza da ta maƙale a igiya jikinta nata kerma.
Ga Jemimah ta biyo bayanta, ba dan Allah Ya sa sun ji ihun su sun zo ba da tuni sun salwanta saboda igiyar tana gab da kwancewa.
Cikin zafin nama Chief Owais ya taimaka masu suka ƙarasa saukowa.
Ransa a matukar bace ya rufe su da fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, abun da ya 6ata masa rai, igiyar da suka ƙulla yanzu da ta kwance sa'ilin da suke hawa ko ta subuce ma wanin su har rai zasu iya rasawa.
Kuka suka kama yi mashi suna bashi hakuri, bai sauraresu ba, ya damƙi damtsen hannun Sajeed ya wurga ma Officers shi ya ce "Ku sanya min shi a boot din mota dina, ba abun da zai hana in hukunta ka, saboda ka yi yunkuri aikata kisan kai.."
gaban Sajeed ne ya fadi rass! A tsorace ya dinga masa magiya yana fadin ya tuba bazai ƙara ba, ƴan uwansa ma suka dinga kuka suna rokon Chief ya yafe masa kada ya hukunta shi.
Bai saurare su ba, akan idon su Officers suka ciccibi Sajeed dake ta turjewa, su kansu sun yi mamakin ƙarfin shi, da kyar suka ɗaga shi sama suka nufi parking space, ƴan uwanshi suka bisu a guje, kafin ma su karaso tuni Officers sun jefa shi cikin boot din motar Chief suka kulle shi.
Bayin Allah ba yadda suka iya, dole suka haƙura, basu ta6a ganin fushin Chief irin na yau ba.
Ko da suka matsa mashi akan ya yi hakuri ya yafe ma Sajeed, nuna su ya yi da yatsa ya ce duk wanda ya kuskura ya ƙara ko da tari ne sai ya sanya shi a boot an tafi da shi, da jin hakan nan fa kowan nan su ya shiga taitayin shi.
Kafin tafiyar shi saida ya mayar da su part din Taj ya kuma kulle su.
A saman floor suka zazzauna suna ta kuka, sautin koke koken da suke yi ne ya farkar da Danejo da Deeja, kusan a tare suka fito daga dakunansu suka nufo su.
Hankalin Danejo ya tashi da ganin halin da suke a ciki, da damuwa akan fuskarta ta tambaye su meya faru? Meyasa suke kuka?
Dakyar ta samu suka labarta mata abun da ya faru.
Ta ce Allah shi ƙara in ma da ƙari ya kara, Chief ya yi daidai da ya tafi da Sajeed saboda baya jin magana, dama ta na lura da take takensa na son guduwa daga part din.
Cikin shesshekar kuka su ka ce in bazata lallashe su ba, ta yi shiru ta barsu da abun da ke damunsu.
Tana murmushi ta ce ai basu ga komai ba, su jira Chief ya gama hukunta Sajeed zai dawo kansu ne, saboda suma sun bada gudummuwa gurin aikata laifin.
wani sabon kukan suka fashe da shi jin abun da ta ce.
Deeja da ke sauraron su kuwa bushewa ta yi da dariya hada dafe cikin ta, tana fadin, "Allah ya ƙara maku, masu kunnan ƙashi, maganinku kenan. Ni dai Allah ya so babu ruwana, bansan anyi ba."
Ta ƙarashe maganar tana yi masu gwalo, haushin ta duk ya cika su kamar su rufe ta da bugu.
Daga bisani Danejo ta soma lallashin su ta ce su yi hakuri ita wasa ta ke yi masu tasan shima Sajeed din ba lallai ya hukunta shi ba.
~________________________________💫~
CSH (Combat Support Hospital)
Katafaren Military Hospital ne masu jinyar majinyatan sojojin da suka samu rauni a gurin yaƙi, asibitin ba a cikin garin Abuja ya ke ba, a kusa da sansanin su yake.
Yana da matuƙar tsaro, cikin shi da wajen shi soldiers ne ke tsaron shi, ga na'urorin dake sanya ido ga duk wani mai motsi ciki da wajen asibitin.
Lokacin da Motar Chief Owais ta ƙaraso cikin asibitin, drivern dake driving nasa yana yin parking sojoji suka bude mashi motar ya fito, a hanzarce suka buga ƙafa tare da sarah ma shi.
Zagayawa ya yi ta bayan motar ya buɗe boot dinta, lokacin da ya ɗaura idanunsa akan Sajeed da ya duƙunƙune a ciki kamar musaki saida ya ji tausayin shi ya kama shi, ganin yadda idanunsa suka yi jawur saboda kukan da ya sha.
Ruƙo hannunsa ya yi tare da taimaka mashi ya fito daga motar, koda ya ga sojoji ta ko'ina suna sintiri ruke da bindigu a hannunsu sai ya kuma fashewa da wani kukan yana roƙon chief ya yafe masa kada ya hukunta shi bazai ƙara ba, ya taimaka ya maida sa gurin ƴan uwansa.
Wani baƙin soja mummuna mara fara'a dake tsaye a gaban su ya ce, "Sir wannan ɗan shilan fa? Karairaya maka shi kake so mu yi ko tsallan kwadi zamu sanya shi?" Da jin wannan maganar, yasa jikin Sajeed ya kama kerma kamar mazari, a tsorace ya la6e bayan Chief Owais ya rurruƙesa yana roƙonsa, dariya sosai sojojin suka yi.
Da yasan yadda Chief ke ƙaunarsu da bai ɗaga hankalinsa ba, ko sauro baison ya ta6a lafiyarsu balle shi ya hukunta su da hannun shi never.
Ruko hannunsa ya yi suka nufi cikin asibitin yana ta zare idanunsa cike da zullumin Ina Chief Owais zai kai shi.
Duk inda suka gifta military doctors din dake zarya tare da nurses with respect suke sara mashi tare da gaishe da su..
Sajeed dake ta ƴan kalle kalle idanunsa suka dinga hango masa patient din dake a ɗakunan da aka kwantar da su, ta glass din jikin ƙofofin yake hangosu, wasu ma sai yawon su suke yi a ciki, ƴan matasan mata da samari irin shi.
A gaban wani medical room suka tsaya da tafiya, wani doc ne ya fito da fara'arsa ya sara ma chief shima ya sara masa bayan sun gaisa.
D.r din har ya buɗe baki zai yi magana ya katse shi tare da kashe mashi ido ɗaya sannan ya nuna masa Sajeed.
"Me laifi ne! Baya jin magana, ina so ka shiga da shi cikin dakin, ku cire masa kunnansa daya, sannan ku yanke harshen sa.."
Sajeed ya fasa ƙara yana fadin, "Nashiga uku, wayyo Inna lillahi! Yaya Owais na tuba bazan kara ba, na roƙe ka dan Allah ka yi hakuri, ka yafe min, wlh mutuwa zan yi idan suka cire min harshe na.."
a gigice ya zu6e kan gwiwowinsa ya rurruke kafafun Owais, ya dinga rokonsa yana kuka..
Murtuke fuska Owais ya yi, "Ku yi abun da na ce! Kar ku saurare shi." Rushewa ya yi da wani kukan,
Docs din suka ce, "An gama sir,"
Da ya ga dagaske suke, jikinsa na bari ya mike tare da watsawa da gudu, sai dai kafin ya fuce, sojojin dake sintiri suka cafkoshi suka dawo da shi gaban Chief Owais, Docs din suka rurruke shi yana turjewa tare da waiwayen Owais da ya kawar da kansa gefe, docs din suka tura shi cikin dakin..
"Ku sake ni, ku kyale ni in tafi, wallahi kada ku ta6a ni.." Bai ƙarasa maganar ba, sakamakon abun da idanunsa suka nuna mashi wanda yake ganin kamar ba gaskiya ba ne..
Tana a kwance kan medical bed sanye da patient gown, sai sharar baccinta take yi, daga kan table din gefenta kayan marmarine a cikin plate data fara sha ta rage sauran.
Murza idanunsa ya yi da hannayensa don ya ga ko gizau take yi mashi amma still ita ya gani.
Gaba ɗaya ya ruɗe ya rasa gasgata abun da yake gani.
"Kamar twin sister dina? Ni kaɗai nake ganinta! Ko mafarki ne..?" Fusge kanshi ya yi daga hannun docs din a rude ya nufi gadon ya ɗan zauna daga gefe ya ƙura idanunshi akan fuskarta.
Jini ɗaya ba wasa ba, ko a mafarki ya ganta zai shaidata, duk min canzawar da za ta yi, saboda warinsa ce.
A hankali ya ɗaura yatsunsa dake kerma saman fuskarta, ya ɗan shafa ta har izuwa kan curly hair ɗinta, komai nasu iri ɗaya, jinsi ne kaɗai ya bambanta su.
Muryarsa na rawa ya furta, " GAB.. riella! Da gaske ke ce? Ke nake gani? Ba mafarki nake ba.?"
Sambatunsa ne suka katse mata baccinta, a hankali ta buɗe idanunta, tana ɗaura su kanshi ta zabura ta miƙe zaune, wani irin tsantsar farin ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu.
"My twin Bro! Kai ne da gaske nake gani a gabana? Ashe da rabon zamu gana da juna, na yi zaton bazan ƙara ganinka a rayuwana ba.."
wata irin ruguma suka yi wa junansu kamar zasu koma mutun daya, a lokaci ɗaya suka fashe da kukan farin ciki.
"Kasan irin uƙubar dana sha? Baka ta6a nemana ba, Ka manta da ni! Ba ka damu ina a raye kona mutu ba, ni kadai nake hauka na akan ka, ganin ka da na yi ya tabbatar min da ka riga ni barin kurkukun ƙaddara.."
cikin kunci ta furta tana kallon shi.
Duk sai ya ji ba dadi, cikin karyayyar murya ya ce, "Ba haka bane, kina a raina, na damu da ke, kamar yadda kike nema na nima haka nake neman ki, ki yi hakuri nasan ban kyauta maki ba, ba yadda zan yi ne..."
Bai ƙare maganar ba ta daka mashi tsawa, "Ƙarya kake yi Gabriel, na tsani kaina dana damu da kai. Dama na sani na kashe kaina tuntuni, kalli yadda ka sauya kana cikin kwanciyar hankali, ni ina a can cikin azabar rayuwa, ban taba mantawa da kai ba, in ni ce wallahi bazan iya barin ka ba, koda zan rasa raina ne .."
Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda bakin cikin da ta ji, jikinshi duk ya yi sanyi zuciyarshi ta karaya, yasan sister din nashi da zuciya, sai anyi da gaske zata sauko daga kan dokin zuciya..
"Dan Allah ki daina kuka zanyi maki bayani.." Bai ƙare maganar ba ta rufe shi da bugu kamar ta samu jaki, ta dunkule hannu ta shiga kai mashi naushi.
saboda yasan bai kyauta mata ba yasa shi kasa dakatar da ita.
Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da Docs din dake a ɗakin, tsantsar tausayin su ne ya kama su.
"Gabriellah, ki daina bugunsa, i will explain to you.. "
Owais ne ya faɗa, cikin shesshekar kuka ta ce, "Ka barni in ci ubansa, baisona banza shasha, wa nake da shi in bashi ba? Ni fa ƙanwarsa ce, twin sister ɗinsa, ciki ɗaya muka fito, don me zai barni cikin wahala ya tafi? Kunsan irin cin zarafin da aka yi min? Wannan mahaukaciyar karyar ta sa giant ya yi raping ɗina, ni kaɗai nasan azabar dana sha, mutuwa kadai ne ban yi ba..."
gaba ɗaya ta labarta musu abun da ya faru da ita, Gabriel ya yi kukan bakin ciki kamar ransa zai fita.
Docs din dake a dakin duk saida idanunsu suka ciko da ƙwalla saboda tausayinta.
Chief Owais ya karaya da jin abun da ya faru da ita.
Haɗuwa suka yi su duka suka dinga lallashinta har saida suka samu ta tsagaita da kuka.
Chief Owais ya ce ta yi hakuri, sun san an cutar da rayuwarta amma ta sani Gabriel bada son ranshi ya tafi ya barta ba, bashi da mafita ne saboda ba a guri ɗaya suke ba, bayan haka sune silar da har suka san labarin kurkukun ƙaddara, da labarin ita kanta, saboda Sajeed shine ya dinga yi masa maganar ƴar uwarsa dake a kurkukun kaddara akan ya taimaka ya ɗaukko ma shi ita, bayan haka mahaukaciyar karyar da take magana akanta ta riga da ta mutu tun ranar da suka kai farmaki!
Maganganun Chief Owais sun yi tasiri a cikin zuciyarta, jikinta ya yi sanyi har ta nemi yafiyar Gabriel akan faɗan da ta yi masa ya ce mata kada ta damu komai ta yi shi baiga laifinta ba, shi yakamata ya nemi yafiyarta, ta ce ta yafe masa amma kar ya ƙara tafiya ya barta, ya yi murmushi ya ce bazai ƙara maimaita wannan kuskuran ba, hugging din juna suka ƙara yi cike da farinciki.
Daga bisani Sajeed ya dubi Chief Owais da hawaye akan fuskarsa ya ce shi baisan tayaya zai gode masa ba, yau ya shammace shi, ya yi mashi surprise din da bai ta6a zato ba, da farko ya yi zaton hukunta shi zai yi, ashe yar uwarsa zai nuna masa, ya ce, " Chief kai wani irin mutunne mai kyakkyawar zuciya? Na yi imanin zuciyarka ta daban ce, samun irin ka zai yi wuya a duniyar nan. Ka kyautata mana a rayuwa, ka yi mana abun da baza mu ta6a mantawa da kai ba, Allah ne kadai zai iya biyan ka..."
Yayin da Sajeed ke furta masa kalmomin nan murmushi ne dauke akan fuskarsa.
Itama Gabriella ta yi masa godiya, ya ce su godewa Allah, saboda shine ya kaddara zai zama silar taimakon su.
Da sauri Sajeed ya sauko daga kan gadon ya yi sujjada don godiya ga Allah, da ya ga shiru Gabreilla bata sauko ta yi ba, ya miƙe ya ruko hannunta ya ce ta zo suyi sujjada su gode ma Allah, a rude ta ce, "Bansan me kake nufi ba, bazan yi sujjada ba, ni ba musulma bane, ko ka manta?".
"Har kina da za6in addini a yanzu? baki ga wadanda suka taimake mu musulmai bane! Nima yanzu musulmi ne, Ki daina kira na Gabriel, bana so sunana Sajeed, kema na musuluntar dake, sunanki Sajeeda daga yanzu."
maganar shi taba su nishadi.
A nan take ya biya mata shahada ta musulunta ya kuma raɗa mata suna SAJEEDA, dama tuntuni ya ke ta tanadin sunan da zai sanya mata kalar na shi idan Allah ya haɗa su, bayan da ya samu sai ya adana sa a cikin zuciyarsa.
Chief ya ce su jira shi zai shiga cikin asibitin gurin su Omar, suka amsa mashi da toh.
Bayan fitarsu daga dakin ya rage saura su biyu.
Sai dadi suke ji kamar yau suka fara sanin juna.
Ta tambayeshi ya bata labarin ta yadda suka ku6uta daga kurkukun ƙaddara kuma a ina yake da zama?
Bayan da ya labarta mata, ta ji dadi sosai har ta ƙosa ta ga sauran prisoners ɗin da yake a tare da su, sai ta ji dama tun farkon kai su kurkukun ba a raba masu ɗaki ba, saboda ta ji sun fi su samun gata ba kamar su ba da aka maida dabbobi.
"Ina son nasan meya faru da khala, itama ta ku6uta ko bata ku6uta ba, na ga babu ita cikin wadanda sojoji suka ceto, ina son ta, itama tana sona, ba don ita ba da yanzu babu ni..."
Ta fada idanunta cike da ƙwalla.
"Ban so wani abu ya sameta, ina so ta rayu saboda in taimaka mata, ta faɗamin bata da kowa, itama cutar ta aka yi aka kaita kurkukun ƙaddara."
Tambayar ta Sajeed ya yi wacece Khala? Nan take ta labarta masa irin taimakon da ta yi mata, duk da baisan wacece ita ba ya ji ta kwanta masa a rai, kuma yana son ya ganta saboda taimakon da ta yi ma yar uwarsa. Kwantar mata da hankali ya yi ya ce zai tambayi Chief game da ita don su ji in tana a raye.
Bayan fitar Chief Owais daga ɗakin bai nufi ko'ina ba sai ɗakin da aka kwantar da amininsa, shigar sa dakin ya yi daidai da fitowar Omar daga toilet, yana tafiya daƙyar daƙyar, jikinsa sanye da kayan mara lafiya, kwata kwata bai lura da mutun a ɗakinsa ba, gadon sa ya nufa yana niyyar haurawa don ya kwanta unexpected muryar Owais ta katse shi, "Alhamdulillah, Ya Allah na gode maka da ka farfaɗomin da aminina! Na gode Ya Allah..." Cike da farin ciki Big Guy ya waiwayo tare da kallonsa.
Bazai iya jira ya ƙaraso ba, da sauri ya nufesa suka rungume juna, irin sosai ɗin nan.
"Na yi kewarka Omar, kullum da tunaninka nake kwana, ina ta zullumin kada na rasa aminina, bansan ina zan samu madadinka ba." Cikin shesshekar murya ya furta kamar zai fashe da kuka.
Daɗi da farin ciki suka lullu6e Omar, in a cool voice ya ce, "Nima na yi kewarka bugun zuciyana, na so a ce kaine mutun na farko da idanuna suka fara yin tozali da shi a lokacin da na farfado amma sai na ga akasin hakan, baka ji yadda na ji ba, bansan meya faru ba tun bayan dana fita hayyacina a gidan kurkukun kaddara, amma da docs suka faɗa mini kana nan da ranka da lafiyarka sai na ji farin ciki ya cika ni, saboda ni damuwana akanka ne, ina son ka aminina." Ya faɗa yana ƙara hugging dinsa, daga gani sun yi kewar juna sosai, farin ciki duk ya cika su.
"Omar, ina fata babu inda ke yi maka ciwo a yanzu? Ka ci abinci? Ka yi wanka?" Dariya ya yi, "Ka kwantar da hankalinka, doctor ya tabbatar min da na samu lafiya, raunin da na ji a brain ɗina ya warke.." Leƙa kansa Chief ya yi ya dudduba daidai inda aka yi masa ɗinki, ya ji daɗin ganin yadda gurin ya warke sosai.
"Allah ya ƙara maka lafiya da tsawancin kwana aminina.." Da fara'arsa ya amsa masa da, "Ameen, kaima haka mutumina."
"Am sorry Omar, na yi maka laifi, kwana biyu ban leƙo na duba ka ba, bani da kwanciyar hankali, abubuwa da dama sun faru masu daɗi da marasa daɗi..."
Damuwa ce ta bayyana akan fuskar Big Guy, "Don Allah ka faɗa min meya faru? Me ake ciki? Dame dame ya faru bayan doguwar sumar da na yi? Ina Danish? Ina Salsabeel da Taj? Ina U.s armies? Ya labarin kurkukun kaddara da Elders da su na farka a raina? Har yanzu baku gano su wanene ba?"
Kamar ɗan jarida ya tsare shi da tambayoyi.
Girgiza kai Chief ya yi cike da takaici ya ce, "Omar, zan fada maka amma ba yanzu ba, na fi so lafiyarka ta inganta, bana so kaji abun da zai ɗaga maka hankali..."
Bai kare maganar ba, Omar ya ce, "Kada ka damu da lafiyata na ji sauƙi, kawai ka fada min! In ba haka ba hankalina ba zai ta6a kwanciya ba wallahi.." Matsa mashi ya yi akan ya fada mashi saboda ya kagara da ya ji me ya faru..
Ba don ya so ba, cikin karyayyar murya ya fara zayyana masa abubuwan da suka faru,
wa'iyazubullah! Lokaci ɗaya idanun Big Guy suka rikiɗa suka koma jajir, zufa ta fara tsattsafo masa saman fuskarsa, tsantsar tashin hankali da ruɗani ne akan fuskarsa, al'ajabi ya kama sa, damuwa da baƙin ciki suka mamaye zuciyarsa duk a lokaci ɗaya..
Cikin shesshekar murya ya furta, "Owais, jin komai nake kamar ba a gaske ba, kamar a mafarki ya faru, ina ma ace ban farfaɗo daga coma din nan ba, in mutu kawai!" Ya faɗa hawaye masu ɗumi suna sauka kan kuncinsa..
Wani irin kunci da baƙin ciki ne suka tarar masa a cikin zuciyarshi, idanunsa sun kaɗa jajir..
"Ban yi mamakin jin mahaifina ne Jan Wuya ba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya, amma wallahi, rantsuwar ɗan musulmi tun da labarin kurkukun kaddara ya riske mu na ji a raina mahaifina yana ɗaya daga cikin azzaluman da suke da sa hannu a cikin sa, na yi shiru ne saboda bani da hujjar da zan tabbatar da zargina akan shi shiyasa ban ta6a faɗa maka ba. Amma zuciyata ta karaya da jin cewa baba Obie shine Shugaban kurkukun ƙaddara! Hankalina ya tashi Owais, ban ta6a jin tsanar rayuwar duniya irin na yau ba. Owais meke damun su ne? Wani irin neman duniya ne wannan? Da zalunci da mugunta? Me suke nema ne wai? Wani irin tushewar basira ne haka? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!.."
"Baba Obie bai kyauta ma rayuwarsa ba bai kuma kyauta maku ba, wallahi nafi jin zafin halin da kuka shiga akan wanda ni na shiga, saboda baba Ya zalunce ku, Ya dade Yana ha'intarku da fuska biyu, Owais, wai dan Allah da gaske ne? Ba mafarki ba? Wannan wata irin baƙar kaddara ce Allah ya jarabce mu da ita?"
Ɗaura kansa ya yi akan kafadar Chief Owais ya fashe da kuka tamkar ana zare ransa.
Cikin sanyin murya Owais ya ce,"Shiyasa ban so ka matsa min akan in fada maka ba Omar! Saboda nasan ba zaka ji dadi ba.."
"Allah Ya isa tsakanina da shi, Allah ya wulaƙanta rayuwarsa tun a gidan duniya, Allah ya haɗa shi da dukkan musiba da fitintunun duniya, Allah ya saukar masa da cututtukan da zasu hana sa kwanciyar hankali, ko na minti ɗaya ban son ya ƙara jin dadin duniya. Lalacewar sa kawai nake son na gani, ban ta6a tsanar wani mutun kamar yadda na tsani mahaifina ba, shaiɗanin mutun azzalumi, fasiƙi mai kafurar zuciya, mutumin da tun da ƙuruciyata yake nema na, ni wai! Ɗansa na cikinsa! Shine Ya 6ata min rayuwata ya jefa ni a harkar safarar miyagun ƙwayoyinsa, ya hana rayuwata sukuni, ya ƙi bari mahaifiyata ta bani tarbiya, ya raba ni da danginsa, ya dinga sarrafa ni son ranshi. Owais ina da ciwon baƙin cikin da ya ƙunsa min, wallahi Owais ba don Allah ya ƙaddara zuwan ka cikin rayuwata ba, da yanzu nima ina ɗaya daga cikin giant din kurkukun kaddara, Allah ne ya tsare ni, wataƙil addu'ar mahaifiyata ce ke bibiyar rayuwa na, shiyasa bai yi nasara akaina ba..." Kasa ƙarasa maganar ya yi wani kalulun baƙin ciki mai tattare da radadi ya sarƙe muryarsa, ya kuma fashewa da kuka yana tari.
Cikin sigar lallashi Owais ya daura tafukansa a saman bayansa a hankali yake dan bubbuga sa yana lallashinsa.
"Omar, ka yi hakuri, ka yi hakuri, kuka bashi bane mafita ba, muma mun shiga mawuyacin hali, wanda na yi imanin dukkanmu in aka bincika lafiyarmu babu wanda za a samu batare da ciwon zuciya ko hawan jini ba, saboda depression din da ya kama mu, amma ba yadda muka iya, dole muka yi hakuri saboda bamu isa mu sauya abin da Allah ya kaddara faruwarsa a cikin rayuwar mu ba, bawa bai isa ya gujewa kaddararsa ba, iya cuta dai an cuce mu, an yi mana bakin ta6o, amma ba komai akwai Allah, su ke tunanin sun zalunce mu, wallahi bamu suka zalunta ba, kan su suka zalunta, sun kashe rayuwarsu da kansu, sun yi asarar duniyarsu da lahirarsu!"
"Na fi jin tausayin ku Owais, ni bana jina a matsayin kowa, na rayu batare da dangina ba, bakowa ya sanni ba ko a family ɗinmu, ku kuwa duniya ce ta san ku, ina jiye mana halin da zamu shiga idan asiri ya fallasu mutane suka sani, bana so ahalinmu su muzanta a idon duniya, bana son laifin da bamu muka aikata ba ya shafe mu, mutane bakowa keda fahimta ba, wasu dama jiran mu suke yi, mun tara maƙiya da mahassada nasan da zarar sun ji abun da ke faruwa zasu yi farin cikin samun hanyar da zasu baƙanta mana rai don su ga raunin mu. Owais ya zamu yi? Meye mafita Owais um?"
"Omar mafita ɗaya ce! Shine mu yi hakuri mu rungumi kaddara! Mu dogara ga Allah, mu miƙa lamuranmu gare shi, mu aje batun mutane gefe ɗaya, addu'a ita ce takobin da zamu kare kanmu daga dukkan me nemanmu da sharri."
Gaba ɗaya komai da suke tattaunawa a cikin kunnan Salsabeel yana gani kuma yana sauraron su, tun da suka fara magana.
Bawan Allah ashe ya ji labarin zuwan Chief a bakin docs din dake kula da su, shiyasa ya yanke shawarar zuwa ya gan shi ya ji shiru bai leƙo shi ba.
Unfortunately ya iske shi a dakin Omar suna tattaunawa, kunnuwansa sun jiyo masa abun da ya karya masa zuciyarsa, yana daga tsaye bakin kofar ɗakin, hannunsa ɗaya ya ɗan karkace da ɗauri a jikin shi, fuskarsa ta jiƙe sharkaf da hawayenshi, so yake ya yi kuka sosai amma ya kasa, saboda bai son su san ya ji bai san ya zasu ɗauki abun ba, duk da shi bai zo da niyyar ya yi masu la6e ba.
Ba zai iya jurewa ba, ya gaza yarda Danish babu shi a doron duniya, yaron da ya kwallafa rai akan son ganin ya haɗu da iyayensa ya kuma samu farin ciki mai ɗorewa a rayuwarsa, ga kuma tausayin Owais da Omar da ya kamasa, da farko ya yi farin cikin jin sun gano su wanene elders saboda shi kanshi ya ci burin ya gansu da ainihin suffarsu, amma da ya ji akwai kakan Owais da mahaifin Omar sai ya ji zuciyarsa ta karaya, jikinsa ya yi sanyi lakwas, damuwa da tashin hankali suka baƙunci zuciyarsa. Wlh ya ji ɗacin jin cewa dasa hannunsu a ciki sune ma giggan kurkukun, bayin Allah gwanin ban tausayi yake kallon su..
Jikin sa a sanyaye ya juya zai bar dakin, har ya kusa fucewa muryar Omar ta katse shi, "Salsabeel! Kai ma ka ji komai ko?" Baisan ya ganshi ba, lokacin da zai ɗago da kansa daga kan kafadar chief Owais ya hango shi.
A hankali ya juyo ya fuskance su, "Ku yi hakuri, ba labe nake yi maku ba, na ji zuwan Chief shi na zo nema, sai kuma na taras da shi a dakin ka.."
"Kana nufin baka ji komai da muke tattaunawa ba?" Umar ne ya tambaya fuskarsa a marairaice,
"Ku yi hakuri, amma na ji komai da kuka tattauna, haƙiƙa zuciyata ta karaya, tsigar jikina ta tashi, na ji abun da ya ɗaga hankalina, ya kuma jefa ni a hali na damuwa, wallahi ban ta6a zaton za a samu Elders a family din da ya daga cikin ku ba, saboda kyawawan halayanku, amma idan na tuna faɗar Allah wannan bakomai bane..." Ya faɗa yana tafiya a hankali yake tunkarar su. "Na tausaya ma rayuwar ku, da ahalinku, bansan tayaya zan misalta maku ba, amma na razana sosai..."
Daga gaban gadon ya tsaya tare da goya hannayensa akan ƙirjinsa..
"Sai yanzu na gane dalilin da ya sa lokacin da Danish ya rikiɗa ya zama maciji bai nufi ko'ina ba sai gidan kakanka.."
A ruɗe suka dube shi.
"Kiranye ne ya yi mashi saboda yana son ya mayar da shi gidan kurkukun ƙaddara, ni nasan ba za a rasa gurin da ya ke6ance a cikin ɗakinsa ba, wanda da zarar Danish ya faɗa ciki zai mayar da shi kurkukun ƙaddara ta ƙarfi ta tsiya..."
Cike da takaici suka girgaza kawunansu.
ɗakin yayi tsit na ɗan lokaci kowa da abun da yake saƙawa a zuciyarsa.
Akwai tarin tambayoyin da suka cika zukatansu wadanda suke so su yi ma Owais sai dai damuwa ta hana su furta 💔
A daren ranar suka baro asibitin su dukan su, tare da twins bayan da docs suka tabbatar da lafiyarsu ta inganta ba abun da za su bukata..
Ba sai na bayyana maku irin farin cikin da su Unaisah suka yi ba na ganin Sajeed da twin sister din shi, duk a daren ranar Owais ya dawo da sauran yaran gidansa. Murna a gurinsu kamar waɗanda akaiwa albishir da gidan Aljanna...
Luxury-incense By Sapnah Borno.
Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku.
Wardrobe balls
Kabbasa spray
Chadian khumra
Hawee
Halud
Gabgab
Sandal sukkariya
Kajinguru
Dilka soap
Ready to use dilka
Karkar oil
Turaren tsuguno
Habil
Dorut
Dorot after period
Brown khumra
Dufr khumra
Body milk
Sudanese kuleccam
Chadian dufr kuleccam
Musk khumrah.
Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take
Our Chadian aphrodisiacs are.
Beejay fire
Sata jagab honey
Wetness and sweetness combo
Daka
Great A sabaya
Breast engagement powder
Ciccibi
Gumbar madara
Gumbar dabino
Bita Zaizai
08093772168
Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura
3196407426
First bank
Bature Hafsat Muhammad,
*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*