Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 83 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 83 Complete

Takun Ƙarshe
Idan muka koma bangaren jikokin Baba Obie mazauna ƙasar waje, da matayen ƴa'ƴansa da basu samu halartar family meeting ba, saboda uzururrukan da suka ruƙe su, kwata kwata basu da masaniya game da abun da ke faruwa da ahalinsu na Nigeria saboda ba a sanar da su ba, sai dai kowan nan su ya damu da rashin samun iyayen nasu a waya, sun saba akai akai suna kiran su su ji lafiyarsu, ko su yi fira a family groups din su amma wannan karon komai ya sauya ba kamar yadda suka saba ba, ko sun kira basa samun su, hakan yasa suka fara tunanin su dawo gida don su duba meke faruwa da ahalin nasu.

Mazauna ƙasar wajen ne suka tattauna maganar a wani video call da suka yi tsakaninsu kuma suka yanke shawarar zuwa, batare da iyayensu sun sani ba, haka matayensu ma sun yi deciding biyo sahun mazajen su da suka ji shiru basu dawo ba kuma sun daina picking calls ɗin su.

Sheikh Iman ne ya shawarce su da su kira sauran ahlin nasu su fada masu komai, tun kafin duniya ta ji, gudun halin da zasu shiga idan suka tsinci labarin a waje.

Batare da 6ata lokaci ba suka ɗauki shawarar shi kowannansu ya kira matar shi da ya'yan shi ya umarce su da su bar komai da suke yi su zo gida zuwa gobe, sa'ilin da suke kiran su a waya yanayin muryoyinsu sun ɗaga masu hankali, hakan yasa wasu daga cikin su suka gaza hakura sai gobe su taho. A yammacin ranar flight din su gimbiya Her Excellency Jamila ya yi landing from Kaduna to Abuja, tare da Autanta Dr. Nawaz ta zo shima ba mazaunin ƙasar bane a Uk yake aikin likitancinsa, an ci sa a da safe ya dawo Nigeria sai kuma ga kiran da ya riske su na gaggawa hakan yasa bai yi ƙasa a gwiwa ba ya biyo mommynsa suka taho....

Washe garin ranar kiran sallar asubahin farko, business jet din da ya ɗauko su Zaki Mubarak Obinna ya yi landing a airport, tun jiya jirginsu ya taso su uku ne suka zo tare da Faryat da Ibad, bayan Zaki ya kira daddynsu ya sanar da shi sun ƙaraso, ba tare da 6ata lokaci ba ya tura da motocin escorts suka ɗauko su.

Basu jima da ƙarasowa ba, sai ga kiran hajiya Her Excellency ya shigo wayar Deen bayan ya daga ta sanar da shi gasu a airport sun karaso, bai tsaya bata lokaci ba ya tura da motocin securities suka tafi dauko su, su biyu ne suka zo tare da last born ɗinta Dr. Yusrah.

Wuraren goma sha biyu na safe, mai girma Sharafudeen tare da Iyalansa suka ƙaraso Estate din.

Ba a fi ƴan mintuna da zuwansu ba, sai ga iyalan Senate Lateef sun shigo gidan baban suma..

A hankali ahalin suka fara taruwa a gidan Baba Obie, duk wanda ya zo da walwalarsa da zarar ya ga halin da ƴan gidan suke a ciki sai kaga yanayin fuskarsu ya sauya zuwa tsantsar damuwa da ruɗani, iyayensu mata suka dinga tambayar mazajensu meya faru da su? Meyasa suka rame? Meke faruwa ne babu walwala kan fuskokinsu, ga rashin kuzari, haka ƴa'ƴanma sun tsare su da tambayoyi kamar ƴan jarida, amsar da suke basu shine su jira Shiekh Imam ya ƙaraso.







Hakan ba ƙaramin jefa su a rudani ya yi ba, hankalin Faryat ya ƙi kwanciya tun da ta je ɗakin mommynta ta ga babu ita babu dadynta, duk wanda ta tambaya ina suka je sai ya ce mata ta jira shiekh Imam ya ƙaraso zata ji komai a bakinsa, abun ya 6ata mata rai, dama bata so zuwa ƙasar ba Zaki ne ya taso ƙeyar su ita da Ibad bisa umarnin mahaifinsa.









Around ƙarfe biyu agogon Nigeria ya buga, a daidai wannan lokacin Private jet din da ya ɗauko iyalan Hateem ya yi landing a airport from Dubai.







Tun kafin ƙarasowar su, already prime minister ya tura da motocin canadian polices da zasu ɗauko su tunkafin ma flight din nasu yayi landing, kafin ka ce me gaba daya jikokin Obinna da surukansa sun hallara a gidan sa ƙwansu da kwarkwatar su, tun daga kan iyayensu har izuwa jikokinsa kaf ɗinsu, kowa da kowa, suna ta tambayar ina baba Obie da Hajiya Saratu ganin babu gifcinsu, nan ma ce masu akai su jira Shikeh Imam ya zo zai basu amsar tambayar su, lamarin ya ɗaure musu kai har ta kaiga ransu ya fara 6aci ganin sun ki faɗa musu meke faruwa, sun barsu cikin zullumi da fargaba, gaba ɗaya suka ƙagara da zuwan Sheikh Imam Malik...💔







Gaba ɗaya duk wani motsinsu akan idanun Baba Obie, haka zalika hayaniyar da suke ta yi duk yana jinsu, daga dakinsa yana kallon komai dake faruwa a gidan saƙo da lungu ko sauro ya gifta sai ya ganshi ta cikin laptop dinsa, farin cikinsa  ragagge ne, a da in ya ga ahalinsa sun taru daɗi yake ji amma a yanzu kunya da fargaba ya ke ji saboda yasan tonan asiri za a yi masa kuma da zarar sun ji abun da yake aikatawa zasu tsane shi su shiga halin baƙin ciki da danasanin kasancewar su wani bangare nasa.







Sir Mubarak ne ya kira shiekh Imam ya sanar da shi cewa kowa ya hallara na family dinsu suna son su bayyana masu komai, ya taimaka ya zo don ya yi masu nasiha gudun halin da zasu shiga, Sheikh Imam ya ce yanzu haka yana akan hanyar zuwa estate din nasu.







Before ya ƙaraso gaba ɗayan su suka hallara a main falo, iyayen suna a zazzaune saman Sofas yayin da ƴan mata da samarin family din suka zazzauna kan rug, babu mai walwala akan fuskarsa..







Bayan ya iso ya shigo da sallama a bakinsa, cikin girmamawa suka gaishe da shi in ka cire Faryat da ta ɗage kai sama tana hura hanci, kamar bata gansa ba, ko arzikin mayafi babu a jikin ta, wata ƴar iskar short gown ce a jikinta ta marasa ɗa'a wadanda suka gaji rashin mutunci, ta kifa facing cap a saman kanta ta saki gashin ta a gadon baya, ga wani ɗan iskan shade data mannawa idanunta daga ka ganta dai ka ga ƴar duniya, a tsiya ce ta ke tauna gum a bakinta, sautin har fita ya ke yi ƙas ƙas, ba don iyayensu basa a cikin nutsuwarsu ba da tuni Sir Mubarak ya korata ta ɗauko mayafi, su twins da suka saka ta tsakiyar su, sun raku6e ko kaɗan ba annuri akan fuskarsu sai zallar damuwar halin da suka baro mommynsu  a asibiti.







A hankali Shikeh Imam yake ƙare musu kallon da ya sa duk suka sha jinin jikinsu ga waɗanda basu san meke faruwa ba.







Ɗaura idanunsa ya yi akan iyalin Hateem dake a zaune kan doguwar sofa, sheikha Mujeedat tana a gefen Hateem, ta ɗauki wankan royal abaya ta alfarma, as usual ta saka chain mask akan fuskarta, kyawawan idanun nan nata suna akan Hateem da ya sadda kansa ƙasa yama kasa ɗagowa saboda zullumin abun da zai biyo baya idan suka ji abun da ya tara su, yana jin tsoron ya rasa gimbiyarsa fiye da yadda yake jin tsoron tozarcin da zasu fuskanta a gurin al'umma, saboda yasan koda ta haƙura zata ci gaba da zama da shi da baƙin tabon family dinsu ba lallai Royal Family ɗinta su yarda a zubar musu da mutunci ba, dama kafin auranta saida ya fuskanci ƙalubale ya sha wahala kafin aka bashi ita duk da tarin dukiyarsu saboda tsada ne da su, basu cika auren bare wanda ba jinin su ba, kuma ba royal family ba. Ruƙe hannunsa ta yi a cikin nata gam ta harɗe yatsunsu hakan yasa shi jin wata irin nutsuwa na shigar shi..







Gimbiyar izza Nazli da Yazrin suna a zaune daga gaban Sofa din da iyayensu suke akai, gaba ɗayansu royal gown ne a jikinsu sun yi rolling, tun da ta sadda kanta ƙasa bata ƙara ɗagowa ba saboda tsabar izza.







Mai girma Sharafuddeen shima ya haɗa nasa matan guri guda, yana a tsakiyar su saman doguwar Sofa, su Hajiya Laura anyi zugudum ta zabga tagumi da alama ba kwanciyar hankali a tare da su, daga ita har kishiyar tata, Gimbiya Malika dama tuntuni suke zargin da akwai abunda ke faruwa a family din, tun kan abun da ya faru da hajiya Saratu, mijinta Pravin da Baba basu zo duba ta ba, kuma mijin nasu ya ƙi basu amsar tambayoyin su.







Idan muka koma bangaren Iyalin His excellency Abdul Razak, Hajiya Muhibbat dake a zaune gefensa ta daura ƙafarfa ɗaya kan ɗaya, kowa ya shiga damuwa amma ita da alama ko a jikin ta, hasalima wayarta take daddanawa tana yi tana taunar gum a bakinta, gashi ta zuba uban ado kamar amarya..







Turai tafi kowa rashin sakewa, ta damu baiwar Allah, gabanta sai faɗuwa ya ke yi, tun da Sir Mubarak ya faɗa mata maganar meeting din da zasu yi, ran ta ya bata akan Hajjaty da Pravin ne amma da ta ga an kira kowa na family din sai ta ruɗe saboda ta fahimci ba abun da take hasashe bane, wannan yafi karfin laifin da su Hajjaty suka aikata.





Sir Mubarak dake a gefen ta kwata kwata hankalinsa baya akan kowa ya lula duniyar tunanin makomar rayuwar family ɗin su.





Ƴa'yansa suna a zaune gaban Sofas din da suke akai, Zaki da ya lumshe idanunsa kwata kwata bai so ya zo Nigeria ba, saboda baya son ma kusanta kanshi da abun da ya yi silar barin shi, sai gashi mahaifinsa ya dawo da shi. Ibad dake zaune gefensa na hagu abun ka ga mai kuruciya a kai, game yake bugawa a Ipad dinsa.





Daga ɗayan bangaren Dr. Jazz ne ya langwa6e kansa jikin sofa, bawan Allah har rama ya yi cikin ƴan kwanakin nan saboda damuwar rashin ganin baba Obie baya picking calls dinsa, kullum wayarsa a kashe, ba kamar yadda suka saba ada ba, a rana sau uku yake kiransa kuma baya missing picking call nasa, dama tun lokacin da baba Mubarak ya faɗa masa baba ya yi tafiya bai yarda ba sai da ya zargi wani abu daban, ga kuma abun da ya faru da hajiya Saratu, yau da aka tara su ya shiga ruɗu sosai, gabansa sai faɗuwa yake yi.







A bangaren Deen kuwa, shima yana zaune kan sofa tare da uwargidansa Jamila, batasan matsayar ta ba, kanta ya ƙulle, ta rasa gane meke shirin faruwa? Amma tana jin babu lafiya a family din..







Chief Owais yana a zaune dirshan kamar mai neman gafara, ba zaka ta6a gane halin da yake a ciki ba, gefe da gefensa Ziyad ne da Captain Yaseer sun saka shi a tsakiyar su, Dr Nadeem yana a gefen Captain, damuwa ce ƙarara akan fuskokin su, da ya ke su sun san komai.


Filin dake a tsakiyar Sofas din wasu jikokinne zaune saman Carpet, Dr.Nawaz sai Yusra ƙanwar Yaseer tare da Hindu ƙanwar Owais, da kuma Zulaihat ƙanwar Ziyad, sun jera layi kowannan su ya yi zaman cin tuwo, babu wanda gabansa baya faɗuwa, tun ma kafin su ji me za a faɗa musu.







Haka zalika Hajiya Madina tana a zaune gefen Senate Lateef, hannunta ruƙe cikin nashi sai tausar shi take yi ganin yadda ya yi sukuku kamar ba laka a jikin shi..💔







Sai da Shikeh Imam ya kammala kallace su tsaf kafin ya samu guri ya zauna kan Sofa din da ke fuskantar su, duk suka bi shi da ido gaba ɗaya sun ƙagara da son jin me zai ce..







"Ana ta ja mana rai, ni banga amfanin ɗauko mana malami ba, sai ka ce dai masu iskokai balle ace za'a mana rukiya.." 



faryart ce take gunaguni bata kai ga ƙarasawa ba, Zayn ya make bakinta da tafin hannunsa ya buga mata warning, harara ta watsa mashi da yake ba kunya ce ta ishe ta ba..







"Nifa na rasa ganewa, kaina ya kulle, meke faruwa ne? Meke damun kowa ne? Nifa bana son tashin hankali, kowa ka tambaya sai ya ce a jira sheikh a jira sheikh ga sheikh din ya zo amma ya yi shiru yana ta kallon mu kamar ya samu tashar bollywood..." 



Rai a ɗan bace Dr.Nawaz ya yi maganar shima da yake ba kunya ta ishe shi ba, tsagera ne..



"Karka kuskura ka ƙara magana!" A ɗan tsawace Nadeem ya faɗa, kallonsa ya yi tare da yamutsa fuskarsa batare da ya furta kalma ba.







"Mijin mace ɗaya, yau ahalin namu ba lafiya, kamar masu zaman makoki, ni bansan meyasa ka matsamin akan in zo ba, ina tsaka da hidimar biki kasa na baro dangina, nayi nayi ka faɗamin meke damunka ka ƙiya, ga sheikh din ya ƙaraso ya wani tsare mutane da idanunsa kamar wasu masu laifi, wlh zan tafi ne idan na gaji da zama, kuma dai kasan bana zaman jin wa'azi ehe..." Her excellency Muhibbat ce ta fada tana kallon Abdul razak hada murguɗa ƙaramin bakin ta, tana karkaɗa ƙafarta..



Da yake yasan halin kayansa bai biye mata ba..







"Nifa Allah na gani, malaman sunnar nan ba burgeni suke yi ba, wlh da nasan tara mu za'a yi don a yi mana wa'azi ba abun da zai sa in wanko ƙafa in biyo mommy mu zo nan.." Cike da takaici Yusra ta yi maganar tana jifar Imam da harara a fakaice.



In a cool voice Hindu ta ce, "Pls, Yusra, mu ƙara haƙuri, bai kamata kina fadin maganganun nan ba.." cuno baki ta yi ita ala dole an takura mata..







Gyaran muryar da sheikh Imam ya yi musu ne ya ja hankulansu ga dubansa, gaba daya suka tattara nutsuwarsu da hankalinsu a kansa, a hankali ya zauna kan Sofa din dake fuskantar kowannan su.









"Innalhamdu lillahee, nahmaduhu wa nasta'eenuhu wa nastaghfiruhu, wa na'oodhu billaahi min shuroori anfusinaa wa min sayyiaati a'maalinaa. Wa man yahdillahu fala mudillilahu, wa man yudlil falaa haadiya lah "Alhumdulillah. Indeed, all praise is due to Allah....'





ya ɗan dakata yana dubansu kafin ya ce, "Sallu Alal nabiyyul Kareem, Sallallahu Alaihi Wasallam..." 



atare suka haɗa baki gurin karasa ambaton Sallallahu Alaihi Wasallam



kafin suka fara yin salatin annabi, Faryat dai ta ƙi tsayar da hankalinta guri guda, bayan sun kammala ya soma magana cikin harshen turanci saboda yana son kowan nan su ya ji me ya ke faɗa,



"Nasan gaba ɗayan ku kun ƙagara ku ji dalilin da yasa aka umarce ku da ku baro komai da kuke yi ku zo nan, wataƙil an takura maku amma abu ne na gaggawa wanda da bukatar ku haɗu domin mu nemawa kanmu mafita a tare game da musibar da ta kunna kai a family din nan.. "



Cike da tsantsar ruɗani suke jefawa junansu kallon kallon ga waɗanda basu san meya faru ba.



Numfasawa sheikh Imam ya yi kafin ya daura da cewa, "Kafin mu fara sanar da ku, ina so in fara tunasar da ku da nasiha, saboda gudun halin da zaku shiga..."



 Maganganun sheikh Imam sun rikita lissafin kwakwalan su, sai zare idanunsu suke yi cike da fargaba.





Tun da ya fara yi masu nasihar suka yi shiru suna sauraran shi, ko tari babu wanda ya yi a cikin su, da alama nasihar ta ratsa zukatansu, jikinsu ya yi sanyi lakwas saboda tsoron Allah da ya ƙara shigar su, duk da akwai tarin fargaba da zullumin abun da zai biyo bayan nasihar tashi don sun san dole akwai maƙasudin yin ta.







"Jazakallahu Khairan Malam, mungode da nasiha, Allah ne kadai zai iya biyan ka.." Hajiya Madina ce ta yi maganar cikin sanyin murya,







"Sai dai gaba daya hankalin mu ba a kwance ya ke ba, mun damu da ganin halin da mazajen mu suke a ciki, sannan babu Baba, Saratu ma bamu san ina take ba, munyi munyi su faɗa mana gaskiyar abun da ke faruwa sun ƙi sanar da mu, sun ce mu jira ka ƙaraso za mu ji komai a bakinka, don Allah malam ka faɗa mana, koma menene in wani ya rasu ne in kuma wani abun ne a fada mana, we're all muslim mun yi imani da kaddara mai kyau da mara kyau,.." 





Ta karasa maganar fuskarta a yamutse, gaba daya sauran suka tsoma bakinsu akan a fada musu meke faruwa.





Shiru Sheikh Imam ya yi, shi kanshi yana jin fargaban sanar da su, saboda ya lura akwai masu ƙarancin tawakkali a cikin su.







"Bismillah Owais, ka fada masu komai dake faruwa..." Ya faɗa idanunsa akan Chief Owais da ya raku6e kansa jikin Sofa, gaba daya suka mayar da dubansu gare shi.







Tunani ya ke yi taya zai fara sanar da su? ya zasu dauki abun? Me zai biyo baya?







Ba kaitsaye ya fara sanar da su ba, saboda harshen sa yayi rauni, ba zai iya ɗaga muryarsa ya yi magana mai tsayi ba.





A hanakali ya zaro wayarsa daga cikin trouser pocket dinsa, ya mike cike da rashin kuzari a jikinshi ya ɗaura wayar saman c-table din dake a gaban Imam Malik, bayan ya kunna masu video din dake ɗauke da duk wani bayani game da gidan Kurkukun ƙaddara da miyagun ayyukan da ake aikatawa a cikin sa..." 







Ya ƙure musu volume yadda kowa zai ji dakyau, zama yayi dirshan gaban table ɗin tare da sadda kan shi ƙasa..







Da ya ke cikin harshen turanci ya yi audio din kowannansu yana sauraro kuma yana fahimtar me ake cewa, tun suna jin abun kamar shirin wasan kwaikwayo har suka fara ruɗewa da jin irin azabtarwar da ake yiwa matasan yaran da basu ji ba basu gani ba. Lokaci ɗaya suka ruɗe, suka fara tambayar Owais wai dagaske ne abun da suke sauraro yana faruwa ko dai ƙagaggen labari ne na almara? Gaba daya sun kasa yarda da gaske ne saboda aganinsu ba zai ta6a yiwuwa a rayuwar zahiri ba, don ko a tarihi basu ta6a jin makamancin labarin kurkukun ƙaddara ba, sai dai abun da ya ɗaure musu kai chief Owais ne ya ke yin magana a cikin audio din, sun gane voice dinsa ne.





Hajiya Laura ta ce yaushe Owais ya zama ɗan jarida mai karanta hausa novel? Abun da daure kai.."





Her excellency Muhibbat ta ce, "Ni na rasa ganewa, mu da muka zo don mu ji meke faruwa da mazajen mu why za'a kama bamu labarin ƙanzon kurege..."





Lokacin da audio din ya yi nisa hankalin wasu daga cikin su ya tashi matuƙa, ƴan matasan cikinsu har sun fara zubda ƙwalla saboda yadda labarin ya ta6a zuciyar su har suna fadin wannan rashin imanin ya yi yawa, yaran nan ana zabtar da su wlh, saboda baƙin zalunci na wasu mutanan da babu Allah a ransu, kowa dai yana ta tofa albarkacin bakinsa, wadanda suka fi tausayi a cikin su irin su Jazz da Hindu da Zulaihat da Turai tuni sun fashe da kuka saboda tausayin yaran da ya kama su tsigar jikinsu har tashi take yi, musamman da aka zo kan labarin Unaizah da Majnoon wa'iyazubilla! Kuka sosai suke yi abun ya ta6a zuciyar su, hatta Gimbiya Mujeedat saida ta matse ƙwallarta, itama Hajiya malika zuciyarta ta yi rauni ta dinga fadin Owais ku yi mana bayani mana, wani darasi ne ake so mu ɗauka acikin labarin nan? Meyasa kuka kunna mana shi? Ko dan mu ƙara imani ne um?"



 

Cikin sanyin murya Owais ya ce mommy ki yi hakuri ki ƙarasa sauraran shi, ta ce toh Owais Allah yasa mu ji Alkhairi, duk rashin tausayin su twins saida jikinsu ya yi sanyi lakwas dama zuciyarsu a raunace take duk sunyi sukuku da su a ransu suna ayyana in da gaske labarin kurkukun kaddara ke faruwa ya wadanda abun ya faru da su zasu ji?





Dr. Nawaz da Faryart da Yusra ko gizau basu yi ba, tabbas labarin ya ta6a zuciyoyinsu sai dai ba kamar sauran ba, saboda su a tunaninsu bazai ta6a zama gaskiya ba, ƙagaggen labari ne kawai,  jin abun suke yi wani iri.







Ibad sarkin tsoro ga tausayi da ya addabe shi, tuni ya aje game din da yake bugawa, jikinsa sai kerma ya ke yi kamar mazari hakan yasa Sir Mubarak ya rungumo shi a jikin shi.





A hankali Zaki ya zaro hanky daga aljihu ya soma share ƙwallar dake gangaro masa saman kuncin sa, zuciyarsa ta karaya.



Shiekh Imam dake kallon fuskokinsu a hankali yake karantar yanayin su, tun anan ya fahimci masu rauni da marasa raunin cikin su..



Hatta Yazrin so take ta fashe da kuka ta kasa sai dai ta sadda kanta ƙasa, gimbiyar izza kuwa tun da ta fara sauraron Audio din bata motsa ba, dama ita haka take da wuya mutun ya iya karantar abun da ke a ranta ta yanayin fuskarta, saboda tsabar izza, Amma fa da alama ta razana da jin labarin kurkukun kaddara, duba da yadda yatsu ta suke ta kerma, cheeks dinta sun yi jawur saboda kaɗuwar da ta yi, haka zalika Hajiya Jamila tausayi yasa ta kasa jurewa, sai faman sharce ƙwalla take yi da yatsun ta.



Cikin rauni na murya Jazz ya ce, "Tun da uwata ta haife ni a duniyar nan ban ta6a jin labari mai ban al'ajabi ba irin wannan! rashin imanin ya yi yawa, wasu mutane ba tsoron Allah, zalunci da mugunta kadai suka sa a gaba, na rasa gane me yasa idon wasu mutane ke rufewa akan neman duniyar da zamu mutu mu barta, basu tuna cewa suma fa halittar su aka yi kuma zasu mutu su koma ga Allah ne, amma dai yaran nan sun bani tausayi wlh, an azabtar da rayuwar su..."





 Bai ƙare maganar ba, cikin karyayyar murya Ziyad ya ce, "Wlh tun da na fara aikin jarida inje in ɗauko rahoto da sauransu, har kawo yau da nake ruƙe da matsayin director, ban taba jin makamancin wannan labarin da muke sauraro ba.." Ya faɗa kamar baisan komai ba.







Kafin audio din ya kare gaba daya fuskokin wasu daga cikin su sun jiƙe sharkaf da hawaye..



Shiru suka yi yayin da zuciyoyinsu ke a cike fal da tunanin kurkukun kaddara da prisoners..







Kwatsam ba zato ba tsammani suka tsinkayi muryar Owais acikin kunnuwansu yana fadin, "Sheikh Imam ya yi maku nasiha don haka ku yi haƙuri da abun da zaku ji daga gare ni..." shiru ya ɗan yi kafin ya numfasa yana mai jin shakkar furtawa..



In a breaking voice ya ce, "Nasan kun yi tunanin labarin almara ne, to ba haka bane, da gaske ne ya faru, kuma bakowa bane shugaban KURKUKUN ƘADDARA FA CE KAKANMU OBINNA, PRISONERS DIN DA KU KA JI LABARINSU AKWAI JIKOKINSA A CIKIN SU...."



 Bai ƙare maganar ba, sakamakon wani abu da ya katse masa hanzarinsa, a ruɗe yake kallonsu ganin yadda iyayen su mata da grandchilds ɗin suka zabura gaba daya suka miƙe daga zaunan da suke, fuskokinsu ɗauke da tsantsar ruɗani, cikin 6acin rai hajiya Malika ta ce, "Owais kana hauka ne? Kasan me kake faɗa kuwa? Meke damunka ne??" A faɗace ta fada..



Hajiya Muhibbat ta ce, "Wannan wani irin zancen banza ne Owais? Ko ka fara shaye shaye ne? In ba haka ba ka rasa wa zaka hada da fasiƙan mutanan nan sai baba Obie? Uban da ya haifi Ubanka..!" Rai a 6ace ta faɗa kamar zata doke sa..



A firgice Jazz yake girgiza kanshi yana fadin wlh ba gaskiya bane Yaya Owais dan Allah ka daina fada, bazai ta6a yiwuwa ba, Baba ko ƙiyashi ba zai iya kashewa ba, balle rai, wlh ba haka bane ba gaskiya bane, ni nasan wanene Baba..."



 Kuka ya kama yi musu kamar ƙaramin yaro.



Huyawa Hajiya Jamila ta yi akan iyayen su maza ta soma tambayar su,"Dama Owais ya samu ta6in hankali shine baku taba faɗa mana ba? Me yasa ba za ku kaishi asibiti likitan mahaukata ya duba shi ba uhum? Dan Allah ku yi magana mana! Kun yi shiru kuna jin kalamil ƙabihin da Owais ke faɗa akan kakansa...!" 







Ta faɗa cike da tashin hankali,





Matsawa Hajiya Madina ta yi kusa da Owais, ta damki damtsen hannunshi ta fusgo shi har saida ya miƙe ta tasa ƙeyarsa gaban Sheikh Imam ta ce, "Don Allah ka yi masa rukiya, Owais ya haukace, wlh bayin kansa bane, Owais ba zai ta6a fadin maganar nan da hankalinsa ba, zai iya yiwuwa aljanu ne suka shige shi.."





tsananin tausayinsu ne ya kama mazajensu da shi kanshi sheikh Imam ɗin da Chief Owais, wlh sun ƙara karya musu zuciya, ganin yadda suka yarda da surukinsu.







Cikin fushi Malika ta nufi Owais ta fusgo shi kamar zata doke shi ta ce, "Owais ban ji dadin furucin da ka yi akan Baba ba, dan ubanka meke damunka ne? Baka da hankali? Maza ka zuƙunna ka ba kowa hakuri kuma ka je ka nemi yafiyarsa saboda ƙazafin da ka yi masa!"





 Runtse idanun shi ya yi gam, a hankali wasu zafafan hawaye suka fara shararowa kan kuncinsa, cikin shesshekar muryarsa mai rauni ya furta, "Sheikh bazan iya da su ba, ni dama nasan za a rina, ka taimaka ka yi musu bayanin da zasu fahimta, wlh ba ƙazafi na yi masa ba, shine Elder na gidan kurkukun ƙaddara kamar yadda ku ka ji. Zaku ya tuna yaran da nake ruƙo a gurina? Waɗanda na ce maku sojojin America ne suka tsince su a dajin Evil Forest kuma suka damƙa case din su a hannun hukumar mu? A ranar farewell dinner na Uncle Hateem na zo da su kuma nasan kowan nan ku ya gansu, to wadannan yaran suna daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, kuma akwai jininku a ciki..." 



nan fa ƙwaƙwalensu suka fara tariyo masu fuskokin yaran masu bala'en kama da wasu daga cikin su.





still basu gasgata maganar shi ba, amma fa sun fara shan jinin jikinsu, maganarsa ta haifar musu da kokwanto..





"Idan har yanzu baku yarda ba zan iya nuna maku videos din yaran da muka kubutar..."





wayarsa ya ɗauko ya kunna masu videos din su Unaisah a questioning room.





Sun ɗan fara yarda amma still basu gasgata ba, saima cewa suka yi koda za su yarda labarin na gaske ne amma ba zai ta6a yiwuwa Baba ya aikata ba, saboda su sun yarda da shi sun kuma san halin shi.





"Daddy ku yi musu bayani, watakil ku su yarda da ku..."



Hajiya Laura ta ce karma su wahalar da kansu, ai wlh ko shi Obie din ya faɗa da bakinsa ba zasu yarda ba..



Cikin raunanniyar murya mai girma Sharafudeen ya basu labarin abun da ya faru a ranar da momma ta bayyana, gaba ɗaya ya fayyace musu komai da ya faru.



Wlh Sunyi matuƙar razana, sun firgita sun shiga matsanancin ruɗani da tashin hankali, musamman da suka ji Momma tana a raye bata mutu ba, lamarin ya rikirkita tunaninsu har suna haɗa baki gurin tambayar tayaya hakan zai yiwu mutumin da ya mutu tsawon shekaru ashirin ya dawo a raye? Bayan su da idanunsu sun shaida mutuwarta, sai dai idan fatalwarta ce ta bayyana.



Duk ta inda Owais ya taro su sai sun nemi abun da zasu fake da shi akan ba gaskiya bane, har mazajen su sunyi kokarin fahimtar da su akan gaskiyar zancen amma sun ƙi yarda.





Sheikh imam ma ya yi kokarin fahimtar da su amma sun ƙi ma sauraron su.



Cikin sanyin murya Hateem ya ce, "Banga laifin ku ba, mu ma lokacin da mu ka ji labarin, mun ƙaryata da farko, amma baba ya karya mana zuciya, saboda ya kasa kare kanshi kuma ya amsa laifinsa, yanzu haka baba yana a ɗaki ya kulle kansa tun ranar da asirin shi ya tonu..." Maganar Hateem ta ƙara ɗaga hankulansu.



"Bayan haka cikin sunayen elders din da Momma ta faɗa ta kira sunan Pravin yana ɗaya daga cikin su, saboda rashin gaskiya Pravin ya gudu daga gidan nan tare da Hajjaty tun ranar da abun ya faru, kuma shine ya yi silar kwanciyar hajiya Saratu jinya, saboda ta kama su suna yunƙurin guduwa daga gidan nan, yanzu haka tana a kwance gadon asibiti ita da momma."



 

Kamar a mafarki su twins su ke sauraron abunda Sir Mubarak ya ke faɗi, Bayin Allah a tare suka ɗaura hannayensu a saman kawunansu alamar sun shiga uku, kafin ka ce me tuni sautin koke kokensu ya cika wurin, Faryat ma batare da sun ankara ba ta yanke jiki ta faɗi a sume babu wanda ya lura saboda ɗimaucewar da suka yi.







"Momma ba fatalwa bace, da gaske ita ce, bata mutu ba, tana a raye, Baba shi ya ƙulla makircin mutuwarta, lokacin da aka kawo gawarta da sunan sun yi accident din mota bamu ga fuskarta ba saboda ta ca6e da raunuka, ashe ba gawarta bace, Allah kaɗai yasan a ina baba ya samo gawar da ta yi kama da gawarta watakil ma rufa ido ya yi mana muka dinga ganin kamar ita ce..." Deen ne ya faɗa a raunace yana dubansu.







Dafe kawunansu suka yi, kusan a tare suka shiga ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun daga iyaye mata har ƴa'yan nasu, cikin shesshekar Kuka Malika ta ce, "Wlh da gaske ne! Na yarda da maganarku, sai yanzu na gane wacece tsohuwar da aka kawo asibitinmu villa, dama tun da suka zo da ita nake ta yi mata kallon sani, amma saboda canzawar da ta yi shiyasa na kasa ganeta ashe momma ce bata mutu ba.."



"La'haula walaquwwata Illa billah! Kai jama'a! In kuwa haka ne Baba ya gama da mu, ya yaudari yardar da muka yi masa, ya zalunce mu ya cuce mu, tsawon shekara nawa muna haihuwar yara su zo ba a raye ba, ashe sadaukar da su yake yi gidan matsafa, arzikinsa na jinin ƴa'ƴanmu ne jama'a, mun shiga ukun mu! Da wani ido zamu dubi duniya! Wlh baba ya karya mana zuciya, muna yi masa kallon mumini nagari ashe mutumin banza ne matsafi, mutuncinsa ya zube a idanunmu, wallahi ba zamu ƙyale sa ba, mu dai an cuce mu an goga mana mummunan tabo wlh..." Hajiya Muhibbat ce ta ke ta sambatun rashin ɗa'a



"Wlh dana san haka, ba abun da zaisa in auri jininsa, yanzu gayanan mu da ba ƴa'yansa ba daga surukantaka an jaza mana musiba da bala'e, ana yi mana kallon mutane masu daraja saboda mun auri jinin dattijon arziki ashe dattijon banza ne tsohon najadu, wannan fasikanci har ina! Kawai an zubar mana da mutuncin mu wlh!"



"Yadda muke alfahari da shi na kasancewar shi mutun nagari da ya haifa mana mazajen da muke alfahari da su, ashe ba mutumin kirki bane azzalumi ne, wlh sai Allah ya saka mana cin zalun da ya yi mana, ya ja mana abun kunya, ai wlh mutane suka ji wannan abun kunyar mun shiga uku! Shiga cikin jama'a sai ya gagare mu..."



Kamar mahaukaciya sai 6a6atu take yi, babu wanda ya fahimci me take cewa saboda koke koken da ya cika falon, kuma ta yi maganganun ne cikin harshen shuwa. Maids din gidan dake leƙen su sun ji komai, bayin Allah sun yi kuka da idanunsu kamar ba gobe, su kansu Baba Obie ya karya musu zuciya, sun kuma ji tausayin halin da ya jefa ahalinsa, sai yanzu suka gane dalilin da yasa cikin kwanakin nan mutanan gidan suka shiga mawuyacin hali da kuma dalilin da yasa suke sa ake kawo masu abinci daga restaurant, ashe gujewa cin haram suke yi.





Alƙalamina shima ya yi rauni, bazan iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyoyinsu sun karye, ga wata matsananciyar damuwa mai tattare da faɗuwar gaba da ta cika zukatansu, sun yi kuka kamar ransu zai fita, babu babba ba yaro, babu mai lallashin wani kowa ta kansa yake yi, duk da sanyin A.c din dake ratsa fatar su hakan bai hana su fitar da gumi ba, gaba ɗayan su babu wanda zazza6i bai kama sa ba, harda masu ciwon kai.



Nan take suka fara yanke jiki suna faɗuwa ƙasa a sume, kusan mutun goma suka sume, Zaid da ya gama haukacewa cikin ɗimuwa ya nufi c-table ya ɗauki glass vase din dake akai ya ɗaga sama yana kokarin buga ma kansa, bai aune ba yaji an cafki hannunsa idanunsa jawur ya dubi Chief da ya ruke sa, fashewa ya yi da kuka yana fadin ya ƙyalesa ya kashe kanshi ko ya samu sassaucin raɗadin da zuciyar shi take yi mashi, mutuwa ya ke so ya yi wlh sai ya kashe kan shi.





Chief baisan sa'adda ya dauke shi da mari ba saboda zafin kalmar kashe kan shi da ya furta aikuwa nan take ya faɗi a sume, hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba ya yi zaton zuciyarsa ce ta buga ya mutu, hankalinsa ya rabu gida biyu, kwata kwata kowa ya rikice, jikokin sai kokarin illata kansu suke yi, iyayensu ne ke ta kokarin hanasu aikatawa wlh duk sun haukace, daga sun taro wannan sai wannan ya 6alle gida ya rikice, hauka tuburan, Zayn da ƙunci ya mamaye shi babu wanda yasan ya zame jiki ya nufi kitchen ya ɗauko wuƙa yana kokarin dadarata akan wuyanshi, maids din gidan dake kallon komai dake faruwa aka samu wata ta ganshi aikuwa ta fasa ƙara tana fadin zayn zai kashe kanshi a kitchen, da gudu Sir Mubarak ya nufi kitchen din a lokacin har ya fara yanka gefen wuyan shi jini duk ya wanke shi, a zafafe Sir Mubarak ya fusge wuƙar ya jefar da ita, ya dinga kifa masa maruka har saida ya sumar da shi.



Ya salam! sun yi tunanin mafita ne da suka fara sanar da su kafin su ji a bakin duniya gudun kar a ci zarafin su, ashe kiran nasu da suka yi a gida suka faɗa masu basu tsira ba, yaran nasu ne wasu ba tawakkali, suna da ƙarancin ilimin addini akai, ba kowan nan su bane zai iya ɗaukar ƙaddara, bayin Allah tun da suka taso rayuwarsu basu san wahala ba, basu san tashin hankali ba, basu san rashi ba, Allah ya basu komai, nasara da gatanci, wayewa ta yi masu yawa, rayuwarsu da dabi'unsu duk na turawa ne, dama irinsu basu cika ɗaukar ƙaddara ba, in mummunan abu ya faru da su sukan kamu da depression daga nan sai su kashe kan su toh abun da ke kokarin faruwa da su kenan.



Ba don Allah ma yasa sunyi dabarar kiran su gida suka fara faɗa masu ba, watakil sai dai su ji labarin duk sun kashe kan su.





Da abun ya ci ƙarfin su, a karshe sai dai suka kira docs, suka dinga rurruƙe su suna yi masu sedative injection tun da nasihar ta ƙi shigar su, basu ganewa depression ne na farat ɗaya ya kama su.







Kowa ya fi jin tausayin ƴa'yan pravin, bayin Allahn nan suna a tsaka mai wuya, da ƙyar ma su dawo hayyacinsu batare da sun samu ta6in hankali ba.





Al'amarin ya ɗaga hankalin Imam Malik da iyayen su, har nasiha aka yi musu don su dauki dangana, amma sai gashi suna abu kamar ma basu ji nasihar ba, ba irin kokarin da basu yi ba amma sun kasa tanƙwara wasu daga cikinsu, addu'o'i Sheikh Imam ya dinga karanto musu da kyar suka samu suka fara maimaita addu'o'in a cikin zukatansu, ta haka ne suka fara samun sassauci daga baƙin cikin da ke damun su, abun da ya fi karya zukatan iyayensu ganin tun yanzu sunata kokarin kashe kansu to ina ga idan aka fallasa sirrin mutane suka ji? Aka fara tsangwamar su!  Akwai sauran Rina a kaba..


*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426 

First bank 

Bature Hafsat Muhammad,


bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post