Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 84 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 84 Complete

Takun Ƙarshe

HAJJATY

Bari mu koma baya muji meya faru da Hajjaty bayan su Sir Mubarak sun yi nasarar cafke su.

Tun bayan da ta suma, bata kara sanin inda kanta ya ke ba, lokacin da ta tashi farfaɗowa a wani ɗaki ta tsinci kanta a ƙwance saman gado, ga ƙarin ruwa sanye a hannunta, cikin disasshiyar murya take ambaton sunan Praveen! Sam ta manta da abun da ya faru.

Da kyar ta tattara sauran karfin da ya rage mata ta samu ta dan motsa jikinta ta miƙe zaune, tana bin ko'ina da kallo,

 Tanata tunanin a ina take? Meye faru? Ina Praveen.

Unexpected ta tsinkayi Muryar Sir Mubarak a cikin kunnanta.

"Ina fata kin tashi lafiya? gabanta ne ya faɗi, a rude ta kalleshi, yana a tsaye bakin kofar dakin jikin shi sanye da kakinsa, nan take ta tuna da komai da ya faru.

Cikin shesshekar murya ta ce,"Yaya Mubarak, dan Allah ku yafe mana laifin da mu ka yi maku, wallahi mu ba mazinata bane, da auran mu, munsan bamu kyauta ba da muka 6oye maku, amma ku yafe mana, mun tuba ba zamu ƙara ba, koda ba zaku maida mu cikin ku ba, ku yafe mana zamu tafi mu bar maku ƙasar gaba ɗaya amma dan Allah ku duba zumuncin dake a tsakanin mu, ko dan saboda iyalin Praveen ku taimaka ku ƙyale shi, kada ku kashe min ɗan uwana, shi kaɗai ne dangina da ya rage mini a duniya, na roƙe ka Ya Mubarak..

A hankali hawayen da suka taru cikin idanunta suka soma dira kan kuncin ta.

A tsanake ya ke bin ta da kallo, kwata kwata babu alamun zai furta kalma saida ta ƙarashe maganartata, ya matso ya zauna kan kujerar dake a agaban gadon nata.

"Baki bani amsa ta ba! Ya jikinki kin tashi lafiya?"

Cikin shessheka ta ce, "Ban tashi lafiya ba, jikina babu sauƙi, in har ba ƙyale Praveen ku ka yi ba, ban ji daɗin yadda kuka buge shi ba, ban yi zaton haka daga gare ku ba."

"Ina so nasan taƙaitaccen tarihin rayuwarki da ɗan uwanki Praveen." 

"Idan na fada maka za ku yafe mana?" ta yi narainare da idanunta.

murmushi ya yi batare da ya furta mata kalma ba.

"Ni ɗiyar uncle dinsa ce, Mun taso a gidan marayu, bamu da asali bamu da dangi, a bakin Praveen na ji labarin abun da ya faru da danginmu, saboda ni a lokacin yarinya ce ban mallaki hankalina ba, sanadin zuwa biki danginmu suka yi hatsarin jirgin ƙasa gobara ta kama, mutane da yawa suka rasa rayukansu, a lokacin Praveen shi ya goya ni a bayansa ya daka tsalle ya duro daga cikin jirgin, muka faɗi ƙasa duk mu ka ji munanan raunuka har muka fita hayyacin mu, ƴan sanda ne suka kai mu asibiti, bayan da muka samu lafiya, sun tambayi Praveen meya faru? Bayan daya fada masu, sun tausaya mana sun kuma jinjinama Praveen da ya iya ku6utar da mu daga cikin jirgin ƙasan.


Bayan da muka samu lafiya suka mika mu gidan marayu. A rayuwana bani da gatan da ya wuce Praveen, shine uwata shine ubana, shine dangina, kuma shine komai nawa, bamu samun kulawa a gidan marayun, ba abinci mai kyau, ba sutura mai kyau, Idan gwammanati ko masu kuɗi suka kawo mana tallafi, bamu sani, masu kula da gidan marayun ne suke cinyewa sai su bamu kaɗan wanda ba zai ishe mu ba, Praveen shi yake fita ya yi aikin ƙarfi don ya sama mana abincin da zamu ci, da suturar da zamu sanya, idan bani da lafiya Pravin shi yake nemo kudin da zai kaini asibiti.."

 Sir Mubarak dake sauraronta zuciyarsa ta karaya tun kan ya ji ƙarashen labarin su.

"Kwatsam muna zaman mu lafiya a gidan marayun, sai ga wani attajiri ya zo zai yi adopting, tun da ya ɗaura idanun shi akaina ya kwallafa rai ya ce ni yake so a bashi, masu kula damu su ka shawarce shi ya dauke mu mu biyu ni da ɗan uwana ya nuna kin amincewarsa.


A lokacin Praveen baya kusa ya fita neman kudi.


Haka suka bashi ni, na dinga kuka ina kiran sunan dan uwana Praveen.


Basu saurare ni ba, suka nuna min fin ƙarfi gurin ɗaukana ina turjewa suka tura ni cikin motar mutumin.


A dai dai lokacin da motar zata tafi sai ga Praveen ya dawo, ta window glass din motar mutumin na hango sa, na dinga kwala masa kira cikin sa'a ya hango ni, hankalinsa ya tashi ya bi bayan motar mu a guje.


Tafiya muka yi mai tsayi, Praveen bai daina bin motar ba.


Har muka ƙaraso gidan mutumin, ya fito daga mota ya ɗauke ni ya shiga dani ciki, na yi zaton ya yi adopting ɗina ne don ya raine ni tare da iyalinsa, ashe mutumin banza ne, ya dauke ni ne don biyan buƙatar kansa, a lokacin da yake kokarin keta min haddi, Praveen ya ritsa da shi, da ya ke yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, cikin fushi ya dauki kwalbar giyar da mutumin ya sha ya aje akan table, ya kwaɗa masa a saman kansa tare da caccaka masa a cikinsa har saida ya kashe shi.


Hankalinshi ya tashi da ganin abun da ya aikata, cikin sauri ya goya ni a bayanshi, inata kuka ya gudu da ni, da kuɗin hannunsa ya yi amfani muka koma Delhi da zama, gudun kada asirin mu ya tonu a gane mu muka kashe shi.


Bamu da kowa a Delhi, babu wurin kwana, sai dai mu ra6a a wani gidan abinci, anan muke kwana, idan gari ya waye masu kuɗi suka zo cin abinci, Praveen ya kan goge masu motocinsu su biya shi kudi, da waɗannan kuɗin ya ke yin amfani gurin biya mana buƙatunmu, wani lokacin har bara yake yi amma ni bai ta6a bari na fita nema mana kudi ba, shi ya ke fafatuka ni sai dai in ga ya siyo abinci mai rai da lafiya da suturar sanyawa, daga baya madam mai restaurant din ta ɗauke shi aiki, har ta bamu ɗakin da zamu dinga kwana a ciki."


lokacin da ta ƙarasa masa labarin sai ta fashe da kuka.


Sir Mubarak ya tausayama rayuwar su, musamman ita, saboda ya fahimci batasan komai da Praveen ya aikata ba.


"Me kika sani game da auran shi da Saratu?"


"Mun fara soyayya ni da shi tun yana da shekara ashirin, ni kuma ina da shekara goma sha biyu, soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu, amma saboda bamu da halin da zamu yi aure yasa muka jinkirta, to a lokacin da ya ƙara girma ya kai shekara ashirin da biyar, yana da abokai da manyan mutanan da yake yi ma aiki suna biyan shi kuɗi, akwai lokacin da ya zo min da maganar zasu tafi neman kudi shida abokansa, na saka rigima akan kar ya tafi ya bar ni, ya dinga lallashina, har ya samu na amince ya kai ni gurin madam me restaurant, ya bata kudi masu yawa ya ce ta kula masa da ni. Tun bayan da Praveen ya tafi ban ƙara jin ɗuriyar shi ba, kullum sai na yi kukan rashin shi, bana jin dadin rayuwata, da shi nake kwana da shi nake tashi, kullum cikin sa ran ganin shi na ke yi, madam din dake kula da ni ita ke lallashina idan na fara kukan rashin shi. Unexpected wata rana sai gashi ya kira madam a waya ya ce a bani mu yi magana, na yi murna da jin muryarshi ya lallashe ni ya ce in ƙara haƙuri zai dawo mini da abun mamaki, har ya ce zai dinga turo min kudi in sayi duk abunda nake so, tun daga ranar da ya kira kullum sai ya kira ni a wayarta mun gaisa, inta tambayar shi yaushe zai dawo na gaji da jiran shi, still hakurin ya ke bani Lokaci ɗaya rayuwata ta sauya tun da Praveen ya fara tura ma madam kudi, ta sanyani a makaranta, ta siya min surutu masu kyau, komai da zan buƙata siya min take yi, na dinga jin dadi Praveen ya yi kudi zamu daina shan wahala. Wallahi Yaya Mubarak ni bansan Praveen ya yi aure ba, bai fada min ba, ban ma san baya a ƙasar India ba, tsawon lokaci bai waiwayi Delhi ba.


Ranar da ya dawo na yi murnar da bazata misaltuba, nayi mamakin sauyawar shi, yayi min kyaun da bai ta6a yi mini ba, ya zama ɗan gayu mai arziƙi, madam kanta tasha mamakin arzikinsa, har biyayya take masa sau da ƙafa saboda kudinshi.


Koda na tambayesa tayaya akai ya samu arziƙi? Nan ya fara bani hakuri na ce masa meyasa zai bani hakuri kawai ya bani amsar tambayana.


A nan yake faɗa min, ya yi mini ƙaryar sun je neman kudi shi da abokansa, gaskiyar magana ba haka bane, tafiyar da ya yi batare da abokansa ya yi ta ba, Allah ne ya haɗa shi da wani mutun mai arziƙi ɗan kasar Nigeria ya zo ganin ƴarsa ne dake karatun Medicine anan Delhi, shi kuma ya ta6a taimakon yarinyarsa har ta ji dadi ta nuna tana son su ƙulla abota, lokacin da baban yarinyar ya zo kawo mata ziyara saita haɗa shi da mahaifinta don su gaisa, bayan da suka gana da mahaifinta ya tambayesa su wanene danginsa? Yana karatu? Ko ya fara aiki? Sai ya faɗa masa baida kowa, har ya bashi labarinmu, mutumin ya tausaya masa ya ce zai taimakesa da aikin yi, da shi da ƴar uwarshi amma sai in har ya amince zai auri ƴarsa da ke son shi.


Ya ce mini saboda baya son ya rasa damar da ya samu, kuma yana son rayuwar mu ta inganta, shiyasa ya amince ya bi mutumin da ƴarsa Nigeria, a can aka ɗaura musu aure


A lokacin da ya bani labarin na ji kishi mara misaltuwa, zuciyata ta karaya amma da ya lallasheni ya faɗamin baya sonta, ya aure ta ne saboda mu samu dangin da zamu jingina da su, mu kuma samu arzikin da zamu wadata kanmu, na ce na amince amma bana so ya yaudare ta, saboda na ji ya ce baya son ta ya aureta, kuma ya taimaki rayuwata da tashi, kada ya nemi kudi ta haramtacciyar hanya, kada ya aikata laifin da zai jefa rayuwarmu cikin wahala, komai zai yi a rayuwa kada ya zalunci wani, nasihar da nake yawan yi masa kenan.


To daga baya ne ya zo zai tafi da ni Nigeria, a lokacin mun yi aure har ma na haifi yarona Naufal da baifi shekaru goma sha ɗaya ba a lokacin, ita kuma matar tasa ta Nigeria tana da ƴa'ya uku a lokacin, duk da ban ta6a ganinsu ba amma ina ganin hotunan su da videos dinsu a wayar shi duk idan ya zo. Ina son ƴa'yanshi sosai saboda ina yi masu kallon yan uwana kuma danginmu....


"Lokacin da Praveen ya zo da ni Nigeria, bai fara kaimu estate ɗinku ba, sai ya kaimu wani gida ya ce in fara zama a ciki, satin mu ɗaya a gidan Naufal ya yi rashin lafiyar da ta yi silar mutuwarshi, a lokacin har mun kai shi asibiti amma ya riga da ya mutu, na yi kuka kamar raina zai fita, har yau bazan manta raɗaɗin da na ji ba, na rasa Naufal.." Ta faɗa tana share hawayen ta.


Sir Mubarak ya ce, "Bamu san komai game da yaron ki ba, bayan da ya rasu su wanene su ka yi jana'izar sa?"


Cikin shesshekar kuka ta ce, "Bayan da muka je asibitin suka tabbatar mana da mutuwar sa, na dinga kuka kamar raina zai fita, docs da nurses suka dinga lallashina a lokacin ma bana jin harshen hausa ban san me suke cewa ba, sai idan Praveen ya fassara min da indiyanci nake fahimtar me suke faɗi, a ƙarshe na fita hayyacina na yanke jiki na faɗi a sume, ban ƙara sanin meke faruwa ba, lokacin dana farfaɗo na ganni a gadon asibiti kwance ga Praveen a gefe, cikin ruɗu na tambayesa da gaske Naufal ya mutu ko mafarki na yi? Ya ce min inyi hakuri ba mafarki bane, da gaske Naufal ya rasu, yau sati ɗaya kenan bana a hayyacina, harma sunyi jana'izarsa, sun ƙone gawarsa a crematorium kamar yadda muke wa mamaci a al'adarmu ta hindu, bazan iya misalta maka halin da na shiga ba a lokacin.


Bayan rasuwar Naufal da wata ɗaya, ya ce zai kawo ni gurin dangin matarsa, amma yana so ya gargaɗe ni kar in kuskura in faɗa ma wani akwai aure a tsakanin mu, idan ba haka ba, zai rasa auran shi, kuma zasu kai ƙarar mu kotu.." 


Ya yi min barazana sosai, ya ce duk abun da ya faɗa akaina in amsa da haka ne na amince masa, ranar dana fara tsintar kaina a cikin estate ɗinku bazan misalta farin cikin da na ji ba, duk da wasu basu kar6e ni da hannu bibbiyu ba, waɗanda nake ta zumuɗin gani saida na yi danasanin haɗuwa na da su saboda ƙyarar da suke mini. Hajiya Saratu ta tsane ni, ƴa'ƴanta ma sun tsane ni, basu san ni auntyn su bace, kuma ni kaɗai ce dangin ubansu da ya rage a duniya, amma na yi masu uziri komai da ya faru Praveen ne sila, da tun farko ya faɗa masu matsayina a gurin su ya kuma daraja ni da ba su tsane ni ba, kuma hada ƙarin muna zaune a gidanku shi ya ja min ƙasƙanci a gurinsu. Kuma wlh ya so ya maida ni gidansa amma ni na nuna bana so saboda na saba da ku, ina son ahlinku, na ɗaukeku kamar dangina da na rasa..."


Bata ƙarashe maganar ba, ta ji ya saka hanky kan fuskarta, a hankali yake share mata hawayenta, idanunsu a cikin na juna, duk sai ya ji ba daɗi, ya yi danasanin marin da ya yi mata, kuma da ya san bata da sanya hannu da ba abun da zaisa ya tuhume ta.


"Ya Mubarak, ka taimaka ma rayuwarmu, ku yafe mana, ku bar mu mu ci gaba da zama tare da ku, zamu gyara kuskuren mu"


 Murmushin takaici Sir Mubarak ya yi.


"Ki faɗa min meyasa kika bi Praveen kuka gudu? Kinsan laifin da ya aikata..?" Gabanta ne ya faɗi rass!


Cikin rashin nutsuwa ta fayyace masa komai da ya faru.


Girgiza kai ya yi cike da takaicin ƙaryar da Praveen ya yi mata.


"Hmmmm, Praveen ba gaskiya ya faɗa maki ba, ba Hajiya Saratu bace me laifi, batasan da aure a tsakanin ku ba, kuma ba ita bace ta tura maku aljanu ba, hasila ma tsoron hulɗa da mai aljanu take yi balle har ta yi mu'amala da su, bayan haka yanzu haka da nake maki magana, Hajiya Saratu tana a kwance gadon asibiti.."


 Cikin ruɗu da tashin hankali ta furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un! Meya faru da ita? Meke damunta? Meyasa praveen ya yi min ƙarya ne? Ni dai Allah Ya sa bashi bane ya yi silar kwanciyarta gadon asibiti ba..!"


Ta faɗa da damuwa akan fuskarta.


"Ya Mubarak ka fadamin meke faruwa? Wani laifi Praveen ya aikata ma ku? 


Shiru ya yi yana sauraron muryar Owais dake yi masa magana ta cikin earbuds din dake a maƙale da kunnansa, komai da suke tattaunawa yana sauraron su, Sir Mubarak ne ya kira shi don ya ji komai.


Cikin harshen yarbanci ya ce, "Owais, ina fata ka ji komai?"


On the Other hand Owais ya ce, "Na ji Uncle, Hajjaty bata da laifi, bata san komai da Praveen ya aikata ba.."


"Ta nemi in faɗa mata meke faruwa kana ganin yakamata mu sanar da ita?"


"Uncle, ka fadamin ta yi 6arin ciki, nasan i war haka jikinta babu lafiya, jininta zai iya hawa, a yadda na ji shaƙuwarta da Praveen, idan ta ji abun da ya aikata zata shiga mawuyacin hali ne, amma me zai hana mu bari sai ta ji sauƙi sosai?"


"Owais, ka yi magana mai ma'ana, na gode da shawararka."


Daga haka suka yi sallama ya mayar da dubansa ga hajjaty, dama jiran shi take yi ya gama wayar,


"Pls ka faɗamin wani laifi ya aikata? Dan Allah kada ka ce zaka 6oye min, na fada maka bani da kowa in ba Praveen ba, shine gata na, bana so na rasa shi! kuma me ke damun Hajiya Saratu?"


Numfasawa ya yi kafin ya ce, "Allah shine gatan bawansa Hajjaty, zan faɗa maki amma ba yanzu ba, ki fara samun lafiya tukunna, sannan karki damu da maganar hajiya Saratu, ta ji saukin jikin ta yanzu."


In a cool voice ta ce, "Shike nan zan jira har zuwa lokacin da zaka fadamin! Amma dan Allah ina Praveen ya ke?"


"Karki damu, Praveen yana a wurin mu, kuma mun sanya doc sun yi masa treatment na rauninsa."


"Zan iya ganin shi?"


"A'a, ba yanzu ba." Gyaɗa  kai tayi, "Shikenan..."


"Amma yana inane? Kuma ni a ina nake?"


Bai amsa mata ba sallamar Nurse ta katse su, mikewa ya yi ya nufi nurse din, "Pls, ki ci gaba da bata kulawa, duk abun da take bukata ki yi mata shi, ina so ta samu cikakkar lafiya."


"Okay sir, zan yi iyakar bakin kokarina.." Juyawa ya yi tare da kallon Hajjaty da ke kallon shi.


"Zata kula da ke, ko me kike bukatar ci ko sha ki tambaye ta zata yi maki, idan kika zauna salin alin, Praveen zai kasance cikin ƙoshin lafiya..  " 


tana kokarin yi masa magana ya sa kai ya fuce daga ɗakin, kamar ta fasa ihu..


"Pls, baiwar Allah, ki fadamin ina ne nan? Meyasa ya kawo ni? Kuma meke damuna ne?"


"Am sorry ma'am, bai bani izinin in faɗa maki inda kike ba, bansan komai ba, abun danasani ya kira ni ne don in duba lafiyar ki.." Shiru ta yi zuciyarta duk ba dadi.


To fa manema labarai sun fara dandazo a layin Obie Estate sun haɗa uban cunkuso, burin su kawai su samu damar ganawa da ahalin Obie don su samu na ɗaukar rahoto, ba dan dakarun sojojin da ke a kewaye da Estate din ba da tuni sun 6urma ciki saboda tsabar zaƙuwa, masu ruwa da tsaki a mulkin ƙasar, sun kasa sun tsare suna jiran jin meke faruwa? 


Haka zalika ƴan jami'iyar Jdp da App sun ƙagu da su san meke faruwa, saboda duk sun ji labarin kewaye gidajen ƴan jam'iyarsu da soldiers suka yi, dama cikin yan kwanakin nan mutane sun fara tsegumin rashin jin ɗuriyar baba Obie, basu ji labarin yana a ƙasar ne ko ya yi tafiya ba, haka Alhaji Musa ma sun ji shiru babu duriyar shi, Ɗan-iya da ya fi kowa baki kusan kullum suna samun labaran yan siyasa a bakinshi ta gidajen radio da shafukansa na social media shima sun ji shiru ba labarinsa.


Saboda yadda mutane ke kiran layukan su a waya yasa suka kashe wayoyin su.


Alhamdulillah Hajiya Saratu ta samu lafiya, har an sallame ta, amma momma har yanzu memory ɗinta bai dawo ba.


A main Falo na gidan baban suka haɗu gaba ɗayan su domin tattaunawa game da shawarar ya zasu yi da jama'ar da ke jiran su ji daga bakin su? Kowan nan su yana fargaban asirin mahaifinsu ya tonu, saboda gudun tozartar da zai yi da kuma su kansu, suna zullumin mutuncinsu da zai zube a idon duniya.


Gaba ɗaya sun nuna basu san a fallasa sirrin, saboda basu son asirin shi ya tonu a bainar jama'a, suna jin fargaban abun da zai biyo baya, da kuma halin da uban nasu zai shiga, kuma basu son a gurfanar da shi gaban kotu, sun ƙwammace su bashi poison ya sha ya mutu, saboda basu son ma su ga tashin hankalin da zai fuskanta, ƙwara ya mutu su san babu shi a duniyar, duk da mutuwar ba hutu bace a gare shi, amma su a wurinsu ƙwara tun da ba a gabansu zai fuskanci abun da ya shuka cikin kabarinsa ba, amma in yana a raye sun san ba ƙyale shi za'a yi ba, dole ya fuskanci mummunan hukunci mai tsanani, ba zasu iya jure ganin halin da zai shiga ba, kuma ba zasu iya kashe shi da kan su ba, sannan basu son ya kashe kan shi, sun rasa ya za su yi da shi? 


Duk da fushin da suke yi da shi hakan baisa sun daina jin ƙaunar shi ba, kwata kwata ba su son ya wulakanta a idon duniya, duk da sun san ko sun rufa mashi asiri hakan ba zai hana asirin shi ya tonu ba, sannan Allah yana sane da komai, ko sun rufa masa asiri wallahi ba zai tsira ba tun a gidan duniya sai ya ga sakayyar abun da ya aikata, sai Allah ya kamasa, tayaya ma zasu goyi bayan rufawa azzalumi asiri? Bayan sun san Allah baya a tare da azzalumai, sun kuma san hakan ba daidai bane zama su ja ma kansu ne, bayan haka idan har suka nuna son kai, suka nemi su rufa masa asiri ko su 6oye shi, Allah ba zai bar su ba su kansu.


Hajiya Saratu ta yi kuka tamkar ranta zai fita, ta dinga magiya tana roƙon yayyan nata akan kar su tona asirin Baba, kada su miƙa shi ga hukuma, su taimaketa su taimaki rayuwarta, idan ta rasa baba ina zata saka ranta? Su bar shi in har ba so suke zuciyarta ta buga ta mutu ba, lallashinta suka dinga yi suna bata hakuri tare da tunasar da ita akan kuskuren rufa masa asiri, aya da hadisi suka dinga janyo mata inda Allah da manzonSa suka yi magana akan azzalumai amma Hajiya Saratu ta burkice masu, kwata kwata bata ganewa ita kawai mahaifinta take so, ta kasa ganin laifinsa, tama ƙi yarda cewa ya aikata, idanunta sun rufe akan son baban nata, tausayin shi ta ke ji, bata son ya tozarta kuma batason a ta6a lafiyar shi, har faɗi take ita ta yafe mashi abun da ya yi mata suma su taimaka su yafe mashi, sannan kada su bari a raba ta da shi, tun da yana da sihiri ya 6ace kawai ya nisanta kanshi da duniyar mutane ya je can ya yi rayuwarshi, lokacin da take faɗin maganganun nan tana kuka mai tsuma zuciya, ba ƙaramin karya masu zuciya ta yi ba, tsananin tausayinta da kaunarta ne ya kama su.


 Sun ga juriyarta da haƙurinta, ta basu mamaki baiwar Allah, duk irin zaluncin da baban ya yi mata ita bata gani ba, tama riga su furta ta yafe mashi duniya da lahiri, babu wanda bai zubar mata da ƙwalla ba a cikin su.


Ta fama masu raunin dake a zuciyoyinsu, in har zasu biyewa son zuciyarsu da halin da Hajiya Saratu take a ciki to kuwa ba zasu bari baban nasu ya fuskanci hukuncin da ya dace ba.


A ƙarshe dai gaba ɗaya basu da wata mafita da ya wuce su miƙa shi ga hukuma, ba yadda suka iya. Sheikh Imam da ya kawo mazu ziyara ya ji komai da ya faru shi ya gargaɗesu ya ja masu kunne akan kar su kuskura su biyewa son zuciyarsu, su yi hakuri su rungumi ƙaddara, su manta cewa shi mahaifinsu ne, su dinga tuna zaluncin da ya yi masu da al'umma ta hakane zasu samu kwarin gwiwar fallasa shi, amma idan suka yi kokarin rufa masa asiri don gudun kada duniya ta ji toh su sani Allah yana a sama yana kallon su, bazai taba barin azzalumi da wanda ya taimaki azzalumai ba, har da nasiha sheikh Imam ya yi masu. A ƙarshe ba yadda suka iya, don dole suka miƙa wuya, a halin yanzu basu da burin da ya wuce babansu ya mutu kafin lokacin da za'a gurfanar da su a gaban kotu 😭


Chief Owais ne ya fara sakin videos din da suka ɗauka na Prisoners a shafukan hukumarsu na Instagram, Facebook da Youtube channel dinsu, wanɗanda ke da mabiya miliyan dubu ɗaruruwa daga kowani sassa na duniya.


Yayin da Director Ziyad ya tutturawa manajojin Obie News Network labarin kurkukun ƙaddara da ya rubuta shi a wayar shi tun daga farko har ƙarshe, komai da ya faru a gidan kurkukun kaddara daki daki ya rubuta, ya basu umarnin su fara buga labarin a jaridarsu, sannan su kuma yaɗa shi ya shiga ko'ina na duniya.


Yana a gidan radion nasu kiran Chief Owais ya shigo wayarshi, bayan ya ɗaga ya ce yana gayyatar gaba daya Press corps na ONN, da ƙarfe ɗaya su halarta a Isod Headquarter zasu tattauna da su.


Lokaci na cika motocin shahararrun ƴan jarida suka fara tururuwar shigowa isod headquarter.


Wasu ruƙe da Camrecorders, wasu sun ruƙe Michrophones..


A katafaren Comference Room na headquarter din suka gudanar da taron..


Gaba daya senior agent suka hallara, tun daga DG, CI, Coo, Senior Agents, U.s armies, General Noah, kusan duk mai ruwa da tsaki a binciken Kurkukun Ƙaddara sai da ya hallara a comference room din Taj ne kadai bai samu zuwa ba.


A saman kujeru kowan nan su ya zauna yayin da manema labarai suka kewaye su.


Bayan sun gabatar da junansu, U.s Armies ne na farko da suka fara bada labarin farkon haɗuwar su da Prisoners din da suka ku6uta daga kurkukun kaddara har suka haɗu da su a dajin evil forest.


Bayan sun gama, Chief Owais ya daura da nashi tun daga farkon ta yadda U.s Armies suka tuntu6e shi da case din yaran, ya bayyana masu yadda ya ji farkon da abun ya riske shi, bayan ya ɗan dakata team members din shi suka ɗaura da nasu bayanin game da Kurkukun kaddara..


Daga bisani Chief Owais ya bayyana masu ta yadda suka fara gano su wanene Elders, Ya ilahi! Ilahirin press corps din dake agurin saida suka razana matuƙa, jin abun da basu ta6a zata ba, hankalinsu ya fi karkata akan Chief Owais, saboda kansu ya ɗaure sosai, mamakin su ta yadda har ya iya tonawa kakansa asiri da kan shi!!!


 Gaskiyarshi ta yi matuƙar razana su. 


Lokacin da yake lissafa sunayen Elders, tsantsar rudani ne da razana suka bayyana ƙarara a cikin idanun manema labaran dake a kewaye da su, zan iya cewa tun da suke daukar rahoto basu ta6a daukar labari mai girma da razanarwa da kuma karya zuciya irin wannan ba! Abun ya ta6a su matuƙa.


Duk wani abu da suke tattaunawa kaitsaye mutanan duniya suke kallon shi, wasu ta tv dinsu, wasu ta radio, wasu ta facebook live, wasu a instagram live, kai ko'ina fa labari ya bazama


Bayan da suka gama fallasa komai da ya kamata mutane su sani, manema labaran suka fara yi masu tambayoyi suna amsa masu ba tare da jin shakka ba.


"Yallabai, ya kuka ji kaida ahlinku lokacin da asirin kakan ka ya tonu?"


"Yallabai, wani hali kuka shiga da kuka ji kakan ku shine Shugaban kurkukun kaddara?"


"Yallabai zamu iya sanin ina Elders suke a halin yanzu? 


"Yalla6ai, ba ku tunanin fallasa asirin kakanka da ka yi zai shafi ahlinku da muƙaman su?"


"Yalla6ai gaba ɗayan mu mun kasa yarda da bun da kunnuwanmu suka jiyo mana, saboda rudanin da muka shiga, shin da gaske kakanka dattijon arziƙi yana da sa hannu? Mutum mai ƙima da daraja a duniya, wanda kowa ke girmamawa?


"Yallabai ko zamu iya sanin ina fursinonin kurkukun ƙaddara suke? Mun dai ga video dinsu amma bamu san a wani hali suke ba, da buƙatar a bamu damar tattaunawa da su."


"Sir, ina Zaheer Tajuddeen da Uzair? Zamu iya ganawa da su?  Saboda ƴan jaridar mune ta jihar Joss da muka nema muka rasa tsawon shekaru, muna ta neman su ruwa ajallo!


Tambayoyi iri iri ƴan jarida ke yi mashi.


A lokacin Owais ya yi rauni, idanunshi sun kaɗa jawur, yana mai jin baƙin cikin fallasa asirin Grandpa dinsa da ya yi, amma ya zai yi? Baya da mafita da ya wuce wannan! Ya zama dole mutane su ji miyagun laifukan da ake aikatawa a doron ƙasa ko dan su ɗauki darasi, su kuma ƙara imani da tsoron Allah su kuma kiyaye kan su.


Gaba ɗaya kowa dake a gurin saida ya fahimci halin da yake a ciki, da ido abokansa suka dinga kwantar masa da hankali tare da dafa kafaɗunsa suna ɗan ƙarfafa mashi gwiwa don ya jure.


Ji yake kamar an ɗaura masa nauyin duniya akansa, dauriya kawai ya ke yi.


Cikin sanyi murya mai rauni ya soma magana cikin harshen turanci,


"Bazan iya misalta halin da family din mu suka shiga ba a lokacin da muka gano dasa hannun jagoran family dinmu, ko ban fada maku ba, kun sani, kowan nan ku zai iya ƙiyastawa a ranshi ya radadin abun yake idan wanda ka yarda da shi ya karya maka zuciyarka? Mun shiga mawuyacin halin da ba zai musaltuba! Ina fata mutane zasu yi mana adalci, kada su tuhume mu ko su zarge mu akan laifi da kakanmu ya aikata, kuma kada a juya mana baya ko a tsangwami ahlinmu saboda bamu da laifi, bamu san komai ba saida asirinsa ya tonu, in har aka daura mana laifin kakanmu zamu shiga mawuyacin hali fiye da wanda muka shiga. Ina roƙon mutane da su agaza mana, su tausaya ma rayuwar ahlinmu, kada wannan abun ya zama silar da za'a dinga cin zarafin mu! Komai da ya faru da mu, muƙaddari ne daga Allah, dama can rubutacce ne, kamar yadda bamusan komai ba, toh haka kowa ma zai iya faruwa da shi. Dalilin da yasa na fito bainar jama'a tare da abokan aikina na fallasa komai saboda hakkinku ne ku sani, bamu 6oye maku komai ba, saboda muna so ku ji kuma, don ku ƙara imani ku kuma ɗauki darussa daga labarin kurkukun ƙaddara, duk kuma wani mai aikata wani laifi a 6oye ya ji tsoron Allah ya daina tun kafin asirin shi ya tonu"


"Akwai wanda ya tambaye ni, ba mu tsoron fallasa asirin kakanmu da muka yi ya shafi ahlinmu da muƙaman su?"


Ya faɗa da murmushi akan fuskarshi, girgiza kai ya yi ya ce, "babu tsoro ko fargaba a tare da mu, kafin mu fallasa asirin saida muka yi wannan tunanin, amma bashi ne damuwar mu ba, saboda ba duniya muka zo nema ba, komai da muka mallaka a gidan duniya zamu bar shi, in har za'a yi mana adalci, bai kamata a tuhume mu ko a ɗaura mana laifin da bamu muka aikata ba, laifin wani baya shafar wani, bayan haka koda wasu sun zarge mu akan abun da ya aikata ina so su sani koda zai shafi muƙamanmu ba zamu damu ba, saboda idan muka mutu daga mu sai halin mu za a binne mu, muƙaman mu baza su cece mu ba, halinmu shi zai cece mu. Mun yi imani da Allah, kuma mun yi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, kuma mun san abun da ya faru da mu jarabawa ce daga gare shi, Allah shine shaidar mu, koda wannan abu zai shafe mu ba zamu damu ba, mun san dole akwai waɗanda ba zasu fahimce mu ba, akwai waɗanda kuma jiran rauninmu suke yi don su muzguna mana, to ina so su sani babu gudu babu ja da baya, ba zamu ta6a karaya ba, saboda Allah shi zai yi mana hisabi ba su ba, duk wanda yayi yunƙurin yin amfani da wannan damar don ya 6ata mana suna ko dan ya 6ata mana rai toh ya sani Allah yana kallonsa zai yi mana sakayya, akwai kuma ranar ƙin dillanci. Bayan haka, duk abun da kasan in akai maka ba zaka ji daɗi ba toh kada ka yi ma wani, kuma ka guji 6ata ran wanda baida abun dogaro da ya wuce Allah, ko don saboda fursinonin kurkukun ƙaddara yakamata mutane su san irin kalaman da zasu furta idan ba haka ba wani hali kuke tunanin zasu shiga? Idan ana fama masu raunin dake a zuciyar su? Da yawa waɗanda suka sadaukar da su iyayensu ne, wasu kawunnansu, wasu danginsu, na sani a cikin masu kallo na da sauraro na, akwai iyaye, akwai kawunnai, akwai yayye da ƙanne, kunsan ƙuncin da ake ji idan aka ta6a naka ko aka ci zarafinsa, da wannan nake roƙon kowan nan mu da mu kiyaye harshen mu, gaba ɗayanmu bamu ke da iko da kawunanmu ba, abun da ya faru da wani mara daɗi ka ji dadi ko ka yi dariya kaima baka wuce ya faru da kai ba, don haka idan har ba zamu faɗi alkhairi ba, ya fi mu ja baki mu yi shiru..." 


Kalaman Chief Owais ya ta6a zuciyoyin miliyoyin jama'a dake kallon su, ta ko'ina comments ɗin mutane ne ke ta yawo a social media..


"A halin yanzu, gaba ɗaya fursinonin da muka ku6utar suna a ƙarƙashin kulawar mu, in sha Allah zamu duba yiyuwar baku damar tattaunawa da su kaitsaye, bayan mun gama shari'ar Elders, bayan haka zamu buɗe shafukan da zamu dinga kawo maku duk wani abu da ya shafe su" CI ne ya amsa ma ɗan jaridar da ya yi tambayar..


"Elders suna a tsare hannun hukumar mu, ba zaku samu damar ganawa da su ba, har sai zuwa lokacin da za'a yi shari'ar su, zamu ci gaba da kawo maku bayanai game da su, ku ci gaba da bibiyar shafukan hukumar mu ta ISOD" Coo ne ya faɗa yana mai tabbatar masu da maganar shi.


A ƙalla saida suka shafe awa suna tattaunawa da manema labarai tun suna amsa masu tambayoyi da marmari har saida suka fara galabaita.


In a short time, labarin Kurkukun Ƙaddara ya bazu kamar wutar daji, ƴan jarida, gidajen talabijin, gidajen yaɗa labarai na duniya, da kuma shafukan sada zumunta sun cika da labarin kurkukun ƙaddara, BBC ne, Fox news channel, Cnn, msnbc, Newsmax, ko'ina zancen Kurkukun kaddara ake yi, labarin ya zama ruwan dare, Elders suna ta shan tsinuwar jama'a, DG da hukumarsu tana ta shan yabo daga bakunan al'ummar duniya, kowa ya jinjinawa kokarinsu musamman Dg da ya iya fallasa asirin kakansa, ya burge jama'a ya kuma siye zuciyoyin mutane, ta ko'ina yabonsa ake yi, mutane suna ta nuna tausayawarsu ga Prisoners, ba a ta6a samun labarin da cikin rana ɗaya ya samu billions of audience daga sassan duniya ba irin shi🔥


Ta ko'ina shafukan sada zumunta sun cika da hashtag


#JusticeForTheVictims#justicefortheprisonersoftheprison ofdestiny #RemoveThemFromPower#punishthem#justicemustbeserved#


Hada masu zanga-zanga ta online, wasu ma fitowa suka yi daga gidajen su, suka bazama kan tituna, inda suka buƙaci a yiwa fursinonin kurkukun ƙaddara adalci, a ƙwace wa Elders muƙamansu, a kuma gurfanar da su gaban kotu don su kar6i sakamakon laifukan da suka aikata.


Hukumomin Human Right na ƙasashe daban daban kama daga Uk, America, Saudi arab da sauran ƙasashe sun buɗe wuta akan a hukunta Elders daidai da abun da suka aikatawa yaran da ba su ji ba basu gani ba.


Haka zalika shuwagabannin ƙasashen ƙetare da aka samu ƴan ƙasar su cikin Elders da Prisoners suma sun buɗe wuta akan ba zasu lamunta ba, sun yi gargaɗi akan a gaggauta yankewa Elders tsattsauran hukunci a kuma mayar masu da yaran ƙasarsu da aka fitar, bayan haka zasu bibiyi shari'ar har sai sun tabbatar da anyi adalci, idan ba haka ba zasu ɗauki tsattsauran mataki.


Gaba ɗaya hankalin duniya ya dawo kan Elders da Prisoners, abun ba iya Nigeria ya shafa ba, saboda Elders ɗin da fursinonin akwai jinsin wasu nahiyoyin..


Waɗanda suka fi shiga tashin hankali dangin Elders, Mutane sun fusata hakan ya sa jinin su akan akaifa ya ke, neman su suke ruwa a jallo don su fanshe abin da aka yiwa fursinonin kurkukun ƙaddara, ba dan sojojin dake kewaye da gidajansu ba, da tuni mutane sun sanya musu fetur sun ƙone su, ko su saka masu bomb saboda yadda suka zuciya, burinsu su yi arba da ɗaya daga cikin su don su ƙone shi.


Lokacin da labarin abun da ke faruwa ya riski jam'iyar su Alhaji Musa, a lokacin ma suna tsaka da yin party meeting a conference room na headquarter dinsu, kwatsam sai ga kira ya shigo layin party leader ɗinsu Alhaji Bukar mai Guduma, bayan da ya ɗaga kawunsa ya ce su duba abun da ke faruwa a labarai.


Nan fa suka kunna news, hankalinsu ya tashi matuƙa sun razana da jin labarin kurkukun kaddara, babban tashin hankalinsu hada ɗan jam'iyarsu Alhaji Musa, shine abun da ya fi razanar da su ya kuma jefa su a ruɗani sosai, sun yi baƙin cikin kasantuwarshi ɗan jam'iyar su, ya ja masu tozarci da tsana daga al'umma dama basu da farin jini, wannan abun kunya da firgici har ina, gaba ɗaya sun yi Allah wadai da Elders, duk da baƙin cikin da Musa ya ƙunsa masu hakan bai hana sunyi farin cikin jin cewa hada Baba Obie a ciki ba, dama da haushin shi a cikin zuciyarsu, tun lokacin da ya bar jam'iyarsu ya kafa tashi jam'iyar suke ta neman hanyar da zasu 6ata mashi suna su kuma lalata jam'iyar tashi, sai gashi cikin sauƙi yanzu sun samu damar da zasu 6ata ahlin Obie da jam'iyar su.


Haka zalika ƴan jam'iyar APP ta su baba Obie, sun tashi da mummunan labarin da ya karya zuciyoyinsu, ya haifar masu da matsanancin tashin hankali da damuwa..


Haƙiƙa baba Obie ya karya zukatan mutanan da suka yarda da shi, kowa idan ya ji labarin da farko sai ya sanya kokwanto akan ba zai iya aikatawa ba, amma daga sun ga videos ɗin Chief Owais da yake kora jawabi sai jikinsu ya yi sanyi lakwas, saboda sun san jikanshi ba zai yi mashi ƙarya ba.


Bangaren masu ruwa da tsaki a mulkin ƙasar sun razana da jin labarin kurkukun kaddara, sun kuma ɗimauce da jin cewa dattijon arziki uban maza, mutun mai daraja da ƙima a idon duniya shine shugaban kurkukun kaddara, kan wannan al'amarin har zaman tattaunawa suka yi a majalissa kowa ya tofa albarkacin bakinsa kan al'amarin, wasu suna goyan bayan a tsige ƴa'ƴansa daga muƙamansu yayin da wasu suka ƙi goyan bayan a yi hakan saboda basu yi wani laifi da zai sa a sauke su daga kan power ba, majority ɗinsu suna goyan bayan ahalin Obie ɗari bisa ɗari, kaɗanne suke nema su dangana su da laifin uban su. Har ƙuri'a suka jefa cikin kaso ukku kaso biyu suna goyan bayan  ƴa'ƴan Obinna.


Bari mu koma bangaren Iyalin Alhaji Musa mu ji meke faruwa da su? 


Da farko sun 6oyewa Hajiya Sarah abun da ke faruwa, kwata kwata suka ƙi sanar da ita, tayi tayi da su su faɗa mata meke faruwa sun ƙiya, kowa fargaban sanar da ita yake yi saboda suna jin fargaban halin da zata shiga, ba irin magiyar da bata yi masu ba, har kuka ta yi masu akan su faɗa mata abun da suke 6oye mata, idan ma mutuwa Musan ya yi kada su ji shakkun sanar da ita, zata fahimce su kuma zata rungumi kaddara, still suka ki sanar da ita, tsawon kwanaki sun barta a duhu, damuwa ta hanata sukuni, ta riga da ta sa ma ranta cewa wani mummunan abu ne ya faru shiyasa suke shakkun su sanar da ita, tun lokacin da sojoji suka kewaye gidan da kuma fitar da suka yi da daddare batare da saninta ba, abun da ya fi damun ta rashin dawowar Alhaji Musa gidan, tsawon kwanaki bata ji ɗuriyarshi ba, layukan wayoyinsa duk a kashe kum baya nemanta, duk wanda ta kira cikin abokan huldarsa da ta sani don ta ji ko su ya tuntu6e su sai suce mata a'a basu ji daga gare shi ba.


Daga ita har Zeenatu sun damu, sai da ta kaiga ko abinci basu ci sosai, basu bacci, ko office ta daina zuwa komai nata ya tsaya cak..


Tsananin tausayin su ne kullum ya ke ƙaruwa a cikin zukatan su hajiya Layla, musamman da ta dinga bin su ɗaki ɗaya bayan ɗaya tana roƙon su akan su sanar da ita meke faruwa? 


Ta je ɗakin Benazir tana kuka ta roƙe ta ta faɗa mata amma ta ce ta yi hakuri ba zata iya ba, saboda bata son ta zama silar da zata shiga mawuyacin hali.


Bayan ta fito daga dakin Benazir ta je dakin Dr Shureim shima ta roƙe shi akan ya faɗa mata, amsar da Benazir ta bata irinta shima ya bata, kamar sun haɗa baki.


Zuciyarta ta sosu, still bata yi fushi da su ba, ta je ɗakin hajiya Layla ta roke ta itama ta ce ta yi haƙuri sanin bashi da amfani, bazata iya fada mata ba..


Kowa ta tambaya amsa ɗaya suke bata.


Lokacin da haƙurinta ya ƙare, ta kira su dukan su a main falo ta ce kodai su faɗa mata abun da suke 6oye mata ko kuma ta tafi tabar ƙasar tare da Zeenatu, ba zasu sake ganinta ba har abada, zata koma gurin family ɗinta.


Hankalinsu ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda sun san muddin ta koma gurin danginta, daga ita har Zeenatun zasu iya canza addini su koma nasu, dama ta ta6a faɗa masu iyayenta sun yafe ta daga family dinsu saboda auran za6inta da ta yi, tun farko sun nuna basu son ta auri baƙar fata wanda ba ɗan addininsu ba amma ta bijire masu ta auri Musa ta baro kowa nata.


Wannan maganar da ta yi ne yasa suka yanke shawarar sanar da ita komai dake faruwa.


Gaba ɗaya suka haɗu wurin fayyace mata komai tun daga kan cin amanar da Musa ya yi mata ya rabata da jinjirarta da kuma munanan ayyukan da yake aikatawa.


Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..."


Kalmar ƙarshe da suka ji ta furta nan take ta yanke jiki ta faɗi, gaba daya suka rufa akanta suna ambaton sunanta haɗi da bubbuga jikinta don ta farka.


Cikin sauri Dr. Shureim ya dauko ruwa suka yayafa mata shiru bata farfado ba, a ƙarshe suka yanke shawarar kaita asibiti, suna a wannan halin sai ga motar hajiya Laura ta shigo gidan, a haukace ta fito daga motar jikinta na 6ari ta nufi ciki don ta faɗa ma yayanta abun da ke faruwa, lokacin da ta shigo sun yi mamakin ganinta, matar da kwata kwata babu ruwanta da su saboda rashin jituwar ta da hajiya Layla yasa ta ɗauke ƙafarta da zuwa gidan, suna ganinta suka fara tambayarta meke damunta? Ganin babu takalma a ƙafafunta, ɗan kwalinta ma a hannu ta ruƙe shi, cikin shesshekar murya ta ce ina yaya Musa? Tana son ganin shi! akwai abun da zata faɗa masa.."


Kwata kwata bata a nutsuwarta, ilahirin jikinta kerma yake yi, bata ƙare maganar ba, ta hango Hajiya Sarah dake a kwance kan floor ba numfashi Benazir ta rungume kanta a saman laps dinta sai yayyafa mata ruwa ta ke yi tana ambaton sunanta ta ƙi ta farka.


A ruɗe Laura ta tambayi me ke faruwa, kamar jira hajiya Layla take yi ta tambayi ba'asi aikuwa ta shiga zayyana mata komai dake faruwa, Alhaji Ubaid yanata ƙoƙarin dakatar da ita amma ta ƙi sauraron shi.


Tashin hankali ne tsantsa kan fuskar Laura, ita da ta zo kawo ma yayanta labarin abun da Obinna ya aikata, ashe shima yana daga cikin Elders ɗin wa'iyazubillah! Ta gaza yarda da abun da kunnuwanta suke jiyo mata, cikin ruɗu da gushewar hankali ta watsa da gudu ta nufi part ɗin yayanta tana fadin ba zai ta6a yiwu ba, hajiya Layla ƙarya ta ke yi mata, yayanta baya da sa hannu! Baisan komai ba, ƙazafi take yi masa dama tasan ta tsane shi.."


 bayan ta shiga part ɗinsa bata taras da kowa ba.


Ta zaro wayarta ta dinga kiran layukan wayarsa gaba ɗaya a kashe take samun su, nan fa jikin taƙaura ya yi la'asar saboda bata ta6a kiran sa ta ji wayarsa a kashe ba sai idan da dalili, zama tayi akan couch ɗin dakin, duk ta bi tasha jinin jikinta, gabanta ya shiga faɗuwa rass rass, tsoro da firgici suka cika zuciyarta.


Bakomai take ji ba fa ce tsoron kada maganar da hajiya Layla ta faɗa mata akan yayanta ta tabbata gaskiya ne, ya za ta yi? Bata da wani gata da ya wuce shi, da shi ta dogara, shine shaƙiƙinta abun tunƙahonta, bata tunanin zata jure tozarci da kunyar duniya. A ƙalla ta shafe awanni tana jiran dawowar yayanta don bata fidda ran zai shigo gidan ba.


Jin shiru bai dawo ba ya sa ta fito daga ɗakin, bata iske kowa ba, a bakin maids din gidan ta ji cewa sun tafi kai Hajiya Sarah asibiti.


Kwata kwata bata damu da halin da ta riski matar yayannata ba, ita kawai damuwar ta yayanta ya zo ta ji daga bakin shi in gaskiya ne abun da ta ji a bakin hajiya Layla.


 Har dare ya yi Musa bai dawo ba, ƙarshe a gidan ta kwana washe gari ta dasa zaman jiran shi, ba ci ba sha tun jiya rabon da abinci ya gifta ta makoshinta.


Kwana ɗaya da wuni mutanan gidan basu dawo ba, a lokacin Hajiya Laura ta sare da jiran yayan nata, kwatsam ta risƙi labarin kurkukun ƙaddara dake ta trending a social media, a nan ta ji cewa hada Alhaji Musa cikin Elders, kuma shine Jan Wuya mugun uban da ya yaudari ɗiyarsa, har labarin Unaizah ta karanta ta kuma ga hotonta da ke yawo a social media.


Batasan sa'adda ta saki wayar ta fadi ƙasa ta fashe ba, ƙunci da baƙin ciki suka cika zuciyarta, ta dinga kuka tana tsine ma yayan nata da ya jefa su a cikin musiba, a ƙarshe komawa ta yi cikin part ɗinsa ta kulle kanta, ta hargitsa ɗakin ta dinga zaƙulo kayayyakinsa tana watsarwa a ƙasa tare da  tattake su da kafafunta, kamar mahaukaciya sai sambatu ta ke yi tana ɗura masa ashariya, tana cikin halin kwatsam ta ji wani abu ya tokare ƙirjinta me raɗaɗin gaske, a gigice ta daddafe ƙirjinta da tafukanta, jikinta ya dinga kerma, cikin fitar hayyaci ta dinga zubda gumi nan take ta yanke jiki ta faɗi tana kakari still hannuwanta na dafe da kirjin nata, ga shi ba wani a kusa balle a yi gaggawar taimaka mata, bayan dan lokaci gaba daya ta daina motsi hannuwanta suka faɗi gefe 😳


A bangaren Hajiya Sarah tun ranar da suka kaita asibiti aka kwantar da ita, bayan gwaje gwajen da docs suka yi mata a ƙarshe sun gano abun da ke damunta, sakamakon mummunan labarin da suka gaya mata ne ya yi silar kamuwarta da anxiety attack, wanda silar hakan hawan jini da ciwon zuciya suka yi mata mugun kamu, wanda idan har likitoci basu iya ceton ta ba za su iya rasa ta ne.


Hankalinsu ya tashi matuƙa har sai da suka yi danasanin faɗa mata ganin mawuyacin halin da suka jefa rayuwarta, kwata kwata bata a hayyacin ta.


Basu tashi sanin suna a cikin tsaka mai wuya ba, sai da Tani ta kira Dr Shureim a waya ta faɗa masa sunga Laura a ɗakin Musa babu numfashi a jikinta,  sun kuma je kiran Zeenatu don ta ci abinci, itama sun isketa kwance a ƙasa bata motsi, sai lokacin ne suka tuna da babu Zeenatu a tare da su sun barta a gida, tsawon kwana ɗaya suna asibiti gurin jinyar Hajiya Sarah. 


A asibiti suka baro hajiya Sarah karkashin kulawar likitoci, Lokacin da suka dawo gidan cikin sauri Alhaji Ubaid da Hajiya layla suka nufi ɗakin Musa, Dr Shureim da Benazir suka nufi up ɗakin Zeenatu.


Shigar su ke da wuya, kwatsam suka hangota a kwance saman gadonta, maids ɗinne suka kwantar da ita bayan da suka taras da ita a ƙasa bata motsi.


Kallon juna suka yi cikin rudu da tashin hankali, sam sun kasa ta6a ta sun rasa gane meya faru? Tani da ta biyo bayansu tana kuka ta miƙa masu wasiƙar data gani akan gadon Zeenatu.


Yatsun hannun Dr Shureim na kerma ya kar6a tare da buɗe ta, suka haɗu shi da Benazir suna karantawa.


Na ji komai da ya faru, daddyna ɗan kungiyar asiri ne, ya raba ni da twin sister ɗina, ya zalunce ta, ba zan ta6a yafe masa ba. Kamar yadda ya sadaukar da ita ya yi silar mutuwarta, nima ya rasa ni na har abada, bazan ci gaba da rayuwa ba, zan bi ƴar uwata Unaizah, mommy ki yi hakuri da hukuncin da zan yankewa kaina, Yaya Shureim, Aunty Benazir ku yafe min, bazan iya jure baƙin cikin da daddyna ya ƙunsa mini ba, ya yaudare mu. Yanzu na gane dalilin da yasa ya ke yi min kulle saboda baya son ina fita don kada wanda yasan Unaizah ya ganni asirinsa ya tonu, kuma na gane dalilin da ya sa Azeezaty ta ruɗe a ranar da ta fara ganina har ta kira ni da sunan Unaizah ashe yar uwata ce da su ka yi rayuwa da ita a gidan kurkukun ƙaddara, Allah Ya isa daddy! Bamu yafe maka ba, Allah Ya wulaƙanta rayuwarka, in sha Allah hakkin Unaizah ba zai barka ba!


Abun da ya faru lokacin da suke ba Hajiya Sarah labari, ashe Zeenatu ta fito daga bedroom dinta, tana kokarin shiga falon ta tsinkayi maganganunsu a cikin kunnanta, ta ji komai da ya faru hakan yasa ta ɗimauce, dama mai haƙuri bai iya zuciyata ba, hankalinta ya tashi zuciyarta ta karaya da jin labarin twin sister ɗinta da bata san da ita ba, hakan yasa ta juya da gudu ta nufi ɗakinta, tana shiga ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, babu wanda ya san me ya faru, har ta gama kukan ta rubuta wasiƙar da Tani ta tsinta a ɗakin.


Lokacin da suka kammala karanta wasikar, zubewa suka yi agabanta saman gwiwowinsu suka fashe da kuka suna fadin meyasa zata kashe kanta bayan tasan babu kyau! Meyasa zata yi masu haka?"


Idan muka koma bangaren Hajiya Layla da Alhaji Ubaid lokacin da suka shiga bedroom din Musa, a kan floor suka hango hajiya Laura a kwance babu numfashi.


Da suka tatta6a jikinta a sandare suka ji shi, sun rasa gane ta mutu ko tana a raye saboda ruɗu, Lami ce ta kawo masu ruwa suka yayyafa mata a jikinta, ko gizau bata yi ba, nan fa hankalinsu ya tashi gaban su ya shiga faɗuwa.


Suna a wannan halin suka soma jiyo muryoyin Benazir da Dr Shureim cikin tashin hankali suke ƙwala masu kira suna fadin, "Daddy, Mommy! Kuna ina! Ku zo ku gani! Zeenatu ta kashe kanta, ta mutu, babu zeenatu..."


 Basu san sa'adda suka saki Laura ba, Jikinsu na 6ari suka nufi falon har suna bangazar juna ita da Alhaji Ubaid, a daidai Lokacin sun nufo su Dr Shureim ne ya ɗauko gawar Zeenatu a saman kafadar shi.


Wa'iyazubilla! bazan iya misalta maku tashin hankalin da iyalan Elders suka shiga ba, ƙuncin rayuwa da baƙin ciki ne ke addabarsu ta ko'ina ba sauƙi gaba daya sun sare da rayuwar duniya.


A bangaren iyalan Ɗan iya, suma sun fuskanci nasu ƙalubalen bayan da asirin mahaifinsu ya tonu, suma sun ji komai game da kurkukun kaddara sun kuma ji hadda mahaifin su cikin Elders..


Gaba ɗaya saida shiga mutane ya gagare su saboda tsangwamar su da ake yi, dole suka killace kansu a gida.


Duk wani mai hulɗa da su saida ya ja baya da su, kyara da tsangwama ba wanda basu fuskanta ba a gurin mutane, hatta shiga social media saida ya gagare su, saboda munanan maganganun da mutane suke yi akansu, ubanninsu sun ja masu abun kunya, bayin Allah, su da ba laifin su ba.


Jarabta ce daga Allah kuma da suka yi haƙuri suka jure, cikin ikon Allah sun fara samun maslaha, manyan malaman addini na ƙungiyar sheikh Imam Malik dama wasu manyan malaman duniya sun tsawatarwa mutanen dake cin zarafin su akan laifin da bana su ba, sun yi nasiha sun yi wa'azi akan halin da iyalan elders suke a ciki, kuma cikin ikon Allah sai gashi sun fara samun sassauci, mutane sun gane kuskuren su na ƙuntata masu da suke yi, musamman da suka ji labarin abun da ya faru da twin sister ɗin yarinyar da labarinta ya ta6a zuciyarsu, hankalin kowa ya tashi da jin Zeenatu ta kashe kanta, mahaifiyarsu kuma tana a kwance rai hannun Allah sakamakon abun da mijinta ya yi ma ƴarta, su kansu ƴan'uwan nata basu san ya akai labarin Zeenatu ya fita ba, hasalima basu son asani saboda abu biyu, na farko basu tabbatar da mutuwar Zeenatu ba! Bayan da suka kaita asibiti doc ya faɗa masu da yiyuwar doguwar suma ta yi saboda babu alamun ta sha poison ko lahani na ciki ko na waje a jikinta, abu na biyu saboda tsoron surutun mutane, amma sai dai suka ji labarin yana yawo a social media tare da hotunan Zeenatu. Sai daga baya suka gano cikin ƴan aikin  gidanne suka fitar da labarin, aikuwa ransu ya 6aci matuƙa, har mataki suka ɗauka akan ƴar aikin da ta yaɗa labarin duk da ta janyo masu tausayar al'umma.💔

Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura

3196407426 

First bank 

Bature Hafsat Muhammad,

 *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post