Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 85 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 85 Complete

Takun Ƙarshe

Daga alƙalamin Hafsat Bature Boss✍️

Kowan nan su yana a zaune kan kujera cikin Cell ɗin Isod, A hankali Chief Owais ke duban fuskar Praveen da ya sadda kanshi ƙasa cikin tsananin tashin hankali da fargaba, gaba ɗaya babu nutsuwa a tare da shi ga rashin koshin lafiya, la66ansa sun kumbura suntum, gefen idonshi na dama ya kumbura harda kwantsa a cikin su, gaba ɗaya jikinshi a kumbure yake ga tarin raunukan da ya ji sakamakon bugun da su Sir mubarak suka yi ma shi, har yau bai dawo daidai ba.

Bakomai chief yake kallo a cikin idanun shi ba face tsantsar tsoro, firgici, da damuwa mai haɗe da ƙunci da baƙin ciki, saboda nauyin Chief Owais da ya ji ya sa shi kasa jure kallon shi.

Girgiza kai Chief Owais ya yi, "Praveen, Allah ba azzalumin bawanSa bane sai dai bawa ya zalunci kan shi. Me ya ja maka Praveen? Ma ya kai ka aikata miyagun laifukan nan? Meyasa ka biyewa son zuciyarka da son abun duniya wanda zamu mutu mu barshi duk min daren daɗewa?" Girgiza kai ya yi cike da danasani ya ce, "Bada son raina ba, ba halina bane, sharrin shaiɗan ne da sharrin zuciya, nasan ina da son kuɗi sosai, zan iya komai don in samu kuɗin da zan rufa mana asiri ni da ƴar uwata, amma wallahi ban ta6a kisan kai ba, sai da na haɗu da Obinna..." 

Bai ƙare maganar ba ya dakatar da shi, "Ka iya kuma cin zarafin mata ko? Ko ka yi tunanin bamu ji abun da kake ma ƴan aikin gidanmu ba? Ka dinga masu barazanar za ka sa a kore su daga aiki duk don ka samu su baka haɗin kai, bayan haka kaine ka yi silar ciwon marwa..." Cike da tsana ya ke kallon shi.

"Dama can babu imani a zuciyarka Praveen, baka da tausayi kuma kai ɗin mugu ne, ƴar uwarka kaɗai kake tausayi, grandpa ya faɗa min duk wanda suka saka a kungiyar kurkukun ƙaddara da son ran shi....

Sunnar da kan shi ƙasa ya yi.

"Ka faɗa min tayaya akai ka haɗu da Saratu? Da kuma yadda akai baba ya sanyaka a ƙungiyar kurkukun ƙaddara? Karka ce zaka yi min ƙarya ko ka 6oye min wani abu, ƴar uwarka tana a hannunmu, idan ka yi laifi ba kai zamu hukunta ba, ita zamu hukunta.." Faɗuwar gaba ya ji, a ruɗe yake duban Owais da jajayen idanunsa..

"Na roƙe ka, kada ku ta6a Hajjaty, bata da laifi, batasan komai ba, na ji zan amsa maka tambayoyin ka.." Murmushin gefen fuska Owais ya saki, ya fahimci Hajjaty ce lagwon shi.

dakyar ya ke magana yana sakin nishi.

"Farkon haɗuwa na da hajiya Saratu a restaurant ɗinmu ta zo cin abinci, ni na je kai mata abincin, kawai saboda na goge cokali da rigata ta falla min mari, ta sanya hannu ta 6arar da kayan abincin ƙasa, ta soma zazzaga min masifa tana faɗin shiyasa bata cika son cin abincin indiya ba ƙazamai ne mu, ƙasƙantattu marasa hankali.."

 A lokacin na ji zafin marin da ta yi min, raina ya 6aci da kalamanta amma ban nuna ba, saboda na hango agogon hannunta ta zinari ce, bayan haka ni ina girmama masu kuɗi koda zasu wulaƙanta ni ne indai zan samu abun da nake so.

Har zata tafi na ce mata ta 6arar da abinci bata biya kuɗin ba, cikin fushi ta tura hannu cikin handbag ɗinta, ta zaro dala ɗari ɗari bama na kuɗinmu rupee ba ta watsa mini kan ƙirjina ta juya ta fuce, na shiga washe baki ina tattara kudin da suka zube a ƙasa, wanda a ƙalla a kudinmu na indiya sun kai dubu ɗari biyar, nan fa na fara tunanin ta wace hanya zan ƙulla alaƙa da ita? Tun da na fahimci tana da arziƙi kuma ƴar masu kudi ce.

Daga nan saina fara bin diddiginta, tun a ranar da ta shige motarta na bi bayanta da mai abun hawa, na ga ta shiga Medical University, a nan na fahimci ɗaliba ce ta zo karatu daga wata ƙasa, saboda na lura ba jinsinmu ba ce.

Da na ci gaba da yin bincike akanta saina na gano ƴar Nigeria ce, kuma ta fito daga babban gida na masu arziƙi, a jami'ar babu wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya, tun daga ɗalibai har malaman shakkar 6ata mata rai suke, ita kuma bata da mutunci, ta ƙware gurin bullying ɗin mutane. Na ɗauki lokaci ina shawarar ta yadda zan shiga jikinta, a ƙarshe dubara ta faɗo mini a rai, na haɗa baki da abokaina na sa su farmaketa akan hanyarta ta dawowa daga makaranta zuwa gidanta da take zama don na gano ba a hostel take ba, katafaren gida gare ta harda masu aiki da masu tsaron gidan amma bata da driver ita ke driving da kanta saboda bata son ana sanya mata ido idan zata fita, a yadda na ji.."  

Ya ɗan dakata yana mayar da numfashi.

Dg ya nutsu yana sauraron shi.

"A ranar da ta fito daga school cikin motarta, batasan muna a biye da bayanta ba saman baburan mu, idan ba zan manta ba wuraren ƙarfe biyar na yamma ne, akan idon mu ta shiga gym, har lokacin da ta fito ta shige motarta, ta kuma nufi mall ta shiga, duk muna biye da ita, har sai wuraren ƙarfe takwas na dare sannan ta nufi hanyar komawa gidanta, kasantuwar ba jama'a layin da ta shigo, nan muka samu damar farmakarta, abokaina suka fara tarar motarta, suka tsoratar da ita da addunan hannayen su, dama plan ne muka shirya mata, suka yi mata barazanar zasu yi mata fyaɗe sannan su kashe ta, cikin ruɗu da tashin hankali ta ce su kyaleta ta tafi kar su kuskura su ta6a ta, idan ba so suke su rasa rayukan su ba, idan ma kuɗi ne suke so tana da su zata basu ko nawa suke so, amma kar su ta6a lafiyar jikin ta, saida na bari sun fara ƙoƙarin raba ta da kayan jikinta tukunna ni kuma na fito daga inda na la6e na nufe su da tsawa na ce, 'Kar ku kuskura ku ta6a ta, idan ba so kuke ku rasa rayukanku ba!' Ina ƙarasawa muka cuɗanya da su faɗa ya kaure a tsakanin mu, ta yi ta mamakin yadda na dinga bugun su, ni ɗaya na bubbuge su, har sai da suka arta a guje suka bar arean wurin.

Kwata kwata bata gane fuskata ba, dama ranar da muka haɗu a restaurant bata yi min kallon arziki ba, a lokacin ban wani nuna zaƙewa ba, ina haki ina gyara hannun riga ta na dube ta na ce, 'Ki kiyaye fita a irin wannan lokacin, idan ba haka ba, 6ata gari zasu lalata maki rayuwa' Kamar dai yadda jaruman film ɗin indiya suke yin acting, na juya zan tafi ta yi saurin shan gabana, duk da girman kanta saida na burgeta still wani kallon ƙasƙanci ta ke bina da shi ganin suturar jikina irin ta marasa galihu ce, cikin sanyin murya ta ce min ta gode da taimakon da na yi mata, ba don ni ba da tuni sun yi nasarar cutar da ita. Na yi murmushin gefen fuska ganin plan ɗin mu na aiki, na ce mata kar ta damu na saba taimakon mutane, kawai ta bi shawarata.

Ta ce min meye sunana? Kuma a ina nake da zama..

Na ce mata Praveen, ina a layin dake a gaban nasu.

Ta ce ta yi mamakin ƙarfina, ta yi zaton abun da take gani a indian movies ƙarya ne, amma yau ta ga zahiri.." Na yi dariya, daga nan ta ce min in ba damuwa mu yi musayar number, idan tana buƙatar taimako zata dinga kira na, jikina na 6ari na bata number wayata, bayan mun yi rabu na je muka haɗu da abokaina mu kai ta murna kowa ya fara hasasho kuɗin da zai samu.

Sai da na jera kwanaki ukku ina tura mata abokaina su farmake ta, kuma a duk lokacin da suke zuwa ni ke taimakonta, bata ta6a gane cewa nike turo mata su ba, idan ta tambaye ni ya akai a duk lokacin da miyagu suka farmaketa nake zuwa kamar aljani? Na ce mata saboda na damu da ita shiyasa nake bin diddiginta. Daga haka shaƙuwa ta fara shiga tsakanina da hajiya Saratu, ko da ta nemi sanin dangina na ce mata bani da kowa sai ƴar uwata ɗaya mu marayu ne, asalin danginmu masu arziƙi ne, silar hatsarin jirgin ƙasa muka rasa kowa namu, wanda kuma maƙiya ne suka farmake mu a cikin jirgin ƙasan suka kashe kowa sai ni da ƴar uwata kaɗai muka rayu, tun daga nan rayuwa ta sauya mana muka koma marasa galihu.

A lokacin ta tausaya min sosai, har ta ce min zata taimaka mana.

Sannu a hankali soyayya ta fara shiga tsakanin mu, muka shaƙu da juna, bata ta6a tambaya ta game da ƴar uwata ba, kuma bata ta6a zuwa inda nake ba, sai dai ni in je gidanta, sai da ta kaiga nine drivern dake tuƙata duk inda zata je saboda in dinga bata kariya.

Lokacin da ta kammala karatu, makaranta ta shirya masu graduation celebration, mahaifinta ya zo delhi, a gidanta ya sauka, ta kira ni a waya tana murna ta faɗamin daddynta ya zo daga Nigeria tana so in zo mu haɗu, amma bata so in sanya kayan yan jagaliya, in nemi kaya masu kyau cikin waɗanda take siya mun in saka saboda mahaifinta babban mutunne mai arziƙi da duniya tasan da zaman shi, idan har ya gano wanene ni zai raba mu ne, na ce mata toh.

A ranar da zan je, na ɗauki wanka na mutunci na je gidanta, a falo na zauna, masu aiki suka kawo min lafiyayyan abinci, daga bisani ta fito tare da daddynta, kallo ɗaya da na yi masa saida gabana ya faɗi saboda kwarjinin da ke gare sa, da kallo ɗayan na fahimci hamshaƙin mutunne. 

Jiki na a sanyaye na miƙe muka gaisa da shi cikin harshen turanci.

Mun yi fira da shi kaɗan,  bayan Saratu ta gabatar mashi da ni, ta kuma faɗa masa abun da ya faru da danginmu da kuma taimakon da na ke yi mata, ya nuna jin daɗinsa sosai, da zan tafi har kyautar agogo ya bani mai tsada.

Bayan dana dawo ni da abokaina muka je kasuwa muka siyar da agogon, mun samu kudi sosai, muka raba kuɗin ni da su, nawa kason na je kasuwa nayi ma Divya siyayyar kayan sawa.

Lokacin da Hajiya Saratu zata koma Nigeria, ta ce min in har ina so mu auri juna dole in biyota mu tafi Nigeria in ga danginta, sannan koda zata aure ni, sai dai ni in zauna a ƙasarta amma ita bazata iya zama a india ba.

Abu ɗaya ne damuwata, ƙanwata da zan tafi in barta, kuma ina son in tafi saboda nasan idan na bi Saratu zan yi arziƙi sosai, hakan yasa na yanke shawarar bin ta.

Bayan da mu ka zo Nigeria, kawunnanka sun nuna ƙin amincewarsu da auren mu, ƙiri ƙiri suka nuna min tsana da tsangwama saboda ni ba jinsinsu bane kuma bani da asali, bayan haka basu yarda da ni ba, duk na bi na tsargu amma saboda mahaifinku ya tarbe ni da hannu bibbiyu ya nuna min ƙauna yasa na saki jikina na ba banza a jiyar su, bayan kwanaki da zuwa na gidan ku, baba Obie ya kira ni a part ɗinsa mu biyu muka zauna muna fuskantar juna.

Ya ce min yasan komai game da ni da kuma rayuwata..

A ruɗe na kallesa na ce bangane me yake nufi ba,

ya yi murmushi ya soma zayyana min tarihin rayuwata tiryan tiryan, gabana ya faɗi na bi na ruɗe jin ya gano komai game da ni.

Ya kuma cewa yasan ni nake saka abokai na su farmaki Saratu don in kawo mata taimako, meyasa na ke yin haka?

Da mamaki na ce masa tayaya akai yasan duk wannan?

Ya ce min Saratu autar shi ce, yana sonta fiye da komai, kuma duk wanda ya ra6e ta yana bibiyar rayuwarsa saboda baya son abun da zai cutar da ita, ta yadda akai yasan komai game da ni da kuma manufata, abokaina yasa yaransa suka kama, ya basu za6i kodai su faɗa masa komai game da ni ya biya su kuɗi, ko kuma ya basu kashi kuma su faɗa ta tsiya, sai suka za6i su faɗa masa komai don ya basu kudi.

Bayan da ya kai min ƙarshen maganar tashi ya tambaye ni meyasa na yi haka?

Ganin ya gano komai yasa na bayyana masa manufa ta, na ce saboda ina son in yi arzikin da zan kula da rayuwar ƴar uwata, saboda ita na ke yin komai.

Anan ne yake faɗa mun zai yi min hanyar arziƙi mara yankewa, kuma zai bani auran Saratu harma da gurin da zamu zauna ni da ƴar uwata, zai ɗauki ɗawainiyar cin mu da suturar mu, sannan zai sama min aiki a kamfaninsa amma bisa sharaɗin zan yi komai ya ke so!

Na yi murna mara misaltuwa na ce masa na amince koma menene zan yi ya faɗamin kawai, ya ce min na tabbata zan yi? baya son na yi danasani daga baya, ko in nuna bazan iya ba, na ce masa aini in dai akan kuɗi ne zan iya komai amma banda kisa, ya saki shu'umin murmushinsa. Bayan da ya faɗamin komai game da kurkukun ƙaddara, na razana, hankalina ya tashi, na bi na ruɗe na ce bazan iya ba rashin imanina bai kai nan ba, ina jin tsoron in jefa rayuwata da ta ƴar uwata cikin haɗari, ni dai ya yi hakuri ya barni in koma India zai fi min kwanciyar hankali.

Dariya ya yi ya ce ai nama riga dana shiga ƙungiyar kurkukun ƙaddara tun da har na matsa ya faɗa min, kuma nasan sirrin su, kodai in amince ta lalama ko kuma ya kashe ni sannan ya kashe ƴar uwata Divya, za6i ya rage nawa.

Ba yadda na iya, da na zauna na yi tunani, zuciyata ta raya min in amince masa ko don saboda alƙawarukan da ya ce zai yi min.

Hakan yasa na amince, nima na zama member na kurkukun ƙaddara, daga bisani da likafa ta ci gaba, ya mayar da ni cikin Elders saboda yana so na, kuma yana nema na.

Runtse ido Chief Owais ya yi wata kibiyar baƙin ciki ce ta soke shi, cikin rawar murya ya furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."

 Praveen duk ya sha jinin jikin shi ganin irin fusatar da Owais ya yi.

"Daga baya, shine ya bani iznin in kawo ƴar uwata gidan bayan da na faɗa masa na aureta hada yaron mu ɗaya, ya ce min idan ta zo baya son kowa yasan komai tsakanin mu, zata kasance yar aiki saboda baya son Saratu tasan tana da kishiya,  kuma baya son asan alaƙar dake a tsakanin mu, shi kuma yaron mu baison kowa yasan da shi, saboda sadaukar da shi zan yi...

Kasa ƙarasa maganar ya yi idanunsa na tsiyayar da ƙwalla.

"Ka zalunci kanka Praveen, meyasa lokacin da ya nemi ya jefa ka a gur6atacciyar harkarsa baka ƙi amincewa ba? Meyasa baka faɗa ma wani ba ko ka kaishi ƙara gurin hukuma? Kai wlh da dai irin wannan musibar ƙwara ka bari ya kashe ka kai da ƴar uwar taka sai ya fi maku kwanciyar hankali!" Cikin fushi ya ƙare maganar.

"Kaima ka sani Owais, kakanka ya fi ƙarfina, wlh babu wanda zai yarda da ni koda na faɗa, kuma ban isa in gudu ba, bayan haka hada son abun duniya ne ya rufe min idona, amma ko a cikin Elders ni kaɗai ne mai rauni, ban ta6a kisan kai da son raina ba..."

 cikin ƙunci ya ƙare maganar tasa.

"Owais ku taimaka mini, ku rufa min asiri, wlh na tuba, na yi danasanin hali irin nawa, na kuma yi danasanin sanin hajiya Saratu a rayuwata, saboda mahaifinta ne silar komai, Hajjaty bata da kowa in ba ni ba, ina jin kunyar tasan abun da na aikata.." Ya ƙarashe maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro..

Ko kaɗan Owais bai ji tausayin shi ba, amma ta wani wurin ya ɗan tausaya mashi saboda kakansa ne ummul aba'isin komai amma shima mai laifi ne.

"Bayan kasan kai mai laifi ne, maimakon ka miƙa wuya cikin lalama, sai ka zagaya ta bayan fage, kaje ka ɗauki yar uwarka don ku gudu, da hajiya Saratu ta ritsa ku shine ka huce haushinka akanta, ka yi mata bugun kawo wuƙa, in ban da kai ɗin mugu ne, mara hankali, ba kai tunanin ƴa'ƴanka ba? Ita wadda ka cutar ba uwar ƴa'ƴanka ba ce? Koda ba don Allah ka aureta ba, baka tunanin wani hali ya'yanku zasu shiga? Wani irin uba ne kai mai son kai da zon zuciya?" Duƙar da kansa ƙasa ya yi, hawaye nata sintiri kan kuncinsa.

"Ko kakanmu da ya kasance azzulami bai gudu ya bar ahlinsa ba, saboda soyayyar mu yasa shi miƙa wuya, kai fa?" Ya faɗa cikin 6acin rai.

"Ka so ka kashe ta Allah bai nufa ba ta rayu.. " Gabansa ne ya faɗi a razane ya ke duban Owais..

"Bayan da ta ji sauƙi, mun faɗa mata mun kama ka zamu kawo ta gurinka don ta ɗauki fansar abun da ka yi mata, kasan me ta ce?" Jikinsa a sanyaye yake duban Owais..

Ipad ɗin hannunsa ya daddana, kafin ya juyo masa da screen ɗin ta, wata irin kunya ce ta lullu6esa ganin Hajiya Saratu a zaune kan gadonta, fuskarta duk tabo, video call ne Owais ya kira ta, tana kallon Pravin da ya muzanta ya kasa haɗa idanun shi da nata.

Murmushi ta sakar ma shi,

"Ka aure ni saboda dukiyata, da kuma sura ta ko? Dama masu iya magana sunce kwaɗayi mabuɗin wahala ne, yanzu wa gari ya waya Pravin? Kana tunanin makomarka kuwa? Mutum mai tarin zunubi irin ka, wlh ka mutu Praveen, ka kashe kanka da kanka, kana cikin musiba. Zafin cin amanar da ka yi mini, ya fi bugun da ka yi min raɗaɗi a gurina, na yi danasanin auranka, na kuma yi danasanin haifa maka ya'ya da har ka samu damar sadaukar da wasu azzalumi, kaima ka sani, nima ban ta6a sonka ba, na aureka ne, saboda makircin da ka ƙulla min don ka ci arziƙi, kuma ba zan rama ba, na yafe maka, ka ji da hukuncin da kotu zata yanke maka, da kuma abun da zaka taras a cikin kabarinka na sakamakon zunubin da ka aikata. Na tsaneka, kai ba abun a tausayamawa bane, mahaifin mu bashi ya jefa ka a halin da kake a ciki ba, saboda shi ba Allah ba ne da in ya ce ka yi abu ya zama dole ka yi, bayan haka, meyasa lokacin da ya yi maka ta yi baka fallasa asirinsa ba, ko da zai kashe ka ne ka ƙi amince masa, yanzu bala'en da kake a ciki ko mutuwa ba zata zama hutu a gare ka ba wlh. Praveen ka shiga uku! kana cikin musiba dumu dumu, ina taya ka murna sai mun haɗu a kotu.

Ta ƙarashe maganar idanunta cike tab da ƙwalla tare da murmushin takaici akan fuskarta.

Bai ta6a jin karayar zuciya da danasani irin na wannan lokacin ba, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba kamar ransa zai fita

"Praveen yanzu ba lokacin kuka bane, lokaci ne da zaka fara tunanin menene makomarka! Ai ba ka ga komai ba, shawarar da zan baka shine, ka daure ka tanadi hawayenka, zuwa lokacin da alƙali zai yanke maku hukunci..." 

Yana kuka hadda majina ya ce, "Ki taimaka min Saratu! Ki taimaki rayuwana, in har da gaske kin yafe min ki sa baki, su yafe min su fitar da ni daga ciki, ko don albarkacin ƴa'ƴan mu, wlh na tuba, na bi Allah, na yi danasani zan sauya rayuwata, zan ma nisanta kaina da kowa..." 

Girgiza kai hajiya Saratu ta yi, "Praveen babu mafita, babu taimakon da zan iya yi maka, ka riga da ka jagula komai, kai koda zan iya fitar da kai Allah ba zai ƙyale ka ba, dole ka ga sakayyar rayukan da kuka zalunta, don haka ka yi haƙuri kawai ka girbi abun da ka shuka. Taimako ɗaya da zan iya yi maka shine zan roƙi yayyena, su bar Hajjaty ta ci gaba da zama cikin mu, saboda na tausaya mata bayan da na ji tarihin rayuwar ku, in sha Allah Hajjaty ba zata wulaƙanta ba, zamu zama danginta daga nan har ƙarshen rayuwarta, ba zata yi maraicin rashin wani nata ba.."

ta ɗan dakata da yin maganar tana ɗan girgiza kan ta kafin ta ɗaura da cewa,

"Ƴa'ƴan mu zasu kasance ƙarƙashin kulawar yayyena da kuma ni! Ba za su yi maraici ba, bayan da suka san komai da ka aikata sun tsaneka fiye da yadda suka tsani mutuwarsu, wlh da zasu ganka ido da ido da sai sun kashe ka har lahira, amma karka da mu, zan sama musu uba na gari wanda zasu yi alfahari da shi!"

tana ƙarashe maganar ta katse video call din

Komai da suke tattaunawa, observers suna kallon su ta Computer ɗin su.

Wata irin ƙara mai cike da baƙinci ya fasa, ya kama kuka kamar ransa zai fita, ya dinga yi ma Owais magiya akan su yafe masa kar su hukunta shi, ba laifinsa bane, baba Obie ne ya ja ma shi.

Owais bai saurare shi ba, ya miƙe ya fuce daga cell ɗin,

Har ya fita yana jiyo ihun da Praveen ke yi kamar zai fasa dodon kunnan sa.

*game Bukatar Kurkukun ƙaddara Ya tuntu6i number din nan 08103884440*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post