On the previous days (kwanakin baya)
HAJIYA ADAMA💔
Tana a zaune kan darduma jikinta sanye da hijab, wayarta dake ajiye kan gado ta fara ringing, saida ta kammala addu'o'in da ta ke yi ta miƙe cike da sa ran surukanta ne ke kira saboda ta yi kewar su.
Ɗaukar wayar ta yi tare da duba sunan me kiranta, ƙanwarta ce Fatima, picking call ɗin ta yi, tana kara wayar a kunne ko sallama ba ta yi ba, muryar fatima ta katse ta da tashin hankali ta ce, "Aunty kin ji abun da ke faruwa?"
"Wani abu ne kike magana akai fatima?"
"Wai kina nufin bakisan badaƙalar da ake yi a cikin ƙasar nan ba?" Yamutsa fuska ta yi, "Look, kada ki ɗaga min hankali, kawai ki faɗa min menene?"
"Hmmm, Aunty labari da ɗumi ɗuminsa, baya faɗuwa da baki, ki yi maza maza ki shiga social media ki gane wa idonki."
Cikin sauri ta katse kiran, tana kunna wi-fi ta fara cin karo da labarai iri iri na Kurkukun ƙaddara, tun tana daga tsaye har ta fara ganin jiri jiri jikinta na 6ari ta zauna tana ci gaba da bibiyar labaran.
Tiryan tiryan ta karance shi tsaf, hankalinta ya tashi matuƙa, ta razana ta kuma kiɗima, hotunan fursinonin ta buɗo tana duddubawa unexpected ta fara cin karo da video din Angel da Batool, zumbur ta miƙe tana zare idanunta, muryarta na rawa ta furta, "Bab...baby Angel! Angel!! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.. !"
Ruɗu ne yasa ta saki wayar ƙasa ta futo a guje ta nufi falo don ta faɗa ma Abdalla, tana shigowa ta iske shi zaune kan kujera sai kuka yake yi kamar ƙaramin yaro, zufa duk ta wanke jikin shi, ya tasa plasma tv a gaba yana ta kallon tattaunawar su Dg da manema labarai.
Yama fita shiga tashin hankali, nufar shi ta yi, cikin rawar murya ta ce, "Mijina kaima ka gani ko? Yanzu nake ganin labarin da ya tada hankalina! Ka ga Unaisah da Taj suna a raye, kuma ka ji mummunar ƙaddarar da ta faɗa masu..?" Idanunta suka cicciko tab da ƙwalla ta zauna gefen shi, tare da dafa kafaɗar shi, sai kuka yake yana kallon labaran, jikin shi har wani jijjiga ya ke yi.
Cikin shesshekar kuka ta ce, "Tun da har Taj da Unaisah suna a raye, wataƙil shima Uzair yana a raye, ya kamata mu tashi mu tafi gurin su..." Girgiza mata kai ya yi hawaye na sauka kan kuncin shi ya dubeta da idanunshi waɗanda suka kaɗa jawur, "Akwai abun da na daɗe ina 6oye maki, amma yanzu tun da asirin su ya tonu gaskiya ta yi halinta, nima zan bayyana maki komai..."
Wani irin faɗuwar gaba ta ji, a dabarbarce ta furta, "Bana son ji, pls kada ka faɗamin in dai kasan ba alkhairi bane, ka barni kawai in ji da abun da ke damuna"
Miƙewa ya yi tsaye. "Ya zama dole ki sani Adama.." miƙewa ta yi tsaye itama tana zare idanunta cike da fargaban abun da zai sanar da ita.
"Kada kace min kana ɗaya daga cikin su!"
Wani irin kallo ya ke yi mata
"Bana ɗaya daga cikin su, amma akwai wani abu da ya ta6a haɗa ni da ɗaya daga cikin su, wanda ya yi silar samuwar arziƙi na!"
Da tsawa ta katse shi, "Are you out of your mind! Abdallah me ka aikata? Waye ka sani a cikin su? Tayaya ya zama silar samuwar arziƙin ka ? Ko hakan na nufin kaima ka ta6a sadaukar da wani naka??" Sam ya kasa cigaba da magana saboda fargaban yadda zata ɗauki abun.
"Kada ka ce min kaine ka yi silar 6acewar su Uzair!" Ta faɗa tare da kama kwalar rigar shi da hannayen ta dake ta kerma..
"Assalamu Alaikum." A kunnansu suka tsinkayi muyarsa, hakan yasa suka dakata da maganar da suke yi,
Kusan atare suka dubi kofar falon jin muryar mutumin da suka daɗe basu ji ta ba, wani irin annurin farin ciki ne ya cika su duk da halin da suke ciki, har suna haɗa baki gurin furta "TAJUDDEEN."
Yana a tsaye bakin kofar falo fuskarsa ɗauke da murmushin farin ciki ya amsa da na'am mommy Adama and My Only Uncle.
Cikin sauri ta nufe shi, suka yi hugging din juna, ta ɗago tana shafa fuskarshi ta ce, "Taj, dama kuna a raye baku ta6a neman mu ba Taj?" Tsawon shekara bakwai! kasan irin neman da muka yi maku kuwa? Meyasa baka tuntu6e mu ba?" Ta faɗa fuskarta a yamutse, hawaye sai sintiri suke kan kuncinta, daga yanayin su ya fahimci sun ji komai.
Matsowa kusa da Uncle Abdallah ya yi, da sauri ya rungume Taj kamar zai mayar da shi cikin shi..
Sai ya ji kamar ya haɗa jikin shi dana mahaifin shi Zaheer, saboda Uncle Abdallah madadinsa ne, shi kaɗaibne shakikin mahaifinsa kuma ɗan uwansa na kusa da ya rage masa a duniya.
Haka Uncle Abdallah shima ya ji kamar ya rungume mahaifinsa Zaheer, sun yi kewar juna.
"Alhamdulillah! Taj, ashe da rabon zamu gana da juna? bayan tsawon lokaci da muka neme ku muka rasa? Taj ka ga yarda ka manyanta? Ka ƙara girma ka yi kyau.."
Ya faɗa bayan ya raba jikinshi daga na Taj ya dafe kafaɗunsa da tafukansa, idanunsu a cikin na juna, kamar yadda yake mamakin sauyawarshi shima haka yake mamakin tsufan da Uncle ɗin nasa ya fara.
"Na yi kewarka Taj. Na ji komai da ya faru da ku, yanzu muka gama kallo a news."
"Taj Ina Uzair? Ina Angel? Nasan suna a tare da kai." Hajiya Adama ce ta faɗa cike da ƙaguwa.
Numfasawa ya yi tare da cewa, "Ku yi haƙuri na yi laifi da ban faɗa maku ba, amma nima bada son raina na ba, ya zama wajibi mu 6oye kanmu idan ba haka ba masu farautar rayuwar mu za su kashe mu ne, amma bamu manta da ku ba, kuna aran mu ko yaushe, mu ma mun yi kewar ku sosai."
"Amma Taj, ko a waya ai ka kira ka sanar da mu kuna nan, kasan halin damuwar dana shiga na rashin ku?"
"Uncle, Dg shine ya hana kowa yasan muna a raye, kuma shi ne ya taimaki rayuwar mu.."
Jinjina kai Abdallah ya yi, "Allah ya saka masa da alkhairi, na ji dadin ganinka Taj, mu shiga ciki mu zauna, amma tayaya akai kasan inda muke?" Ya faɗa tare da ruƙe hannunsa ya nufi Sofa da shi, hajiya Adama tabi bayansu baiwar Allah duk ta ƙagu da ta ji ina Uzair ɗin ta..
Bayan sun zauna, Hajiya Adama ta shiga kitchen don ta hada mashi abun da zai ci, sai zumudi take yi..
Duk in ya kalli Uncle ɗin nasa sai ya ga kamar Uzair saboda kamannin shi dake a kan fuskarsa.
"Taj, ka yi haƙuri ban baka kulawar da ya dace ba, gani nake kamar komai da ya faru laifina ne Taj, zamana Korea bai amfanar da ni komai ba, da a ce ina kusa da ku wataƙil da hakan bai faru ba.." Ya faɗa tamkar zai fashe da kuka.
A hankali Taj ya ɗaura tafin hannunsa kan kuncinsa ya soma share masa ƙwallarsa.
"Pls Uncle mu manta da komai da ya faru, tunawar baida amfani.."
"Taj, ba zaka gane ba, akwai damuwa a tare da ni, ina jin ciwon abun a raina.." Ruƙo hannayensa Taj ya yi, "Uncle, nima na fahimci halin da ka ke a ciki, nasan bai wuci akan ɗan uwana uzair bane ko?" Maimakon ya amsa mashi tambayar shi sai cewa ya yi
"Baka bani amsa ta ba, tayaya kasan inda muke da zama?" Ya kuma tambaya.
Murmushi Taj ya yi, "Anila ce ta tura min da address naku."
"Masha Allah, ashe kun haɗu da ita" Jinjina kai ya yi, "Eh..." Bai ƙare maganar ba, Hajiya Adama ta shigo falon hannayenta ruƙe da tray na kayan abinci ta ɗaura akan c-table.
"Nagode mommy, har yanzu kina nan yadda na sanki."
Murmushi ta yi kawai.
"Bari na ɗanɗana girkin mommyna na yi missing na shi." Murmushi suka saki suna kallon shi yayin da ya soma cin abincin sai santi yake yi masu, in ya yi wani abun sai ya dinga tuna masu da Uzair, ɗabi'unsu iri ɗaya sak..
Bayan da ya kammala ci, ya maida hankalinshi akan su.
"Taj, har yanzu baka amsa min tambayana ba? Ina Uzair?"
Haɗa ido suka yi da Abdallah, da kai ya yi masa alamar kar ya faɗa mata, dubanta ya yi in a cool voice ya ce,
"Mommy, lokacin da abun ya faru ba a tare da Uzair muka bar gida ba..." A taƙaice ya labarta mata komai da ya faru bai dai faɗa mata game da irin mutuwar da uzair ya yi ba.
Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu, sun shiga damuwa sosai, kwantar masu da hankali ya shiga yi.
"Yanzu haka Angel tana a tare da mommynta a gidan dg.."
"Taj, komai da muka ji game da kurkukun kaddara da gaske ne? Don ni wlh ji na yi kamar shirin film ne ko irin hausa novel, saboda yadda kaina ya ɗaure, ko a tarihi ban ta6a jin labarin da ya ta6a zuciyata irin shi ba." hajiya Adama ce ta tambaya tana kallon shi,
Jinjina masu kai ya yi cike da tabbaci ya ce, "da gaske ne komai da kuka ji"
"Meyasa ba ka zo mana da Unaisah ba?"
"Zuwa nan gaba in sha Allah zan zo maku da ita har ma da mommynta"
Tun da suka fara magana Uncle Abdalla bai sanya baki ba, gaba ɗayansa babu walwala a tattare da shi, Taj ya lura da yanayin shi.
Firar yaushe rabo suka yi cikin raha da annushuwa..
Kiran sallar azhar da aka fara yi ne ya katse masu firar ta su..
A tare da Uncle Abdallah suka tafi Masallaci..
Hajiya Adama ta zauna tana ta jiran su dawo, burinta ta ji menene Abdallah yake son sanar da ita? duk da tana jin zullumi da fargaban abun da zata ji.
Bayan da suka dawo daga masallaci, Uncle Abdallah ya ruƙe hannun Taj ya ja shi suka zagaya daga bayan gidan, kan kujerun shaƙatawa suka zauna suna fuskantar juna..
"Taj, na ji dadi da Allah ya bayyana mun kai da ranka da lafiyarka, tsawon lokaci ina addu'a akan Allah ya bayyana min ku cikin ƙoshin lafiya.."
Murmushi taj ya yi, ya ji daɗin maganarsa.
"Nima haka Uncle, na ji dadi dana same ku da ranku da lafiyarku, na yi farin ciki mara misaltuwa.."
Shuru suka ɗan yi na wani lokaci Taj ya lura da yanayin fuskar Uncle din nasa..
"Uncle, na fahimci akwai abun da ke damunka, kuma akwai abun da ka ke son faɗamin tun zuwa na na lura da hakan, don Allah ka sanar dani.."
Shuru ya ɗan yi jimm kamar yana jin shakkun ya faɗa
"Tajo, ina so ka fara fadamin gaskiyar meya faru da ku! Uzair yana a raye ko ya mutu? Pls kada ka 6oye min, ni ba yaro bane, kafin wannan anyi min rasuwa, na rasa iyayena da yayana mafi soyuwa a gare ni, a yanzu babu abun da bazan iya jurewa ba, saboda na yi imani da ƙaddara"
Jinjina kai Taj ya yi, kalamansa sun sa shi jin zai iya faɗa masa..
A tsanake ya labarta masa komai da ya faru lokacin da Uzair ya kira sa a waya cikin tashin hankali ya sanar da shi abun da ke faruwa da shi, bai dai ce sun ƙona Uzair ba, amma ya ce mishi su yi haƙuri su fidda rai da Uzair saboda babu shi a raye, shekara bakwai da rasuwarsa yanzu."
Girgiza kai Uncle Abdallah ya yi idanunsa sun ciko tab da ƙwalla, ya ji zafin mutuwar Uzair dama saida ran shi ya bashi baya a raye, wani baƙin ciki ne ya mamaye zuciyarsa, dafe kansa ya yi da tafin hannunsa yana tariyo rayuwar sa da ɗansa mafi soyuwa agare sa, yanzu shike nan ya rasa Uzair babu shi a doron duniya? Uzair ya mutu? Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un! Ya faɗa a cikin ran shi.
Taj da ke kallonsa jikinsa ya yi sanyi da ganin halin da Uncle din nasa ya shiga.
"Ka yi haƙuri Uncle, nasan dole ka ji zafin mutuwar Uzair.." Bai ƙare maganar ba, Uncle abdallah ya katse shi cikin raunanniyar murya ya furta, "Bakomai Taj, dukkan mai rai mamaci ne, nagode daka faɗa min. Allah Ya jiƙan Uzair, Allah ya gafarta masa, Allah ya kai rahama ƙabarinsa." Amsa masa ya yi da ameen ameen,
"Su kuma waɗanda suka yi silar mutuwar shi Ubangiji Allah Ya wulaƙanta rayuwar su, in sha Allah zasu ga sakayyar abun da suka yi masa.." Shiru suka yi jigum kowa da damuwa a cikin ran shi.
Har na tsawon mintuna babu wanda ya tanka a cikin su.
"Taj, dagaske kun kama Elders kamar yadda na ji a labarai?"
Jinjina mashi kai ya yi, "Hakane Uncle, mun kama su, yanzu haka suna a cikin cell na headquarter ɗin mu."
"Alhamdulillah, na ji daɗi da Allah ya fallasa asirin su. Don Allah Taj kada ku raga musu, ku azabtar da su har sai sun tsani rayuwar su..."
Murmushi Taj ya yi, "kar ka damu Uncle, yanzu haka idan ka gansu saika tausaya musu saboda raunukan dake a jikin su.." Ya faɗa da zolaya, wani kallo Uncle Abdallah ya yi masa. "Allah Ya kiyaye inji tausayin su, ai sai dai ma inyi masu Allah shi ƙara.." Ƴar dariya Taj ya yi.
"Idan muna fira da kai, sai in ji kamar yayana ne Zahir saboda komai naku iri ɗaya, na yi rashi Taj, Allah ya jiƙan shi da rahama." Zuciyar Taj ce ta karaya tunawa da mahaifin nasa, "Ameen" ya amsa..
"Allah Ya jiƙan Yahanasu da mama, Allah Ya kyautata makwancinsu."
hawaye ne ya ji sun ciko idanunsa.
Amsawa ya yi da, "Ameen don son Annabi."
Shiru suka yi na wani lokaci, still ya lura da akwai abun da Uncle ɗin nasa yake son sanar da shi, kamar yana jin shakkar fitarwa ne.
"Uncle, idan akwai abun da kake son faɗa min pls kada ka ji komai ka sanar da ni, a yanzu bani da tamkarka kaima haka."
jinjina kai Uncle Abdallah ya yi, "Ka faɗi gaskiya Taj, da akwai abun da nake son sanar da kai, duk da ina jin fargaban yadda zaka ji abun a ranka, amma zan sanar da kai saboda inaso ka taimaka min, ita kaɗai ce damar da nake da ita."
ya ɗan numfashi kafin ya ɗaura da cewa,
"Shekarun baya da suka gabata, Hajiya Adama ta ta6a yin matsananciyar rashin lafiya kamar bazata rayu ba, bayan da likitoci suka duba ta sai suka gano ta samu matsalar da sai anyi mata tiyata zata samu lafiya, kuma in har ba ayi saurin yi mata ba zata iya rasa ranta, ni kuma a lokacin bani da halin da zan iya biyan kuɗin da suka buƙata, bani da wani wanda zai tallafa min saboda iyayen mu ba hali gare su ba, yayana ma baida kudin da zai iya taimaka mun da su, shima fama yake yi da iyalin sa, ita ma haka iyayenta ba masu ƙarfi bane, hasalima talakawa ne sosai, ko kafin in aureta nasha wahala saboda basa bama talaka auren ya'yan su sai masu arziƙi, sun mayar da su kamar jarin su saboda Allah ya yi su da kyau. Taj ba irin wahalar da ban sha ba gurin fafutukar neman kuɗin da zan biya a yi mata aiki, amma na kasa tara adadin kuɗin da suke buƙata, ranar da na koma asibitin don duba lafiyarta, sai na tarar babu ita a ɗakin da suka kwantar da ita, ko da na tambayi nurses sai suka ce kuɗin gadon da muka biya sun ƙare, in har ina so su mayar da ita dole saina biya wasu kudin. Hankalina ya tashi matuƙa, na shiga nemanta, da ƙyar na ganota a bakin wata bishiya ta asibitin kwance a ƙasa, sai kuka take yi ta daddafe cikinta, wasu bayin Allah ne suka kewayeta suna tambayarta ina ƴan uwanta? Wa ya kawo ta asibitin? Bata da kowa ne.
Cikin sauri na je na daukota na koma da ita asibitin, na dinga roƙon su akan su taimaka mini su mayar da ita zan biya kudin zuwa gobe, da ƙyar na samu suka amince zasu mayar da ita, amma suka gargaɗe ni akan in har ban kawo ba zuwa gobe, babu wani uziri da zasu kar6a daga gare ni, bayan da suka mayar da ita kan gado, na baro asibitin na fara tunanin me zan siyar dan in biya kuɗin aikin nata? Na duba na hango bani da komai, a lokacin ko gidan kaina ban mallaka ba, a gidan haya nake da zama, kadara ɗaya da nake da ita, mashin ɗina, a ranar da nake shirin zuwa in siyar da shi, kwatsam sai ga kira ya shigo wayata da baƙuwar number.
Da farko ƙin ɗagawa na yi, anata kira sai daga baya na yi picking na kara a kunne tare da yin sallama.
Mutumin ya amsa min bayan mun gaisa na tambaye shi wanene saboda bangane me magana ba, na ga baƙuwar number.
Yace min eh dama yasan bazan gane shi ba, saboda ban san shi ba, amma shi ya sanni, maganar gaskiya ya ganni a asibiti ne, shima a lokacin ya je duba marasa lafiya, dama ya saba zuwa bada tallafi a asibitin, toh ya ji komai dake faruwa hatta matata da suka sauke daga kan gado duk yana a wurin yana bibiyar mu saboda mun bashi tausayi, shiyasa ma har ya kar6i contact ɗina agurin nurse.
Na ce Allah sarki, na gode sosai da nuna damuwa akan mu.
Ya tambaye ni na samu kuɗin da zan biya kudin aikin nata ne?
Nace masa a'a, ban samu ba, yanzu nake shirin zuwa in siyar da mashin ɗina duk da kona siyarma ba isa zasu yi ba, amma inason in fara biyan rabi don suyi mata aikin daga baya na cika.
Yace min kar a yi haka, idan na siyar da mashin dina ni kuma da me zan dinga yawo? Ina ma amfanin siyarwar bayan kuɗin ba isa za su yi ba, abun da za'a yi shi zai biya kudin komai harma da jari zai bani."
Na yi ƴar dariya na ce nasan ma wasa yake yi min, saboda nasan babu mai iya yi min wannan taimakon, duba da yadda taimako ya yi ƙaranci."
Yace min wallahi da gaske yake yi, idan ina so in tabbatar da abun da yake faɗa zai bani address dinsa in neme sa.."
Bayan mun yi sallama da shi, sai ga saƙon address ya shigo wayata, a lokacin hankalina bai kwanta da shi ba saina ƙi neman shi, bayan da na tafi kasuwa don siyar da mashin ɗina aka rasa samun wanda zai siye shi da daraja, sai tayin wulakanci da ake yi min, ga shi lokaci yana ta gudu har marece ya yi ina ta neman wanda zai siya da kirki ban samu ba, a ƙarshe na sha wahalar banza na dawo gida, da na ga bani da mafita saina yanke shawarar kiran mutumin don in faɗa masa zan zo.
Bayan mun yi waya, na shirya na tafi gidan da ya yi min kwatance.
A falo muka zauna ni da shi, ban iya ganin fuskarsa ba saboda ya saka mask, ya kuma sanya glass a idanunsa, bayan mun gaisa na gabatar masa da kaina.
Ya ce min ai ya gane ni, kar inji komai in saki jikina, ba kaina ya fara tallafawa marasa ƙarfi ba, ya saba zuwa asibiti duba marasa lafiya har ma ya biya kuɗin jinyar su, da ya faɗi hakan saina ji hankali na ya kwanta sosai, ya ce min sai dai ya ji kuɗin da za'a yi mata aikin suna da yawa, zai biya rabi kyauta amma rabin zai bani a matsayin bashi, cikin sauri na ce na amince amma idan har yana da aikin da zan yi masa ya faɗa min in ya so cikin kuɗin aikin sai ya dinga zare bashin da ya ke bina.
Ya yi murmushi ya ce min bashi da aikin da zai bani amma in har na amince zan bashi duk abun da ya ke so a matsayin biyan bashin toh zai bani.
Na ce masa bangane me yake nufi ba? Ya ce min kar in damu ba wani abu bane, kawai yana son mu yi yarjejeniya in har ya bani kuɗin komai ya buƙata zan bashi.
Da ya ke a buƙace nake na amsa mashi da na amince in dai ina da abun, nan take ya shiga ɗaki ya dauko jaka ya miƙa min tare da cewa in ɗauka miliyan biyar ne a ciki, na ruɗe a lokacin na ce masa sun yi yawa bazan iya kar6a ba, kuma bani da hanyar da zan iya biyan shi, sai dai ya rage ya bani daidai kuɗin da nake buƙata, ya ce dama ce a gare ni, in yi amfani da ita tun kafin in rasa, da jin haka sai na yi masa godiya , daga bisani muka yi sallama na tafi.
Washe garin ranar, bayan da na je asibitin na biya kudin aikin ta. Cikin sa'a bayan an yi mata aiki ta ji sauƙi kamar bata ta6a yin ciwo ba, bayan da suka sallame mu muka dawo gida, ban ta6a faɗa mata game da yarjejeniyar kudin dana kar6a bashi ba.
Taj wlh sai da nayi danasani, ni bansan da mugun nufi ya shiga rayuwata ba, ban yi bincike akanshi ba, saboda kuɗin nake cikin buƙata bani da yadda zan yi Taj, tun bayan da ya ban kuɗin ban ƙara jin ɗuriyar shi ba, nama manta da batun bashin da na ci, da kudin na fara neman na kaina ina ɗan ta6a kasuwanci harma na samu aiki a companyn kasuwanci. Lokaci ɗaya Allah ya buɗe min kofofin samu, na mallaki gidan kaina, na sayi mota, a lokacin Uzair ya zama matashi na dawo da kai gidana, kwatsam! wata rana sai ga kiran mutumin nan ya zo yasa akai masa sallama da ni, bayan na fito na yi mamakin ganinsa still fuskarsa da takunkumi, bayan mun gaisa na yi masa iso muka shiga ciki, a bayan gidana muka zauna ya ce ya ji shiru kona manta da bashin shine, nace masa ban ta6a mantawa ba, da abun nake kwana a raina, saboda ina son in sauke hakkinsa dake a kaina, don haka yanzu tun da mun haɗu ya faɗamin da me zan biya shi?
Da buɗar bakinsa sai cewa ya yi, "Ƴa'ƴa yake so in biya shi da su." Na yi zaton zolaya ta yake yi, na yi dariya na ce don Allah ya daina zolaya ta, mu yi magana ta gaskiya, da me zan biya shi bashin, ya kuma ce min rai yake so, dana fahimci dagaske yake sai na ce masa ai ba a biyan bashi da rai, ban ta6a ji ba, kuma ni ban da ran da zan biya da shi, bama zai ta6a yiwuwa ba, in dai zan biya sa sai dai in biyasa da abun da ya bani ko ya fadi wani abun daban!
Girgiza kai ya yi da kakkausar murya ya ce, "Na manta yarjejeniyar mu ne? Idan nasan ba zan iya bashi abun da yake so ba meyasa na kar6i kuɗinsa?" Raina a 6ace na ce, "Amma dai malam baka da hankali ko? Kawai saboda ka bani bashin kudi sai ka ce in baka rai? Kamar wani ran kaza? To wallahi bazan bayar ba, komai zai faru sai dai ya faru, a ina aka ta6a haka? Kudi sun isa su sayi darajar rai ne.. !" Na gaggaya masa maganganu cikin bacin rai saboda naga rainin wayon nasa ya yi yawa, cikin fushi ya ce oh shi zan ma butulci? Bayan halaccin da ya yi min? dama ba a gane halin talaka sai ya yi kuɗi, wato yanzu na samu bakin gaya masa magana ko? Ba don shi ɗin ba ai da yanzu na rasa matata, amma shike nan zai tafi amma fa in sani zan biya abun da na yi masa.
Bayan fitarsa, abun ya dame ni, na yi ta tunanin meyasa yake son in biya shi bashi da rai? Me zai yi da ƴa'ƴa? Gashi dai da hankalinsa ba mahaukaci bane balle in ce ko ya samu ta6in hankali ne, can kuma raina ya bani ko dai irin waɗanda basa haihuwa ne waɗanda Allah ke jarabtarsu da son ƴa'ƴa.
Da sauri na bi bayan shi, a lokacin yana kokarin shiga motarshi na dakatar da shi na tambayesa meyasa ya ke son ya'ya? Cikin karyayyar murya ya ce,
Saboda rashin da ya yi, a lokacin baya yana da mata ɗaya da ƴa'ƴa biyar, sanadin haɗarin jirgin sama ya rasa su, shi kuma a lokacin ya samu matsalar haihuwa yanzu haka yana da aure amma bai ta6a samun haihuwa ba, yana son ya'ya sosai. Na tausaya mishi na ce mashi indai haka ne meyasa ba zai je gidan marayu ba ya yi adopting, sai ya ce min baya son ruƙon maraya yana da wuya, kuma yawancin su basu jin magana, shi yasa ya fi son waɗanda suke da iyaye, jarirai da zasu raina shi da matar shi, in yaso daga baya idan Allah Ya sa ya samu warakar lalurarsa zai mayarwa mai su, shiyasa ya bani bashin nan saboda yana so in taimaka masa in share masa hawayensa, har kuka sai da ya yi min.
Taj tausayin sa ne ya cika zuciyana, har bansan sa'adda na ce masa na amince da yarjejeniyar mu, a lokacin ban san meke damuna ba, idanuna sun makance burina kawai in taimake shi, ji nake in har ban taimaka masa ba, zan iya rasa raina.. " Taj da ke sauraron sa tsantsar ruɗani ne akan fuskar sa.
_"A lokacin nasan idan na faɗa ma hajiya Adama ko wani daga dangina ba zasu yarda ba shiyasa na yi shiru da baki na, a lokacin baku cika zama gida ba kuna zuwa makaranta. Sau biyu Adama tana haihuwa ina sace jariran tare da haɗin bakin mutumin da likitansa, bata ta6a sani ba, sai dai ta ga ta haifi jariri ya zo babu rai, likitansa ne ke yi masu allurar da zasu yi kamar sun mutu, babu wanda yasan lokacin da muke aiwatar da hakan..."_
To fa!Kallo ya koma sama, hankalin Taj idan ya yi dubu toh ya tashi, tsantsar al'ajabi ne ya kama sa! A ransa ya ayyana ashe kurkukun ƙaddara bai bar kowa ba! Abun ya zo har takan Uncle dinsa!"
"Ƴa'ƴa biyu na bashi, mace da namiji, a lissafina yanzu namijin zai kai shekara ashirin, macen kuma ba zata wuce shekara sha takwas ba idan suna a raye, Taj kamar bani da hankali, ban ta6a sanin gidansa ko wani nasa ba, yadda kasan an rufe min bakina na kasa tambayarsa hakan, wallahi ko fuskarsa bansani ba, kullum da takunkumi nake ganin sa, a duk lokacin da na yi yunƙurin tambayarsa game da hakan sai in ji kamar an kulle min baki na..."
"kuma tun bayan da na bashi ya'yan ban ƙara marmarin in waiwaye su ba ko in tuntu6i mutumin in ji wani hali suke a ciki, gaba ɗaya namanta da babinsu, har tsawon shekaru, sai daga baya ne a lokacin kun 6ace babu ku, muka shiga mawuyacin hali na buƙatar ƴa'ƴa, ga hajiya Adama ta daina haihuwa ko 6ari bata yi har asibiti muke ja docs suka ce matsala ta samu a mahaifarta ba lallai ta sake haihuwa ba, daga ni har ita mun shiga matsananciyar damuwa, na fi jin tausayinta saboda ni na cuce ta, na bayar da ya'yanta batare da sanin ta ba, ina jin fargaban ta ji maganar nan, nasan har rabuwa zata iya yi da ni, ni kuma banason duk wani abu da zai raba ni da ita. Taj lokacin da tunanin mutumin ya dawo min akaina, a lokacin na yi arzikin da zan iya biyansa kaf kuɗinsa harma da ƙari batare dana girgiza ba, na sha kiran layinsa baya ɗagawa, har saƙonni na tura masa baya min reply, har na fidda rai da zai ɗaga kira na, unexpected wata rana ina ƙara jaraba kiran shi ya ɗaga,
(Idan masu karatu zasu iya tunawa, a kwai lokacin da Hajiya Adama ta yi ma Abdallah la6e yana waya a ɗakinsa har ta jiyo shi yana yin waya da wani mutumi, bari mu tariyo wayar da ya yi a wannan lokacin👇)
"Ka yi haƙuri nasan ba haka mukai da kai ba, na sa6a alkawari amma ka dubi halin da nake a ciki, lokaci ɗaya na rasa ɗana bayan haka na rasa ɗan yayana tare da ƴarsa, na rasa yayana da kakata, kai kaɗai ne zaka iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kuɗin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su in dai suna a raye na ƙwammace na ƙare rayuwata a talauci akan in ci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..."
Muryarsa a marairaice ya yi maganar kamar zai yiwa mutumin da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya.
Cigaban labari
"Na rasa ya zan yi Taj, nasan na cuci kaina, na kuma cuci yaran dana basa, bansan me ya yi da su ba, saboda ina zargin komai da ya faɗamin game da labarinsa ƙarya yake yi min, damfarata ya yi, kuma ba hakanan ya ƙyale ni ba. Ban tashi gane hakan ba, sai yau da na kalli news na ji labarin kurkukun ƙaddara da fursinonin cikinsa sai na dinga ji araina da wuya in mutumin nan ba yana a cikin matsafan ba, duk da bani da tabbaci, amma in har ya tabbata za'a iya samun yaran in suna raye.."
ya karashe labarin da hawaye a cikin idanunsa.
Numfasawa Taj ya yi cike da tausayinsa a cikin zuciyarsa ya ce, "Uncle na fahimci damfararka ya yi, kuma ya gusar maka da hankalinka daga tunaninsa da ya'yanka, babu tantama zai iya zama cikin matsafan.."
Cikin sanyin murya ya ce, "Taj, tayaya zamu iya sanin idan yana a cikin su? Tayaya ma za a iya gane yaran nawa idan suna a raye, bayan koni bansan kamannin su ba?"
"A labarin daka bani baka faɗamin sunan mutumin ba"?
Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya ce, "Sunansa dana sani wanda ya ta6a faɗa min Alhaji Ja'afar Dila."
Jinjina kai Taj ya yi tare da kwantar masa da hankali ya ce in sha Allah zai yi magana da Dj, idan ma yana a cikin su za su gano shi, zai yi iya ƙoƙarinsa saboda shima yana son yaran ko dan ya samu cousins ɗin da zasu maye mashi gurbin Uzair"
Abdallah ya ce yana son su bar maganar nan a matsayin sirri tsakanin su, ko mutuwar Uzair baya son hajiya Adama ta sani, yafi son sai sun samu mutumin nan da ƴa'ƴansa sai su faɗa mata komai, yasan koda zata ji zafi ba za ta yi fushi da shi ba, zata yafe masa saboda tana da haƙuri kuma tana son shi sosai.
Abun da basu sani ba, gaba ɗaya firar da suka tattauna a kan kunnan Hajiya Adama da ke yi musu la6e, kuka mai cin rai ta ke yi, ta toshe bakinta da tafukanta duk don kada sauti ya fito su jiyo ta, sai da taga sun miƙe ta watsa da gudu ta koma cikin gidan ta shiga toilet, ta wanke fuskarta don kar su gano ta, baiwar Allah ta ji zafin mutuwar Uzair sosai, ƙunci da baƙin ciki suka mamaye zuciyarta, ta dinga karanta addu'o'in neman sassauci a cikin zuciyarta, kwata kwata bata ji haushin abun da Abdallah ya yi mata ba, duk da bai kyauta mata ba da ya 6oye mata ya'yanta da ya bayar, kamar baisan irin yadda mata ke shan wahalar naƙuda kafin su haihu ba, wata tara ta raini ciki, ya dauka ya ba wani? Batare da sanin ta ba? Kamar ta ce masa batason ƴa'ƴan! Amma ta yi masa uziri saboda ta fahimci mutumin yaudararsa ya yi kuma hada asiri ya yi ma shi, bayan haka komai ya yi saboda son da yake yi mata ne, fatanta Allah yasa su gano mutumin nan don ya basu ƴa'ƴan su, Allah yasa suna a raye shi kaɗai ne hope ɗin da take da shi a yanzu.
Kafin tafiyar Taj saida suka shigo ciki, ta fito suka ƙara ɗan ta6a hira cike da ƙarfin hali, kafin suka rako shi har bakin motar shi ya yi masu sallama, suna ta ƙara tuna mashi suna son ganin Unaisah ya ce zai kawo masu ita in sha Allah. Bayan da ya tafi ko bayan da suka koma cikin gidan hajiya Adama bata bari Abdallah ya gane ta ji komai ba, a 6oye take shan kukanta, tsoffin hotunan Uzair ta dinga ɗaukowa tana kallonsu, da su take kwana da su take ta shi..
__________________________________
A bangaren Natasha kowa ya manta da batun ta saboda halin da suka shiga, amma kullum ne sai chef ɗin da dg ya ba ɗawainiyar kula da ita ya je kai mata abinci sau uku a rana, daga bisani dg ya kira Ummi ya damƙa mata wasiƙar Unaizah da ya kar6a a hannun Unaisah, ya ce ta kai ma Natasha sannan ta faɗa mata wanene Musa, da kuma miyagun ayyukan da yake aikatawa.
Bayan da Ummi ta je ɗakin bata saurari haukan Natasha ba, ta zauna ta fyaɗe mata komai game da Musa tun daga biri har wutsiyar sa, Ya salam! Natasha ta razana sosai, hankalinta ya tashi matuƙa, ta ji baƙin ciki da takaicin cin amanar da Musa ya yi mata, sai yanzu ta gane dalilin da yasa baya son ta san kowa nashi, ta daɗe tana mamakin dukiyar shi, saboda baya gajiya da basu kuɗi ita da Unaizah, ashe ba mutumin kirki bane ɗan blood cults ne, ba komai ya fi karya mata zuciya ba, face sadaukar da Unaizah da ya yi, ashe kwata kwata Natasha batasan inda ya kai Unaizah ba, ya 6oye mata komai, ita a yadda ya faɗa mata gurin mommynta zai mayar da ita, ita kuma Unaizah ya yaudare ta da sunan zai kaita korean school. Abun da ya faru a lokacin da zai sadaukar da Unaizah, Natasha bata a ƙasar, batasan komai ba, sai dai ta dawo ta taras da babu Unaizah agidan ta. Natasha ta yi kukan baƙin cikin da bazan iya misalta shi ba, a lokacin da Ummi ke bata labarin yadda Unaizah ta ƙare a gidan kurkukun ƙaddara, ta yi danasanin ƙulla alaƙa da Musa, ta tsane mashi sau ba adadi, gaba ɗaya ta ji rayuwar duniya ta sire mata, musamman da ta karanta wasiƙar Unaizah da Ummi ta bata, baƙin cikinta Unaizah ta mutu da tunanin harda ita Musa ya ci amanarta, bayan ita batasan komai ba. A ranar saida Ummi ta yi tunanin Natasha bazata rayu ba, saboda yadda ta dinga fasa ƙara tana fitar da gumi akan fuskarta, ta dinga lallashinta tana roƙonta akan ta yi haƙuri abun da ya faru ya riga da ya faru, yanzu haka Musa yana a hannun hukumar Isod zasu kai shi kotu, amma ina Natasha ba ta fahimtar komai...
__________________________________
ISOD HEADQUARTER
DG OWAIS💪🔥
Yana a tsaye gaban ƙofar shiga Cell, a hankali yake danna code ɗin ƙofar, bayan da ta buɗe ya shiga daga ciki,
Wa zan gani idan ba Ɗan iya ba,
Yana a kwance kan floor kamar mushen jaki, warinsa ya cika cell din, 6arin mazaunansa ya ƙone fatar duk ta sa6ule jawur ba ƙyan gani, sakamakon ƙonewar da ya yi, badan ana yi mashi treatment ba da tuni naman wurin ya ru6e, amma da yake basu son su mutu sun fi so su fara girbar abun da suka shuka tun a gidan duniya shiyasa suke duba lafiyar shi, kwata kwata babu gashin gemunsa ya ƙone ƙurmus, yatsunsa duk sun lankwashe sun ƙone, ko sutura babu a jikin shi sai ɗan pant ƙarami irin na mata, sai nishin azaba ya ke saki, daga gani yana jin raɗaɗi ba kaɗan ba, cikin fitar hayyaci ya ke yin sambatu yana fadin, "Wayyyo Allah na, Wayyo na shiga uku na baniiiii, na baniiii, na baniiiiii na lalace, jikina zafi, ku sosa min bayana, ku sosa min ɗuwawuna ƙaiƙayi nake ji, ku cire min ciwon jikina, zan mutu..."
Girgiza kai Owais ya yi ko kaɗan bai ji tausayin shi ba. A hankali ya zauna kan kujera tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana kallon shi.
"Baka ga komai ba Dan Iya, wannan somun ta6i ne na daga azabar dake tunkaro ka, ko ka manta rayukan da kuke ƙonawa da fetur? Ya ka ji raɗaɗin na raunin jikin ka?"
Da ƙyar ya iya juyo da kansa ya dubi Owais da idanunsa da suka kaɗa jawur kamar jan gauta, hancinsa sai tsiyayar da tsinkakkar majina yake yi gwanin ban ƙyama.
Ƙaton le6en nan nasa ya ƙonu da wuta ya yi sumtum kamar ganda.
Daga gani yana jin azabar radadi ta ko'ina a jikin shi.
Muryarsa ma bata fita, guragura ya ke magana..
"Ba dati, na tuba, ku min rai, na gane kushkurena, Ku kai ni asibiti su cire min ciwon jikina, su canza min wata fatar, don Allah..."
Ƙyalƙyacewa da dariya Owais ya yi, duk da ƙyanƙyaminsa da yake ji, maganarsa ta bashi dariya.
"Sai da Lokaci ya ƙure maka, ka ga asirinka ya tonu baka da mafita tukunna zaka tuba? La'anannen Allah, azzalumi mai safarar ƴa'ƴan mutane ya kai su inda za'a azabtar da rayuwarsu, tayaya kake tunanin mu zamu yafe maka? In banda ma kai ɗin wawa ne jaki, kamar yadda baku da imani baku da tausayi, kuma baku iya yafiya ba, muma haka jami'ai muke akan mugaye irin ku, bamu da tausayi, idan muka fara azabtar da su sai sun ɗanɗani kuɗar su.."
ya ƙarashe maganar cikin fushi tare da bugun gaban table ɗinsa.
Fashewa da kuka Ɗan iya ya yi, nan take ya fara 6urkuta tusa da fitsari daga kwance, DG ya yi saurin zaro hanky daga aljihunsa ya toshe hancin shi, cike da jin ƙyanƙyami ya furta, "Abun ƙyama, yanzu ina tsafin nan naka? Da bakin ka? Suna ina? Ko zasu iya taimakon ka?" Ya faɗa yana ɗage masa gira.
Fashewa ya kuma yi da wani kukan, bakinsa har ya fara fitar da jini,
"Ka daina bana son ji, ka rabu da ni inji da abun da ke damuna, ka kira min matata da ya'yana su zo suga halin da nake a ciki..."
"Su yi maka uban me idan sun zo? Ka yi tunanin kana da wani dangi ne da ya rage maka? Matarka da ya'yanka sun ji komai da ya faru, sun tsanake saboda ka ja masu abun kunya, ka bar masu mummunan tabo a matsayin gadonsu, wulaƙantacce! ....."
Alkalamina bazai misalta tashin hankalin da Ɗan iya yake a ciki ba, wata irin wutar baƙin ciki ce ke ci a cikin zuciyar shi.
"Ban zo don na sawwaƙe maka radadin da kake ji ba, na zo ne don in tambayeka menene alaƙarka da Abdallah Muhammad Buzu, kuma su wanene ƴa'ƴansa daka sadaukar a kurkukun ƙaddara? Kada ka ce zaka yi min ƙarya! na riga dana san komai, kaine mugun da ya damfare sa ya kar6e masa jarirai har biyu!"
(Abun ka ga jami'i mai kaifin basira, bai nuna hasashe yake yi akan shi ba, saboda yasan ɗan iya shine leader na bangaren safarar ya'yan mutane na nan Nigeria zuwa kurkukun ƙaddara. Bayan haka salon yadda yake damfarar mutane ya 6oye fuskarsa da mask ya yi shige da mutumin da malam Jazuli ya bada labarinsa, uwa uba sunan da Abdallah ya faɗa a matsayin sunan sa wato Ja'afar Dila, toh Ja'afar din asalin sunan shi ne da ba kowa ya sanshi da shi ba, saboda nickname ɗinsa ya boye asalin sunan sa, ta haka Owais ya gane shine ya damfari Uncle Abdallah, bayan da Taj ya labarta masa komai."
Mugu da yake shaiɗaniyar zuciyar na nan, yana huci yace, "Banshan wa kake magana akai ba, ni banshan wani Abdallah Muhamamd buzu ba, babu wasu ya'ya nashi dana sadaukar, duka ƴa'yan nawa ne."
"Kada ka yi min ƙarya, ka duba halin da kake a ciki, wlh in baka faɗamin gaskiya ba zansa a shafa maka ruwan attarugu a jikin ka.."
Yawu ya haɗiya yana faman zare na mazurai ya ce, "Na san shi, shima member ne na kurkukun ƙaddara, shi ya sadaukar da ya'yan shi da kan shi, bani na sadaukar mashi da ya'ya ba, na rantse maka da Allah ban damfare sa ba..."
Cikin fushi Owais ya ce, "Ba zaka daina yi min karya ba? Ko so kake in aiwatar da abun da na fada?"
Ya ƙarashe maganar tare da kanga wayarsa a kunne, "Ku shigo min da ruwan attarugu cikin cell din Ɗan Iya..." Tunkan ya ƙarashe maganar ɗan iya ya dabarbarce cikin razana ya shiga zayyana mashi komai.
"Ka sadaukar da ya'ya talatin, na ga sunayen su, amma tayaya zan iya gane su wanene ya'yan Abdallah Buzu a cikin su? Ya ce min su biyu ne ya baka? Suna a raye ko sun mutu?"
Yana faman sakin tusa ya ce, "Haris da Deeja..."
Ajiyar zuciya Chief Owais ya sauke, dama saida ranshi ya bashi sune saboda akwai kamannin Abdallah a tare da su.
"Ka taimaki kanka Ɗan Iya.." Yana faɗa ya miƙe ya fuce daga Cell din.
Flashback
BARI MU KOMA BAYA MU JI MEYA FARU A TSAKANIN DAN IYA DA ANA A RANAR DA AKA NEME TA AKA RASA❗❓
Bayan tafiyar su gidan hajiya Adama, ya rage saura Ana kaɗai a cikin gidan, gyara gidan ta fara yi goge goge da share share, bayan da ta kammala bata huta ba, gashi ta gaji sosai, amma a haka ta koma kitchen ta ɗaurawa Baby Junaid Cherie don tasan da ya dawo zai fara neman abinci..
Ta kuma ɗaura girkin abincin rana, tsawon awanni tana zarya zuwa kitchen gurin duba girkin da ta ɗaura..
Idan ta ga komai daidai saita koma falo ta ɗan huta, dama da wayarta a hannunta da take chatting da sisters din ta, hakan yasa kaɗaicinta ya ragu. Hankalinta ya fi kwanciya ganin babu mai takura mata a gidan, mutumin da ta tsana fiye da mutuwarta, ko gifcinsa bata son gani saboda cin zarafin da yake yi mata, ya addabeta, shine silar damuwarta, kullum cikin fargaban shi ta ke..
A lokacin bata kawo komai a ranta ba, bayan da ta gama girkin lunch din ta kashe gas ta nufi bedroom din ta, ganin ɗaya ta yi yasa ta shiga toilet ta ɗauro alwala, ta ɗauko hijab dinta da take ta 6oyonta don kar a ganta a gane ta musulunta ta zura ta a jikinta, kafin ta kabbara sallar a tsanake, da ta kammala ta zauna ta fara kai kokenta gurin Allah.
Cikin ƙanƙan da kai take cewa, "Ya Allah, Ka fidda ni a halin da nake a ciki! Ka fi kowa sanin halin da baiwar nan taka take a ciki, ni bazan iya da shi ba, amma nasan kai zaka iya da shi, Ya Allah, ka kare ni daga sharrin Ɗan Iya, na tsani abun da yake yi mini, na tsane sa, ina jin zafin najasar da yake goga min a jikina! Ya Allah Ka raba ni da shi, Ya Allah ka tona masa asiri..."
Kuka ne ya 6alle mata, tana jin ciwon abun, yadda yake nuna mata fin ƙarfi, ya ci zarafinta, kuma ta kasa tona masa asiri, saboda tasan kota faɗa ba yarda za'a yi da ita ba, bayan haka a duk lokacin da ta yi gigin tona masa asiri sai ta ji kamar an shaƙe makoshinta, bayan haka ya yi mata barazanar zai kasheta in har ta faɗa ma wani abun da yake yi mata..
Addu'o'inta duka akan ɗan iya ne..
Ciwon kai ta fara ji, A hankali ta kwantar da kanta saman darduma, bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita..
Almost 1 hour tana sharar baccinta, kwatsam knocking din kofa ya farkar da ita, a dan firgice ta farka, gabanta na faɗuwa ta miƙe, ta yi zaton ɗan iya ne shiyasa duk ta sha jinin jikin ta, cike da zullumi ta furta, "Wanene?"
"Your husband to be..."
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Mahboob..
Da sauri ta cire hijab din jikinta ta daura kan gado, kafin ta je ta buɗe masa ƙofar..
Idanunsu na shiga cikin na juna, ta yi saurin sakar mashi murmushi, tare da mayar da idanunta akan j
Junaid da ya goyo a bayansa ya yi nisa a baccinsa.
"Me ya ke damunki ki ne? Na ga idanunki sun yi ja?"
"Wataƙil don na yi bacci ne" Ta bashi amsa da fara'arta.
"Ina mutanan gidan suke ne ko har sun tafi ne?"
"Sun tafi tun ɗazu, ni kaɗai ce a gidan... " ..
"Okay, ya faɗa tare da janyo Junaid daga bayan shi ya miƙa mata, "Take care of his excellency, ki kwantar da shi, idan ya tashi daga bacci pls ki yi mashi wanka, ki bashi abinci..." Murmushi ta yi shima ya yi mata murmushin.
wani kallon ƙauna suke jefawa junansu.
Bayan ta kar6i Junaid ta rungume shi a ƙirjin ta..
"Your command is my wish, amma kai ba zaka ci abincin ba? Ko baka jin yunwa..."
Girgiza kai ya yi, "Sauri nake yi zan tafi kallon match, bana so na yi missing, idan na fita zan biya gidan abokina zan ci abincin acan..."
Har ta buɗe baki zata ƙara furta kalma, ya yi saurin ruƙo yatsanta me sanye da zoben da ya bata ya manna mata kiss, ta saki baki cike da mamaki, ya ɗago tare da kashe mata ido ɗaya, "Take care of your self." Ya faɗa tare da juyawa cikin sauri, har ya kusa fucewa daga falon ya ji ta ƙwala masa kira,
"MAHBOOB" Faɗuwar gaba ya ji, a hankali ya waiwayo tare da daura idanunsa akanta, murmushi ya ga tana sakar mashi, "Lafiya ? Ya tambaya"ko akwai wani abu da ki ke son faɗa min"? Ya faɗa yanayi mata murmushi.
Girgiza kai tayi, "No, ka yi min kyau ne." Bai furta kalma ba, ya ɗaga mata hannu tare da sakar mata murmushi ya fuce.
Ji ta yi kamar tabi shi ko ta roƙe shi ya dawo ya zauna saboda faɗuwar gaban da take ji.
Fitowa ta yi daga dakin, ta nufi ɗakin Anila, tana kokarin kwantar da Junaid kan gado ya farka da rigimarsa yana ambaton sunan Mommy, koda ya ji muryar Ana sa'ilin da take lallashinsa nan fa ya fara kuka yana fadin shi mommy yake son gani, gurinta zai je,.
Lallashin shi ta yi da wayou da dubara ta ce, "In har kana son ganin mommy, ka yi shiru ka daina kuka, zan kawo maka abinci ka ci ka ƙoshi, idan na yi maka wanka sai mu bi su anguwa.." Yana faman yamutsa fuska da shagwaba ya ce, "To ina suka je, shine ma ta tafi ta barni.."
"Suna a gidan mommy Adama" tur6une baki ya yi..
Dakyar ta shawo kanshi ya yi shiru,
Ta miƙe da sauri ta je kitchen ta zubo masa cherie a plate, ta haɗo masa da juice ta kawo masa, da kanta ta zauna tana bashi yana ci, bayan da ya gama ta mayar da kayan abincin kitchen..
Ta dawo dakin, cire masa uniform dinsa ta yi, ta ɗauke sa suka shiga toilet, bayan ta gama masa wankan, ta fito da shi, jikinshi ɗaure da towel,
tana ta tunanin ya zata yi da shi? Gudun kar ya saka mata kuka in ya ga ta ƙi kai shi gurin mommynsa. cikin sa'a taga ya kama bacci, murmushi ta yi tare da kwantar da shi kan gado.
"Baby Junaid, asha bacci lafiya, ni ma bari na je na yi wanka, don nasan idan ka farka ba zaka barni in yi ba.."
Juyawa ta yi da sauri ta fuce daga ɗakin ta koma nata ɗakin ta shiga bathroom don ta yi wanka.
Bayan da ta shiga ciki, fara tu6e kayan jikinta ta yi ta ɗaura towel ta kunna shower, har zata zame towel din ta tuna da mahboob, murmushi ta yi tana tuna murmushin da ya yi mata kafin ya tafi, shagala ta yi da tunaninsa, har ta manta da abun da ya kawota toilet ɗin.
Kwatsam! Yanayin bugun zuciyarta ya sauya, ta dinga jin kamar wani abu zai faru da ita, fasa wankan ta yi ta mayar da kayanta ta fito da sauri don ta dubo baby Junaid, cikin sauri take tafiya, har ta kusa ƙarasawa ga bedroom din Anila kwatsam ta ji motsin mutun a cikin kunnanta, kwata kwata bata ga lokacin da ya shigo ba, ga dukkan alamu bata ƙofa ya shigo ba, ya yi tsafinsa ne, wata razana ta yi gabanta ya shiga faɗuwa, kwata kwata Allah bai nuna masa ita ba, ya wuce ya nufi bedroom ɗinta, Hankalinta idan ya yi dubu toh ya tashi, tun da ta ga ya nufi bedroom dinta tasan cewa ita yake nema, akan idon ta ya fito ya nufi kitchen ya ga babu ita, ya shige can ciki yana bin ɗakuna tare da kwaɗa mata kira da buɗaɗɗiyar muryarsa Ana, Ana
cikin sanɗa ta lalla6a ta shige ɗakinta ta datse kofar, ta ɗauko wayarta jikinta na kerma kaf kaf ta shiga camera, ta saita fuskarta.
Daurewa ta yi cikin ƙarfin hali ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tasan ba lallai ta rayu ba.
_Na yi maku wannan video don in bayyana maku halin da nake a ciki, ina ji araina kamar wannan ce dama ta ƙarshe, nasan kun kyautata mun a rayuwa, kuna so na, mun shaƙu da juna, amma ba lallai kowan nan ku ya yarda da abun da zan faɗa ba, nima bada son raina ba, bazan jure fasiƙanci da yake aikatawa da ni ba, in har ban tona masa asiri ba, zan haɗiyi zuciya ne na mutu saboda baƙin cikin shi, bakowa nake magana akai ba face Uncle Ɗan Iya, ya kasance yana kwanciya da ni a duk lokacin da nake tsaka da yin jinin al'ada, ban ta6a sani ba, sai dai in farka inji raɗaɗi a gabana, abun yana damuna amma saboda ban san meke faruwa da ni ba shiyasa ban kawo ma raina mutunne ke saduwa da ni ba, ina ganin abun kamar a mafarki ya ke faruwa, nama yi zaton aljanu ne, shiyasa a lokacin da damuwa ta mamaye zuciya ta, na yi duhu na rame, duk kuka nuna damuwa akaina na kasa fayyace maku komai saboda bansan amsar da zan baku ba. A ranar dana musulunta, a ranar na gano wanene ke yi min hakan, ina a kwance ya afka min da tsakar dare kamar yadda na saba gani a mafarkina, da ya ga na ganshi zan fasa ihu sai ya toshe min bakina ya hana ni yin magana, na yi kukan baƙin cikin da ba zai misaltu ba, ban ta6a zaton zai yi min haka ba. Ina ganin girmansa ina ganin mutuncin ahlinsa da suka zama majinginata, a lokacin na yi kokarin in fasa ihu ko in bangaje shi don in gudu amma ya sanya min ƙarfi, ya yi min sihirin da jikina ya mutu na kasa motsawa ya kwantar da ni kamar matatta ya biya buƙatarsa da ni, ban tashi farkawa ba, sai washe garin Allah, cikin mawuyacin hali na yi wanka na yi sallah, na kasa tunkararshi saboda ina kokwanton in shine ya yi min hakan a zatona jinni ne ya bayyana da suffarsa, amma daga baya na gano shine shaiɗanin da kan shi, batare da sanin kowa ba na je har ɗakinshi da niyar in zazzaga mashi masifa in kuma yi masa iyaka da kaina, amma koda na je na gama 6a6atun bakina na kuma ce zanto na masa asiri sai cewa ya yi, ina tunanin zan iya tona masa asiri? Idan ma na faɗa ma mutanan gidan wa nake ganin zai yarda da ni? Bayan ni ɗin bakowa bace, bare ce ƴar aiki ƙasƙantacciya mara galihu, zai fi in shiga taitayina shi mutunne mai haɗarin gaske yana da tsafi a jikin shi, komai nake yi yana kallona, in har na ƙara furta zan tona masa asiri, ko na yi gigin faɗama wani abun da ya ke yi min, da ni da wanda na faɗamawa zai haɗamu ya kashe. Bani da mafita, sarrafa ni yake yi da sihirinsa, ba irin magiyar da ban yi masa ba akan ya tausayawa rayuwata, ya daina aikata fasiƙanci da ni, shi fa musulmi ne kuma yasan babu kyau, namiji ya kusanci macen da ba muharramarsa ba! Haramun ne, ko don saboda mutuncinsa da na iyalinsa ya rufawa kansa asiri ya ƙyale ni, in ba haka ba zan gudu in bar masa gidan, bayan na tona masa asiri...
Ba irin barazanar da ban yi masa ba, amma ya ƙi saurare na. Bai da imani bai da tausayi, mugu ne..."
ta ɗan dakata tana share ƙwallarta, fuskarta akan Camera..
watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda ya ce ba zai kyale ni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kun ga ni kaɗai ce a gidan, yanzun nan na ga shigowar shi shiyasa na gudo ɗaki don in samu damar yi maku video. Don Allah don son ku da manzon Allah saw a duk lokacin da kuka kalli videon nan ku yi gaggawar kaishi ƙara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku 6ata lokaci, saboda shi ɗin mutum ne mai haɗarin gaske, ya sha yi min barazana akan in har na kuskura na faɗa ma wani abun da ya ke mini wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na faɗamawa shi yasa na kasa sanar da ku..."
Bata ƙarashe maganar ba ta yi saurin katsewa, bugun zuciyarta ya tsananta jin takun tafiyarsa gab da ɗakinta.
Cikin sauri ta janyo pillow ta zuge zip ɗinsa ta fasa soson ciki ta tura wayar a ciki ta maida ta rufe, juyowar da zata yi keda wuya kwatsam ya banko ƙofar dakin ya shigo.
Cikin rawar murya ta furta, "La'ila ha illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin!"