Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 87 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 87 Complete

Takun Ƙarshe

 Daga Alƙalamin Boss Bature🔥🌹

Cikin rawar murya ta furta, "La'ila ha illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin!"

 ƙyalƙyacewa ya yi da tantiriyar dariyarsa ta shaiɗanu tare da ɗaura kwartayen idanunsa akan fuskarta ya shiga washe jajayen haƙoransa...

"Dama saida raina ya bani zaka dawo don ka cutar da ni! Wai kai wani irin shaiɗanin mutunne? Mara imani da tausayi? Meyasa ba zaka rabu da ni ba? 

"Saboda kinsan sirrina! Ba zan ƙyale ki ba, ke barazana ce a gare ni..." Bai ƙare maganar ba ta katse shi cikin fargaba ta ce, "In har baka fara bibiyar rayuwata ba, tayaya ni zan san sirrinka? Meyasa kake aikata fasiƙanci da ni? Laifin me na yi maka? Kawai don ka azabtar da ni? Wallahi ƙwara na mutu da in ci gaba da haɗa jikina da naka! Kasa na tsani kaina, saboda ƙazantar da kake goga min!..."

 Cikin shesshekar kuka take yin maganar idanunta a cikin na shi, "Ba zan ƙara bari ka kusance ni ba, ko dai ka fita daga rayuwana ko kuma in tona maka asiri uban kowa yasan me kake aikatawa..." 

Ko gizau bai yi ba, sai ma wani shu'umin murmushi da yake saki, "Tun da har kin san komai, kuma kina barazanar zaki fallasa sirrina, ba zan ƙyale ki ba Ana, dama na faɗa maki dama nake jira da zan salwantar da rayuwarki kuma na samu...!"

 Gaba ɗaya ta ruɗe da jin maganarsa, gumin tashin hankaline ya fara tsattsafowa ta ko'ina a jikinta, kafin ka ce me tuni tsigar jikinta ta fara tashi haiƙam, la66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!

Ja da baya ta soma yi tana neman hanyar da zata ku6uta daga gare shi, duk inda ta yi sai ya taro ta, gaba ɗaya suka hargitsa ɗakin nata, ta dinga ɗaukar abubuwa tana jifar shi da su, ba yadda bata yi ba don ta ku6uta amma ta kasa saboda ya toshe duk wata hanya da zata iya guduwa, a ƙarshe ya damƙi wuyanta ya maka da bango ya matse ta, idanunta suka firfito waje, numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa, ta dinga fitar da nishi tana harba ƙafafunta..

Cikin shakakkar murya ta furta, "A.. Al... Allah  bab ba zai ta6a barin ka ba, Allah sa...ssai ya saka min cutarwar da kayi min, idan kana tunanin kashe ni shine mafita ka jira ka gani, ni zanyi silar tonuwar asirinka, kaima zaka mutu ne... " 

 Akan idanunta ya girgiza jikinshi ya riƙiɗa ya sauya suffar shi ya zama dodo, tsantsar tsoro da tashin hankali mara misaltuwa suka ziyarci zuciyarta, duk da tashin hankalin da take a ciki bakomai take tunanowa ba face ƴan uwanta da Aunty Anila sune damuwarta, babban baƙin cikinta zata mutu batare da ta fallasa asirin shi ba. Bata da mafita da ya wuce Allah, yana kallonta da idanunsa da babu ɗigon imani a cikin su, A haka da ya shaƙeta jikin bangon kokarin keta mata haddi yake yi.

Tana a cikin mawuyacin halin nan kwatsam idanunta suka hango mata Baby Junaid dake kokarin buɗe ƙofar dakin ta, ya zuro hannunsa ta ciki.

Wani irin faɗuwar gaba ta ji, kamar ta fasa ihu, saboda tsoron kar Ɗan Iya ya gansa don tasan muddin ya gansa sai ya kashe shi.

Da ƙarfi ta dinga yin kuka tana fasa ƙara, duk don ta hana shi jiyo sautin muryar Junaid dake kiran sunanta.

Junaid da ya ji kukanta, ya fago da idanunsa kaitsaye suka sauka akan bayan ɗan iya, a firgice ya razana tare da kware bakinsa ya fasa gigitacciyar ƙara ya bi ya ruɗe tsigar jikinsa ta shiga tashi ganin dodo.

Wani iko na Allah kwata kwata dan iya bai jiyo shi ba, kuma ya bashi baya, kuma harda ihun da Ana ke saki ya hana ya jiyo kukan Junaid. 

Girgiza kanta ta dinga yi, da hannu ta dinga yi masa alamar ya gudu ya gudu.

Nan take ɗan iya ya ji aransa akwai mai kallonsa, yana kokarin juyawa,

Junaid da ya gama razana cikin ikon Allah tsoro yasa ya juya a guje ya nufi ɗakin mommynsa, yana gudu towel dinsa na ƙwancewa, har tuntu6e ya yi ya faɗi ya miƙe da ƙyar yana kuka ya shige ɗakin su.

Yana shiga ya fara neman gurin da zai 6oye kansa.

Jikinsa na kerma ya buɗe wardrobe, ya taka gidan farko ya ruƙe na biyu da hannayensa ya haye sama ya kutsa cikin kaya ya 6oye, adai dai lokaci ɗan iya ya saki Ana ta yanke jiki ta fadi ƙasa bata mutu ba sai dai ta fita hayyacin ta.

Ya juya cikin sauri ya fito daga dakin ya soma neman wanda ya shigo gidan ya dudduba ko'ina bai ga kowa ba, har ɗakin Anila ya shiga a lokacin Baby Junaid ya daɗe da sumewa, bai ji wani sauti ko alama da zai bayyana masa akwai mutun ba.

Hankalinsa ne ya kwanta da ya tabbatar babu kowa kuma ya tuna basu dawo ba, ya baro su acan gidan Abdallah babu wanda yasan ma ya dawo gida.

Lokacin da ya koma ɗakin ya taras da Ana,  sungumarta ya yi a saman kafaɗarshi ya 6ace daga inda yake ya dira a ɗakin sirrinsa,  ya ajiyeta anan bayan da ya kafeta da sihiri ta yadda bazata iya ta6uka komai ba in ba da izininsa ba, ko magana ba zata iya yi ba, balle ta motsa jikin ta, kwata kwata bata a hayyacin ta. Ashe tsawon lokacin da suke ta neman Ana tana a ɗakin sirrinsa, shi kaɗai ya san inda ya 6oyeta, ba ci ba sha, bata iya komai, ta zama mutun mutumi, babu rabon Ana ta rayu, ya riga da ya gama da ita.

Daga baya ne da ya tabbatar ta mutu sai ya haƙa rami ya binneta a ciki, sati ɗaya kafin zuwan Isod Agents, shiyasa lokacin da suka haƙa ramin suka taras da gawarta bata yi komai ba saboda bata daɗe da mutuwa ba da kuma ikon Ubangiji.. 🥹

RIJF (ANAH)

(Kunji komai da ya faru a tsakanin Ɗan iya da Ana)

__________________________________🔥🌹

"Cau cau, gafara dai, namiji Uban maza, The mastermind behind the conspiracy da girman kujerarka Uban munafukan duniya, sarkin mugaye, an buga da kai an barka Jan wuya Alhaji Musa. Ƙaramin su babbansu, ko ku ce big boss, duk nine. Mai izza, mai arziƙi, mai jiji da kai, shugaban azzaluman duniya, wanda mutuwa ke tsoronsa, dodon dodonni, wanda ya fi ƙarfin kowa saboda sihirin sa..."

Kirari ya ke yi ma Alhaji Musa yayin da ya ke shiga cikin Cell ɗin da ya ke.   (😂)

Abun al'ajabi ba ya ƙarewa duniya, ni kaina da nake rubutawa saida na razana da ganin ɗan tahalikin nan, garƙame a cikin Cell, wato ruwa ne ya daki babban Zakara.

Ba ka jin komai sai sautin nishinsa da gurnaninsa kamar wani namun dawa, yana a zaune dirshan a ƙasa kamar mabaraci, ko suturar kirki babu a jikin shi, sai gajeran wando baƙi, ƙafafunsa a ɗaure suke da leg irons.

Dana kallesa sai da gabana ya faɗi ganin yadda halittarsa ta sauya, rabin fuskarsa ya lalace sakamakon Acid din da Unaisah ta watsa masa, fatar gurin ta zagwanye gwanin ban ƙyama, da ido ɗaya yake gani Sakamakon ruwan acid din da ya shiga idonsa ɗaya ya lahanta shi, gaba daya fatarshi ta lalace da raunukan bulalan da Evils suka yi ma shi har yau bai daina jin raɗaɗin azabar su ba, idan suka fara masa zogi ba halin ya sosa  saboda da zarar ya sosa sai fatar ta ɗuri ruwa ta fashe ta dinga fitar da gur6ataccen ruwa mai ɗoyi, kafaɗarsa ta hagu da Unaisah ta yanka da zarto ta kumbura suntum har surgery aka yi masa a gurin amma still bai warke ba, ciwon har ya shafi hannunsa na dama ya kumbura suntum ya zamar masa jalli joga.

Gaskiya Unaisah ta lahanta bawan Allahn nan ba kaɗan ba, da zai samu damar da zai ku6uta wallahi ita ce mutun ta farko da zai fara kashewa har lahira, a yanzu haka da yake zaune wutar baƙin ciki ce ke ruruwa a cikin zuciyar shi.

idonsa ya kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin sa, ga wani jan ruwa da ya kwanta a ciki

Yana jin kirarin da DG ke yi ma shi, ya murtuƙe fuska kamar gwaggon biri saboda muni, ƙyanƙyami da ƙyamarsa ne suka cika Owais ya kasa zama sai dai ya tsaya a tsaye, ya toshe hancinsa da hanky

"Allah ya yafe maka Musa, tun a duniya kenan ka fara ganin sakamakon zunuban daka aikata, ina ga idan aka binne ka inda dukiyarka ko wani abu da kake taƙama da shi ba zai cece ka ba sai mugun halin ka? Ko da yake ba zuwa na yi don in yi fira mai tsayi da kai ba, nasan yanzu ka gane Allah ɗaya ne! Da juyi ɗaya Allah ya rikito da kai, ya kar6e komai da kake taƙama da shi, ya ɗebe albarkar rayuwarka, ya raba ka da kyawun suffarka! Ya kar6e dukiyarka da ƙarfin sihirinka! Ya raba ka da kowa naka, ya kuma zubar maka da mutuncinka, ya bar maka ranka da baƙar zuciyarka don ka ga ishara da idanunka, kai hatta ƴan jami'iyarka sun soke ka daga member ɗin su, sun ma ce a ƙaddara cewa basu taba saninka ba, saboda kowa gudu yake ya ra6eka ta shafe shi. Matarka tana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, tun lokacin da ta ji abun da ka yiwa jinjirarta daka raba ta da ita, nan take ta yanke jiki ta faɗi, yayanka Alhaji Ubaid ya yafe ka daga zuri'arsu, ya ce a daina ma kiran ka da Musa Wadata, saboda Alhaji Mu'azzam Wadata ba ubanka bane, ya fayyace ma kowa dangantarku, mahaifiyarku ƴar aiki ce a gidan su, halinta sak irin naka, bayan da mai gadin gidansu ya yi mata ciki, ta ƙulla makirci ta ce cikin Alhaji Mu'azzam ne, sai da tasa ya aureta bayan ta yi silar mutuwar mahaifiyar su Alhaji Ubaid, ta asirce Alhaji Mu'azzam, da ta haifo ka, ta ci gaba da mu'amala da mai gadin gidan, harta samu wani cikin ta haifi ƙanwarka, saboda Mu'azzam ya samu matsalar haihuwa, ƴa'ƴanta duk ba nashi bane, ta yi ne don ta ci gadon shi. Abun da na fahimta, shaiɗaniya ce ta haifi shaiɗan, mugun halinka a nono ka tsotse shi..."

Tunkan Owais ya ƙarashe maganarshi Musa ya fasa wata irin kururuwar baƙin ciki, har saida gefen bakinsa ya fashe jini ya dinga ɗiɗɗigowa, dama a raunace bakin yake, abun da ya fi tsana a rayuwar sa shine tushen shi, wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarsa, ya ji zafi da Alhaji Ubaid ya fallasa sirrinsa wlh da zai gansa a gabansa ba abun da zai hana ya binnesa da ran shi.

Yana gurnani cikin fushi ya furta, "Idan ma kana faɗamin ne don in saduda, to ka daina, ba a halicci zuciyata da rauni ba, ba zan ta6a karaya ba, ba abun da zaisa na yi nadamar abun da na aikata!

Ƙyalƙyacewa da dariya Owais ya yi hakan ya 6ata masa rai..

"Ina mamaki ne mutumin da rabin fuskarsa ya lalace, ba hannu ɗaya, ba ido ɗaya, wai shine ya ke da audacity din da zai iya furta wannan maganar? Me ya rage maka da bazaisa ka yi nadama ba? Bayan ga tsoro nan da tashin hankali kwance cikin idonka...." 

wata shu'umar dariya ya saki kamar jaki na haniniya.

"Na ci dubu sai ceto, ba yadda kuka iya da ni, na riga dana ci riba, babu hukuncin da za ku yi min wanda zai kai wanda na yiwa rayukan dana azabtar, raina ɗaya ne tak, da shi na kashe ɗaruruwan rayuka, da shi na azabtar da rayuka, da shi na 6ata zukatan rayuka, wanda har abada ba za a ta6a mantawa da ni ba.." 

ya faɗa yana damula mummunan bakinsa.

Owais ya ji zafin maganarshi, ganin kamar babu alamun karaya a tare da shi, a ransa ya furta wannan wani irin shaiɗanin mutunne? Anya mutun ne Musa? Gaba daya Elders sun saduda banda shi, in wani ne yake a halin da yake a ciki wlh ko kalmar alifun bazai iya furtawa ba, amma da ya tuna wanene Musa gurin girman kai da izza sai ya fahimci koda ya karaya ba zai bari ya gane ba ko dan ya baƙanta masa rai.

Hakan yasa shi sakin murmushin gefen fuska.

Kafin ya soma yin magana cikin nutsuwa yana kallon cikin idanunsa.

"Waɗannan rayukan daka azabtar yanzu suna a cikin rahamar Ubangiji, sun barka da tarin hakkinsu akan ka, idan kana farin ciki saboda ka zalunce su to ka daina, kanka ka zalunta Musa! Ai kai musulmi ne, kuma ka san Allah baya yafe hakkin dake atsakanin bayinSa. Me ya ja ma shiga halin da kake a ciki?" Ya faɗa yana nuna sa cike da ƙyanƙyami.

"Hakkin waɗannan rayukan, sune zasu baibaiyeka da fitintinu iri iri har abada, bayan haka bari na yi maka fashin baƙi tun da na fahimci kai dabba ne, jahili, kuma daƙiƙi.."

 cikin fushi ya ke jifar Owais da harara da idonsa ɗaya kamar ƙwayarsa zata faɗo ƙasa.

"Yanzu na ƙara yarda cewa zalunci ƙaiƙayi ne da ke komawa kan me shiƙa, abun da baka sani ba, silar tonuwar asirin ka, ƴar ka Zeenatu ta kashe kanta saboda jin wanene Ubanta da kuma zaluncin da ya yi ma ƴar uwarta Unaizah..."

bai ƙare maganar ba Musa ya yi wata irin zabura kamar zai miƙe, ya zaro idonsa waje cikin tashin hankali da baƙin cikin jin abun da kunnuwansa suka jiye ma shi

"Meyasa na ga tun yanzu ka fara karaya, ai ban kai ka in da na ke son ka je ba, bayan haka rayukan daka ƙullawa makirci cikin kankanin lokaci sun warke daga raɗaɗin da ka ƙunsa musu, Shureim da Ummi suna atare da ƴar su Batool, da zarar mun gama shari'arku, zamu shafa fatihar auren su..."

 cikin ƙunci da damuwa ya ƙara murtuke fuskarsa, ji yake kamar ya binne kansa don bakin ciki, zuciyarsa sai tafarfasa take yi..

"Sheikh Imam malik, da ka ƙullata a ranka, ka daɗe kana zaluntarsa don ka ƙunsa masa bakin cikin da zai yi silar mutuwar sa, a yanzu haka yana nan da ransa da lafiyarsa, harma ya je gano matarka Sarah da ke a kwance gadon asibiti, ka duba ka ga fa duk irin cutarwar da ka daɗe kana yi masa bai ji komai ba.."

Wata wutar baƙin ciki ce ta taso mashi ya dinga buga kansa jikin bangon bayansa, jikinsa ya ɗau zafi rau, ya Ilahi, Ya rasa ina zaisa ranshi ya ji dadi? Duk tsawon lokacin da ya ɗauka yana wahalar ƙulla masu makirci don ya baƙanta masu rai kenan yanzu komai ya tashi a banza? Hakan na nufin haƙarsa bata cimma ruwa ba? Kwata kwata Imam bai ji zafin komai ba a ransa? Shifa duk a zaton shi imam malik yana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, ciwon zuciya ya kama shi ashe wai har yana da kuzarin da zai iya taka ƙafar sa!

Chief Owais da ya lura ya haɗa masa sha tara na baƙin ciki wani sanyi ya ji yana ratsa zuciyarsa..

"Ka kwantar da hankalinka mana ai ban ƙarasa maka labarin ba, ƙanwarka Laura..." Zare idanunsa ya yi cikin damuwa.

"Sakamakon razanar da ta yi lokacin da ta ji komai game da kai, ta haɗiyi zuciya ta mutu."

gigicewa ya yi gaba ɗaya ya rikice har baisan sa'adda ya fara cizge akaifunsa ba, duk ya faffasa su, jini ya dinga tsattsafowa.

"Sannan, na ji abun da ya faru da kai, na taya ka baƙin ciki, ashe shatun bulalin jikinka, Evils ne suka zane ka, bayan sun tu6e maka suturarka ka dinga ihu kana kuka, suka shafe maka jikin ka da gishiri suka jefa ka cikin ruwa, na ce dama tsakanin shaiɗan da ɗan uwansa shaiɗanu ana samun sa6ani? Sai kuma na ji wai na hannun damanka Mark ne ya ci amanarka, ya musanya maka zuciyar Batool da ta giant, abin takaici!  A ƙarshe burinka bai cika ba, kuma zaka mutu baka cika shi ba...." 

Wani nishin baƙin ciki da Alhaji Musa ya saki nan take ya burkuta zawo a cikin wandonsa, wari ya cika cell ɗin.

Chief Owais ya toshe hancinsa da bakinsa da hanky, har sai da ya yi kakarin mai.

Da ƙyar ya iya furta, "Ƙato da kai kana sakin kashin zaune, ko ka yi zaton ni kaɗai nake tare da kai..."

Ya faɗa tare da nuna masa surveillance cameras ɗin dake a kowace kusurwa, "Ba wai iya jami'an isod ke kallon ka ba, duniya ce take kallonka..." 

Wata zabura Alhaji Musa ya yi jikinsa ya hau kerma kamar mazari, tashin hankali tsantsa ne akan fuskarsa, kunyar duniya ta kama shi.

6a66akewa da dariya Owais ya yi, "Haba ranka shi daɗe, meyasa tun yanzu zaka razana? Ba zaka bari mu shiga kotu ba.." 

Ya faɗa tare da juya masa Screen ɗin Ipad ɗin hannunsa, wai ashe tun zaman shi live video ya ke ɗauka.

Alhaji Musa ji ya yi kamar ya haka ƙasa ya binne kansa saboda wutar bakin cikin dake azabtar da zuciyarsa, Owais ya gama da shi, ya kashe shi da ranshi, ya ruguza duk wani mutuncinsa a idon duniya, yanzu kowa ya ga mummunar suffarsa da halin da ya ke a ciki.

"Da zaka ga sharhin da mutane suke yi akan ka, sai ka ji ka tsani kanka, tsinuwa ce da la'anta ta ko'ina, sai kuma dariya da yi maka Allah shi ƙara." 

buga kansa ya yi jikin bango da ƙarfi.

So yake ya mutu sai dai ba halin mutuwa, da biyu suka ɗaure mashi ƙafarshi da ɗayan hannunsa marar ciwon, don sun san zai iya amfani da su gurin kashe kan shi, ga zuciyar tashi da ke ta ƙonuwa da bakin ciki ta ƙi bugawa bare ya ware, lokacinsa bai yi ba. Tun a duniya ya fara ganin sakamakon zunuban da ya aikata, da ya ke jaki ne yafi jin kunyar duniya baisan tun awurin zare ransa zai gane kuskuren sa.

"Unaisah ta yi maka ta'asa Musa, ka ga kuwa mummunar halittar jikinka? Kamar gwaggon biri, so ta yi ta kashe ka, amma mahaifinta ya hana abata damar da za ta yi hakan saboda ba ya son ƴarsa ta zama silar mutuwar wani, bayan haka mun fi so ka fara gir6ar abun da ka shuka anan kafin ka baƙunci ƙabarinka.

zufa ta wanke fuskarsa, sai faman gurnani ya ke yi da nishi.

"Na ga duk abubuwan da nake so na gani a tare da kai, amma banga nadama ba, sai dai itama nadamar za ta zo maka ne a yayin da ka ga wannan..." 

Ya ƙarashe yin maganar tare da zura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya zaro wasika,

"Ka nemi duniya ido rufe, ka biyewa son zuciyarka, ka dinga yima mata ciki suna haifa maka ƴa'ƴa, ba kai tunanin iyayen ya'yan da su kansu yaran wani hali zasu shiga ba idan su ka ji irin cin amanar da ka yi masu, ka kasance me son kai Musa, burinka ka faranta ranka, ka nakasa waninka in har zaka samu abun da kake so, nasan Unaisah ta faɗa maka game da wasikar da ƴarka Unaizah ta bada a baka, to gata nan ta bani in baka, ya rage naka, in ma ka karantata ko ka ketata, matsalarka ce, amma zai fi ka karantata, ita ta rubuta da kanta.." 

a hankali ya ɗaura masa wasiƙar daga gabansa.

Tun kafin ma ya buɗe wasiƙar ya karanta abun da ke a cikinta, wasu tagwayen hawaye suka fara zarya kan kuncinsa.

Har Owais ya fuce daga cell din bai lura ba, ya kafe idanunsa akan wasikar da ya gaza buɗewa, yana jin fargaban ya ga me Unaizah ta rubuta masa!

Lokaci ɗaya ya fara tariyo komai nata, gaba ɗaya ƴa'ƴansa da ya sadaukar bai ta6a yi ma wani son da ya yi ma twins ɗinsa mata ba, Zeenatu da Unaizah kuma su kaɗai ne ya samu ta hanyar Aure cikin waɗanda ya sadaukar, son duniya ne da ya rufe masa ido ya ja ya sadaukar da su gashi nan yanzu ya ja dukan su basa a raye saboda zaluncin shi.

Da yatsun hannunsa mai ciwon ya samu ya buɗe wasiƙar da ƙyar, yana ganin handwritting ɗinta ya shaida ita ta rubutata, ta yi rubutunne cikin harshen da ta fi ji british english, da ƙyar ya samu nutsuwar karantata.


Idan wani ya zalunci yaro, iyayensa ne na farko da yake fara kai kukansa wajen su, amma idan iyayen nasa ne suka zalunce sa, wurin wa zai kai kukansa? Ni da bansan akwai wanda ya halicce ni ba? Laifin me na yi maka daddy? Me na yi maka dana cancanci wannan hukuncin daga gare ka? Ka sani kokwanton anya kai ubana ne? Anya kana da zuciya a ƙirjin ka? Uba koda azzalumi ne shi zaka same shi da son ya'yan shi sai dai ya zalunci na wasu, me na yi maka? Yanzu na gane dalilin da yasa ka hana in san kowa naka, ka 6oye min real identity ɗinka, ni ina kokwanton ma zai yi wuya idan ba sato ni ka yi ba. Ka yaudare ni, ka ci amanata, ka ha'ince ni, ashe wasan da kake yi min da dariya da gatancin da kake bani duk kana yi ne saboda ka riga da ka sadaukar da ni saboda biyan buƙatarka, ina farin ciki daddyna yana sona, yana gatanta ni, baya son 6acin rai na, ya fi sona fiye da komai ashe na yi kuskure, ka ci amanar yardar da na yi maka, baka ta6a sona ba, ka karya zuciyata. Daddy na rasa wani zunubi na yi maka! Ubangijin da ya halicce ni ma ka hana in san shi, ka yi min ƙaryar babu wani addini, idan na ga kana yin sallah sai ka ce motsa jiki kake yi, kawai saboda ba ka son in ra6i rahamar ubangiji na, ka hanani duniyata ka kuma hana in nemi lahirata daddy, kun haɗu kai da mommy kun gur6ata rayuwata, ka yaudare ni, ka ce korean school zaka kaini, ashe gidan matsafa ka sadaukar da ni. Burinka ya cika, sun wulaƙanta ni, kamar karya suka maida ni, mutun shidda a kaina, manya waɗanda suka fi ƙarfin shekaruna, ni ɗaya, shekarata sha shidda, ka fi kowa sani. Abun da suka yi min ban ji zafinsa ba fiye da yadda na ji zafin cin amanar da ubana ya yi min, meyasa baka kashe ni ba tun farko? Wallahi na yi danasanin kasantuwarka ubana, mugu, azzalumi, mara imani, alade mai kwanciya da ƴar cikinsa. In sha Allah sai rayuwarka ta wulaƙanta, kukan baƙin ciki da na yi sai ka yi ninkin baninkinsa, radadin azabar da na ji sai ka ji mafiyinsa. Na tsanake! Na tsanake ka!! Ka kawo ni kurkukun ƙaddara don matsafa su amfana, nima na amfana, addinin daka hana in sani, ka ke boyemin don kar Allah ya tuhume ka, ƴar uwata Unaisah ta fayyace min komai, ita ce ta ganar da ni wanene mahaliccina, bayan haka silar zuwa na kurkukun kaddara, Allah ya haɗa ni da yan uwa masu sona tsakani da Allah, sun bani tarbiyar da baku bani ba, sun bani kulawar da baku bani ba, ku kuma ku je ku da Allah, ga duniyar nan, ita da kuke nema Allah ya bar ku da ita daddy, ku ga idan zata amfane ku, kuma duk min daran daɗewa kuma zaku zo inda nake. Allah ya isa ban yafe maka ba! Allah ya saka min cutarwar da ka yi min

Bai ƙare karanta wasikar ba ya fashe da kukan baƙin ciki, wani irin ƙunci mara misaltuwa ne ya baibaye zuciyar sa, kuka har da majina, ya jibge guri guda kamar bijimin sa, haƙiƙa kalaman Unaizah sun karya zuciyar shi, sun sa shi jin raɗaɗin da ba zai misaltu ba, gaba ɗaya ya rasa meke masa daɗi, cikin shesshekar kuka ya ke ambaton sunanta Unaizah Unaizah, kwatsam! Ta soma yi masa gizau a cikin idanunsa, ya zama kamar mahaukacin kare, ya dinga haushi yana kai hannu zai kamo ta sai dai ya ji ya cafki iska..

A ranar da Isod agents suka zo tafiya da baba Obie, kowa da kowa na family dinsa saida Ya hallara a babban falon gidan sa, tun daga kan ƴa'ƴansa, jikokinsa, hada Sheikh Imam malik shima ya zo, momma ma tana nan, jiya jiya aka sallame ta daga asibiti, ta samu lafiya, memory ɗin ta ya dawo.

family din matayensa da suke a tare da su duk suna anan, wasu suna a zaune kasa suna jimami, wasu suna a zaune kan kujera sun zagba tagumi, wasu ma kasa zaman su kayi, kowa ya shiga tashin hankali da damuwa.

A gaban Kofar dakinsa Agents din suka tsaitsaya Chief Owais ne agaba, dama Ya faɗa masa idan suka kammala binciken su suka kama Elders zai buɗe ƙofar, bayan da yayi knocking ƙofar cikin karyayyar Murya yace"baba mun zo mu tafi da kai headquarter din mu,  jibi za'ayi zaman shari'ar ku"

kowa Jiran fitowarsa ya ke yi wasu Allah Allah suke Ya mutu adakin karya fito da ransa.

Lokacin da suka fara jiyo alamun zai buɗe ƙofar dakin, Hajiya saratu tayi kukan kura ta dira agaban kofar dakin, Ta daddafeta da hannayenta, tana kuka ta dinga rokonsa tana fadin baba dan Allah kada ka fito, baba na roke ka, baba ka 6ace ka tafi wani guri kayi rayuwarku, in ba haka ba zasu azabtar da kai, su kashe mana kai, dan Allah baba ka taimaki rayuwana, banason ka tozarta a idon duniya, bana son su ta6a lafiyar jikin ka, .... " 

lokacin da ta ke yin wannan maganar a cikin harshen Igbo tayi, Bakowa ya fahimci me take cewa ba, Yayyenta ne kadai suke jin harshen mahaifin na su.

Kowa dake agurin saida ya tausaya mata, baiwar Allah duk tabi ta haukace ta dinga kuka kamar karamar yarinya babu wanda bai zubda mata kwalla ba.

Ƙiri ƙiri taƙi bari ya fito, taƙi kaucewa taba Agents din hanyar da zasu kama shi.

A lokacin yana sauraron maganganunta acikin kunnansa, harya buɗe ƙofar, ya kasa motsawa saboda yaji saratu ta daddafeta ta hanasa ya karasa fitowa, kuma kowa ya kasa kawar da ita saboda karya masu zuciya da ta yi.

Ya yi kukan zuci mai radadi, Ya kara jin danasani fiye dana ranar da asirin shi ya tonu, ganin irin halin daya jefa ya'yan shi, kuma still basu daina jin shi a amtsayin Ubansu ba, saratu ta bashi tausayi ta karya mashi zuciya.

Dakyar Sharafudden da sir mubarak suka rabata da kofar dakinsa, tana turjewa suna janta, ta dinga kokarin ƙwacewa.

Lokacin daya fito babu wanda gabansa bai fadi ba, sun razana da ganin yadda ya sauya cikin ƙanƙanin lokaci, Ya rame sosai, tsufansa ya fito, dakyar yake iya ɗaga kafarsa, bakar jallabiya ce a jikinsa mai hula, Ya rufe rabin fuskarsa da takunkumi, saboda kunyar hada ido da su yasa bai iya dagowa ya dubi kowan nan su ba, har saida suka hada baki gurin furta Baba.

Tukunna a hankali ya ɗan dinga satar kallon fuskokin su ɗaya bayan daya tun daga kan ya'yan shi ya fara, har izuwa kan jikokinsa, akan fuskar kowan nan su ya karancin halin da suke a ciki, bai taba jin kunyar kansa irin na yau ba, jikinsa yadinga kerma kamar mazari, kukan saratu Ya cika kunnansa akan idon shi yaga Sir mubarak da Sharafudeen sun nufi daki da ita, tana ta kiran sunan shi tana fada masa ya 6ace kada ya bari su tafi da shi, a karshe ma hada zagi tadinga hada masa baba tana cewa ya 6ace, wallahi in ka bari suka tafi dakai Allah ya isa ban ya fe maka ba.

Bai ƙara tabbatar da raunin mace da tausayinta ba sai yau, Duk irin abun da yayi wa saratu ya aura mata mijin da shi yasan ba son ta ya ke yi ba, Ya kuma gur6ata shi, amma ahaka take nema ta cece shi saboda bata son ataba lafiyarsa.

A daki suka sanya saratu, tare da twins din ta, suka umarce su da su zauna tare da ita, gudun kada ta lahanta kanta, daga bisani su ka kulle dakin, ta yadda ba zata iya fitowa ba.

Tadinga bubbuga kofar, twins suna rurruketa tana bangaje su, su fadi ahaka zasu mike su cigaba da ruƙe ta.

Babu wanda ya ƙara furta kalma, tun bayan da suka ambaci sunan shi.

Ko handcuff agents din basu sanya ma shi ba, saboda nauyin yin hakan agaban Dg sukeji.

Lokacin da ya ke tafiya agents din na biye da shi, yayin da yake kallon kowa dake a kewaye da shi, karaf idanunsa suka sauka akan Jazz dake ta kuka kamar ransa zai fita, mommynsa turai ta rungume kansa a kirjinta, ita ta hana ya motsa da ba abun da zai hana yayi irin haukan da saratu ta yi, saboda kaunar da ya ke ma baba Obie, bakomai ne ya fado masa aranshi ba face maganganun da suka ta6a shi da baba Obie.

baba, Bana jin daɗin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba

 Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buɗi baki sai yace ni ɗan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba_

Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family ɗinka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina ɗaya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa

A cikin ransa yake tariyo komai yayin da yake kallon Jazz, at same time jazz daya ga irin kallon da baba obie yake masa shima saiya tuna da ranar da sukayi maganar..

_ Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani ɗan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ƙaddarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ƙaddararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita"

Jazz baka ɗauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance

Fashe wa ya kuma yi da wani kukan Aransa ya shiga furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Baba meyasa ka kasance azzalumi? baba me yaja maka? Meyasa ka sauya daga yadda nasanka? Ka karya zuciyata baba..."

Aransa yayi maganar, adaidai lokacin baba obie ya ɗauke idanunsa da daga kan Jazz, ya dan girgiza kan shi, hawaye na sauka kan kuncinsa..

Sau ɗaya ya haɗa idanunsa dana Momma ya yi saurin kawar da su gefe cike da jin kunyar ta data kamashi, itama ta zubda  kwalla kamar ruwan hawayen ta za su ƙare.

Bayan da suka fito gaba ɗayan su, Chief Owais ya buɗe mashi backseat na Motar shi..

Bai kaiga shiga ba, Sai ga Mota ta kunno kai cikin estate din kaitsaye ta nufo gurinsu da matsakaicin gudu tana gab da zata karaso gudunta ya ragu slowly tayi parking a gefen su.

Gaba ɗaya suka ƙura idanunsu akan Motar suna jiran ganin wanene zai fito.

Amininsa ne Jan kunne Ya fito daga motar, fuskarsa jaga jaga da hawaye, kayan jikinsa sun yi squeezing kamar mahaukaci, ko takalma babu a kafarsa.

Tsantsar tashin hankali da damuwa ne akan fuskarsa.

Sunyi mamakin ganin shi, bayan yasan neman shi akeyi don a kama shi, Owais ne kaɗai yasan da maganar zuwan shi, saboda tuntuni baba Obie ya faɗa masa ya ce zai mika wuya saboda baba Obie kuma ya cika alkawarinsa ya kawo kan shi, don a hukunta su a tare..

Gaba ɗaya haushin shi da tsanar shi su ke ji, gani suke kamar shine ya jefa mahaifinsu a halin da ya ke a ciki, Ko arzikin kallon mutunci bai samu agurin su ba, kwata kwata baya a cikin nutsuwar shi, kamar ya fara samun tabin hankali.

tun da ya fito bai nufi kowa ba sai baba Obie, Bai kaiga karasowa ba, Ya'yan baba Obie Suka kare ubansu cikin fushi suka daka mashi tsawa, su ka ce babu shi babu ubansu, tsakanin su sai dai hange daga nesa, amma ya gama kusantar inda mahaifin su ya ke.

Baba Obie Yana kallon aminin nasa da ke ta ambaton sunan shi yana roƙon su akan su bar shi ya gana da amininsa shi kaɗaine zai iya kwantar masa da hankali.

Baba Obie yaso su barshi suyi magana amma suka ki basu dama.

Akan idon shi, agents suka sanya mashi handcuff a hannayenshi, suka tura shi cikin motar su.

Owais Yace ya shiga daga ciki, cikin sanyi jiki ya shiga ya zauna, ya rufe masa cardoor din.

Ta gilashin motar yake ta kallon ya'yansa da jikokinsa dake ta kuka kamar ransu zai fita.

Chief owais da kan shi yayi driving din baba Obie.

Duk suna atsaitsaye motocin suka fuce daga Obie estate, gaba da bayan su motocin sojoji ne dana yan sanda saboda su ba su tsaro..

Lokacin da ya ke yin driving dinsa yana satar kallonsa ta mirror, zuciyarsa ta karaya da ganin yadda baba Obie ke ta kuka hada magina a hancin sa.

Cikin shesshekar murya yaji yana fadin kaicona, na zalunce kaina, na zalunci ya'yana da jikokina, na zubda mutuncina, na kashe rayuwar ya'yana da kaina, na kashe rayuwata, bani da hankali, dabbane ni, bazan taba yafewa kaina ba

ya dinga zagin kansa yana aibata kansa.

Kasa magana Owais yayi saboda baida abun da zai iya furta masa, amma daya tuna taimakon da yayi masu sai yaji zai iya masa wani abu.

"Baba bani da abun da zan iyayi maka, ka riga da katabka babban kuskure, shawara ɗaya da zan baka shine, Ka tuba ka musulunta ka komama Allah kafin mutuwarka, ko dan ka samu sassauci" ya faɗa ne kawai don ya kwantar masa da hankali amma shi kanshi yasan ina! 

"Owais, Allah ba zai ta6a kar6ar tubana ba, koda na kar6i musulunci, babu abun da zai sauya Owais, ayyukana gaba daya irin na yan wuta ne, tun a duniya owais nasan menene makoma ta, duk wanda ya aikata mai kyau ya sani owais, na aika zunubbai masu yawa munana, hakkin rayukan dake akaina basu kirguwa, ina jin kunyar mahaliccina, ina jin fargaban ranar da zan farka in ganni a cikin ƙabarina daga ni sai mugun halina Owais, wallahi na kasa kashe kaina ne saboda tsoron abun da zan taras a cikin ƙabarina, wallahi na zalunci kaina saboda neman duniyar da zamu mutu mu barta, gayanan naja ma kaina da ahlina.

 maganganunsa sun jefa chief owais a hali na damuwa.

"Duk da haka baba, ka musulunta in har dagaske ka tuba, kuma ka ji tsoron haɗuwarka da Allah, bansan hukuncin da kotu zata yanke maku ba, amma nasan zaku yi zaman gidan yari, kaga in hasashe na ya tabbata zaku samu sauran lokacin da yarage maku a duniya, hakan na nufin kana da sauran damar da za kayi ta yin istigfari",

Girgiza kai yayi cikin kunci yace"owais, koda Allah zai yafe ma kowa zunubinsa banda irin mu, fir'auna ma daya nemi ya musulunta kasa karasa furta shahada yayi ruwa ya haɗe da shi, dafa hankalin mu mun sani muka take sani Owais.."

"Baba Ka fahimta, kai ba musulmi bane, atlease in ka musulunta da imani a zuciyarka ko yayane zaka iya samun sassauci.." 

magiya owais yadinga yi masa yana driving a hankali saboda baison suyi saurin karasawa Headquarter din su, sarai baba Obie Ya lura da yadda ya ke yin driving din ya kuma fahimci dalilin dayasa ya ke yin hakan.

"Owais, zanyi tunani akan maganar ka.." 

"Baba baka da lokaci daya wuce wannan! Dama ce agareka, daga  jibi zamu shiga kotu za'a yanke maku hukunci, ba lallai mu sake haduwa ba, musuluntar da zakayi ita zata bamu kwarin gwiwar yi maka addu'a ko bayan ba ranka.." 

maganar Owais ta kayar masa da gaba.

Duk yadda yaso ya shawo kanshi abun ya gagara, ya fahimci yana son ya musulunta sai dai yana jin fargaban koya musulunta Allah bazai kar6i tubansa ba, kawai ya cire rai ne da komai.

Har suka ƙaraso Headquarter din baba Obie bai kar6i tayin Owais ba.

da shi da amininsa agents suka tasa su agaba Owais Yana a ruke da hannun kakansa Ya kasa sakinsa yana ta nanata masa kalmatusshahada don ya kar6a amma yaƙi ya furta abakin sa.

Gaba ɗaya Isod agents din dake a head quarter din da sojojin tun shigowar su, suka cire hulunansu tare da sadda kansu ƙasa, alama ce ta nuna girmamawa ga kakan dg.

A inda cells dinsu suke suka nufa da su, suna jiyo kururuwar sauran Elders din da su ka kulle a ciki, sai dai basu Iya ganin su, saboda kofar cells dinsu ta dabance, na waje bazai iya ganin na ciki ba, haka shima na ciki bazai iya ganin na waje ba, amma jami'an dake kula da bangaren cctv suna kallon komai da su ke yi a cikin cells din.

Bayan da suka saka kowan nan su, A cikin cell, suka kulle su.

DG bai iya barin headquarter din ba, saboda bayason Ya tafi yabar kakansa.

Bawan Allah Har dare Yana a nan, a karshe ma Cikin cell din Ya shiga, Ya zauna tare da shi, ya dinga kwantar masa da hankalinsa.

Har ya samu ya ɗan nutsu Ya dakata da yin kuka, sannan Ya soma tambayarsa yayin da suke a zaune kan kujera suna fuskantar Juna daga tsakiyarsu table ne mai ɗan tsayi.

"Owais, Idan akwai abun da kake son sani game dani ko kurkukun kaddara ka tambayeni na baka dama, nasan daga yau ba lallai Mu sake samun damar da zamu gana da juna ba... " 

cikin sanyin murya yace"ka fara fada min idan akwai inda ke yi maka ciwo a jikin ka, zansa docs dinmu su duba ka"

Yace a'a baya bukata, saboda a halin yanzu babu likitan da zai iya shawo kan abun da ke damunsa.." 

gwiwarsa ta sare da jin maganar sa.

"Tayaya zamu iya gano dangin fursinonin kurkukun ƙaddara da suka rage? Nasan mawuyacin abune mu iya ganowa da kan mu, bamusan ma ta ina zamu fara ba"

"Owais, baku da matsala da wannan, akwai bayanin da zan yi maka wanda zai amfane ku, sadaukarwar kurkukun ƙaddara kala biyu ce! Sadaukarwar jini da sadaukarwar mallaka, duka dai dole sai na jini ake sadaukarwa, amma akwai banbanci, ita sadaukarwar mallaka wanda zai yi ta, ba zai taba zama member na kurkukun kaddara ba, zamu yi yarjejeniya da shi ne, zai bamu abunda muke so, shima zamu bashi abun da ya ke so, da ga zarar ya sadaukar mun bashi abun daya keso to shikenan, mun raba jaha da shi, babu mu babu shi, ba member ɗin mu ba ne, Elders su kaɗai ne members na kurkukun ƙaddara, da sauran ma'aikatan ciki, tun lokacin da salon tsafin mu ya sauya muka gano cewa in muka sadaukar da jinin mu munfi samun karfin sihiri da iko, daga nan salon tsafin ya sauya wanda ada, ba sadaukarwar jini mu ke yi ba, mutun zai kawo ko ba jininsa ba mu kar6a mu biya masa buƙatarsa daga bayane komai ya sauya.." 

ya ɗan dakata yana mayar da numfashi kafin ya dasa da cewa 

"Littafin rijister na fursinoni wannan litattin da alƙalamin sirihi na rubuta shi, tun shekarar dana gurfanar da gidan kurkukun ƙaddara, ni ne mutun na farko dana fara sadaukar da jikokina na farko da yan ukuna suka haifa (Yana nufin Senate lafeef, Abdul razak, da sir mubarak) bayan na aurar da su tun suna da shekara ashirin da biyar a duniya, a lokacin basu shirya yin aureba amma saboda manufata akan abin da nake hari, ni na matsa masu har saida suka amince akayi aurensu da matayensu, kusan atare matayen su suka fara haihuwa, jariran suna zuwa ba araye ba, har sau biyar a shekara biyar, tukunna na barsu suka samu ya'ya bibbiyu daga nan naci gaba da sadaukar da jariran su, ko sun nemi su hana matayensu haihuwa ganin sunata wahalar daukar ciki yara suna zuwa ba'araye ba, ni nake canza masu ra'ayi, in nuna ina son inga jikokina da yawa saboda bani da dangi suyi haƙuri zan cigaba da nema masu maganin matsalar su, in sha Allah idan suka cigaba da jarabawa za su haifi masu rai, da haka na dinga samu suna haifamin ya'ya ina sadaukarwa"

Shi wannan Littafin rijistar na fursinoni yana ɗauke da sunan wanda yayi sadaukarwa da bayanansa, da kuma sunan waɗanda ya sadaukar, amma banda mutanan farko da suka fara sadaukarwa saboda lokacin ba cigaba, amma fursinonin da aka sadaukar daga baya duk na rubuta wadanda suka sadaukar da su, kuma babu wanda yasan inayin recording din nan sai Aurora, itace mutun ta farko data fara sani, tasan sirrina fiye da kowa, kuma da iznina tasani saboda kundin Yana da makulli a jikin shi, mai karfin shirine kadai zai iya buɗe shi, owais in har ku ka duba littafin zaku samu saukin gano duk wanda ya sadaukar da jininsa, bayan haka nima za ku ga adadin jikokina dana sadaukar da sunayen su har ma da sunayen mahaifan su, da kuma sauran Elders kowa akwai bayanansa a ciki fiye ma da haka za ku samu a cikin littafin sai dai bansan ko za'a iya samun littafin ba tun da nasan yanzu babu Kurkukun ƙaddara"

Bayan daya ƙarashe maganar su ka yi shiru kowa da abun da ya ke sakawa aranshi, ta wani bangaren Owais yaji dadin bayanin daya basa game da littafin saboda zai taimaka masu sosai.

"Baba a tsawon shekarun da ka ke sadaukar da jikokin ka, baka taba jin nadama ko rashin jin dadin irin azabtar da su da ka ke yi ba? Ko dan su ba kai ne ka haife su ba? Bakasan ciwon su ba"? 

Murmushin takaici yayi"Owais, ba lallai ka fahimceni ba, Wallahi mugune ni, zuciyata ta ƙeƙashe, ba ɗigon imani ko tausayi araina, tun lokacin da aminina ya bani shawara akan in kar6i gadon iyayena da suka barmin saboda muna a hali na talauci da matsin rayuwa, gashi ana farautar rayuwar mu, bayan haka muna da burin muyi arziƙi mu daukaka a fadin duniya, a lokacin dana mayar da sihirin jikina daga nan ne, Zuciyata ta rikiɗa ta koma irin ta shaidanu, sai nayi mugunta ko na zalunci wani nake jin dadi.."

 owais da ke sauraron shi, jikin shi yayi sanyi lakwas.

"Ina son Ya'yana fiye da kaina, fiye da kuma komai na duniyar nan, amma Jikokina da nake sadaukarwa ban taba danasani ba, Sai akan Yaro ɗaya wanda banyi niyar sadaukar da shi ba, na kuma yi danasanin sadaukar da shi, saboda bada son raina ba, tsantsar son da nakeyi masa ne Yaja mashi! Kowa yasan cewa kaine jikan da na fi so, a zahirin rayuwa, amma a baɗini, son da nake masa yafi na sauran jikokina harya zarce son da nake ma ya'yan cikina, tunkafin a haifesa nake jiran zuwan shi duniya saboda Allah ya jarabceni da son shi, kuma tunkafin a haifesa nasan cewa shi ne magajin kurkukun kaddara, Nasan za ka yi mamaki, amma ni kowani ɗa da ya'yana zasu haifa sai nayi duba akan shi don insan menene acikin matayen su, a canada aka haifesa, a asibitin Family din aurora, lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi, for the first time da nayi tozali da shi sai da na razana, ganin ya ma wuce yadda nake tsammanin shi..."

"Wanene"? Ya tambaya yana duban shi.

"Hmmm, ko ban fada ba, nasan ka san wa nake magana akan shi, auraro ta fada maka ko ba haka ba" jinjina mashi kai ya yi.

"Amma naji kace shi kaɗaine zai iya gadonka sihirinka meyasa? Kuma me hakan ke nufi"

"Owais, ilmin mu ne na matsa fa, abun bin jini ya ke yi, tun da ga kaka da kakanni, bakowa ne zai iya hawa karagar mulkin Elder ba, dole sai wanda kaddarar ta fadamawa ba.."

"Ina neman ƙarin bayani akan Sauran yaran, ƙaddarar Kurkuku da Bugun Zuciyar Kurkuku? Tayaya akai kuka za6e su a cikin fursinoni, kuka basu mukaman nan, Kuma kuka dauƙaƙa darajar su fiye da sauran prisoners din, sannan kuma saida Zuciyar Batool za'a iya dawo da ran kurkukun kaddara abun ya ɗaure mun kai na"!

Murmushi Elder yayi"tun kafin a haifesu muke jiran su suma.."

 ɗan zaro ido Owais yayi.

"Nasan za ka yi mamaki, mu matsafan kurkukun kaddara munsan da akwai yara da za'a haifa wadanda zasu zo da wata baiwa wadda zai yi wuya asamu mai irin ta a duniya, amma bamusan ta ina zasu 6ullo ba, abu ɗaya da muka iya ganowa a duban mu, shine za'a haife su a ɗaya daga cikin family din Elders"

"Kuma cikin ikon Allah hasashen mu Ya zamana gaskiya, ni aka samu ɗaya a family dina, musa Kuma aka samu biyu daga family dinsa.. " 

asannu Baba Obie ya fayyace masa komai.

Yaji dadin bayanin nan sosai.

"Zaka iya tuna wani ɗan Jarida da kuka kashe a lokacin baya, shekara bakwai da suka gabata"?

"Meye sunan shi?

"Uzair Abdallah buzu, ɗan uwan Zaheer Tajuddeen wanda ayanzu ina tare da shi kuma nasan kasan shi..."

 A taƙaice Chief Owais ya maimaita masa labarin don ya tuna masa.

Ƙyalƙyacewa baba Obie yayi da dariya kamar fa ya fara zaucewa

"Owais ƙwaƙwalwata bata mantuwa, tun da ka fadi sunan shi na tuna shi, nasan mahaifin Unaisah, da ɗan uwansa Uzair, Yan jarida mazauna garin Jos, ya'yan wa da kani, Taj yana zaune a gidan Uncle dinsa abdallah mahaifin Uzair..." 

da mamaki ya ke kallonsa jin yadda ya iya ruke komai.

"Inaso nasan ainihin abun daya faru? Tayaya kuka gane Uzair Yana yi maku leƙen asiri har kuka kona shi a cikin motar shi? 

Numfasawa yayi kafin a tsanake Ya soma labarta masa..

"Doka ce duk wanda yayi mana leƙen asiri ko yasan sirrinmu sai mun kashe, idan bazan manta ba, Mun kama Uzair Yana yi mana leƙen asiri agidan gonar mu dake a joss, a lokacin Muna tsaka da tattaunawa game da kurkukun ƙaddara, karfe wani abu na dare, Yaje da camera Yana daukar mu batare da sanin mu ba, kuma a lokacin bamu boye fuskokin mu ba, Yagan mu kuma yaji komai da muke aikatawa, kwatsam Musa ya hango hasken camera din shi.

 ya fada mana akwai wanda keyi mana leken asiri, kuma ya dauki video din mu.

Dayaji mun gane akwai mutun sai yayi saurin shigewa motar shi, Ya bata wuta, muka bishi a cikin motocin mu tare da bodyguards din mu.

Da muka ga zai iya tsere mana, sai nayi amfani da sihirina gurin sarrafa motarshi, burki ya ƙwace mashi, motar ta bugi bishiya ta tsaya cak ta kashe kanta, yana ta ƙoƙarin Ya tada motar taƙi ta shi.

Cikin sauri Ya buɗe motar ya fito da niyar ya gudu sai dai kash tuni mun kewaye Motar shi, yabi ya rude, hankalinsa Ya tashi Ya dinga rokonmu akan mu kyalesa Ya tafi zai fita a harkar mu, bazai tona mana asiri ba, a lokacin munyi mamakin ta yadda haryasan sirrin mu, muka tambaye shi meyasa yake mana leƙen asiri? Kuma tayaya akai yasan inda muke har yazo? Bayan haka dame dame ya sani agame da mu?

 Cikin rawar murya yace ya kai ziyara gidan gonar babansa da marece har dare yayi masa acan, yana akan hanyar dawowarsa ne yaga motocin mu suna shiga cikin dajin dake a kusa da gidan gonar, al'ajabi ya kamasa yayi ta tunanin su wanene a cikin motocin? Me zamuyi da tsakar dare a cikin daji a irin wannan lokacin, shine sai yabi mu don ya gane ma idonsa, yayi ta bin mu har yaga lokacin da muka shiga gidan gonar mu, Yabi bayan mu har yaga abun da muke aikatawa a sirrin ce, a lokacin daya bamu labarin bai bayyana mana cewa bashi kadai ne yasan sirrin mu ba, sai ya boye mana.

Na miƙa masa hannu nace ya bani Wayarsa, bai musa mun ba, jikinsa na 6ari Ya bani, dana duba sai naga babu abun da ya dauka, na tambayesa ina videon daya dauka namu, yace min bai yi saving ba, nace masa kada ya yi mana karya, in har yanason ya tsira da ranshi, Ya faɗa mana gaskiya, Amma ya kafe akan bakansa, mun fahimci yana da kafiya da taurin kai, musa daya zuciya yace"mu kashe shi kawai" dan iya yace"a'a kada mu kashe shi, saboda idan muka kashe shi, ba zamu iya sanin sirrinmu daya sani ba, zai iya yiwuwa bashi ka ɗai ya sani ba, wataƙil ya tura ma wani.

Daya ki faɗa mana gaskiya, Musa ya dauko galon din fetur abayan motar mu, ya fara masa barazanar zai kona sa in har bai sanar damu ba.

Bawan Allan nan, ya razana jikinsa ya kama kerma.

Unexpected muka ga ya yanke jiki ya faɗi.

Da muka dudduba shi sai muka gane firgicine yayi silar da zuciyarshi ta buga ya mutu, bamu ji dadi ba, mun so Ya fara fada mana kafin mu kashe shi da kan mu, musa da yafi mu zuciya ransa ya baci, Ya ɗauƙi gawar Uzair ya zaunar da shi a mazaunin driver, Ya rufe motar, kafin Ya soma zazzaga mata fetur, kwatsam sai ga kira ya shigo wayar Uzair dake a hannuna, dana duba screen din wayar sai naga sunan dan uwana, aminina ya bayyana, Musa ya kar6e wayar daga hannuna ya ɗaga kiran da yaji muryar wani yana kira sunan shi, shine yace mishi idan yana son sanin meke faruwa ya maida kiran video call.

Bayan da suka maida video call, daya tabbatar dan uwan nasa na kallon komai ta screen din wayar, sai Ya karasa zazzagawa motar fetur, Ya cinna mata wuta.

Daga bisani bayan ya katse kiran, muka binciki wayar Uzair din anan ne muka ga firar da su ka yi ta whatsapp chat din su, akan leken asirin da su ka yi mana lokacin da muka handame wani malamin ahlis sunna da ya'yansa, Taj ya nuna kin amincewarsa akan bin diddigin mu, amma Uzair Ya matsa number akan saiya gano su wanene mu don ya fallasa asirin mu.

Da muka ga haka, sai muka yanke shawarar zuwa gidan Taj, Don mu kashe shi, tunda mun fahimci shima yasan sirrin mu.

Bamu tsaya bata lokaci ba, muka garzaya unguwar da taj Yake, adaidai Lokacin da motocin mu suka shiga layin muka hango motarsa yayin da ya ke kokarin guduwa, aguje muka bi bayansa..." 

girgiza kai chief owais yayi, idanunsa suka cuccuko da kwalla.

"Kaji yadda komai ya faru, mu bamu san Taj yana araye ba, ai da tuni mun kashe shi, mun dai san Yarsa tana araye, bayan da muka cinna masa wuta, bamusan tare da yar sa ya ke ba, sai daga baya muka gano cewa tare da yarsa Ya gudu, hankalin mu ya tashi, muka fara nemanta, cikin sa'a muka gano tana araye, hannun Fulanin daji, muka cigaba da bibiyar rayuwarta, har zuwa lokacin da muka ɗauke ta.." 

ya ƙarashe labarin tare da sadda kan shi ƙasa cikin nadama da takaici.

Shiru su ka yi na wani lokaci, babu mai magana a cikin su.

Owais ya zaro wayarsa Ya kira cook ɗinsu Ya umarci a kawo mashi lunch a cell din kakansa

Jim kaɗan Junior agent Ya shigo da madaidaicin tray mai dauke da kayan abinci ya ajiye a tsakankanin su.

"Nasan kana jin yunwa"

girgiza kai yayi"a halin yanzu owais, babu abun da nake jin daɗinsa, ko naci ɗaci zanji"

"Ka daure ka ci, dan Allah"

"In har zaka bani abaki kamar yadda ka sabamin lokacin da kana yaro zanci ." bai musa mashi ba, da ya ke yaji dadin hadin kan daya basu, komai ya tambaya yana amsa mashi, hakan Yasa shima Ya ɗan faranta masa.

Abaki ya soma bashi yana ci suna fira.

"Malaman Jazuli, tayaya akai kuka kama sa yana maku leken asiri? Naji ka ambaci sunan shi, nasan komai game da labarinsa, sheikh imam ne Ya fadamin.."

a takaice ya fayyace masa komai.

Murmushi baba Obie yayi"Allah sarki sheikh imam malik, ashe dama da biyu ya shiga jikina ban ta6a ganewa ba, Allah ya taimakesa da tuni shima mun kashe shi.." ya faɗa yana dan girgiza kansa.

"Malam Jazuli, tun ranar da yaje suka hadu da dan iya agidan gonar mu, akan maganar sadaukarwar da zaiyi, kallo daya dan iya yayi masa ya gane basaja yayi don ya shiga jikin mu, amma sai bai nuna masa ya gane komai ba, har sukayi sallama Ya tafi, arana ta biyu dayazo yi mana leken asiri cikin rashin sa'a dan iya yajiyo kanshin mutun bare a gurin da muke, anan ya gane akwai mai bibiyar mu yana mana leken asiri, amma bamu iya kama shi ba, Harya tsere mana, sai dai abun da baisani ba, mu matsafa ne, idan muka so da sihiri zamu iya ganin komai daya faru abaya ta madubin tsafin mu, ta haka muka gane wanene shi.

Da farko bamu yi niyar kashe shi ba, Na kirasa awaya na gargaɗesa akan karya kuskura Ya fitar da sirrin mu, Ya manta da abun daya gani, ya fita sabgarmu, In ba haka ba, zamu dauki mataki akansa.." da budar bakinsa sai cewa yayi"ta Allah ba tamu ba, bai fara don ya tsaya ba, mu bamu isa mu sa yaji tsoron mu ba, Da Allah ya dogara, mu zaija ma kunne muji tsoron Allah mu daina ta'addancin da mu ke yi, Idan ba haka ba zai tona mana asiri.."

A lokacin nayi ƙoƙarin shawo kansa Yaki saurarena saima Ya kashe min waya, yayi zaton ja damu abune mai sauki, Dan tahalikin nan sau biyu ina masa gargadi akan Ya fita sabgar mu, amma sai Ya nace akan kudirinsa na fallasa mana asiri.

Kaji dalilin dayasa muka farmakesa a tsakar dare muka daukesa da ya'yansa.

Ya karashe labarin tare dakai hannu Ya dauki juice mai sanyi ya kur6a, Chief Owais sai kallonsa ya ke yi, jin komai yake kamar amafarki wai kakansa? Har yanzu yana jin zafin abun aransa.

"Baba, Baka taba jin tausayi ko irin danasani, a lokacin da ka  raba uwa da danta, ko ka kona mutun da ransa, ko ka keta haddin kananun Yara..." 

dakyar ya iya ƙarashe maganar saboda nauyin furtawa da ya ji.

"bana jin komai, na fada maka, duniya nasa agaba, evils din jikina babu Allah aransu, bansan tausayi ko imani ba.." 

"Amma yanzu ina fata babu evils a jikinka da sauran Elders dama kowa dake da sihiri ta 6angaren ka"

Yar dariya baba Obie yayi"kana tambayata ne saboda bakason in an tashi hukuntamu mu 6ace ko evils su taimake mu"? Girgiza kai Owais yayi"a'a kawai inaso na sani ne"

"Babu Owais, Evils sun koma mazaunin su, na kuma binne sihirina babu wanda zai iya tono shi, In ba magajina ba" 

"In sha Allah shima magajin naka bazai ta6a binno shi ba har abada, mun rabu da annoba"

 dariya baba Obie yayi yadda kasan baida wata damuwa.

"karka damu Owais, ai magajin nawa ya ƙyamaci abun a zuciyarsa tun farko shiyasa ko evils suka gaza yin tasiri akan shi, gadai shi amatsayin Evil giant amma bamu isa mu juya shi son ran mu ba, duk da nasan Allah ne ke tsare shi, akwai kariyarsa atare da shi, bayan haka sai gashi Kaddarar da muke tunanin killace ta zai zamar mana mafita, tazo ta sace Zuciyarsa har ma da evils dinsa, ni kaina nagaza sarrafa shi son raina, wannan yarinyar ba ƙaramar ta'asa tayi mana ba, yar mitsila da ita, owais nifa ban ta6a ganinta ido da ido ba, sai dai a madubin tsafina, sai kuma ranar dinner din Hateem, amma ina jin labarin taƙadarancin ta..."

 baisan ya akai maganar baba Obie taso bashi dariya ba.

"Kana jin haushin tayi silar lalata komai naku"? 

"Bana jin haushinta Owais, hasalima burge ni ta ke yi, Ina son yaro masifaffe mara tsoro, mai ƙwarin gwiwa, kuma kaga tayi silar da kuka kawo karshen kurkukun ƙaddara, gaskiya na jinjina mata,..." ya fada da murmushi akan fuskarsa.

"owais nifa lamarin Ubangiji Ya razana ni wlh, yadda komai ya sauya, duk wani munafunci da makircin da muka daɗe mu na yi a boye, tsawon shekaru bamu ta6a yin Kuskuren da wani zaisan koda suffar mu ta asali ba, amma wani abun daure kai, Cikin yan watanni komai ya warware, asirin mu Ya tonu, gamu a cikin cell, mu da muka saba garƙame ya'yan mutane kamar dabbobi, Yau mune a garƙame? Kurkukun da muke ƙuntata rayuwar mutane, mu azabtar da su a cikin sa, yanzu babu shi, muma nan da ƴan kwanaki ka ɗan zamu shige shi, Owais Allah abun tsoro duniya abun tsoro! owais komai dana mallaka ayanzu babu shi, na rasa dukiyata, ya'yana, yancina, mutuncina, gidana, farin cikina, komai owais, ban taba zaton ma rana irin wannan zata zo ba, owais inaga idan na mutu? Aka binne ni daga ni sai mugun halina? Meyasa ban fara tunanin menene makomata ba kafin na aikata badaidai ba? Meyasa banyi tunanin dole fa wata rana in mutu ba? Kuma komai dana mallaka a gidan duniya zan bar shi? kuma ita duniya ba madawwama bace, zama ne na dan lokaci, Kodai kayi ayyuka nagari ka ceci kanka duniya da lahira ko kuma ka dawwama cikin nadama da bakin ciki.."

 ya faɗa da damuwa akan fuskarsa.

"Owais na shiga Uku, na bani na lalace! Ya zanyi Owais! Na riga na 6ata komai! Koda zan tuba Allah bazai yafe hakkin wadanda na zalunta ba, shine zunubi mafi muni da haɗari arayuwa, basa araye balle in nemi yafiyarsu, da zan curo maka zuciyata kaga yadda bakin ciki ke konata da raɗaɗi wlh zakayi mamakin meyasa bata dakata da bugawa ba"

Tausayin sa ne ya kama Owais, har baisan sa'adda ya mike ya zagaya ta bangarensa ya zauna kan table din gaban sa ya rungumo shi a kirjin shi, kukan ma kasa zuwa masu yayi sai dai suka kama yin kukan zuciya, wata irin soyayyar shi Allah ya jarabceshi da ita, bamashi ba duk Wanda yake rayuwa da Obie zaiji irin ta a zuciyarshi saboda yadda yake kyautata ma ahlinshi dama wadanda ba ahlinsa ba kowa nashi ne ga jin kan na kasa dashi da son taimakon wanda baida shi, in badan  haka ba karamar tsanarshi zaiyi ba baba Obie ya cici kanshi suma ya cucesu ..

Kwana su ka yi a rungume da juna, ba bacci, sai zullumi da fargaban hukuncin da kotu zata yan ke mashi.

Kamar yadda suma can Ahlin nasa basu iya runtsawa ba, kwana sukayi a zaune, sun yi kuka har sun gaji damuwa taci tacinye su, saura jiran tsammani

game Bukatar Kurkukun ƙaddara Ya tuntu6i number din nan 08103884440

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post