FLASH BACK, WAIWAYE ADON TAFIYA, BARI MU KOMA BAYA MUJI LABARIN TAYAYA AKAI DANISH YA RAYU? TAYAYA GABRIELLAH TA KU6UTA DAGA CIKIN TAFKIN JINI? KUMA TAYAYA AKAI KHALA TA KU6UTA DAGA TARKON MUTUWAR DA ELDER YA ƊANA MATA?
"Ku fara kokarin ceto rayukan fursinonin dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa daƙunan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh.
Ta ƙara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..." Bayan tafiyarsu zullumi da fargaba Ya cika Zuciyar Tsohuwa Khala, ta kasa tsaye ta kasa zaune saboda tsoron kada su kasa yin nasara akan Giant da Elders tasan muddin suka san dasa hannun ta, Na lahira sai ya fita Jin dadi, bayan tafiyar su da mintuna, Allah Allah take su fara kawo mata firsinonin da suka ku6utar donta taimaka masu su fita daga kurkukun kafin Elders su Ankara.
A lokacin da batai tsammani ba taji motsin mutane a kofar dakin ta, cikin sauri taje gaban kofar, da faduwar gaba ta tambayi su wanene"?
Daga waje tajiyo murya mutun
"Isod Soldiers ne, Chief ne ya umarce mu da mu kawo maki Fursinonin da muka ku6utar..."
ajiyar zuciya ta sauke, jikinta na kerma ta cire sakatar ƙofar, ta leƙa kanta, Sojoji biyar ne tare da matasan Fursinonin da suka fara ku6utarwa dukansu jikinsu kerma ya ke yi bayin Allah..
"ku tsaya a bakin kofar dakina, Ni zan tafi da wadannan furnonin, Idan wasu sojojin sun sake ku6utar da wasu fursinonin ku ce masu su kawo su gurin da ku ka shigo kurkukun" amsa mata sukayi da toh, a hanzarce ta dubi fursinonin ku biyo ni"
Cikin sa'a suka karaso wurin a lokacin sauran sojojin da suka karaso suna ta durowa ta cikin tagogin ta ko'ina sune sun cika wurin.
suna ganin khala suka gane itace tsohuwar da danish ya fada musu zata basu hadin kai idan suka karaso..
"Kun gama shigowa Ko akwai wasu sojojin" ta tambaya tana dubansu, sukace sun gama shigowa sauran sojojin da suka rage awaje, matukan jiragensu ne dana motocin su..
Jinjina kai tayi tare da kallon Sojojin da suka rage a bakin tagogin rufin suna ta kokarin ɗaure igiyoyi masu gwa6i da tsawo jikin tagogin saboda idan zasu koma da su za su yi amfani gurin haurawa sama su fuce.
Hakan ba karamin dadi yayi mata ba, batare da bata lokaci ba, suna gama daure igiyoyin suka zuro da su kasa har kan ground floor din gurin tace ma fursinonin su kama igiyoyin su haura sama idan sun isa suyi rarrafe akwai kofar da zata 6ular da su, wani Soja yace mata daga sun fita zasu iske sauran sojojin da ke a waje, already sun shirya komai.
Bayin Allah sun kasa bin igiyoyin saboda basu iyaba, sai da sojojin suka taimaka masu gurin kwatanta masu yadda zasu bi igiyar, cikin ikon Allah sai gashi sun kama igiyoyin a hankali har suka haura sama, tun suna hawa daya bayan daya har suka koma suna hawa uku uku..
Suna kammala hayewa, sai ga wasu fursinonin gungu guda sojoji sun tafo da su, a gaggauce suka koya masu yadda za su bi igiyoyin.
Na karshe da sojoji suka kawo sune wadanda su Danish suka ku6utar a dakin Fiɗa, hada mata masu ciki, yawanci ba koshin lafiya gare su ba, dama da taimakon sihirin Danish suka miƙe akan kafafun su har suka iya tafiya, dakyar suke bin igiyar, wasu ma daga cikin masu juna biyun hada kukansu saboda radadin da suke ji, tsananin tausayinsu ya kama sojojin da khala, sai dai ba yadda zasu yi da su, a haka suka haura saman rufin gaba ɗayan su, masu juna biyun sunfi shan baƙar azaba, saboda kuntatar da cikin su yayi, suna nishi da haki ga yanar data cika rufin da kananun kwari masu harbi da suka addabesu da kyar da sidin goshi suka karasa bakin Kofar da sojoji ke gadin ta, sai da suka taimaka ma kowani prisoner gurin mikewa saboda sagewar da gwiwowin su sukayi yasa basu iya mikewa, kaitsaye sojojin suka dinga shigar da su cikin jiragensu da motocin su, nan ma saida suka koya masu yadda zasu shiga, saboda basu san komai ba, hasalima tsoron jiragen su ke yi da motocin, bayan sun shigar da su duka, matukan suka tada jiragen da motocin ba 6ata lokaci suka basu wuta, da gudun gaske kamar zasu tashi suka nufi hanyar barin dajin da su gudun kada akawo masu farmaki ta bayan fage, tun acikin motocin sojojin suka rarraba musu ruwan sha, masu rauni a cikinsu kuma suka fara basu taimakon gaggawa dama suna da emergency box din su mai dauke da kayan agaji saboda tsaro.
Idan muka koma cikin kurkukun bayan sojojin da ke kawo yaran sun tabbatarwa khala da sun kammala kwashe fursinonin da ke a ciki.
Hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ganin bata ga yarinyar data kwallafa rai akan son ta taimake ta ba, arude tace ma sojojin su sake dubawa dakyau saboda ita tasan adadin fursinonin da suka rage a cikin kurkukun akwai wadanda babu"
sojojin suka ce"Danish da Salsabeel sun tabbatar masu da babu sauran fursinoni,"
da ta matsa lamba akan su sake dubawa suka ce mata akwai bakwainin da suka gani a wani daki cikin containers kuma ba zasu iya jigilar daukarsu ba, saboda suna a cikin hadari basu da isasshen lokaci.."
jikinta ne yayi sanyi lakwas taso duka acece su saidai bazai yiwu ba kamar yadda suka fada, cikin sanyin murya tace"akwai Allah, yana atare da su, shiyasan yadda zaiyi da rayuwarsu, duk da haka bayan bakwainin da kuka ce kun bari, akwai yarinya daya da babu a cikin fursinonin Ni banganta ba, kuma nasan ta, na ta6a taimakon ta, ni zanje na nemota da kaina"
tana faɗa ta 6ace ma ganinsu, bata dira a ko'ina ba sai cikin ɗakunan fursinoni ta dinga bi tana dubawa sako da lungu, batare data bari wani yaganta ba, sai dai ita tana ganin yadda Giant da sojoji suke faɗa
Ko'ina ta duba ban da ground floor da Hall din da ake bada horon zama giant saboda tasan zuwanta zai iya haifar mata da matsala.
Damuwa ce ta cika zuciyarta, Hankalinta Ya tashi matuka, aranta ta furta"ina kika shiga Gabriella? Ga taimako kun samu, bana so damar nan ta wuce ki, Inaso na cika maki alkawarin dana daukar maki! Ko dai sun kashe ki ne"?
abun da take jima fargaba kada ace sun haɗu da tsohuwa inno don tasan kuwa muddin suka hadu sai Ta cutar da ita, ba karamar wahala tsohuwa khala tasha ba gurin neman Gabriella, saida ta haɗa uban gumi akan fuskar ta.
A karshe ta buga sandar hannunta a ƙasa tayi shiri donta samu damar ganin abun daya faru da Gabriela bayan giants sun fito da ita daga dakin ta, sai dai kash bata ga komai ba a inda ta buga sandar sai dai taga kasan gurin yayi jajir kamar jini ya 6are..
Abun ka ga mai ilmin matsafa, zukunnawa tayi gaban gurin tayi dogon nazari akan ma'anar launin jan, nan take ta gano me hakan ke nufi.
6acewa tayi 6att daga gurin.
Lokacin da ta shigo ke6a66en wurin da tafkin jinin nan yake, bata iya ganin komai ba saboda idanunta basu cika gani ba idan babu wadataccen haske.
kware murya tayi da karfi ta shiga kwala mata kira Gabriel! Gabriel! Gabriel, Kina ina? Kina jin murya ta, ni ce khala! Idan kina jina kiyi min alamar da zan gane a ina kike"!
Saboda yadda take kware murya tana magana makoshin ta har zafi ya ke mata.
ranta ne ya bata ko bata anan ne? Watakil tayi kuskure a duban da tayi, juyawa tayi har ta daga kafa da niyar ta fuce Unexpected kunnuwanta suka soma jiyo mata sautin wani azababben nishi mai hade da gurnani daga ji koma wanene keyin nishin yana a cikin mawuyacin hali, kuma yana fama da karancin iska da zai shaƙa.."
saboda tsabar zumudin taga wanene, ta juya tana lalube da sandarta harta cimma bakin tafkin.
batai aune ba taji safkar hannun mutun akan kafarta kamar laluban hanya ya ke yi.
cikin duhun nan ta damƙi hannun da iya karfinta na karshe ta janyo da ita aikuwa gaba daya suka kife ƙasa, lokacin da khala ta miƙe tana laluba jikin mutumin data tsamo daga cikin jinin, Hankalinta ya tashi saboda ta gane Gabriella ce, taji tausayin halin da take a ciki, ganin yadda jini ya wanke jikinta, baka iya ganin komai nata, kuma tayi mamakin yadda har ta kai wannan lokacin a cikin tafkin jinin batare data suma kota mutu ba, ta jure ƙarni da ɗoyin jinin data shaƙa, ko magana bata iya yi sai nishi ta ke yi, kofofin hancin ta da bakin ta sai malalar da jini su ke yi.
Idan har ta ce zata tsaya ta bata taimakon gaggawa anan za'a iya riskarsu, hakan yasa batai wata wata ba, ta dafe bayan gabriella da ke a kwance ƙasa, tayi masu sihiri suka 6ace daga gurin gaba ɗaya.
Basu dira a ko'ina ba, sai cikin dakin Khala, kamar an wurgo su daga sama, suka faɗo kasa.
wannan jinin da su Chief owais suka gani malale a kasan dakin Khala, ba jinin kowa bane face jinin da Gabriellah ta amayar, da hannu khala ta dinga buga mata dunduna, ta dinga sakin aman jini har saida ta fitar da jinin da ta sha.
miƙewa khala tayi da sauri ta nufi daya daga cikin tulunan dakinta mai dauke da ruwa mai sanyi, ta kinkimo tulun ruwan da hannunta daya, yayin da dayan hannun ke a ruke da sandarta, ta dawo gaban Gabriella ta ƙwarara mata ruwan a jikinta.
sai lokacin ta fara dawowa hayyacin ta, aje tulun kasa khala tayi, ta zukunna tare da kwalfar ruwa a tafin hannunta ta wanke mata fuskarta, ta kwafa mata bakin tulun abaki ta shiga kuskure bakin ta, duk wannan abun da khala tayi mata bata san wacece akanta ba, saida tasha ruwa sanyi ya ratsa makoshinta, tana dagowa da rinannun idanunta suka shiga cikin na khala, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, cikin sauri khala ta rungumeta a kirjinta, ta shiga lallashinta, tasan ta da zuciya, cikin shesshekar kuka ta zayyana ma khala abun daya faru tsakanin ta da tsohuwa inno, tace mata tayi hakuri ta jure, ta manta da komai, yanzu ga taimako sun samu, sojoji sunzo har ma sun ku6utar da fursinonin kurkukun gaba daya, a lokacin wani ihun farin ciki ta saki, arude tace mata ina dan uwanta gabriel? Shima sun fita da shi"? Khala tace mata eh, sune ma na farko da aka tafi da su" ta faɗa mata hakanne don ta samu ta shawo kanta tabi su su tafi.
Cikin sauri Khala ta nufi bookshelves din dakinta ta zaro kundi biyu ɗaya na tarihin kurkukun ƙaddara ɗayan kuma littafin rijistar fursinoni ne ta rungumesu a hannunta ta nufi wata tsohuwar jakar fata dake makale jikin bango ta curota ta zazzage kayan cikinta, ta zura kundaddakin a ciki, Gabriella duk tana kallon ta bayan data gama ta miƙa mata Jakar tace ta ruke ta da kyau, suna da mahimmanci, Idan ta fita daga kurkukun ta bama sojojin, tace mata toh.
Batare da bata lokaci ba, Ta janyo hannunta, suka fito daga dakin, lokacin da suka karasa gaban sojojin dake tsaron tagogin rufin ta damka masu gabriela tace su tafi da ita, cike da tashin hankali tace ma khala tazo su tafi tare, khala tace a'a su fara tafiya zatazo daga baya, idan sojojin sun kammala yaƙin zata biyo su, fashewa da kuka Gabriella tayi, ta sanya musu rigima akan bazata tafi ba in har khala ba zatazo su tafi atare ba, bata son ta tafi tabarta, gani take kamar zata mutu ne..
ganin zata 6ata musu lokaci yasa sojojin suka tasa ƙeyarta, tana ji tana gani suka rabata da khala, har ta fara bin igiyar bata daina waiwayen Khala ba, tana atsaye tana kallonta, fuskarta dauke da murmushi tace karta damu, tayi mata alkawarin indai da rai da lafiya zata zo inda su ke, sannan idan ta hadu da dan uwanta Gabriel ta gaishe mata da shi.
itama tana kuka tace ta kula mata da kanta, duk runtsi duk wuya karta bari ta mutu, tana son ta.." bayan Gabriela ta dura ta rufin, ta rarrafa ita kadai tana kuka tabi hanyar da zata 6ular da ita...
Saida sojojin dake tsaron gurin su ka ce ma khala tabi ta su tafi tace masu a'a, bazata iya tafiya batare da ta ga karshen fadan ba, saboda akwai burin da take da shi, tana son taga nasarar su akan idanunta, in har ta tafi zullumi da fargaban a wani hali suke a ciki bazai bari ta zauna lafiya ba.."
badan sun so ba suka ƙyale ta.
Idanun ta cike tab da kwalla, ta juya ta nufi hanyar komawa dakinta, zuciyarta a cike fal da kewar Gabriella, tana son yarinyar ta shaku da ita, tana son su sake haduwa sai dai tana ji aranta da wuya ta rayu, bayan irin 6arnar da tayiwa Elder bayan ta shiga dakin kasa zama tayi saboda zullumin awani hali su Danish suke a ciki..
Ta yi zurfi a tunaninta kwatsam tajiyo takun tafiyar mutun abayanta, juyowar da za tayi keda wuya idanunta suka sauka akan Elder Obinna daya faɗo a fujajen jikinshi sai tsuma ya ke yi saboda tsantsar bacin rai, har wani gurnani yake fitarwa..
wani irin faduwar gaba taji, Hankalinta ya tashi matuƙa.
kallon kallon su ke jefawa junansu sam ya kasa magana, tun da taga ya kawar da idanunsa daga kallonta ya mayar da su akan akwatinan karfen da ke a kasa da buhunbuhunan makaman da tabari, nan fa tasha jinin jikinta, zufar tashin hankali ta fara wanko mata fuska, adabarbarce ta furta"E..el..elder...."
bata karasa maganar ba, Ya daka mata tsawa tamkar zai fasa dodon kunnanta, Yana huci cike da bakin Ciki Yace"kin bani mamaki! Dake za'a haɗa baki a ci amanata? nayi kuskure dana barki araye tun farko.."
duk da tsoron shi da take ji hakan bai hanata yin karfin halin cewa"kamar yadda nima ka bani mamaki Obinna, kaine ka fara cin amanata tun farko.."!
bata ƙarasa amayar da abunda ke aranta ba, taga ya nufota gadan gadan Jiki na bari ta soma ja da baya, zagaye dakin suka dinga yi, ta soma yin tsalle tana hayewa kan tukwanan kasan dake adakin cike da tsoron karya kamata, cikin tashin hankali ta dinga daddafe bangon bayanta da tafin hannunta wanda ya 6aci da jinin data goga a jikin Gabriella, wanda silar hakan Yasa sahun yatsunta suka fito radau a jikin bangon kamar an zana shi, gaba ɗaya saida ta faffashe tukwanan da kafafunta, da ta ga zai cimmata ta 6ace ta koma kan gadonta, ransa ne ya 6aci nan take yayi tsafi gaba daya gadon da take akai ya jirkice wanda silar hakan ta kundumo ƙasa har kanta Ya da ku ta suma.
Bata kara sanin inda kanta yake ba, sai dai ta farka ta tsinci kanta a dakin da yake hukunta wadanda suka ci amanarsa nan take ta fahimci shine ya kawota nan..
(Kunji yadda akai Elder Ya rutsa da Khala🔥)
Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ƙafarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana ɗaga ƙafarsa kafin Ya dire ta ƙasa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ƙarasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ƙarfin shi na ƙarshe ya ingizasu gaba ɗaya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kan shi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi...
(Evil wall rijiya ce mai faɗi da tsawo, tsohuwar rijiya ce da tayi shekaru aru aru tun zamanin kakannin Elder tun kan Elder ya gurfanar da kurkukun ƙaddara rijiyar ta ke anan, gaba ɗaya rijiyar ginin dutse ne tana da hatsarin gaske mutun bazai iya rayuwa acikin ta ba idan har babu sihiri a jikin shi, saboda giggan shaidanun dake rayuwa a cikin ta, ko maƙiyi na banayiwa fatan ya tsinci kanshi a cikin rijiyar koda a mafarkinsa ne saboda izayar da zai taras, daga jikin kowace kusurwa ta rijiyar yanace dadda6e da Evil spiders da manyan kunamu jibga jibga, ga giant snakes din dake bin jikin bangwayen rijiyar, gaba dayansu evils ne suka rikida ba ainihin kwarin ba ne.
ga wasu zanunnuka masu ban tsoro jikin bangwayen rijiyar, ga wasu halittu bakake munana, masu idanuwa barkatai a jikin su, wasu gashi gashine buzu buzu a jikin su, wasu halittun kuwa har kananun macijjai suke fitarwa ta bakin su, bala'i iri iri, daga kasan rijiyar wani irin fadi gare shi, hada koramar ruwan jini na sihiri da manyan duwatsu, ga wata gajeruwar bishiya mai rassa tare da manyan ganyayyin da sukayiwa kasanta inuwa, daga kasan ta akwai wata shimfiɗa ta alfarma da akayita da jan carpet mai fadi anan giant din da suke horaswa ya ke zama kamar gunki bazai taba motsawa ba, in ba evils sun tashi bashi horo ba, koda yaushe da bakar izayar da zasuyi mashi, kamar yadda na fada abaya, tun suna bashi wahala su tsoratar da shi har sai sun kaiga bugun shi da bulalai su dinga azabtar da shi da masifu iri iri tun yana kuka ya suma su farfado da shi, har sai ya koma yana yin komai daga kwance tun daga kan amai, fitsari, kashi, saboda azabar da su ke yi masu takansa su fita hayyacin su, da zarar Elders sun tura ka rijiyar kayi bankwana da farin ciki da duk wani jin dadi, kunnuwanka ba zasu ƙara jin sauti mai dadi ba, sai na tashin hankali, baka da abinci daya wuce ƙwari da kwan halittun dake a ciki, ruwan sha kuwa sai dai kasha jinin dake a cikin tulunan da suka aje maka, ko wanka baka isa kayi ba, cikin kazanta zaka zauna shiyasa dayawa matasan da suke diba idan zasu basu horon zama giant da wuya suke tsalle rijiyar shaida nu, mafi rinjayen su anan suke rasa rayukan su.
Rijiyoyin suna da yawa kowani giant a rijiya daya zasu kulle shi, kamar kabari, babu shige babu fuce, rayuwar kunci da azabtarwar, daga lokacin da tsoro yabar idanunsu, suka jure wahalar har suka fara rama bugun da evils keyi masu idan suna gabza fada atsakaninsu to daga nan evils din zasu gane zai iya jurewa, anan ne zasu zana mashi tattoo abayanshi yana kuka da ihu kamar ana zare ranshi saboda azabar raɗaɗi, irin tattoo din da su ke yi masu, ba irin wanda muka saba gani anayi bane, da akaifu evils suke zana masu shi abayansu, a faɗan da suke gabzawa da giant, idan yayi nasarar jure azabtarwar su ya rayu bai mutu ba, daga nan ne zasu samu matsugunni a jikin shi, su gauraya da shi ta yadda zasu ba shi ƙarfin su.
A Lokacin da Danish Ya damƙi jeremiah ya ingiza su cikin rijiyar, Tun kan su dira kasan rijiyar a saman iska, suka fara gabza faɗa a tsakanin su baka iya jin sautin komai saina buge buge da naushe naushe da nishinsu hadi da gurnanin su kamar zakuna, bugun mutuwa sukewa junan su, babu imani babu tausayi, kowa jininsa akan akaifa ya ke, zuciyar su a wuya take, musamman jeremiah daya kasance mugun mutun, Ya tsani Danish tuntuni, ba dan komai ba sai don saboda lokacin da suke ƙanana yafi Danish yiwa elders biyayya idan suka bashi Umarnin ya aikata rashin imani jiki na bari zaiyi, danish kuwa kafiya da taurin kai ya ke yi masu, gashi Allah ya jarabce su da son shi, sai da takaiga sai sun haɗa da yi mashi sihiri suke samun abunda suke so, saboda yadda suke gatanta shi yasa Jeremiah ya ke yi mashi hassada, ya kullaci abun aran shi, yasha kulla makirci don ya sanya tsanar danish a zuciyar elders sai dai bai ta6a nasara ba, shiyasa a yanzu dayaga sun fada rijiya su biyu ya ke ta kokarin kawar da shi don ya fanshe bakin cikin daya kunsa mashi.
wani jahilin naushi ya kaiwa Danish a tsakar mararsa, har saida Ya firgice saboda azabar daya ji, bai kaiga dawowa dai dai ba, jeremiah ya tallabe kansa da faffaɗan tafukayensa Ya buga jikin bangon rijiyar, tuni kuzarin jikin shi Ya ragu dama ya fara galabaita sosai saboda yakushin da Evil giants sukayi mashi a filin daga, duk da haka bai sare ba, jini na fita ta bakinsa da hancinsa, da bayan kansa, a haka Ya damƙi kan jeremiah Ya daddage da dukkan karfinsa ya maka shi jikin bango, amma kamar ya hada dutse da dutse kwata kwata babu alamun jeremiah Yaji jiki kamar ana kara masa karfinsa abunka ga sabon garkuwa, don bala'e kusan sau uku suna rikida su canza halittar su, kamar zasu kashe junansu babu tausayi ko kadan burin kowan nan su yayi nasara, kafin kace me tuni Wata irin kura mai hade da hayaki tamkar guguwa ta bude su baka iya ganin su kwata kwata, cakumar Danish yayi ya nutsa da su cikin rijiyar burinshi ya kaishi ƙasanta don ya azabtar da shi kafin Ya karasa kashe shi, shi kuma baya son yakai kasan rijiyar saboda yana jin tsoron Evils din cikinta su fusata zasu iya tarar mashi yasan cikin dakika zasu iya shafe babin shi.
Duk yadda yaso ya turje saida Ya kasa saboda raunin da yayi, ta karfi ta tsiya Jeremiah Ya ingizasu suka kundumo kasan rijiyar gaba dayansu saida kawunansu suka daku.
Duk da mawuyacin halin da yake a ciki hakan bai hana zuciyar shi tunanin Angel dinsa ba, har lokacin idanunsa basu daina tariyo masa irin haukan da tayi na za'a rabata da shi ba, kalamanta sun tsaya mashi a kahon zuciya, Shagalar da yayi da tunaninta yaja har Jeremiah Ya yi nasarar azabtar da shi, saboda rashin imani da sihiri yayi amfani gurin zane shi da bulalai yayi mashi jina jina, har saida Ya suma kusan sau uku jeremiah Yana farfado da shi.
A lokacin Gaba ɗaya ya fidda rai da rayuwa, kamar jaki haka Jeremiah ya mayar da shi jini da majina ya hada mashi akan fuskar shi, saida Ya raba shi da kakin jikin shi, Yayi mashi zir haihuwar uwarsa dayaga Ya kusa kashe shi gaba daya baya iya ta6uka komai sai ya fara kokarin yin homo da shi saboda ta hakane kadai zai iya ƙwace sihirin jikin shi ya dawo nashi jikin saboda ya ƙara ƙarfi na fitar shari'a, bai kaiga cimma manufar shi ba, kwatsam rijiyar ta fara jijjiga, Lokaci daya sautin dariyar Evils mai matukar tsoratarwa da razanarwa Ya cika rijiyar, alamar Evils sun fusata, A lokacin Danish baisan inda kanshi ya ke ba yana akwance cikin jini rai hannun Allah, soft skin dinshi duk ta 6aci da munanan raunuka ko yatsansa bai iya motsawa..
Jeremiah Yana akansa Yana kokarin cimma manufarsa, Kwatsam ba zato ba tsammani evils suka fara ƙewayesu da suffar halittun da suka sauya masu tsotarwa, kamar kyankyasai saboda yawansu, manyansu da kananan su, koda Jeremiah yaga haka sai ya fara sakin shu'umar dariya yayi zaton zasu goya masa bayane akan abunda yake kokarin yi saboda yanzu shine garkuwar kurkuku.
bai yi aune ba, kwatsam Yaga bakin hayaki ya soma kurdadowa yana fita ta bakinsa da hancin shi, kaitsaye hayakin ya ke shiga ta kofofin hancin Danish da bakinsa da duk wata kofa da iska zata iya ratsa jikin shi.
lokaci daya yabi ya ruɗe ya zazzare jajayen idanunsa kamar na kwartan mazuru, jikinshi ya kama 6ari kamar mazari, yayin da tsoro da fargaba hadi da tsantsar rudanin al'ajabi suka mamaye zuciyarshi, abin da bai ta6a zata ba, ya rasa gane tayaya akai evils suka bar jikinshi tare da sihirinshi suka koma jikin Danish, da alama reshe ne ya juye da mujiya.
cikin rawar murya ya furta bazai yiwu ba, meyasa zakuyi min haka? Ni ne sabon garkuwarku, Danish maci amanane, baya atare da mu! Ku dawo min da sihirina, Ku dawo jikina, ni ne nafi cancanta in samu karfin sihirinsa ba shi ba, ko kun makance ne? Baku da hankali ne"?
Kamar mahaukaci ya dinga sambatu tare da mikewa ya bi halittun dake kewaye da shi Ya dinga yi masu tsawa yana zaginsu kamar zai doke su.
sai masifa ya ke zazzaga masu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, wata irin kururuwa ya fasa kamar zaiyi hauka ya tallabe kansa da tafukansa, Ya dinga sakin kara mai tattare da bakin ciki, Har tsalle yakeyi kamar kwaɗo dama ba sutura a jikin shi.
Girgizawar da rijiyar tayi ne yasa shi dawowa hayyacin shi, tunkan ya juya idanunsa suka safka akan Inuwar Evil din dake abayan shi, yawu ya haɗiya mai daci, gabanshi ya shiga faɗuwa.
juyawar da zaiyi keda wuya idanunsa suka sauka akan Danish Dake atsaye kan kafafunsa, gaba daya idanunsa sun juye sun koma fari fat babu launin su, wani abun ɗaure kai ko ƙwarzane babu akan fatarsa gaba daya raunukan da yaji sun 6ace 6att ko tabo babu in ka cire tattoo dinsa, bakin cikine Ya turnuke zuciyar Jeremiah, kamar ya hadiyi zuciya ya mutu.
Cikin fushi yace"burinka Ya cika Danish, Ka yi nasarar rabani da sihiri na, ba zaka ta6a bari in fi ka ba, ko da na sakanni ne ko da yaushe kaine agaba, na tsane ka danish, bana son ganinka, mutuwarka nake kwaɗayin in gani, bazan kyale ka ba, sai na kwace sihirina sannan In kashe ka.
tun daya fara maganar Danish bai motsa ba, saboda a ba ɗini ba shi bane, Evils ne suka tada shi shiyasa harya iya mikewa tsaye, tsautsayi ne Yaja jeremiah Ya durfafesa da gudu Ya daka tsalle Ya dura akanshi kafin yayi wani yunkuri Danish Ya damƙi wuyan shi duk girman jikinshi Ya daga shi sama, nan take ido Ya raina fata, Ya dinga gurnani yana kokarin kwace kansa sai dai Ya kasa, idanunsa suka zazzago waje, Da azaba ta ishe shi Ya fara yi masa magiya akan yayi hakuri Ya kyale shi, kada ya kashe shi, koya manta abokantakar da ke tsakanin su.
Wata shu'umar dariya Danish Ya fasa hahahahaha da wata irin budaddiyar Murya ya furta"baka cancanta ka rayu ba, saboda baka da tausayi, mugunta da zalunci kadai kasa a gaba, burinka kaga bayana, saboda nafika a komai, yanzu zan saukaka maka kishin da kake akaina, Idan na kashe ka ba zaka ƙara ganina ba, balle har ka ƙulla ce ni aranka"
ya karashe maganar tare da matse wuyansa, ta yadda ko numfashi bazai iya fitarwa ba gurnani ya dinga yi yana ta kokarin kwatar kansa, azaba tasa ya saki fitsari, majina ta dinga zalalowa ta hancinsa..
saida ya tabbatar bazai kara amfanuwa ba, tukunna Ya jefar da gangar jikin shi kasa.
Kunaman dake a cikin rijiyar da macijjai suka daddabe shi, suka dinga kai mashi sara da ɗalli..
ya dinga sakin Ihun azaba, Danish yana atsaye yana kallonshi har saida ransa yabar gangar jikin shi tukunna Ya daka tsalle Yayi sama Ya nufi murfin rijiyar yana karasawa Ya sakar mashi naushi ɗaya nan take murfin Ya balle biyu ya duro akan kafafunsa kuma nan take ya dawo cikin hayyacinsa..
yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa tsantsar tashin hankali da damuwa ganin gawarwakin sojoji barbaje a kasa, wasu gawarwakin ma ginin daya ruguje Ya rufe su ba'a iya ganin su, babu wani mai rai, kuma kwatata babu gawar giants a gurin sun 6ace 6att..
bawan Allah, aruɗe ya shiga neman gawar Chief da ta daddyn Unaisah, da Salsabeel, ya dinga bin gawarwakin yana dudduba fuskokinsu, tuni ya hada gumi, zuciyar shi ta karaya ganin babu corpses din su kwata kwata, da karfi ya dinga kwala masu kira tamkar makoshinsa zai balle shiru babu mai amsa mashi, bakin cikine ya turnuke zuciyar shi, yaji takaici, ganin duk kokarin da yayi don su rayu ya tashi abanza, wata irin ƙara ya fasa mai kuwar gaske har saida ginin Ya girgiza.
Bakomai ne Ya faɗo masa aransa ba face tsohuwa khala, cikin sauri Ya zuƙunna a gaban gawar wani soja, Ya tu6e kakin sa Ya zura a jikin shi..
Daga inda Ya ke yayi tsafi Ya 6ace 6att bai dira a ko'ina ba, sai a tsakiyar dakin tsohuwa khala ya bayyana..
~__________🔥__________🌹_______💫________💔~
Nan ma ya ƙara shiga tashin hankali ganin daskararren jinin daya malale kasan dakin ta ga gadonta daya jirgice nan ta ke ranshi ya bashi sun kashe ta, shikenan ya rasa damar da ya ke da ita, babu wanda zai faɗa masa su wanene iyayen sa in ba ita ba, gashi kuma ya rasa ta yanzu!
baima san tayaya zai iya komawa gurin yan uwansa ba, zu6ewa yayi kan gwiwowinsa tsabar bacin rai, idanunsa suka kaɗa jawur kamar garwashin wuta, tuni jikinsa ya dau zafi rau, yana a cikin wannan halin kamar ance ya wurga idanun shi jikin bangon dakin ta unexpected ya hango kamar zanan wani abu ja
zumbur ya mike ya nufi zanan Ya ƙura idanun shi Yana kokarin gano menene! dakyar ya iya gane sahun yatsun mutunne da jini.
rufe idanunsa yayi tare da zurfafa tunaninsa nan take cikin ikon Allah kwakwalwarsa ta tuna masa da inda keda zanunnukan yatsun hannayen mutane, wato dakin da Elder ya ke hukunta wanda yaci amanar shi, ka'ida ne idan ya gama azabtar da wanda yaci amanarshi saiya fasa tafin hannunsa Ya manna jikin bangon ɗakin, har sai sahun yatsun hannayen shi sun fito raɗau tukunna ya ke cire shi, nan take Danish Ya fahimci Khala ta bar sahunne don wani ya kai mata ɗauki tun da tasan zasu dawo dakin nata idan suka gama faɗan.
lokaci ɗaya ya waro idanun shi waje tare da ja da baya, batare da bata lokaci ba, Ya 6ace daga dakin Khala..
Lokacin da Elder ya juya Giants suka take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta.
Ta kasance ita kadaice a cikin dakin, ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle ta iya kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta.
sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar ɗaukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke, wutar Tana gab da zata rufe jikinta, Danish Ya duro dakin, cike da tashin hankali ya yi sahirinsa nan take wutar ta mutu kurmus, ramin Ya hade kanshi tamkar ba'a ta6a tsaga ƙasan gurin ba, kafafuwanta da suke daure da igiyar kaca nan take igiyoyin suka warware kan su sakamakon tsafin da yayi, kafin ta fado ƙasa ya rigata karasawa kasan fankar, igiyar na karasa kwancewa ta fado kan hannayensa, tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda hancinta ke fitar da jini, fatar goshinta har ta fara konewa ta tattare tayi duhu alamar wuta ta daki gurin sosai.
ga wani irin ƙauri da jikinta ke fitarta, gumi ya wanke ko'ina na jikin ta, rungumeta yayi sosai a jikin shi, kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, idanunshi suka cucciko tab da kwalla, duk da baisan meya faru ba, amma yaji aran shi Elders sun gano taci amanarsu shiyasa suka hukuntata, da ba dan Allah yasa tayi dabarar yin alamar da zai gani ba, da yanzu ta kone kurmus ta yadda ko 6ur6ushinta ba zasu iya gani ba balle susan meya faru da ita.
Cikin shesshekar murya ya dinga kiran sunanta yana fadin kada ta mutu ta barshi, Yana bukatarta arayuwarshi... "
babu alamun zata farka, Ya rasa gane suma tayi ne ko mutuwa ta yi ne..
Zuciyarsa ce ta ankarar da shi akan ya mike ya tafi da gawarta kafin Elders su ritsa da shi.
Yunkurawa yayi tare da mikewa tsaye ya goyata akan bayansa ya tallabeta da hannayensa, daga inda yake ya 6ace bai dira a ko'ina ba, sai a wajen kurkukun ta inda suka bar jiragen su da motocin yaƙin su yayi zaton zai taras da wasu daga cikin sojojin sai dai baiga kowa ba, babu su babu alamar su.
hawaye ne suka wanke fuskarshi, bai san ina zai sanya ranshi ba, Zuciyar shi ta ƙara karaya, kamar zai fashe da kuka.
Watsawa yayi da gudu Ya bazama cikin dokar dajin goye da khala abayansa, kwata kwata baiji nauyin ta ba saboda jikin tsufa, babu nauyi, Hasken rana ne Ya fara ƙwalarsa, ga yunwa da kishin ruwa da suka addabesa, maƙoshin shi har ƙaiƙayi ya ke yi ma shi, rabon shi da abinci tun jiya da suka baro Sansanin sojoji.
Tsawon awanni takwas Yana tafiya daya gaji ne kafafunsa suka rurruke don dole Ya yada zango a gaban wasu bishiyoyi ya kwantar da khala asaman ciyayi ya tasa ta gaba yana kallonta..
saida ya huta kana ya mike ya kutsa cikin dajin don ya samo abun da zai ci.
Duk inda ya duba babu abun da zai ci, a karshe da yaji bazai iya jure yunwar ba, ganyayyaki ya tasa agaba kamar dabba, da dadi da ba dadi ya dinga cusawa abaki yana ciki, saida ya cika cikin shi ya fara jin kishin ruwa kamar zai zauce, a galabaice ya baza ma neman ruwan da zaisha, tunawa da gawar khala daya baro yasa shi hakura da neman ruwan gudun kada namun dawa su handame ta, Yana akan hanyar dawowarsa wani irin hadari Ya haɗu bakikkirin cikin kankanin lokaci ruwa Ya fara safka tamkar da bakin kwarya, da gudu Ya koma gaban bishiyar yana isa ya taras da abun da ya faranta ransa, Khala ya gani ta farfado silar ruwan daya daki fatarta ashe sumane tayi.
cike da farin ciki ya rungumeta a kirjin shi, kafin ya fara tarfa ruwan saman a tafin hannunsa yana bata abaki tana sha, sai kokari ta ke yi tayi masa magana sai dai takasa saboda muryarta tayi rauni
sai dai rungume shi tayi ta dinga sakin gunjun kuka, a lokacin Allah ne kadai yasan farin cikin da tayi na ganin ta rayu kuma Danish ne ya ceto ta, taji dadi mara misaltuwa, Allah ya amsa addu'arta, ba ta ta6a zaton zata rayu ba,..
Tana kuka yana kuka babu mai lallashin wani, Yace mata tayi hakuri baisan meya faru ba, da bazai bari Elders su cutar da ita ba, yama yi zaton ta mutu ashe tana araye, yaji dadin da bazai iya misalta shi ba..."
bai faɗa mata abun daya faru da shi ba, bai kuma nemi ta fada masa meya faru da ita ba saboda ganin halin da take a ciki na jinya..
A daren ranar agaban bishiyar suka kwana, ruwa ya jibge su, saboda babu mafaka akusa da su, kafin safiya tayi gaba daya zazza6i ya yi masu mugun kamu, jikin su yaita kerma..
Daya fahimci yunwa take ji, yaje ya tsunko mata ganyayyakin dayasan ba zasu cutar da ita ba, Yabata don taci, bayan ta kammala ci, Ya zukunna agabanta ta hau bayanshi Ya goyata, tare da mikewa Ya cigaba da tafiya batare da tsayawa ba.
Akan hanyar su Ya labarta mata komai daya faru da su Yace baisan meya faru ba bayan ya fada rijiya, baiga gawarwakinsu Chief Ba yana ji aransa kamar basu mutu ba, saboda a cikin gawarwakin daya gani babu na su duk da akwai wadanda gini ya rufe gangar jikin su, shi damuwar shi mahaifin Unaisah baison ta rasa daddynta..."
yayin da yake wadannan maganganun Khala tana agoye bayansa tana sauraron shi, kwata kwata bata iya magana saboda babu koshin lafiya atare da ita, gaba daya ta raunata, har kwara shi da ɗan kwarin shi, duk da shima yaji jiki karfin hali kawai ya ke yi, kuma hada karin Evils din da ke a jikin shi shiyasa bai rasa kuzarin shi ba..
Hakika ta tausaya ma rayuwar shi, ta damu da halin da suke a ciki, tayi bakin cikin abun da kakansa ya aikata masa, tasan hada alkawarin da tayi masa na zata fada masa su wanene iyayensa shiyasa ya damu da ita sosai, duk da har i wannan lokacin baisan cewa ita din kakarsa ce ba..
A cikin yan kwanakin da su ka yi a dajin, Sun sha bakar wahala, basu da abincin daya wuce ganyayyaki, Ga miyagun namun dawan da suke kawo masu hari badan Danish Yana atare da Khala ba, da tuni sun jima da kashe ta, Ya bata kulawa, baya bari ko ƙwaro Ya ta6a fatarta, duk in zata farka tsakar dare zata taras da shi a zaune a gefen ta Yana gadin ta, sai ta tursasa masa sannan take samu ya runtsa shima, bai ta6a bari ta taka da kafafunta ba, duk in zasu cigaba da tafiya abayan shi yake goyata kamar karamar yarinya.
saboda depression din dake damunta kullum da matsanancin ciwon kai take fama, Ga konuwar da kanta yayi tana azabtuwa, don ma Danish Yana kokarin yi mata treatment da yan dabarunsa na sihiri, shima jikin nashi ba lafiya, mararsa tana matsa masa da ciwo, ga gabobin jikinshi da suka raunata, ahaka wata shakuwace mai karfi ta shiga tsakanin su.
A daren wata rana ne, khala ta ɗanji saukin jikinta, bakinta ya bude, yaji dadi da yaga ta fara magana, tunkan ya tambayeta wani abu ta fayyace masa abun daya faru da ita sannan tace tasan ya ƙaraga da yaji su wanene iyayensa cike da zumuɗi yace mata eh.
Tayi murmushi tace zata yi mashi wata tambaya daya kacal yace yana jin ta, tace ya fada mata lokacin da Owais yaje da su inda ya ke rayuwa, bai ta6a ganin wani mutum mai kama da shi ba sosai.."
baiyi wani dogon tunani ba yace"Chief yana kama dani amma daddy minister yafi kama dani"
"Wanene shi"? Ta tambaya kamar bata sani ba.
Yace"Uncle din Chief.." tana murmushi tace ya bata labarin farkon haduwarsu, nan ya labarta mata tun ranar farko daya farajin muryarshi a lokacin daya dawo suffarshi ta mutane ashe yaji komai da Prime minister ya ke fada, hatta labarin da yaba Taj na dansa daya rasa, a cikin labarin daya bata hada ranar dinner din hateem da komai daya faru da zuwansu garden tare da shi.
Tunkan Ya karasa bata labarin yaga ta fashe da kuka, hankalinsa Ya tashi ya soma tambayarta meya faru? Meyasa take kuka? Ko Labarin daya bata ne"?
Jinjina mashi kai tayi, cikin shesshekar kuka tace"tayaya baza tayi kuka ba? Ko a tarihi bata ta6a jin soyayyar uba da ɗa irin wadda uban shi keyi mashi ba, tunkafin ma yasan shi din dan shi ne"!
lokacin da tayi wannan maganar, ruɗewa yayi, muryarsa na rawa yace ta fada masa wanene daddy minister? Tasan shi ne? Ko shi ne daddynsa"!
Cike da zakuwa yayi tambayar kamar zai hadiyi zuciya saboda zumudin ta fada masa, cikin karyayyar murya tace" shine mahaifinka, Prime minister Hateem, jaririn da kaji yana ba da labari bakowa bane face kai, kaine Omair dinsa, ita kuma matar nan data cire maka mask a ranar dinner din da ku ka je, Itace mahaifiyarka, sheikha Mujeedat, aranar da ta haifeka aranar ne munafukai suka hada baki gurin raba ka da ita"
bata kare labarta mashi ba, sakamakon kukan daya fashe da shi, har saida ta razana da ganin yadda yake kuka a lokaci daya kuma yake dariya, ta rasa gane kukan bakin cikine kona farin cikin sanin su wanene iyayensa? Lamarin Ya daure mata kai tamau, saboda bata ta6a ganin Danish yayi irin wannan kukan ba da dai idanun ta
A ruɗe ta shiga tambayar shi meya faru da shi? Meke damun shi? Meyasa ya ke kuka? Na bakin ciki ne kona farin ciki"?
A lokacin kasa buɗe baki yayi ya bata amsa, tsabar yadda yake kukan jikinshi har jijjiga yakeyi, shatun jiyoyin wuyansa dana goshinsa sun fito ruɗu ruɗu kan fatarsa.
kifa kansa yayi saman ciyayi, hankalin khala atashe Ta dago da shi tare da rungumeshi a kirjin ta, ta ɗaura tafukan hannayenta akan bayanshi, Cikin sigar lallashi ta dinga bubbuga bayanshi tace bata san ya zatayi ba don ta kwantar masa da hankalinsa, tasan idan tace yayi hakuri kamar ta cuce shi ne, amma yayi hakuri tasan an cutar da rayuwarshi, an tauye mashi hakkin shi na rayuwa, an kuma raba shi da iyayen shi, wanda tayi imanin da ace a hannun iyayensa ya taso ko chief Owais bazai kai shi samun gatanci ba, saboda arzikin iyayensa bazai misaltu ba, mahaifinsa prime ministern canada ne, mahaifiyarsa kuma diyar Ruler din dubai ce, amma har yanzu bai makaro ba, taji dadi da Allah ya raya shi, in sha Allah zai hadu da iyayen shi, tana da tabbacin a cikin shekara daya zasu sauya mashi rayuwar shi in har ya koma gurinsu, zai manta da duk wani bakin ciki da azabtarwar da ya fuskanta agidan kurkukun ƙaddara, zai zamanto daya daga cikin matasan da suka fi samun gata agurin iyayen su.."
maganganu masu dadi khala ta dinga fada masa har saida ta samu ya lafa da yin kukan, sai dai Jikin shi yayi zafi rau, da alama zazzabine ya lullube shi, lokacin daya dago da fuskar shi, ta 6aci da hawayensa, idanunsa sun kada jawur, tayi tsammanin zai tambayeta wanene ya sadaukar da shi, sai baiyi hakan ba, muryarshi tayi rauni ta disashe dakyar ta iya gane me ya ke son fada mata..
Cewa yayi yau ce rana ta farko da yayi farin cikin da bai ta6a yin makamancinsa ba arayuwar sa, a halin yanzu baida burin daya wuce yaga iyayensa ido da ido, yana matukar son yagansu koda da numfashin shi na ƙarshe ne..."
tsananin tausayinshi ne ya kamata aranar kwana sukayi a zaune yanata yi mata sambatu akan yadda yake zumudin yagan su har tambayarta yayi zasu ji dadi idan suka san shi dan su ne tace mashi fiye da yadda yaji dadin jin cewa sune iyayen shi..."
A washe garin ranar da sukayi firar, bayan ya sama masu abun da zasu ci, suka kama hanya, dayaga bata sauri yace ta hau ya goyata tace aa bata so ya wahala, tun da ta danji sauki zata iya tafiya da kafafunta, ko ta dafa shi tun da babu sanda atare da ita.
Batasan yadda ya matsu su koma gari ba, batai aune ba taji ya sungumeta akan kafadarsa ya 6ace da su..
Cikin sa'a suka faɗo wani forest din, A gaban wata bishiya ya sauke khala agajiye suka baje kasa nan bacci yayi awon gaba da su.
Har mafarkin prime minister ya yi acikin baccin sa.
Suna tsaka da yin baccin kwatsam ƙarar Mota ta cika kunnuwansu, a firgice suka farka har sun zabura zasu mike saboda sunyi azan wani mugun abunne amma da sukaga ba abun da suka zata bane sai hankalinsu Ya ɗan kwanta.
Wata katuwar motar daukar kayace kirar toyota mai budadden baya, ta kunno kai cikin dajin, dattijai ne guda biyu daga gani wani mahimmin aikine ya kawo su cikin dajin..
Kwata kwata basu lura da su ba, har saida sukayi parking din motar, fitowa su ka yi daga ciki.
ɗaya daga cikin su yana aruƙe da bindiga irin ta mafarauta, yayin dayan qugunsa ke a soke da Sheath Knife, daga gani mafarauta ne ko wani abun suka zo nema a cikin dajin, suna ƙoƙarin wuce wa cikin dajin idanunsa sukayi masu tozali da su, kura masu idanu sukayi kamar sunga wani mugun abu, kamar yadda suke kallonsu haka suma suke kallon su, khala ce ta yi karfin halin yi masu magana tace su taimaka su fitar da su daga dajin, kallon juna sukayi jin tayi magana da yaren da basa jin shi, da ta fahimci basu jin hausa sai ta maimaita maganar cikin harshen turanci.
An ci sa'a suna jin yaren daya daga cikin dattijan yace tayaya zasu taimake su bayan basu san su wanene su ba? Don shi kwata kwata basuyi mashi kama da mutane ba, musamman matashin dake a bayanta" ya fada yana nuna Danish da yatsan shi, dayan dattijon yace"su fada masu gaskiya mutanene su ko aljanu? Me kuma su ke yi a cikin daji"?
Ta lura Danish su ke ji ma tsoro duba da yadda su ke kallon shi ga dukkan alamu kyan shine basu taba cin karo da mai irin shi ba, ga zanan tattoo dinsa dayasa suke zargin dan wata ƙungiya ne ta ƴan ta'adda.
Khala tace ba abunda suke tunani bane, suma mutane ne kamar su, matashin da suke gani atare da ita jikanta ne kaddara ce ta ritsa da su suka tsinci kansu a dajin su taimaka su shigar da su cikin gari.."
Karya ta shirga masu ta dinga rokonsu dakyar ta samu suka aminta da su, su ka ce su shiga motar, su jira su su gama abun daya kawo a cikin dajin, bayan sun buɗe masu motar suka shiga daga ciki, hankalinsu ba karamin kwanciya yayi ba ganin sun samu taimako, nutsawa dattijan su ka yi cikin dajin tsawon rabin awa, kafin suka dawo hannayensu ruƙe da damun ganyayyakin da suka tsinko, abayan motar suka tura ganyayyakin, kafin suka bude motar, suna shiga mazaunin gaba suka yi arba da abun daya daure masu kai, mutanan da suka bari a motar sai bacci su ke yi ga zufa da ta wanke fuskokin su daga yanayin yadda suke fitar da numfashi yasa suka fahimci basu da ƙoshin lafiya.
Jan motar su ka yi tare da bata wuta suka kutsa cikin gari sun danyi tafiya mai nisa kafin suka ƙaraso cikin birnin abomey-calavi da ke a ƙasar Benin.
Koda suka shigo cikin gari, sai suka faka motar suka soma kokarin tada su daga bacci don su faɗa masu sun karaso cikin gari su sauko su tafi..
Sai dai me? Babu alamun zasu farka, har bubbuga kafadarsu su ka yi amma shiru, hakan ba karamin daga hankalinsu yayi ba, abunda suke ma fargaba kada ace sun mutu a cikin motar su, daga taimako?
Har sun yanke shawarar kaisu wani guri su jefar da gawarwakin su, kwatsam tarin tsohuwa Khala ya katse masu hanzarinsu, da sauri suka shiga tambayarta meke damun su ne?ba su da lafiya ne? Cikin disasshiyar murya tace su taimaka su tafi da su gidan su, idan suka sauke su basu san ina zasu dosa ba, saboda su ba yan nan bane, taji suna wani yare da ba irin na su ba, koda suka tambayeta wani gari take a benin? Tace masu ita ba yar benin bace, Yar nigeria ce,.."
waro idanu waje sukayi, alamar mamaki.
Basu kara tambayarta ba ganin halin da take a ciki, saboda basu yarda da su ba, shiyasa suka ki kaisu gidan da iyalinsu suke, don karsu cutar da su, sai su ka garzaya da su gidan gonar su, su ka basu ɗaki ɗaya mai toilet a cikin sa, Ko gado babu sai katifa.
Allah yaso sun fada hannun nagarin, Har abinci suka basu, duk da yunwar da su ke ji sun kasa cin abincin saboda ba irin cimarsu bace, sai dai suka sha kayan marmarin da suka tsinko masu na lambun su.
Bayan sun yi wanka, suka kwanta kan katifar dakin anan bacci yai awon gaba da su..
Dattijan suna leƙan duk wani motsinsu a dakin, saboda suna kokwanto akan su.
Saida suka ga bacci yayi awon gaba da su, suka lallaba tare da shigewa cikin dakin suka soma laluba aljihun wandon danish don suji in akwai kudi su sace su, Yana jinsu yayi shiru kamar yana bacci, jira yake su wuce gona da iri su ci uban su.
Da suka ga babu kudi cike da takaici suka bar ɗakin, tafiya su ka yi sai dare suka dawo a lokacin suna zaune kan katifar suka shigo masu bayan sun gaida khala tayi masu godiya, su kace su yanzu so suke su san komai game da su, tace suyi hakuri zata sanar da zasu amma kafin nan tana so su fara bata waya zata kira gida..
Dakyar ta samu suka ara mata waya, bayan sunyi deal zata biya su kudin katin da zata ci ma su saboda sunga international call ne tace karsu damu zata biya su konawa su ke so.
Saida ta kar6i wayar, ta fara tunanin wa zata kira cos gaba ɗaya ta manta phone numbers din ya'yan ta, Danish ne Yace ta bashi wayar zai kira Chief owais ya haddace numbar sa.
da sauri ta bashi wayar ya kar6a Ya soma danna number din Chief bayan ya gama ya danna mashi kira, har sun fara murna ganin kiran ya shiga amma chief bai ɗaga ba, almost 30 times suna kira baya picking.
har dattijon ya kar6e wayarsa a washe garin ranar da safe, da suka zo kawo masu abinci, ta k
Ƙara roƙonsu su ara mata wayar, dakyar suka bata, ta dinga kiran Chief baya picking, kamar za su yi hauka, gashi tayi tayi da su su kaisu asibiti don aduba lafiyar su, amma suka kiya saboda gudun kada a caje su kuɗi.
A ƙarshe Text message ta tura ma Chief owais, tace owais ka taimaka idan ka ga kiran nan ka neme ni, tsohuwa Khala ce ta gidan kurkukun kaddara, Ina a tare da Danish... 🔥
Bayan Sati ɗaya da ƴan kwanaki da kai farmakin farko gidan Kurkukun ƙaddara
__________CHIEF OWAIS💓
Around ƙarfe sha daya na safe, yana a office dinsa tare da COO Commender Haroon suna dan ta6a fira kan abun daya faru agidan kurkukun ƙaddara..
"Har yanzu na kasa mantawa da tsohuwar nan, ta tsaya min araina, kuma inaji araina har yanzu Danish Yana araye, amma tayaya zan iya gane hakan? Anya Ba zamu koma kurkukun nan ba"?
Ya fada da damuwa akan fuskarsa, Yayin da idanunsa ke a cikin na Haroon.
"Tunanin mu yazo ɗaya Sir, Yaron nan yana araina, bazan 6oye maka ba, wallahi ban ta6a jin kaunar shi kamar yadda naji aranar da muka je kai farmaki, yayi kokari sosai, duk da halin dayake a ciki damuwar shi akan mune baison kowa ya rasa ran shi,..."
Dg yace "Kusan kullum sai Uncle Hateem ya kira ni ya tambayeni Ina baby boy dinsa, sai in rasa amsar da zan ba shi, kasan ya kwallafa rai akan Danish, pls Commender ka bani shawara, tayaya zan san idan yana araye koya mutu"? Ya tambaya yana kallon Haroon daya yayi shiru yana kallon shi.
Numfasawa yayi kafin yace"me zai hana mu sake yin meeting, idan komawar ta kama muyi sai muje, saboda ko da ace Danish Ya ku6uta tayaya za'ae mu iya sani mu? Yaron da baisan komai ba? Bazai iya kawo kan shi gidanka ba Sir, zai ma Iya fadawa wani gurin"!
Maganar Haroon Ta ɗaga hankalinsa, Harya bude baki zai kuma yin magana kwatsam Wayarsa dake akan table ta hau yin ruri, janyo ta yayi tare da duba screen din, ya mutsa fuskarsa yayi batare da yayi picking ba..
"Sir, tun da muka fara magana ake ta kiranka awaya, yakamata ka daga kaji wanene"? Girgiza kai yayi"haroon, kasan bana ɗaga bakuwar number, babu wanda yayi requesting yana son magana dani wannan layin special ne ba kowa yake dashi ba, kuma numbar daga kasar benin ne tayaya zan ɗaga? May be wrong number ne tun jiya suke kira"
Commender Yace"Sir, kayi hakuri ka daga kiran nan, Ni inaji araina kira ne mai mahimmanci, kuma saboda kai akayi shi, kamar yadda kace Contact dinka special ne, babu wanda zai iya hasashen numbarka in ba wanda ya ta6a gani ba, bana so rashin dagawarka ya zama silar da zamuyi danasanin rasa abun da wanda ke kira zai faɗa maka"!
har kiran ya katse baiyi picking ba, Commender haroon ne Ya matsa mashi akan ya daga kiran, yana kokarin bin kiran sai ga sakon da Khala ta turo mashi, wata irin zabura yayi tare da mikewa yana zare idanunsa yayin da ya ke karanta sakon.
A sukwane commender Haroon Ya mike tsaye yana tambayar shi lafiya? Meya faru"? Muryar shi na rawa ya furta"Khala da Danish suna araye! Ina tunanin su ne suke kira na"!
washe baki Haroon yayi, tsantsar farin Ciki da al'ajabi ne akan fuskokin su..
Jikin shi na kerma Ya kira layin, kiran na shiga aka ɗaga.
Cike da zumudi Ya furta"wanene ke magana"?
Muryar Danish ce ta ratsa kunnuwan shi.
"Chief, it's me Danish.."
tsantsar al'ajabi ne ya ruke shi tamau, idanunsa azare, baisan sa'adda Ya yi sujjada ba tare da furta"Alhamdulillah Alhamdulillah.."
miƙewa yayi ya kanga wayar a kunnansa" Danish dama kana araye? Danish Kana Ina yanzu? Tayaya zan hadu da kai"?
Shiru bai bashi amsa ba, yana ta kiran sunan shi har ya yi tsammanin kiran ne ya katse Unexpected yaji muryar dattijo na magana da turanci
"Barka yalla6ai, kana magana da adamu ne, daga nan Abomey-calavi benin".
gaba daya tsohon ya zayyana masa ta yadda suka taimakesu a daji..
wani irin farin ciki ne Ya cika Chief Owais Ya ce ma tsohon su kula da su, zai basu ko nawa su ke buƙata, bai son komai ya same su, yau zai shigo ƙasar.."
Dattijon Yace mashi Toh, Allah ya kawo shi lafiya.."
yana gama wayar, Ya fayyace ma Haroon komai da suka tattauna da dattijon, ɗaga hannayensa sama yayi Tare da yin hamdala Yace dama shi saida ranshi ya bashi kiran nan mai mahimmanci ne shiyasa ya matsa masa akan yayi picking, yanzu abun daya kama suyi shine su kira Pilot dinsu .
Batare da bata lokaci ba, nan take Chief Owais Ya kira jet Pilot din su.
Bugu ɗaya yayi picking,
"Captain I need you to prepare the jet for immediate departure."
"Destination, sir?"
"Abomey calavi benin, to be precise."
"Benin Republic, sir?"
"Yes, I have urgent business to attend to, Ensure all necessary clearances are obtained."
"Understood, sir, What's the estimated departure time?"
"Two hours from now, Make sure we have sufficient fuel for a return trip."
"Consider it done, sir Will there be any passengers accompanying you?"
"Yeah, ni da Commender Haroon ne"
"Okay sir"
Daga haka sukayi sallama, Ya mayar da wayar a cikin aljihunsa, Ruke hannun Haroon yayi a hanzarce suka fito daga office din tsabar sauri lift suka hau ta sauke su down, Suna futowa suka nufi parking space tun kan su karasa SA ya buɗe masu mota, a back seat suka zauna, SA din Ya shiga Ciki, Chief yace Ya wuce da su NAI Aiport, da matsakaicin gudu motar su ta fuce daga Headquarter din..
Lokacin da jirginsu yayi landing a Airpot din dake a cikin birnin abomey calavi..
Bayan sun fito daga Airpot din, Ya kira layin Adamu Ya fada ma shi Location din da zasu same shi.
Bada jimawa ba, Sai ga Motar dattijan ta karaso inda suke, basu sha wahalar gane su ba, saboda Chief ya kwatanta ma adamu kakin da ke a jikinsu.
Bayan sun ɗaukosu a motar suka nufi Gidan Gonar da su, kowa da abun da yake saƙawa aran shi, su suna Allah Allah aransu su isa don suga Idan sune, yayin da su kuma dattijan suke ta ayyana kudaden da zasu samu agurinsu, tun da suka ga yanayin shigarsu suka fahimci akwai arziƙi atare da su.
Lokacin da suka karaso gidan Gonar, bayan motar tayi parking, suka fito gaba dayansu cike da zumudi Chief ya tambayi suna Ina.
Dattijan sukace ya fara biyan su tukunna su nuna masu inda suke!
Commender Haroon yace"karsu raina masu hankali, basu ga kakin dake a jikin su ba? harara daya daga cikinsu Ya watsa masu Yace"Idan har ba zasu biya su ba, to su koma inda suka fito.."
Chief yace su fadi ko nawa suke so, zai biya su da dollar.
Commender Yace ba zasu basu ko sisi ba, ya ma daina maganar zai biya su, kamar fa sunyi kidnapping dinsu ne, wanda hakan Ya sa6a ma doka a matsayinsu na jami'ae su biya kudin garkuwa.."
Chief yace"bazai iya jurewa bane, Yana son ya gan su"
Commender Yace"har yanzu bai yarda da su ba, kada sai sun biya su kudin su ki nuna masu su.." da harshen hausa sukayi maganar hakan yasa dattijan basu iya gane me suke cewa ba..
Haroon Ya ce"sunji zasu biya su ko nawa suke so, amma su fara nuna masu koda hotunan su ne, don su gasgata ba karya suke masu ba"
da sauri adamu ya zaro wayarsa daga aljihu Ya buɗo hoton Danish daya dauka batare da sanin shi ba a lokacin dayake bacci shida khala Ya nuna masu
Farin ciki ne ya lullu6e Zuciyoyin su, nan take Chief ya kar6i account number dinsu saida ya fara canza masu kudin da wayarsa Ya maida kudin kasar su tukunna Ya tura masu kimanin miliyan biyar"
koda suka ga kudin sun sauka a cikin account dinsu, tsabar murna yasa suka zube kan gwiwowinsu sunayi mashi godiya kamar zasu kai goshin su kasa, daga gani Shegen son kudi gare su, gashi daga taimako sun samu kudin da sai sunyi shekaru zasu iya tara su..
Rakiya sukayi masu har zuwa dakin da suke.
Chief ne Ya fara shiga dakin, kaitsaye idanunsa suka sauka akan Danish dake a kwance kan katifa Yana bacci, shi kadai
A hankali Ya zauna daga gefen katifar, Commender Haroon Ya zuƙunna gefe ɗaya, Yayin da dattijan suke atsaye bakin kofar dakin suna kallon su sai faman washe baki su ke yi.
Harara Haroon ya watsa ma su yace "ku rasa a ina zaku aje mai rai sai a wannan kongon gidan" ya fada Yana jifar su da harara, hakuri suka hau ba shi dayake sun basu kuɗi.
Hankalin Chief baya akansu, Zuciyarshi ta karaya da ganin halin da Danish Yake a ciki..
A hankali Ya shafa gefen fuskarshi, ya ɗan bubbuga kirjin shi, numfashi Yaja tare da kokarin bude idanun shi da suka disashe saboda bacci..
"Danish, Chief ne, ka tashi kaganni, Ina atare dakai"
a cikin kunnansa ya tsinkayi muryar Chief, Firgigit ya karasa ware idanunsa da suka kada jawur, yana ganin Chief jikinshi na 6ari Ya miƙe zaune tare da janyo shi suka rungume juna kamar zasu koma mutum ɗaya, gaba daya hannayen chief na a saman bayan Danish, Cikin sigar lallashi ya ke shafa bayansa.
"Ina tsohuwar take? Ko itama sai mun biya zaku nuna mana ita"?
Haroon ne ya fada yana jifar su da harara.
kafin su furta Kalma sai ga Khala ta fito daga Cikin toilet din dakin, dakyar take taka kafarta koda idanunta su ka yi mata tazoli da Chief dake a rungume Da danish sai taji wani irin farin ciki ya lullu6e ta kamar ta zuba ruwa kasa ta sha.
Cikin rawar murya tace "Owais! Danish cousin dinka ne, shine babyn Hateem na karshe da Sheikha mujeeda ta haifa masa, na fada masa komai game da iyayensa"
lokacin da yaji wannan maganar daga bakin Khala baisan sa'adda ya kara matse danish a kirjin shi ba, wani kuka ne ya balle masa, daga shi har danish din aka rasa mai lallashin wani a cikin su.
murmushin farin ciki Haroon Ya saki bayan ya gaishe da khala, Ya juya ya kalli dattijan da suka kura masu ido Yace"pls tun da kun kawo mu mun gansu, ku dan bamu wuri zamuyi magana ta sirri"
Har suna haɗa baki gurin cewa dama abun dayasa suka tsaya suna son suji idan nan zasu kwana, don su kawo masu wata katifar da kuma abunda zasu ci"
cike da kyankyami Haroon Yace"kasan su wanene mu kuwa? Kana nufin a wannan kongon zamu zauna"?
Look bamu bukatar komai daga gare ku, mungode da taimakon da ku ka yi mana, Allah yasaka maku da Alkhairi, ga kuma kudi kun samu, don haka ku tafi, Idan mu ka gama tattaunawa, zamu bar maku gidan gonar ku.."
amsawa sukayi da toh sunata washe baki sufa yau ashar dinsu kakarsu ta yanke saka.
Har suka bar dakin Chief bai raba jikinshi daga na Danish ba, sun ki sakin juna..
Da murmushi akan fuskar Haroon Yace"finally Chief ya haɗu da cousin brother dinsa da ya rasa, dan uwansa mai kama da shi, me jarumta irin tashi."
Cike da farin Ciki khala tace"tana tayasu murnar sake haɗuwa da juna, suyi kuka son ran su, suji ɗumun junansu, babu abun da zai sake raba su in sha Allah"
kalamai masu dadi da karfafa gwiwa ta shiga gaggaya masu.
Lokacin da suka raba jikinsu daga na juna wata irin zuface ta wanke fuskokinsu da jikinsu, ga wani zafi da jikin nasu ya dau ka, Idanun su cikin na juna, yayin da hawaye ke cigaba da shararowa kan kuncin kowannansu.
Cikin shesshekar murya Chief yace"am really sorry danish! Nayi zaton kun mutu, wallahi Bansan kune kuke kirana ba, da tun ranar farko nazo na tafi daku, bansan kana araye ba, Danish kana araina dakai nake kwana dakai nake tashi, saboda yadda na damu dakai har mafarkin ka nakeyi, Danish ashe da rabon zamu sake ganin Juna? ....."
Nan take ya labarta masa komai daya faru, Hankalin Danish Ya kwanta da jin cewa Daddyn Unaisah da salsabeel dinsa suna araye sai dai baiji dadin nasarar da basuyi ba akan Elders..
"Ku faɗa mana tayaya akai kuka ku6uta daga Kurkukun kaddara..." Haroon ne ya tambaya.
"Owais Ni baka ganni ba"? Khala ce ta fada mikewa yayi tare da duban ta..
"Ina sane dake, kema kina araina tun ranar dana fara ganinki da kuma maganar da kika fada akaina, kamar kin sanni! Pls ki fada min wacece ke? Kamar na sanki, Inaso na sani!"
"Owais baka gane ni ba har yanzu? Ka dubeni dakyau, duk da nasan tsufa ya boye ainihin kamannina.." kura mata idanun shi yayi sosai"wadda kike min kama da ita, ta mutu yanzu bata araye,"
Murmushin takaici tayi"owais, zan fada maka abun da kake son ji akaina, ba yanzu ba, saboda a halin yanzu Daga ni har Danish muna bukatar kulawar likitoci saboda ba lafiya gare mu ba..."
nan take ta fayyace masu komai daya faru bayan Elder Ya ritsa da ita.
Hankalin su Ya tashi matuka sun kuma tausaya mata, sun jima suna fira a tsakanin su.
A ranar suka bar gidan gonar, Commender Haroon ne yayi masu booking Hotel Rooms din da zasu zauna, da taimakon adamu da ya shige masu agaba shi da yasan takan Birnin nasu..
Saida khala ta yi jinya a asibiti, na tsawon kwana biyu docs suna yi mata treatment na konuwar da kanta ya yi, Chief bai miƙa danish Asibiti ba saboda baya son ma wani ya gan shi, yasan yadda yake da jan hankali mutane zasu iya daukar hoton shi a boye wanda yin hakan zai iya jaza mashi matsala, tun da idan har Elders suka san suna araye, zasu nemi hanyar da zasu salwantar da rayuwarsu ne, sai dai ya dauki hayar Likitan da zai duba shi a boye, Cikin kwana ki biyu ya dan ji saukin jikin shi.
Ganin sun murmure Yasa Chief Ya fara tunanin Komawa da su Nigeria, koda ya tuntu6i Haroon da maganar komawar su bai goyi bayan su koma tare da su ba, saboda rayuwarsu tana a cikin haɗari, In har Elders suka san suna araye sai sun nemi hanyar da zasu kashe su saboda sune silar da aka kai musu farmaki, kuma yadda suka ci amanar su ba zasu ta6a ƙyale su ba, dole su dauki fansa akan shi ƙwara su nisanta su daga Nigeria har zuwa lokacin da zasu kawo ƙarshen Elders.
Maganar Haroon ta ankarar da shi kuskuren da ya ke kokarin yi dama yana zargin akwai sa hannun nashi a ciki! In har ya koma da danish cikin yan uwansa Elders zasu iya sani tun da yasan suna da yan leƙen asiri.
basu gama yanke shawarar inda zasu boye su ba, Chief Ya ce ma Haroon zai nemi shawarar khala ya ji ra'ayinta.
Bayan daya samu Khala a dakin ta, ya fada mata abun da suka tattauna da Haroon cike da damuwa tace sunyi tunani mai kyau tabbas idan Elders suka san suna araye zasu kashe su ne! Amma tana neman alfarma agurinsa, Ya taimaka Ya haɗa Danish da Iyayen sa! Tana son ya cika burinsa, rayuwa ba tabbas batason ya mutu bai gan su ba"!
Shi kanshi baida burin daya wuce danish Ya haɗu da iyayen sa, sai dai baya jin zai iya haɗa shi da mahaifinsa tun da har yanzu bai kai ga gano su wanene ke da sanya hannu a kurkukun kaddara cikin Uncles din sa ba, wannan dalilin ne yasa shi yanke shawarar zai hada shi da mommyn shi amma fa ba zai hada shi da daddynsa ba har sai zuwa lokacin da suka kammala bincike.
kwata kwata Khala bata nuna mashi tasan wanene Elder ba, ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta faɗa masa wadanda ta sani a cikin Elders ! Kuma yana son yasan tayaya akai tasan Danish cousin dinsa ne dan uncle Hateem! amma taƙi ta sanar da shi, daya matsa lamba tace in har yana son yaji amsoshin tambayoyin shi toh ya koma da ita Nigeria ya kuma hada kowa na family dinsa a estate dinsu, ita kuma tayi masa alkawarin a wannan lokacin ne zata fayyace mashi wacece ita sannan kuma zata tona wani sirri na family din su agaban kowa"!
maganarta ta ɗaure mashi kai, Ya rude ba kadan ba, amma bai musa mata ba,
Abun daya sa khala taƙi ta sanar da shi ta za6i ya koma da ita Nigeria ya kuma tara kowa na family dinsa, badan komai ba sai don tana son ta cika burinta na ganin ta tonawa Elder asirin agaban Ahlin sa.
Masu karatu kunji dalilin dayasa Owais Ya roki alfarmar yana son ayi family meeting a ranar birthday dinsa, saboda bazai iya jira har sai date din family meeting yazo ba, kuma yana son kowa na family dinsu ya halarta duk don ya cika sharuddan Khala! Hakan na nufin dama can Owais Ya san da zuwan Khala.
___________________________🔥
Bayan daya faɗa ma Haroon yadda su ka yi da Khala, shima ya goyi bayan ya hada Danish da mommynsa a boye, tun da ba'a Nigeria ta ke da zama ba, ita kuma khala ya bashi shawarar in sun koma Nigeria da ita su boye ta a guest house din sa kafin zuwan ranar da zai kaita estate din su, Chief yaji dadin shawarar Haroon.
Su uku suka san da wannan maganar, batare da 6ata lokaci ba, Dg Ya kira Sheikha Mujeedat awaya bayan sun gaisa ya fada mata cewa game da binciken da ya ke yi akan Danish, Ya gano cewa dagaske babynta ne da ta haifa babu rai shekara ashirin da suka wuce, yana tunanin akwai wadanda suka kulla makirci gurin raba su da shi.."
Bai ƙare maganar ba, ta katse shi da cewa dama ita tajima da ji aranta jininta ne, saboda kaunar da Hateem ke yi masa da kuma kamanninsa da Hateem! shiyasa ta yi dna test din nan, amma tana so tasan su wanene suka rabata da shi? Meyasa su ka yi hakan? Laifin me tayi masu da har yasa suka rabata da yaronta tsawon shekara ashirin, bata san yana araye ba, daga haihuwarsa ko ɗumin jikinta bai ji ba, ba'a bari ta gan shi ba aka rabata da shi, akayi mata ƙaryar ya mutu! ita kawai so take ta san su wanene su ka yi mata aika aikar nan"!
cikin lallashi chief yace tayi hakuri, ta kwantar da hankalin ta, Sun kusa kammala bincike akan wadanda suke zargin sun raba ta da shi, Yanzu haka da ya ke yi mata magana yana a tare da Omair dinta, sun riga sun faɗa masa cewa itace mommynsa, kuma tun da yaji hakan ya matsa lamba akan su haɗa shi da mamansa, ta taimaka in zai yiwu yana son ta haɗu da shi, amma baya son kowa ya sani! saboda rayuwar yaron tana a cikin haɗari, miyagun da suka rabashi da su suna nan suna farautar rayuwarsa, ya zamana komai cikin sirri zasuyi shi.
kusan ruɗewa tayi saboda farin cikin jin cewa zai hada ta da dan ta.
Cike da zumudi tace karya damu, in sha Allah zata kula da komai, ba zata bari kowa ya sani ba, yanzu ya fada mata da yaushe zai turo shi canada"?
Chief yace "ba a Canada ya ke son su haɗu ba, yafi son ta hadu da shi a dubai, zaifi sirri, Yanzu haka suna a abomey-calabi benin, Zuwa jibi, zai kammala yi masa travel arrangment, kafin ya karaso ta tanadi private docs din da zasu duba lafiyar shi"
Bai kare maganar ba, tace"ba zata iya jiya har sai jibi ba, yanaso ta kasa rintsawa ne?
Dariya yayi jin abun da ta fada ya fahimci ta matsu taga danta.
"owais Zan yi magana da UAE ambassador din mu dake anan benin game da shi, zai taimaka mashi ya samu same-day trip, on non-stop flight"
Ba karamin dadi Chief yaji ba, jin zatayi mashi hanya, saboda a halin yanzu sai sun sha wahalar yi mashi cuku cuku kafin su fitar da shi daga ƙasar tun da karo na farko ne da zai fara tafiya kasar waje ba akan Private jet ba.
Bayan sun kammala yin wayar, batare da 6ata lokaci ba, tun aranar Chief ya shirya mashi kayan daya siya mashi a cikin suitcase.
A time din Yana a kudundune kan gado cikin duvet dinsa tun da Chief ya taimaka masa yayi wanka daga shi sai short Ya baje kan gado bacci yayi awon gaba da shi.
Dakyar Chief ya tada shi daga bacci, bawan Allah ya damu sosai da Jin zafin jikin shi shiyasa ya kagara ya hada shi da mahaifiyarshi watakil saiyafi samun kwanciyar hankali, baya son danish Ya rasa ranshi batare dayaga mommynsa ba..
Sai da ya taimaka masa Ya shirya cikin suit na mutunci, ya zaunar da shi gaban mirror cikin sauri Ya gyara mashi sumar kanshi ganin yadda ta hargitse..
Around ƙarfe 2 na rana, sai ga kira daga UAE Ambassador Ya shigo wayar Chief bayan ya daga cikin girmamawa suka gaisa dayake harkace ta arziƙi da kuma wa ka sani yace sunyi magana da Sheikha Mujeedat game da yaro da take so akai shi dubai yau din nan, Chief yace mashi Eh hakane, yace toh yana bukatar bayanan yaron ko da na bogi ne ya tura masa yanzun nan cos sheikha mujeedat tace bata bukatar a 6ata lokaci
ya amsa mashi da toh after sun kammala wayar, chief ya tura masa bayanan Danish ta email din daya turo masa ta sako.
Bada jimawa ba, sai ga kira daga travel agent, after yayi picking suka gaisa daga muryarsa Chief ya fahimci matashin saurayi ne, sunan Airport din da zasu haɗu ya fada mashi bayan ya gabatar mashi da kan shi a matsayin wanda zai jagoranci tafiyar Danish zuwa dubai.
Suna kammala yin wayar yaje ya sanar da Khala komai da suka tattauna da Mujeedat tayi farin ciki sosai, kafin tafiyar shi har ɗaki Danish Ya sameta, sukayi bankwana kamar karsu rabu da juna.
Chief da Haroon ne suka yi masa rakiya a cikin motar haya suka tafi.
Bayan sun karaso Airport din, sai ga Agent din Ya nufo su da murmushi akan fuskar shi suka gaisa daga bisani Ya mika ma Chief travel documents din Danish daya hada da duk wani abu da za'a buƙata, budewa Chief yayi a tsanake ya dudduba document din, murmushi yayi ganin sun shirya mashi komai, inda ma zai zauna a cikin jirgin business Class ne, ba main seating ba na kowa da kowa, a lokacin Danish fuskarsa a rufe take da mask, Ya kankame Hannun Akhi Owais dinsa a cikin na shi, Dayan hannun shi yana aruke a cikin na Commender Haroon, Agent dinne ya shige masu gaba yayi escorting dinsu to the gate for departure, duk inda suka je da zarar sun nuna masu Id cards dinsu Jiki na 6ari securities ke darewa su basu hanya, basu wani sha wahala ba, suka ƙaraso gaban jirgin da zai hau, chief ji yake kamar zai rabu da ransa saboda mutuwar son dan uwan nasa da yakeyi, da Agent din Ya lura da hakan sai yace mashi karya damu, Brother din shi zai kasance cikin koshin lafiya, zaiyi tafiya mai dadi saboda sun tanadar mashi flight attendants din da zasu kula da shi, just for his security and Comfort, duk da haka hankalin Chief ba akwance yake ba, Yaki sakin hannun danish, dayaga dagaske fa rabuwa zasuyi sai ya rungumesa sosai, Ya manna masa sumbata akan forehead dinsa da neck dinsa har kan Cheek dinsa yace mashi ya kula mashi da kan shi, kada ya sanya damuwa aranshi, Yasan bai cika son mutane ba, Inda zai zauna shi kadaine ba hayaniya, idan yana jin yunwa ko yana bukatar wani abu kada yaji shakkar komai ya fada ma Flight Attendants din da zasu kula da shi ya ƙara da cewa zanyi kewarka danish amma idan na tuna da wa zaka hadu sai inji sanyi araina, lokacin da yake wannan maganar idanunsa sun cicciko da kwalla, Agent din bai taba ganin kauna ta yan uwantaka ba irin na wadannan bayin Allahn daya fara gani ayau ba, Commender haroon Kuwa tuni Yaji kwalla ta cika idonsa saboda tausayin su.
Cikin sanyin murya Danish yace mashi shima ya kula mashi da kanshi, zaiyi kewar shi, badan yana son yagana da mahaifiyarsa ba, da ba abun da zai raba shi da shi, amma ya sani koda basu a tare yana aran shi, ba zai ta6a mantawa da halaccin da yayi masu arayuwa ba, baisan da wasu kalmomi zai iya gode masa ba, abu ɗaya da zai iya cewa shine yayi dacen ɗan uwa nagari, kuma yaya agare sa, Yana matuƙar alfahari da shi, Yana son shi..."
bai bari ya karashe maganar ba, saboda dadin da yaji Ya kuma janyo shi suka ƙara rungume juna cike da so da kauna.
Cikin karyayyar murya Chief yace"kamar yadda yake alfahari da kasancewarshi dan uwansa shima haka yake alfahari da samun dan uwa jarumi irinsa, Yana son shi, bai ta6a yima wani dan uwa shi son da ya ke yi mashi ba.."
ganin abun nasu ba me ƙarewa bane ga lokacin tashin jirgin Yana ta tafiya, yasa Commender da agent suka shiga tsakanin su, dakyar suka banbaresu daga jikin juna, Commender najan Chief, Agent din Yana jan Danish ahaka suka raba su.
har akan matattakalar jirgin bai daina waiwayen Chief Owais ba har saida suka shige ciki, kamar zai fashe da kuka saboda kaunar ɗan uwan nasa.
A wannin da sukayi a cikin Jirgin ba irin gatancin da bai gani ba a gurin masu kula da shi.
sai dai farin cikinsa ragagge ne, saboda yana da damuwa aransa, bai manta da Unaisah ba, sai dai a wannan gabar yafi bukatar Ganawa da iyayensa, Saboda Yana son Ya cika sharuddan da Zai iya rayuwa da ita cikin salama batare data goranta mashi ko ya cutar da ita ba, don har yanzu kalaman data gaggaya mashi sun tsaya mashi arai, bai manta da su ba, amma babu abun daya sauya na daga son da ya ke mata.
~______________________________________🔥~
Kafin jirgin su yayi landing, tuni Sheikha Mujeedat ta riga shi ƙarasowa dubai daga Canada, A cikin private jet din ta ta zo.
Bayan flight dinsu yayi landing a dubai International Airport..
passengers sunata fitowa daga cikin jirgin kowa ka gani hannunsa ruke da suitcase dinsa sai fara'a suke saki, royal guards din da ta turo don su tafo da shi, sun kewaye bakin matakalar jirgin sunata jiran fitowar shi duk sun kagara da suga wanene mutumin da zasu dauka, lokacin daya dira kafarsa akan matakalar, Gaba daya idanu suka koma kan shi, daga bayan shi agent din daya rakosa ne, shi ya ruke masa suit case dinsa da dufel bag din kayansa..
Suna ganinsa suka gane shine sheikha ta turo su su dauko mata, Suna karasa saukowa, guards din su ka yi masa ƙawanya kamar wani sarki, suka take masa baya, Ko kafaɗarsa baka Isa ka goga ba, mutane kansu darewa sukeyi su basu hanya, ganin kakin dake a jikin guards din, bayan sun fito daga airport din suka nufi danƙareriyar Motar da suka zo da ita domin daukarsa, Kirar mercedes benz yar uban su.
A hanzarce wani guard Ya bude masa cardoor na back seat Ya shiga daga Ciki Ya zauna akan seat, Guard din ya saka mashi belt ganin baida niyar sakawa, bayan agent din Ya damka masu suitcase dinsa da jakarsa, Ya leko ta tagar motar sukayi bankwana cos wa'adin aikinsa na rakiya ya kare aranar zai juya.
Sai da yaga tashin motocin tukunna Ya bar pickup area din..
UAE DUBAI
Palm Jumeirah🔥
Off Jumeirah Beach Road
Kai tsaye suka nufi daya daga cikin Katafaren private estate din Sheikha Mujeedat wanda ya ke a palm jumera's exclusive sector, bazan Iya misalta Haduwar Katafaren Gidan ba, Aljannar Duniya ce, anyi almubazzarancin Dirham gurin Ƙera ginin, irin daular da idan ka shige ta saima ka manta cewa da tur6aya aka halicce ka saboda shagala da ababen more rayuwar dake a ciki
Tamfatsetsan gida ne na masu arziƙi wadanda suka gaji mulki da izza, akwai masu tafiyar da gidan wanda ya hada da Staff and services, Personal assistants din ta, Private Chefs na bangaren kitchen, and dedicated House keeping staffs.
Lokacin da Motocin guards din da suka dauko Danish Suka karaso katafaren main enterance na Gidan a jere suka dinga shiga Ciki slowly kamar wadanda suka dauko eggs containers saboda Sheikha ta gargardesu akan karsu yi abunda zai 6ata ransa bai cika son hayaniya ba, suyi driving a hankali.
Bayan sun yi Parking motocin a gaban katafaren Entry hall, time da security guard Ya bude masa murfin motar, Bacci ya same shi yanayi, cikin girmamawa yace "Sir, mun ƙaraso..." bude idanunsa yayi a hankali sun yi ja sun dan disashe, Ruko hannun sa guard din yayi ya taimaka masa ya fito daga Cikin motar, suka ta ke masa baya domin yi mashi rakiya, A hankali Ya ke bin ginin da kallo, wohoho He had never experienced such opulence, Ya tafi da imaninsa, Hankalin sa ya fi karkata akan kosassun dawakan dake harbin iska a tsakar fili gidan
duk da shagalar da yayi da kallon kawatuwar Gidan hakan bai kawar da tunaninsa na son ganin Mahaifiyarsa ba.
Suna ƙarasowa gaban main door ta shiga falo, Escorts din suka juya tare da barin Bakin kofar, Ya kasance shi kadai ne a tsaye, walking slowly Ya nufi ciki ganin ƙofar ta buɗe, wow wani ni'imtaccen Sanyin A.c ne mai haɗe da kamshin bakhhoor burner Ya daki hancinsa mai dadin gaske..
bangon falon ya bi da kallo an yi mashi ado da artwork nasu na royal family with rare callighraphy, mai tsadar gaske na harshen larabci.
Takun Tafiyar dayajiyo ne Yaja hankalinsa ga kallon su, hadiman ta ne Sanye cikin Uniform dinsu, cikin sauri suke saukowa daga kan tagwayen staircase din da ke fuskantar shi, wasu ta bangaren dama wasu ta bangaren Hagu, Arude ya ke kallon su, time din da suka karasa saukowa Kaitsaye suka nufo shi, tare da russinawa kamar zasu durkusa kasa Cikin harshen Larabci Sukayi mashi barka da zuwa, bai iya gane me suke cewa ba saboda baya jin arabic.
Idanunsa sun makance Mahaifiyarsa kadai Yake son gani a lokacin.
Unexpected ya soma tsinkayar muryarta a cikin kunnan shi,
"I've been asking myself how this can be true! Am I dreaming, or is it real? The baby I carried in my womb for nine months, na haifesa ba'a raye ba, shine ya yau ya dawo gare ni da ran shi! bayan shekara ashirin, OMAIR"
a hanzarce Ya wurga Eye Balls dinsa akan ta, tun daga kasa Ya fara Bin ta da kallo, Hadiman dake a kewaye da shi cikin gaggawa suka watse tare da barin falon.
Royal gown ce a jikin ta, tayi rolling wani hadadden Head Scarf (Shayla)asaman kanta.
Kasa motsawa yayi yayin da idanunsa suka shiga cikin nata a lokacin da take tunkaro down ta kan stairs, walking magestically ta nufe shi tare da ware hannayenta, bai iya ganin fuskarta ba saboda chain mask din daya 6oye ta, muryar shi da rauni ya furta"Are you really my mom?"
"You want proof..."?
Jinjina mata kai yayi, Mika mashi hannayenta tayi, Cikin sauri Ya nufe ta Yana isa ta janyoshi tare manna shi kan kirjinta, Ta lullu6e shi da rigarta, yadda tayi tighting dinsa kamar zasu koma mutun daya, bugun zuciyarta a cikin nashi, wani irin yanayi suka ji atare da su mara misaltuwa, For the first time daya fara Jin ɗumin jikin mahaifiyar shi, gaba daya sassan jikin shi sai da suka amsa, jikinsu ya hauyin kerma kamar wadanda sanyi ya kama, ga wani zafi rau da temperature dinsu Ya dauka, Ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, Yau ce rana mafi daraja da ta wanzar da farin ciki acikin zukatansu.
da ta fara manna mashi sumbata kamar zata haɗiye shi kai sai taji ma kamar bata ta6a haihuwa ba sai akanshi saboda wani azababben Son shi da kaunar shi na farat daya da suka mamaye kowani sashi na zuciyar ta.
A lokaci ɗaya suka fashe da kukan farin ciki, kamar ruwan hawayensu zasu ƙare, shashshekar kukansu ta cika kunnuwansu,ƙanƙame ta yayi sosai, a haukace ta fara shasshafa bayan shi tana dan bubbuga shi.
kusan zaucewa tayi ta kasa yarda gudan jinin tane data haifa a mace, Yau gashi agabanta araye da ranshi, batasan da wani baki zatayiwa Allah godiya ba, Yaron ya tafi da imaninta, ture shi tayi gefe ɗaya, ya dago suka hada idanunsu cikin na juna, cheeks dinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, haka idanun nasu sun rune kamar an watsa barkono a cikin su, labbansa sai kerma su ke yi dakyar ya iya furta"mom..."
Durƙushewa kasa tayi ta fuskanci alƙibla, a hankali ta dogana goshinta kasa tayi sujudusshukr domin nuna godiyar ta ga Allah, cikin shesshekar kuka cikin harshen turanci ta furta
"Alhamdulillah, Ya Allah, nagode da kyautar da ka bani, Ina son shi Ya Allah, fiye da yadda nakeson ya'yan da nake da su, bansan meyasa suka raba ni da shi ba, bansan laifi me na aikata masu ba, amma Ya Allah ka sani, kasan komai ya Allah, Ban cutar da kowa ba, Ni an cutar dani an rabani da gudan jini na, Ya Allah ka saka mana, Ka bi mana hakkin mu, wata tara na dauki cikin shi yayi rayuwa acikin mahaifata na jure laulayin shi, nayi nakudarsa na haifi abuna amma saboda rashin imani na wasu mutanan basu barni naga koda fuskarsa ba suka rabani da shi, sai gashi yau Ka dawo min da shi Ya Allah, a lokacin da banyi zato ba...."
kasa jurewa yayi, Zukunnawa yayi tare da dafa kafadunta da tafukansa dake ta kerma, ya dago da ita cikin sauri ta ƙara janyo shi ta rungume shi, Ji take kamar ta mayar da shi cikinta ta sake haifo shi don ta raine shi da hannun ta.
"I know you wonder about me being your mother, just as I do we don't know each other we've never seen each other Maybe you never thought you had parents because you didn't grow up with us amma mu muna tunaninka saboda mun san da yaron mu wanda muka haifa babu rai, kaga yadda Allah ke ikonsa ko"? Ta ɗan numfasa tana sauke ajiyar zuciya, yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta.
"Bansan da wata manufa suka rabani dakai ba, amma inaso su sani basu rage ka da komai ba tun da har suka barka araye ka dawo gare mu, nayi maka alƙawarin zan sauya maka rayuwarka cikin kankanin lokaci, zaka manta da duk wasu wahalhalun rayuwa da kayi abaya, zan gatantamaka in baka dukkan jin dadin duniyar nan, kulawarmu da baka samu ba, har yanzu bamu makaro ba Omair zamu ba ka ita..."
ta faɗa tana shafa sumar kanshi, Yayi shiru yana sauraronta, da hannayenshi biyu ya tallabe bayan mommynsa, wani irin tsantsar so da kaunar junane ya kama su, kamar za su dawwama ahaka.
"Kada na cikaka da surutu, farin cikine Ya cika ni, na kasa samun nutsuwa, kamar in haɗiye ka na ke ji, ɗan uwanka Ya fada min baka jin daɗi, yanzu kana bukatar hutu, Mu shiga daga Ciki.."
ta faɗa tare da ruƙo hannunsa a cikin nata suka mike a tare suka nufi Upstairs, ƙamshin turaren Mommynsa Ya cika hancinsa, zai iya cewa shine kamshi mafi dadin shaka da yaji a duniyar nan, kaitsaye suka nufi katafaren Part din ta, a saman royal bed dinta ya kwanta, da kanta ta cire mashi takalmansa da socks dinsa, tanayi tana kallon fuskarsa, idanunsu a cikin na juna, duk wani motsinta akan idanun shi, ganin abun yake yi kamar a mafarki, wai yau gashi da wadda tayi silar zuwan shi duniya, ta lura kamar akwai damuwa atare da shi saboda yaki sakar mata fuska, har murmushi tayi mashi don ya mayar mata da martani amma saitaga akasin hakan, ta damu da hakan, fatanta Kada yayi fushi da su ko ya zarge su akan abun daya faru da shi na raba su da akayi.
"Ba laifin mu bane Omair, bada saninmu ba, kada ka tuhumemu akan abun daya faru dakai, wallahi da ace munsan kana araye, koda zamu rasa ranmu ne sai mun kwato ka don ka dawo gare mu.."
tayi maganar nan ne yayin da take cire mashi Suit jacket dinsa, hawayenta ya gani sun ɗiɗɗiga akan hannunsa, shi kanshi dayasan iyayensa suna araye, kuma batare da saninsu ba aka sace shi daga gare su, da ba abun da zai hana ya dawo gare su, bai tashin sanin Elders sun cuce shi ba, saida yagano su wanene iyayen sa.
batayi aune ba tafi safkar yatsun hannunsa akan fuskarta, lumshe idanunta tayi kanta har sara mata yakeyi saboda kukan da tasha, A hankali Ya shiga share mata hawayen ta, baisan ita damuwarta rashin sakewarshi da rashin maganar da bayayi mata, gani take kamar baya farin ciki amma tayi masa uziri saboda ta lura kamar rashin sabone yasa shi yin hakan ita kanta badan tanayi mashi kallon gudan jininta ta ba, da bazata iya sakewa da shi ba.
"Me kake bukata In kawo maka"?
Ta tambaya tana kallon shi, har time din bai daina kallonta ba, har saida ta tsargu da kallon..
"Pls kayi min magana, ko zaginane kayi, watakil inji sanyi araina, idan naji muryarka.."
Ƙoƙarin buɗe baki yayi sai dai labban nasa sunyi masa rauni, numfashi Yaja tare da furzar da shi.
Cikin rawar murya mai rauni da sanyi kamar tame yin raɗa ya furta"Stay by my side, don't stay away from me, I need your care, and I want to feel your hug even more, I love you more than anything, Mommy I'm overwhelmed with happiness right now because I'm with you I want to spend the rest of my life with you."
bai kare maganarba, tayi saurin kwantawa gefen shi, ta tallabo kanshi da tafin hannunta, suka ƙura wa junansu ido batare da kyaftawa ba, kamar zasu hadiye junansu, at same time hawaye suka cika idanunsu kafin suka fara zarya kan kuncinsu..
Unexpected yaga ta sanya red tongue dinta akan fuskarshi ta lashe hawayensa kamar yadda ta sabayiwa daddynsa a duk time da hawaye suka zuba daga idanunsa, wani sanyi yaji aransa kamar ta ƙafe ruwan hawayen nan take suka daina zuba, kwanto da kansa tayi kan kirjinta, taci gaba da yamutsa sumar kanshi kamar tanayi mashi susar kadangare..
"I love you more than i love my self, more than everything.." ta faɗa calmly
Daɗi ne yayi masa yawa har bacci ya ɗauke shi bata sani ba, sai da taji shiru tana ta ambaton sunan shi bai amsa mata ba, a hankali ta soma ƙare masa kallo kamar zata lashe shi ita kanta santin ɗan nata takeyi, abun da take ma zullumi tayaya royal family dinta zasu kar6e shi? Zasuyi farin ciki ko kuwa? Tayaya zatayi ma iyayenta bayanin ɗanta ne kuma Jikansu"?
akagare take da Owaisa ya kammala bincikensa don ta samu hujjar fallasa baiyanar Omair dinta ga yan uwa da abokanan arzkinta tasan zasu yi al'ajabin ganin kyakkyawan ɗan.
kamar ta samu tv haka ta dinga kallonsa, har saida ta fara jin bacci, a hankali tayi tighting dinsa a kirjinta donji take kamar za'a ƙwace mata shi.
Tamfatsetsiyar wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta fara ruri kamar ba zata yi picking ba saboda batason komai da zai rabata da jikin danta.
Gudun kada ringing din wayar ya katse mashi baccin shi yasa ta miƙe a hankali kamar wadda ta kwantar da jinjiri ta sauko daga kan gadon ta ɗauki wayar ta duba sunan me kiran ta, My in-law ta gani.
Almost 30 misscalled yayi bata batare data sani ba, saboda hankalin ta na akan baby boy ɗinta.
Gently tayi picking tare da kara wayar a kunne.
"Danish ya ƙaraso"? Daga yanayin muryarsa ta fahimci hankalinsa ba akwance ya ke ba.
"Owais, calm down your mind, Omair Ya karaso, Yanzu haka Yana akwance kan gado yana bacci"
wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauke tare da furta"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah na gode maka"
cikin karyayyar murya tace"Owais, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maka godiya ba, Owais, I couldn't bear it, when I hugged him tightly, I felt an indescribable sense of unconditional love, Owais daga ni har shi munyi kuka tamkar ranmu zai bar gangar jikin mu, Owais na kasa jurewa, bazan matsa maka ba amma ka taimaka min, ku gano su wanene suka rabani da shi tsawon shekarun nan, wallahi bazan ƙyale su ba, ko da hukumarku zata hukuntasu sai nayi ƙarar su Owais, dole su fuskanci hukunci mai tsanani dai dai da abun da suka aikata mana" ta faɗa da tsantsar 6acin rai akan fuskarta.
Bata jira taji me zaice ba taci gaba da cewa
"Owais wani irin rashin imani da tausayi ne? Bansan yana araye ba, shima baisan yana da iyaye ba, bamu san irin rayuwar da ya yi ba... "
tun da tafara magana yayi shiru yana sauraronta, saboda a halin yanzu tana bukatar wanda zata fada ma halin da take a ciki kota rage radadin dake a cikin zuciyarta..
bata kare maganarba ta fashe mashi da kuka mai tsuma zuciya..
Kasa magana Owais yayi saboda tashin hankalin da ya ke a ciki, bai ta6a jin kukan Sheikha Mujeedat ba sai yau, shi damuwar shi Idan taji labarin azabtarwar da Omair yasha agidan kurkukun kaddara baisan Ya za ta ji ba.
"Mommy, bansan tayaya zan lallashe ki ba, amma ki tuna Allah yana atare da masu haƙuri, nayi maki alkawarin zamu gano ko su wanene sukai maku aika aikar nan, kuma zamu dauki mataki akan su, pls mommy, ki kwantar da hankali, ki lallashi zuciyarki, mu godewa Allah daya bayyana mana shi da ranshi ta hanyar da bamu ta6a zata ba, Allah kadai yasan dalilin da komai ya faru mommy, a halin yanzu damuwa bata ki bace, baby Omair Yana bukatar kularki da lallashin ki, saboda baya da koshin lafiya...."
lumshe idanun ta tayi a hankali hawaye suke sauka kan kuncin ta masu ɗumi.
nutsuwa tayi tana sauraron Owais dake lallashinta tare da bata baki.
Kwatsam ta soma jin nishi da gurnani cike da fargaba ta zare dara dara idanunta akan shi wani faduwar gaba taji, Ganin yadda ya ke birgima akan gadon, tafukan hannayensa daddafe da mararsa, gaba daya ilahirin jikinshi rawa ya ke yi, fatar jikin shi ta jike sharkaf da zufa, Idanunsa sun juye sun koma fari fat gwanin nan tsoro.
Da karfi ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Om.. Omair! Meke damun ka"?
Chief owais dake sauraronta aruɗe ya shiga tambayar meke faruwa da shi? Bata kaiga bashi amsa ba ta saki wayar ta fadi kasa, ta haye kan gadon tare da janyo shi yana ta hauka hauka, idanunsa sun kakkafe, lokacin ɗaya ya fara sakin ƙara mai sautin gaske, fuskarsa tayi jawur, duk yabi ya ciccije labbansa Ya faffasa su, gaba daya tabi ta rude, ta shiga tashin hankali mara misatuwa, Tana kuka Yana kuka tare da sakin kara, duk yadda ta kai ga ƙokarin kwantar masa da hankali takasa, fargabanta kada ta rasa shi arana ta farko da ta fara ganinsa amatsayin gudan jinin ta, rungume shi tayi a kirjinta wani zafi da taji a skin dinsa saida ta nemi zaucewa, cikin harshen larabci ta dinga furta Omair Meke damunka? Me ke faruwa dakai! Ya Allah ka kawo masa sauƙi, Omair kada ka mutu ka barni, Omair, dan Allah ka saurareni, inason ka, Ina ƙaunarka Omair, bana so na rasa ka"!
Addu'o'i ta soma karantowa tana tottafa mashi akan sumar shi, ta dinga shafe mashi ita da tafin hannun ta, maimakon taga sauki atare da shi sai taga kamar ana kara masa Ciwon.
tunawa tayi da maganar Chief da yace bashi da koshin lafiya, ta tanadi likitocin da zasu kula da lafiyar shi, a hanzarce ta soma kokarin raba jikinta daga nashi, wani abu daya karya zuciyarta yadda ya ƙanƙame hannayenta yaki bari ta matsa daga jikin shi, Sosai ta fashe da kuka cikin shesshekar murya ta furta"omair ba tafiya zanyi na barka ba! bazan jure ganinka a mawuyacin hali ba, lafiyarka tafiye min komai arayuwata.."
tana ƙarasa maganar ta 6an6are hannayenta daga nashi, ta sauko daga kan gado tana faman share kwalla ta dauki wayar da ta jefar kasa, yatsun hannunta na kerma ta dannawa likitanta kira..💔
After few mins..
Ambulace ta shararowa da matsakaicin gudu zuwa cikin Gidan bayan Sunyi Parking, Medical team tare da nurses suka fara fitowa cikin sauri kowan nansu sanye da Uniform dinsa, wasu sun ruko emergency box a hannayen su..
A Falon suka iske gimbiya Mujeedat, da hannu tayi masu alamar su biyo bayanta, kaitsaye suka nufi bedroom din da Omair Ya ke, a lokacin kiris Ya rage ya ƙundumo kasa daga kan Gadon sai jan numfashi ya ke yi kamar ransa zai fita, cikin zafin nama Gimbiya Mujeedat ta tallabo shi tare da taimakon Docs Suka mayar da shi kan gadon nata, kasa barin dakin tayi saboda zullumi da fargaban kada ta rasa shi, duk tabi ta ruɗe, sai fadi take su taimaka mata kada ta rasa ɗanta, bata so wani abu ya same shi, ji take kamar ta ɗauke masa ciwon ya dawo jikin ta.
Su kansu Medical team din mamaki ne ya kamasu jin kalaman Sheikha Mujeedat akan Yaron da basu san wanene ba ko a zuri'arta basu san da zaman shi ba.
gaba ɗaya suka kewaye shi tare da bada himma gurin fara duba lafiyar jikin shi, duk da halin da suke a ciki na duba lafiyarsa hakan bai hana su yaba ƙyanshi a cikin zuciyarsu ba.
Rage kayan jikin shi sukayi, suka bar mashi short da singlet fara, zanan tattoo dinsa Yasa su jin fargaba.
Komawa tayi daga kofar dakin ta tsaya tana kallon su, jininta akan akaifa takasa tsaye ta kasa zaune gani take kamar basa yin sauri.
Muryar team led din su ta tsinkaya a cikin kunnanta
"Oxygen mask, stat! We need to get his oxygen levels up, And someone get an IV started, saline drip, now!"
cikin sauri nurses din suka buɗe akwatinan, wani nurse ya soma sanya masa oxygen mask over his face, while another inserted the IV needle into his vein.
Daga bisani docs suka fara Examining din shi.
"Pulse is 120, blood pressure's 90/60, Let's get a blood sample for lab tests." wani doc ne ya fada
Da sauri Nurses ya kar6i blood samples din Omair ya tura shi zuwa Lab..
A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacinsa, baima san su wanene akan shi ba, sai kokarin buɗe idanunsa yakeyi ya kasa saboda nauyin da sukayi ma shi.
Gimbiya mujeedat kasa zama dakin tayi saboda tausayin shi, fitowa tayi bakin kofar dakin, ta kifa kanta jikin kofar hawaye wasu nabin wasu akan fuskarta.
"Let's keep him under close observation, I want vital signs every 15 minutes." gaba daya maganganun Doc din a cikin kunnanta, baiwar Allah tasha kuka kamar ba gobe..
Da damuwa ta mamaye zuciyarta, duk in ta rufe idanunta fuskarshi take gani, Prayer room ta shiga, bayan tayi sallah ta dinga yi mashi addu'o'i tana kai kukan ta gurin Allah..
Babu gajiyawa, har sai da kiran Doc Ya riske ta, fitowa tayi daga dakin with respect dr din Ya soma buɗe mata hotuna a tab din sa masu dauke da bayanan ciwon Omair.
Yana magana yana duban fuskar sheikha Mujeedat, Tashin hankaline Tsantsa da damuwa..
Bai karasa Maganar ba ta dakatar da shi, jikinta kerma ya ke yi saboda damuwa..
"Please, I want you to do everything medically possible to save my son.." ta fada idanunta cike tab da ƙwallah
"Consider it done, Your Highness." ya amsa mata kafin ya koma bakin aikinsa.
Tun dare suke duba lafiyar shi, Har asuba ta rutsa da su, da suka bukaci zasu ƙara mashi jini, ita ta bada jinin ta duk da sun nuna in akwai namiji zasu so ace shi ya bada, amma ta kafe kan nata zasu diba, Dan a yadda takeji ko shine kadai jinin daya rage mata zata iya mallakama omair dinta, babu yadda suka iya duba da ganin lafiyayyar mace CE kuma zasu samu enough yadda suke buqata, bayan sunyi gwaji suka sanya mashi.
Kasa jurewa tayi ta nufi bedroom dinta ta dauko waya, anan ta ga miss calls na family din ta, Hada na Chief Owais, kira ta danna mashi after yayi picking yace"meke faru da shi ne? Meke damun shi? Inata kira baki daga ba, duk na damu"
Kuka ne yake kokarin kubce mata amma saboda jarumtakarta ta jure tare da numfasawa ta zayyana mashi sakamakon abunda ke damun shi Omair ta kara da cewa"Owais, bazan misalta maka tashin hankalin da nake aciki ba, pls ka fadamin garin yaya ciwuwwuka sukayi mashi mugun kamu? Bazan tuhume ka ba nasan kana iyakar kokarin ka amma Owais, ciwo kusan biyar duk a jikin bawa? Su wanene suka azabtar da shi"?
Tashin hankali da damuwa sun cika zuciyar Chief, Sai yaji duk ba dadi badan ƙwararan dalilan dayasa Ya damka mata Omair ba, da yasani bai tura mata shi a haka ba, har sai ya samu lafiya yasan zuciyar uwa musamman akan Danta.
Hakuri Ya kara bata yace ta jure komai zata gani atare da shi, ya kuma tunasar da ita yace kada ta manta Allah yana kar6ar addu'ar uwa akan ya'yanta, don haka ta dage dayi masa addu'a in sha Allah Omair zai samu lafiya, sannan Amsar tambayoyin da tayi mashi zata same su a lokacin da suka kammala bincinken su, baiwar Allah bata musa ba tace mashi toh har ta yi mashi godiya.
Bayan ta katse kiran ta kira layin daddynta Sheikh Khalid after yayi picking cikin harshen larabci
yace meyasa yanata kiranta bata picking? yana fata tana lafiya"
rasa amsar da zata bashi tayi.
Jin tayi shiru bata bashi amsa ba yasa shi furta"amsarki nake jira," numfashi taja tare da daidaita nutsuwarta kafin cikin sanyin murya tace"Alhamdulillah, ina cikin koshin lafiya baba, ina fata kaima haka"!
daga yanayin muryarta Ya fahimci babu kwanciyar hankali atare da Gimbiyar tashi.
"Meke damunki? Naji muryarki da damuwa"
da sauri tace"babu abun da ke damuna, mura nakeyi, amma nasha magani, da sauki"
"Allah ya baki lafiya, ki kula min da kanki" ta amsa da ameen.
sun daɗe suna yin waya kafin su ka yi sallama..
Miƙewar da zatayi keda wuya sai ga khadima ta yi knocking kofa.
Fitowa tayi daga dakin Khadimar ta sanar da ita medical team zasu tafi suna jiranta, da sauri ta nufi Down, Khadimar ta take mata baya, tana karasa saukowa down ta iske medical team din, wannan karon da walwala akan fuskokin su ga dukkan alamu sunyi nasara.
Har suna haɗa baki gurin sanar da ita cigaban da suka fara samu akan Lafiyarsa sannan sukace kullum zasu dinga zuwa duba shi har zuwa lokacin da zaiji sauki, godiya tayi masu tare da jinjina, bayan sunyi sallama har suka tafi basu daina santin kyan patient dinsu ba, sun kamu da kaunar shi, sun kosa ya samu lafiya don suyi magana da shi, ba dan suna jin nauyi da shakkar gimbiya mujeedat ba da sai sun tambayeta menene alakarta da shi saboda sunyi mamakin yadda ta rude akan shi, da kuma kamanninsa da Nazli asaninsu bata da ɗa namiji amma sai gashi yau sunga wani zankaɗeɗan saurayi kyakkyawa daya tafi da imanin su, gashi ta gargaɗesu akan bataso kowa ya san wani abu game da kiransu da tayi da kuma yaron, sirrine in har suka sa6a sharadin data gindaya masu zasu fuskanci hukunci, shiyasa ko gulmarsa suka kasa yi sai dai suka bar abun aran su.
Lokacin da tashiga dakin akwance ta same shii Yana sharar bacci, bawan Allah ya sha alllurai.
A hankali ta zauna daga gefen gadon, Ta ruko hannun shi a cikin nata, ta sumbace ce ta ɗago tana kallon fuskarsa dake asanye da oxygen mask.
"Allah ya baka Lafiya Omair, Allah ya tashi kafadunka, ya Allah ka musanya lafiyarshi da tawa, ni kamayar mun da ciwon nashi a jiki na, saboda ba zan juri ganinsa a mawuyacin hali ba, na damu da kai bugun zuciyata..."
duk wani motsinsa akan idanunta, Owais ya kirata yafi sau akirga duk bayan mintuna saiya kira ya tambayi ya jikin Danish saboda ya damu da shi.
Tsantsar kulawa take bashi kamar jinjiri, Lokacin sallah kaɗai ke sa tabar ɗakin, ko motsi ya yi sai ta tambayi yana lafiya?
Ba ci ba sha ko da chefs suka faɗa mata sun kammala shirya mata Lunch, tace masu bazata iya cin abinci ba, su tafi kawai, haka ta wuni har dare tana tare da shi.
A gefen shi ta kwana, ruƙe da hannunsa a cikin nata..
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Har Danish Yayi One Week Agurin Mommyn sa, jikinsa Ya murmure lafiya tafara samuwa a jikin shi, ta ko'ina kulawa yake samu daga bangarori biyu, docs din da ke zuwa duba lafiyarsa kullum da kuma Mommynsa dake tsaye akan sa, itace mutun ta farko da ya ke fara yin tozali da ita a duk lokacin daya farka daga bacci, saboda tsantsar kaunar da take masa da kulawa bata bari ya yi komai da kansa in ba shiga toilet ya kama sa ba, abinci abaki ta ke bashi ya ci, da kanta ta ke wanke mashi sumar kanshi ta gyara mashi ita, bata barin shi cikin kaɗaici.
tun aranar daya samu sauƙi ta lura bayayin sallah, ta kasa yin shiru har dai ta tambayeshi meyasa baya yin sallah yace'' mata in zai iya tunawa shi ba musulmi ba ne, tayi baƙin ciki da jin cewa ba musulmi bane shi, amma data tambayesa yana son ya musulunta babu gaddama yace mata eh yana so, nan take ta biya mashi shahada ya kar6i musulunci, Kuma duk ita ta koya mashi yadda zaiyi alwala da sallah.
Har fita ta ke yi da shi tana nuna mashi wuraren shaƙawata da ke a cikin gidan, duk don ta faranta masa rai saboda tana son ya saki jiki da ita sosai, sannu a hankali suka fara shaƙuwa kullum sai sun shiga Personal gym din gidan a tare suke motsa jikin su, sometimes su shiga Private lounge su shaƙata abunsu harma suyi fira cikin nishadi ta dinga janshi da fira tun yana jin nauyin yin magana da ita harya fara sakewa sosai, wani lokacin kuma takan shiga library da shi ta dauko masu story books tana karanta mashi, sometime su shiga private cinema dinta su kalli movies, ba karamin nishaɗi da ilmi ya ke samu ba, in ka gansu suna wasa da dariya ya yin da su ke yin fira sai ka yi zaton sun daɗe da sanin juna.
in a short time ta mantar da shi trauma din daya fuskanta abaya, gatanta shi ta ke kamar ranta, tarairayarsa takeyi kamar ƙwai a cokali, bata son ko tari ya yi, idan dare yayi a kan bedroom counch ta ke kwana tana fuskantarsa yayin da ya ke yin bacci saman gadon ta, saboda bata iya barin shi a bedroom shi kaɗai.
Saboda shi ta kira ma'aikatan gidan dukan su, ta tarasu a falo ta nuna masu shi ta gargaɗe su akan karsu kuskura suyi ganganci gurin kula da shi, su ɗauke shi tamkar ran su, batason bacin ran shi, cikin girmamawa suka amsa mata da toh.
Ta kuma bawa Private chefs dinta Jotter da doc ya rubuta na diet din sa..
Saboda Omair ta dauƙi hutun aikin ta, ta dakatar da duk wani business nata, gaba daya ta sadaukar masa da lokacin ta.
She becomes his role model, his mentor, and his influencer, Mommynsa ta siye zuciyar shi da kulawarta, soyayyarta, kyautatawarta agare sa, tayi brainwashing nashi, yanzu halayansa da ɗabi'unsa sun sauya, komai nasa natural ne, babu sihiri babu evils gaba daya sun bar jikin shi tun aranar farko da yayi rashin lafiyar nan, Allah ya yaye mashi su, zafin fitarsu ne yasa shi yin jinya.
Halayansa da ɗabi'unsa sun sauya sun dawo ainihin yadda Allah ya halicce shi da su, a lokaci yayi loosing memory dinsa baya tuna komai daya faru a baya, ko ta tambaye sa game da rayuwarsa ta baya sai yace mata bazai iya tuna komai ba.
Mommynsa kaɗai ya sani da hadiman dake yi masu hidima, sai kuma Chief Owais da kullum Ya ke kiransa awaya suyi video call ko suyi phone call duk da ya manta wanene shi? Wata rayuwa su ka yi atare? A lokacin Yana masa kallon Cousin brother dinsa da Mommynsa ta gabatar masa da shi.
Har Lokacin da Prime minister Ya kira ta awaya ya buƙaci Ya na son ganin su a Nigeria, baisan tana a tare da Omair ba, bata faɗa ma kowa ba, iya abun daya sani ta faɗa masa suna da hidindimu a dubai na bikin Ya'yan Uncle din ta, kuma idan ta tafi zatayi sati uku acan, ita ta fara zuwa dubai daga bayane su Nazli suka biyo ta, shi kuma a lokacin ya tafi Nigeria domin ya halarci family Meeting, hakan na nufin ko su Nazli basu san komai game da Omair ba.
A lokacin ta shiga damuwar tayaya zata tafi tabar danta dake bukatar kulawarta duk da akwai maids dake kula mata da shi.
Badan taso ba, Ta damƙa musu amanar shi, taja kunnansu sosai akan su kula mata da shi! Ranar kamar kar su rabu, ya rurruƙeta har bakin motarta da kyar ta shawo kan shi Yabarta ta tafi..
Daga guest house dinta ta wuce Zabeel palace the ruler's resident, kwana biyu tayi kafin su ka shirya tafowa Nigeria ita da Yazrin da Nazli.
Bayan da suka bar ƙasar, cikin ma'aikatan gidanta, aka samu wani munafuki Yaje har fadar Emir ya kai masa tsegumin Yaron da Mujeedat ta ke boyo agidan ta, ta bayan fage, Emir Khalid Ya turo Royal guards don su Binciko masa wanene yaron da ta ke boye"?
Ranar da guards suka zo palm Jumeira cikin guest house ɗin mujeedat, guards dinta na ganin su suka basu iznin shiga saboda sunsan Emir ne ya turo su.
A lokacin Omair Yana a zaune kan dining Chair, Chefs sun kewaye shi, ga abinci sun jera mashi akan table, sunata lallashin shi don yaci abinci yaƙi ci sun rasa gane meke damun shi, ko magana bai yi masu tun bayan da Shiekha ta tafi! basu san kewa bace ke damun shi..
Sa'ilin da Royal guards din suka shigo dining din
Wata razana su ka yi da ganin Omair, su ka ruɗe saboda ganin kyakkyawan matashi mai kama da jiƙar Emir.
Cikin sauri ɗaya daga cikin guard ɗin ya ɗauke shi hoto da wayarsa Ya tura ma Emir duk Fa Yana kallon su a lokacin baisan su wanene ba bai kuma san meya kawo su ba.
Ba'ajima da tura masa hoton ba sai ga kiransa bayan guard din ya yi picking Emir Ya Umarce su da su tabbatar sun tafo mashi da lu'u lu'un nan, Yana son ganin shi a cikin fadar shi"!
Bayan guard din Ya gama yin wayar da Emir, suka Umarci Omair daya taso su tafi fadar mai martaba Khalid Yana son ganin shi.
Rashin sani Yafi dare duhu, Omair baisan wanene mai martaba ba balle yayi musu biyayya ya bisu, hasalima ko kallo ba su ishe shi ba.
Tun suna bashi Umarni yana share su, har suka fara haɗa baki gurin yi masa tsawa akan Ya taso su tafi, kai a karshe da su ka ga yaƙiya sai suka kama lallashin shi..
da sukaga dagaske bazai bisu ba, sai suka fara ƙoƙarin ɗaukarsa ta tsiya, aikuwa Ya fara naɗe hannuwan rigarsa zai yi dambe da su, wayaga Iliya ɗan mai ƙarfi.
Koda Chefs suka fahimci me Ya ke shirin yi cikin sauri ɗaya daga cikin su tayi masa magana cikin harshen turanci tace mashi royal guards ne daga ruler's resident na dubai, kuma mahaifin Sheikha Mujeedat ne sarkin su sannan shine Ya turo su, kada yayi faɗa da su yayi musu biyayya su tafi ba cutar da shi zasuyi ba.
Kasa fahimtarta yayi har saida ta kira sheikha Mujeedat ta faɗa mata abun da ke faruwa, tayi mamakin jin baban ta ya turo guards har guest house dinta don su tafi da Omair, amma bata damu ba nan take Ta umarce ta da ta bashi wayar suyi magana, bayan hadimar ta bashi wayar ya kar6a ya kara a kunnansa ta fayyace masa alaƙarta da mahaifinta tace karyaji shakku aranshi, Yabisu su tafi zai fi samun kulawa agurin daddyn ta.
Bayan da suka kammala wayar ne, ya bi Royal guards din suka buɗe mashi mota Ya shiga ya zauna, suka tada motocin suka fuce daga guest house din ta..