Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 94 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 94 Complete

Takun Ƙarshe

Zabeel Palace

Fadar Zabeel hadaddiyar daular arziƙi ce dake a cikin daular larabawa, kuma Babban mazaunin Sheikh Khalid, mai ɗumbin tarihi da ikon, tana a tsakiyar Dubai, katafariyar Palace din tana a kewaye da kyawawan lambuna, tafkuna, da maɓuɓɓugan ruwa, ga dogayen bishiyin dabino, ta haɗu karshen haɗuwa, Alkamina bazai Iya misalta maku ƙawatuwar Katafariyar daular ba, Aljannar duniya, abun sai wanda ya gani

Tun daga katafariyar main entrance zaka fara cin karo da Royal security Guards karfafa masu kirar Zakuna..

Bayan da Motocin suka karaso, a harabar ajiye motoci suka yi parking, lokacin da Danish ya fito daga Motar, ya ruɗu da ganin haduwar ginin kamar a mafarki Ya ke jin kanshi..

Guards ɗin ne su ka yi escorting din sa zuwa ciki

tun shigowarsu Royal Guards suke ta Zare ido suna kallon shi, duk inda ya gifta idanun su akan shi haka da suka shiga ciki Hadimai da sauran jama'ar Fadar suka dinga binshi da kallo mai cike da tsantsar Al'jabi..

Har cikin Katafariyar Fadar Emir Khalid suka shiga da shiga, Fadawansa na ganin sa Suka zare idanun su  cike da al'ajabi suke bin shi da kallo, Abunka ga wanda baisan takan Fadar Emir ba,  maimaiko Ya zauna saiya Tsaya a tsaye ƙiƙam kamar gunki ko fara'a babu akan fuskarsa babu ladabi babu biyayya, Emir Khalid Yana zaune kan throne dinsa Cikin shigar sarakunan labarawa Na alfarma, Ya nutsu Yana kallon sa.

Cikin harshen larabci fadawan suka dinga umartar shi daya zuƙunna Ya miƙa gaisuwa gurin Emir.

Ko kallo basu ishe shi ba, har saida Emir Ya miƙa masa hannu alamar Yazo gurinsa tukunna Ya nufesa ba tare da jin fargababa, da ya ke yaga kamanninsa da Gimbiya mujeedat kamar yayi kakin ta.

Ruƙo hannunsa yayi a cikin nashi ya rungumosa Yana shafa bayansa..

Karo na farko daya fara ganin shi, duk da baisan wanene shi ba? Menene alaƙarsa da Yarsa Mujeedat? Amma kamanceceniyarsa da surukinsa Hateem da jikarsa Nazli Ya sa ji aransa zaiyi wuya in ba yaron jikansa ba ne duk da yasan Mujeedat bata da ɗa Namiji.

Bai ta6a jin tsantsar ƙaunar bare farat ɗaya a kallo ɗaya makamancin yadda yaji akan Omair ba, Bashi ba Hatta fadawansa sun kamu da kaunarsa, Kyawunshi Ya ruɗe su su da suke larabawa jinsin kyawawa, duk yadda suka kai ga ɗokinsa da jan shi a jiki sai dai sun kasa yin magana da shi saboda Yaƙi basu hadin kai, da Emir kaɗai Ya yarda shima albarkacin mommynsa ya ci.

Daga Palace Emir Ya shiga da shi Cikin gidan, Zo kuga Yadda Royal Family mutane masu ƙima da daraja su Ke kallon Omair kamar zasu haɗiyesa saboda ruɗewar da su ka yi da kyansa da kuma kamanninsa da Nazli.

Kowa Saida Ya hallara Dangin su, tun daga kan Grandparents, parents, Uncles, aunts, elders, kowa da kowa, kyawawan labarawa wadanda suka gaji Sarauta da arziƙi na fitar shari'a..

Kowa Tambaya ya ke yi wanene kyakkyawan matashin saurayin nan? ɗan wanene? daga Ina Ya ke? Wasu ma daga cikin su tambaya su ke yi mijin sheikha Mujeedat yana da wata matar ne da ta haifa masa Yaron ko kuwa Nephew dinsa ne (dan dan uwansa).

Emir ne ya fayyace masu abun daya sani game da Omair, Ya daura da cewa su yi hakuri zuwa lokacin da sheikha Mujeedat zata dawo daga Nigeria, zata fada musu wanene shi, amma Yanzu Yana so kowan nan su Ya ja shi ajiki, su bashi kulawa kamar yadda suke kula da sauran ya'yan sheikha Mujeedat saboda yana ji aranshi da akwai wani abu game da yaron tun da har take 6oyen shi a guest house din ta.! 

 kunsan larabawa da girman kai musamman ga bare amma dayake Omair ya kwanta musu arai sun ganshi da abubuwan ban al'ajabi atare da shi shiyasa su ka yi saurin amince ma shi.

Omair bai ta6a sanin Yana da babban Family na hamshaƙan masu kuɗi ba kuma kyawawan gaske sai da Ya tsinci kanshi a cikin ruler's resident na dubai, ashe shi din ɗan dangine, Ya fito daga tsatson mashahuran larabawa.

Kowa ɗokinsa Ya ke yi, amma Rashin sabo ya hana shi sakin jiki da su.

musamman Emir Ya ware masa katafaren Bedroom dinsa tare da Hadiman da zasu dinga yi ma sa hidima, in a short time Emir Ya siye zuciyar Omair, shine mutun na farko daya fara sakin jiki da shi, saboda kyautatawar da ya ke yi masa, Har takaiga dare kaɗai ke raba su, ya zama kamar ɗan Cikin sa, In zai shiga Palace a tare suke zuwa, su ci abinci atare da shi da iyalansa su fita yawon shaƙatawa, Hadiman Gidan sun sanya mashi ido sosai, kunsan ba'a raba hadimai da tsegumi burinsu kawai su ji wanene shi"?

Daga bisani Lokacin da Asirin kurkukun ƙaddara Ya Tonu duniya Taji, sa'ilin da labarin Ya risƙi Familyn Mujeedat, sun  razana sun kuma shiga tashin hankali da jin wanene surukin su Obinna, Ransu ya 6aci matuƙa, Baba Obie Ya Karya musu Zuciya, Ya ci amanar yardar da su ka yi ma shi, sun kuma fusata sosai, sai da su ka yi dana sanin ƙulla alaƙa da shi saboda basu son abun da zai ta6a mutuncin su duk min ƙanƙantar shi, suna girmama mutuncin su fiye da komai.

dama tunfil azal basu so sheikha ta auri bare ba kuma baƙar fata ɗan Nigeria saboda su a ƙa'ida basu fiye auran bare wanda ba jinsin su ba, abaya lokacin da Mujeedat tazo da Hateem amatsayin wanda takeso ba karamin rikici akayi a family din ba, duk da matsayinsa da arziƙinsa Yasha wahala kafin su bashi auranta, saboda ta rantse ta maya bata da miji a duniyar nan daya wuce Hateem, mahaifinta ne mutun na farko daya fara goyon bayan ta auri za6inta saboda tsantsar son da yake mata fiye da sauran ya'yansa ita kaɗai ce mace kuma autar sa, mahaifiyarta ma ta goyi bayanta, daga bayane kuma bayan sunyi aure Dangin nata suka Fara son Hateem saboda yadda Al'umma su ke yabon kyawawan halayansa.

saboda fallasuwar asirin Obie Har Family meeting su ka yi game da Yanke alaƙarsu da surukinsu, Mafi rinjayen su wadanda su ka fi fusata, sun goyi bayan a kira Hateem Ya saki sheikha Mujeedat, Kaɗanne basu goyi bayan yin hakan ba, daga ciki hada Mahaifinta da kawunta da kuma yayanta sun ce sai dai A kira Mujeedat tazo Nigeria suji ra'ayinta in har ta nuna tana son taci gaba da zama da mijinta babu abun da zaisa su raba su.

Haka wasu daga cikin fadawan Emir Khalid sun shawarce shi da ya yanke alaƙarsa da obinna saboda gudun surutun mutane amma Ya tsawatar ma kowa akan shi bazai Raba Mujeedat da mijinta ba, In har ba itace ta nuna tana son rabuwa da shi ba

Komai da ke faruwa a family dinsu gimbiya Mujeedat bata sani ba, Ta kashe wayarta saboda rashin kwanciyar hankali da damuwa.

Daga baya ne Emir Ya tuntubi Prime minister awaya, Ya umarce shi dayazo Yana son ganinsa, Idan masu karatu ba su mantaba akwai wani kira da Emir yayiwa Hateem Har yaji shakkar zuwa saboda zullumin kada Su raba shi da matar shi, to abun daya faru bayan ya amsa kiran, suka yi tafiyar sirri zuwa dubai tare da Iyalinsa.

Bayan sun isa Airport Royal Guards suka zo Daukarsu a motoci, kaitsaye suka garzaya da su zuwa Ruler's resident, a lokacin Hateem Bashi da nutsuwa, zullumi da fargaba sun cika zuciyarshi Ya damu da fargaban meyasa Surukinsa ke nemansa? yasan Sun riga da sun ji komai a news, kuma yana da tabbatacin kiran da ya yi masa yana da alaƙa da Abun da ke faruwa a family din su..

Kwata kwata Hateem baisan Danish Yana a tare da dangin mujeedat ba, saboda a lokacin baida kwanciyar hankalin da zai iya tunawa da shi, bai kuma san komai game da kasantuwar sa ɗan shi ba.

Bayan da suka Ƙarasa hateem bai samu tarbar daya saba samu agurin wasu daga cikin danginta ba.

 hakan ya ƙara haifar masa da matsananciyar damuwa, ta inda ya ji sanyi aransa Emir da Kawun mujeedat da Yayanta da ma wasu daga cikin su sunyi mashi kyakkyawar tarba, a bangaren Sheikha Mujeedat da ke a cikin gidan suka fara huce gajiyarsu, bayan hadimai sunyi masu hidimar kawo abinci daga bisani bayan sun huta sosai, sai ga kiran Emir ya shigo wayar Mujeedat bayan ta ɗaga yace su shigo ciki yana son ganin su.

Gaba ɗaya suka ɗunguma izuwa Private Living room, A nan suka Iske Kowa na familyn sun hallara suna jiran su.

A lokacin ba Hateem kadai Ya shiga damuwa ba, hada Mujeedat da Su Nazli, saboda sun san mawuyacin abune su ƙyale Hateem batare da sun raba alaƙar su ba.

Cikin zullumi da fargaba suka zazzauna suna fuskantar Emir khalid da sauran family members din.

Falon yayi shiru babu mai magana, Hateem Ya sadda Kan shi ƙasa cike da jin kunyar hada idanu da su, gimbiya Mujeedat ce ke ɗan tausarshi Tana matsa yatsun hannunsa dake a cikin nata duk dan ta kwantar masa da hankali.

Gyaran murya Emir yayi, Hankalin kowa Ya dawo kan shi, cikin nutsuwa ya ce sunji komai da mahaifinsa Ya aikata, basu ji dadi ba, Ya karya musu zuciya, ya kuma ja masu abun kunya a idon duniya, amma ba zasu alaƙanta shi da laifin da mahaifinsa Ya aikata ba, hakika sun tausaya masu sun kuma jajanta musu, sai dai ya sani bazasu lamunci abin da zai taba martabar family din su ba..."

 Lokacin da Hateem ke sauraronsa Hankalinsa Idan yayi dubu toh Ya tashi.

Emir Yana ƙare maganarsa, Khal din Mujeedat Ya daura da cewa"don haka, yayi hakuri da hukuncin da zasu Yanke! Sakamakon Mafi rinjayen family dinsu sun fusata sun nuna rashin goyan bayan alakar sa da mujeedat..." 

khal bai ƙare maganar tasa ba, Mujeedat ta fashe da kuka Hankalinsu Ya tashi saboda sun daɗe basu ga zubar hawayenta ba, Cikin karyayyar murya tace kada su rabata da Hateem! Bazata iya rayuwa batare da shi ba, tayayama zata iya barin shi a mawuyacin halin da ya ke a ciki? Dame zaiji? Su dubi girman Allah kodan darajar ya'yan dake a tsakaninta da Hateem kar su rabata da shi, zata iya rasa ranta su tausaya mashi!"

duk yadda Nazli takaiga izza saida ta sanya baki ita da Yazrin suka taya mommynsu rokon danginta akan kada su raba su da mahaifinsu, ba laifinsa bane, ko Allah baya kama mutun da laifin da bashi ya aikata ba, su tausaya masu! In kuma har suka raba mommynsu da daddynsu suma zasu yanke alaka da su, saboda bazasu taba rabuwa da daddyn su ba.

maganar Su Nazli ta ɗaga hankulan su, saboda suna son su kamar ran su amma still basu canza ra'ayin su ba.

Khalar Mujeedat tace ba zasu taba canza ra'ayin su ba, dole Sheikha ta za6a, ko dai Ta rabu da Hateem ta rayu da danginta, ko kuma taja ma kanta itama su Yanke alaka da ita.

Hateem baisan sa,adda hawayen bakin Ciki suka wanke fuskarsa ba, sam Ya kasa magana sai dai jinjina kansa da ya ke yi.

Daƙyar ya iya buɗe baki, cikin girmama yace baiga laifinsu ba, bai kuma ji zafin hukuncin da su ke so su Yanke mashi ba, mahaifin shi ne yaja ma shi! amma bai ta6a zaton jin hakan daga gare su ba, a matsayinsu na musulmai masu ilmin musulunci, sun san komai ya faru da shi mukaddarine daga Allah, bai kamata su juya mashi baya don mummunar kaddara ta same shi abun da ya faru da shi zai iya faruwa da kowa haka Allah ke jarabtar bawansa ta inda bai zata ba! amma kafin su fara yanke hukuncin raba shi da matar shi, yana neman alfarmar su akan su ba mujeedat za6i tun da tana da Ƴan ci, ta faɗi ra'ayinta akan alaƙarsu, saboda bazai ta6a sakin ta ba, kuma bazai rabu da ita ba, In har ba ita da kanta ta nemi ya sake ta ba, idan kuma su ka ce zasu tilasta masu, zai sanya lauyoyinsa a ciki.

 lokacin da ya yi maganar zuciyarsa a wuya ta ke, yana jin zai iya komai akan Mujeedat..

Gaba ɗaya sun kunna masu wuta babu wani sassauci so su ke kawai su raba su.

A Lokacin da Hateem Ya sare da rokonsu akan su janye maganar raba su, Cikin fushi da 6acin rai ya miƙe cike da rashin kuzari Ya juya da niyar yabar falon harya fara tafiya, Unexpected Ya tsinkayi Muryar mutum a kunnanshi Yana kiran shi da sunan daddy minister...

A sukwane ya dakata da yin tafiyar, Ya kasa motsawa, cikin ruɗu ƙwaƙwalwarsa ke kokarin tariyo masa muryar wanene Yaji a cikin kunnansa? Wanene me irin muryarsa? Wa kuma ya ke kira..."?

Bai ƙarashe zancen zucin nashi ba Ya kuma tsinkayar muryarsa a karo na biyu yace"daddy minister, it's me Danish.. "

Gabansa ne Ya faɗi a ruɗe Ya juya ya fuskanci inda Yake jin muryarsa kaitsaye idanunsa suka sauka akan Danish dake a tsaye sanye cikin shigar larabawa, kasa yarda yayi da abun da idanunsa ke nuna masa, ganinsa ya ke kamar a mafarki, Ya soma murza idanunsa da yatsunsa don ya tabbatarwa kansa daidai yake gani.

Nazli da Yazin Tun fitowarsa suka hango shi, A rude suka miƙe tsaye kan kafafunsu suna bin shi da kallo mai cike da al'ajabi, ganin matashin saurayin da suka ta6a gani a farewall dinner din daddynsu, ba zasu taba mantawa da fuskarsa ba, musamman Nazli, cos a farko data fara ganinsa Taji kishi sosai saboda arayuwarta batason mutum me kama da ita, batason ace wani nada wani abu irin nata, saboda tsabar izzar ta, a lokacin abun daya ɗaure masu kai tayaya akai Yaron da yake a Nigeria ya zo dubai? kuma har cikin gidan family din su? Tayaya hakan zai yiwu? Wama ya kawo sa? Menene alakarshi da su?

Sheikha mujeedat ce kaɗai bata motsa daga inda take ba, saboda tasan komai game da zamansa a gidan su.

Gaba ɗaya babu wanda yasan da zaman shi a falon, amma tun farkon da suka fara tattaunawa ya fito daga dakinsa da niyar ya tafi fadar Emir yana shigowa falon idanunsa suka hango mashi Mommynsa da Prime minister wani iko na Allah kallo ɗaya da yayi masa nan take ya tuna da komai daya manta, hakan nufin memory dinsa daya rasa ya dawo, yayi farin cikin sake ganin Prime minister musamman dayasan cewa daddynsa ne, to anan yaji komai da suke tattaunawa hankalinsa Ya tashi da jin zasu raba mommynsa da daddynsa

Cikin rawar Murya Prime minister Ya furta"Danish! Kaine dagaske nake gani? Ko dai idanuna ne suka nuna min badai dai ba"?

bai ƙare maganar ba, Danish Ya nufe shi da sauri yana isa gabanshi ya rungume shi sosai cikin farin ciki da murnar ganinsa.

Babbar magana! Kallo ya koma sama, sai da Kowa dake a falon ya miƙe a sukwane cikin rudu su ke kallon su.

Cikin shesshekar murya ya furta daddy ni ne, Danish, nayi kewarka, naji dadin sake ganinka arayuwa ta... "

 ji yayi kamar ana wanke damuwar dake a cikin zuciyarsa wani sanyi ne ya ratsa zuciyarsa, Ya ƙara ƙanƙamesa a kirjin shi kamar zasu koma mutun ɗaya sun dauki lokacin kafin Omair ya raba jikin sa daga na daddynsa ya juya ya nufi Emir da mamaki Ya hana sa furta kalma.

zubewa yayi kan gwiwowinsa Ya dafe ƙafafunsa cikin sanyin murya ya shiga rokonsa akan karsu raba mommynsa da daddyn sa, su kaɗai ne fatan da ya ke da shi a duniyar nan! Su taimaka ma rayuwar shi, baisan komai ba baisan kowa ba, baisan Yana da iyaye ko dangi ba arayuwarsa saida Allah ya bayyana masa komai.. "

Sannu a hankali ya fayyace musu irin rayuwar da yayi a kurkukun kaddara cikin harshen turanci, waɗanda basa ji a cikin su Yazrin ce ke fassara musu da larabci saboda sun nuna,suna son suji me Ya ke cewa.

Labarin Danish Ya ta6a zuciyarsu, jikinsu yayi sanyi laƙwas, idanun su suka cuccuka da ƙwalla, tausayinsa ya kama su, sun razana da jin zalunci da kakansa ya yi masa sun kuma sha ruwan mamakin jin cewa jinjirin Mujeedat ne da ta haifa a mace shekaru ashirin da suka gabata.


kafin ya ƙarasa musu labarin tuni hawaye sun wanke fuskar sa.

Bayan ya ƙare ya cigaba da cewa"su duba halin da yake a ciki, baisan ko yana da tsawaicin kwana ba, amma su taimaka masa su barshi Ya samu kulawar iyayensa, su kaɗaine zasu iya bashi abun daya rasa arayuwar sa! Yana son su! Yana son ya rayu da su har karshen rayuwarsa"!

Cikin karyayyar Murya Khal Ya dubi Mujeedat Ya tambaye ta dagaske ne komai da Yaron ya faɗa? Kuma tayaya akai suka gano ɗan su ne"?

Idanunta cike tab da kwalla ta jinjina kanta, cikin raunanniyar murya ta fara basu labarin Danish tun farkon lokacin da Prime minister ya haukace akan son shi da ranar da suka fara ganin shi a farewall dinner din hateem, har zuwa Dna test da ta yi, ta kuma fayyace musu komai da suka tattauna da Owais har ta yi masa hanyar zuwa dubai, anan prime minister yaji komai da suka 6oye masa, bazan iya misalta farin cikin dayaji ba na kasantuwar Danish ɗansa, bakinsa Yaƙi rufuwa dama tun a kallon farko daya fara ganin fuskarsa yaji a jikinsa jininsa ne shi, Ya ilahi, baisan sa'adda Ya durƙushe ƙasa yayi sujudusshukur agaban kowan nan su bai iya ɗagowa ba saima ya kamayin kukan farin ciki.


Gaba ɗaya Al'ummar falon suka furta Allahu Akhbar!! Allahu Akhbar!!!

Cike da nadama Emir Ya ruƙo damtsen hannayen Omair ya miƙar da shi tsaye a hankali ya soma share masa hawayen sa da yatsunsa kafin ya rungumesa a kirjin shi..

Cikin karyayyar murya yace ya yafe masa, yayi danasanin furucin da yayi na raba mommynsa da daddynsa, hakika labarinsa ya karya zuciyarsa, ya tausaya ma rayuwar sa, amma ya yi haƙuri da jarabawowin daya fuskanta arayuwarsa, In sha Allah yayi bankwana da bakin ciki, zasu bashi goyan baya gurin taimaka masa na ganin ya samu abun da bai samu ba arayuwarsa, bayan haka ya soke maganar raba tsakanin Iyayen sa, kuma Ya gargaɗi kowa daya janye maganar baya son a ƙara tadata.

Tun da sukaji maganar Emir Kowa Ya zubar da makaman Yaƙin sa dama tuni jikinsu yayi sanyi, Farin Ciki agurin sheikha Mujedat da Hateem baya misaltuwa, Tun ayanzu sun fara alfahari da ɗan nasu saboda kyautar Allah ne shi agare shi, gashi tunkan aje ko'ina ya fara kawo masu maslaha.

Tsabar Farin Ciki Yasa Yazrin Ta nufe shi jikinta na 6ari cike da dokinsa Ta rungume shi ta fashe da kuka tana fada masa Yar uwarsa ce ita, iyayensu ɗaya,  yayarsa ce ita, daga ita sai shi, tana son shi tana ƙaunarshi kamar ranta, tayi farin cikin kasantuwarsa dan uwan su, tana taya su murna, tun ranar da tagansa ta fara ji aranta jinin su ne shi..

Bawan Allah ruɗewa ya yi da Yazrin ta rungumesa sai yaji wani dadi mara misaltuwa ganin yar uwarsa, a hankali ya sanya hannu biyu ya tallabe ta..

A lokacin Nazli tasha jinin jikin ta, son shi da ƙaunarsa sun mamayi izzarta, girman kai na nema Ya cusa kishinshi amma zuciyarta taƙi aminta da hakan saima azalzalarta data dingayi akan ta je gurin shi ta rungume shi.

Batasan ma sa'adda ta nufe shi ba, ta baya ta rungume shi sosai taji wani daɗi ya lullu6e zuciyar ta, kwata kwata Danish bai san ta ba, lokacin data rungume shi batayi magana ba, saida sheikha mujeedat ta janyo hannunta ta dawo da ita ta gaban shi ta gabatar mashi da ita a matsayin first born dinsu Nazli kuma yayar sa, Ya razana da ganin kamannin su yadda kasan an tsaga kara, hugging dinta yayi tighly su ka ji ɗumin junansu, batasan sa'adda ta saki kukan farin ciki ba, tadinga lallashin shi tana shafa sumar kanshi tana kara kankame shi a jikinta kamar wani yace zai ƙwace mata shi, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi. (🥺)

Dangin Mujeedat sun Tayasu murnar Ganin ɗan su Omair, sun kuma sasanta tsakaninsu da surukin su Hateem.

Tun aranar Mai martaba Ya sanya date din da zai yi ma jikansa Omair Party saboda farin cikin ganin shi, da kuma tayashi murnar haduwa da iyayen sa.

A daren ranar, gaba daya Iyalin Hateem A bangarem mujeedat suka kwana tare da Omair dinsu, raba dare su ka yi suna faranta masa har dinner suka yi a tare da shi, A ƙarshe ma da zasu kwanta yin bacci a tsakiyarsu suka sanya shi kamar wani yace zai sace masu shi.

Lokacin da ranar Partyn ta zo, Khal din Mujeedat ne Ya ba Omair Kyautar tsadaddun kayansu na larabawa da takalma na alfarma, su ya sanya aranar, abi dinsa da umminsa ne suka tayashi sanya kayan a jikin shi, yayi kyan da ba zai misaltu ba, A katafaren Hotel din da babu tamkarsa a fadin dubai aka shirya shi wato Burj Al-Arab cikin katafaren grand ballroom din da ke a cikin hotel ɗin.

Celebrity guests ne suka halarta, mashahuran business leaders na kasar dubai da arabic scholars, uwa uba gaba daya Rulers na UAE Sun hallara, tun daga kan President of the UAE, ruler of abu dhabi, da Ruler of sharjah, da sauran su, ƙwansu da kwarkwatarsu, Emir ne ya gayyace su saboda suzo tayashi murnar bayyanar Jikansa kuma sun amsa gayyatarsa.

Bugu da ƙari a ranar manyan Baki suka zo daga Canada, advisors din Hateem, Chief of staffs, Deputy prime minister tare da Senior cabinet ministers, tun daga canada sukazo a cikin private jet, badan komai ba sai don su yi bikon shugaban ƙasar su daya yi murabus, kwata kwata Hateem baisan da zuwansu ba, saboda basu tuntu6e shi ba, hasalima layukanshi a kashe su ke.

ta yadda akai har sukasan yana a dubai ta hanyar Canadian Polices din da ke a tare da shi.

Zuwan bazata su ka yi mashi, Unexpected ya gansu a Ballroom din da ake gudanar da partyn yayi mamaki cikin girmamawa da karramawa Ya tarbe su da hannu bibbiyu saboda an yi zama na amana, sunyi farin ciki da ganin shi saboda sunyi kewar shi.

Dakin Taron Ya cika makil da al'ummar Annabi, abunka ga taro na hamshakan masu kudi kowa ka kalla kayan alfarma ne a jikin shi, hada manyan mawaƙan larabawa da aka gayyata sai raye-raye da kide-kide su ke yi masu ƙayatarwa, ga Arabian dinner buffet domin baki su cika cikunansu.

Hateem da Mujeedat tare da Mahaifinta harma da kawunta da Her highness sune masu yiwa baki maraba da zuwa..

Saida Kowa Ya hallara, Baka jin komai sai sautin kide kide da raye raye, da firarrakinsu cikin harshen larabci da turanci.

Lokacin da Yazrin da Nazli suka shigo tare da Omair cikin ɗakin taron, sun sanya shi tsakiyarsu, yayin da suka ruke hannayen shi, karkuso kuga Yadda idanu su ka dawo kan su, wadanda basu taba ganinsa ba, tsantsar al'ajabi da rudune Ya cika zukatan su, suka dinga tambayar wanene shi? Dan wanene wannan yaron mai bala'en kama da Prime minister? A lokacin rudewa yayi ganin yadda mutane ke kallon shi, musamman matasan yan matan da ke a gurin ya tafi da imanin su, Jikinsa Ya hauyin kerma yayi saurin la6ewa bayan Nazli, ba karamin nishadi Ya basu ba, ta dinga kwantar masa da hankali tana cewa karyaji komai ya saki jikin shi, kallon da sukeyi mashi na mamakin waye shi su ke amma da zarar sunji wanene shi zasu daina.

Cikin harshen Larabci Gimbiya Mujeedat ta gabatar musu da Omair baby Boy dinta data haifa a mace ya dawo araye, da yake sunsan komai daya faru da dangin hateem nan take suka fahimci Yaron Yana daya daga cikin waɗanda baban Hateem Ya sadaukar, aikuwa sunyi farin ciki da ganinsa, suka soma tayasu murnar ganin Yaronsu tare da yi mashi fatan Alkhairi, Kowa son shi ya ke yi, ɗokinsa su ke yi, Wani irin farin jini yayi a dakin taron kowa zancen shi ya ke yi, manyan baki suka dinga hugging dinsa suna manna masa kiss on his cheeks irin gaisuwarsu ta larabawa, da masu ruke hannunsa suna yin musabaha da shi.

duk yasha jinin jikin shi saboda bai saba mu'amala da mutane ba, idan suka tayashi murnar haɗuwa da iyayen shi, dakyar ya ke iya buɗe baki yayi masu godiya.

Advisors din Hateem sai nan nan suke da shi, har sun naɗa mashi nickname Young president acewar su nan gaba shi ne zai gaji uban shi.

Amma Yayi farin cikin da bazai misaltu ba, musamman lokacin da mutane suka kewayeshi suna   raira mashi waƙa, Daddynsa Ya ruƙo hannunsa su ka yi rawa atare harma da mommynsa, mutane sunata ɗaukarsu videos da hotuna wasu ma live suke dauka.

Haka lokacin da zasu ci abinci Yaji dadi sosai, musamman lokacin da mommynsa ta bashi dabino abaki yaci, sisters dinsa suka ciyar da shi abinci yaci ya koshi, bayan ya gama cin abincin, daddynsa ya shayar da shi ruwan zam zam, a bainar Jama'ar dake dakin taron, idanun kowa akan su gwanin burgewa, wasu ji suke dama ɗansu ne Omair.

Gab da za'a tashi daga taron Celebrities suka fara gasar bashi tsadaddun kyaututtuka na fitar shari'a, Mutun na farko daya fara bashi kyauta kakansa Emir ne Ya damƙa masa kyautar Private jet wanda darajarsa takai $50 million tare da dawakai biyar, President Of UAE Ya bashi kyautar katafaren private villa in Dubai's Burj Khalifa, ruler of sharjah ya mallaka mashi Private yacht.

Chief Of Staffs na canada Ya ce shima baza a bar shi abaya ba, ɗan Hateem kamar dansa ne saboda haka Ya bashi kyautar Luxury penthouse in Ottawa wanda darajarsa takai dala miliyan biyu, tare da gold-plated, luxury cars, Khal din mujeedat shima Ya bashi kyautar Luxury villa a cikin dubai, Elder brother din ta Sheikh Hameed Ya mallaka masa kyautar danƙara-danƙaran SUVs, tare da Rolex watch wadda darajarta ta kai dala ɗari.

kunsan harka ta mashahuran masu arziƙi akwai son gwaninta basa ƙaramar harka, kowa burinsa Ya bashi kyautar da tafi ta kowa, sun maida abun gasa a tsakaninsu, daga wannan ya faɗi kyautar shi sai a samu wani gwanin ya ninka wadda tafi ta shi, kamar basu san zafin neman dukiyar ba, kuma ahaka babu abunda ya ragu na daga arzikinsu, wani ji yake kamar bai cire sisi a cikin dukiyarsa ba, saboda tsabagen arzikinsa.

hmmm Dare Ɗaya Allah kanyi bature, gashi Allah yayi baturen Danish ko ince Omair 😍 nima ya Allah gani da ɗan ƙoƙwan barata 😂 ni ma Allah ka maida ni danshinsa 😄 Ina ma ace ni suke gasar ba kyaututtukan nan, wallahi da tsiya taji kunya😄 just for fun

 Lokacin da suke gasar bashi kyaututtukan kowa Yana faɗin tashi kyautar, Gimbiya mujeedat da prime minister Sun yi farin ciki mara adadi, Omair baisan meke faruwa ba, sai da Yazrin ta dinga yi masa bayanin kyaututtukan da suke bashi in bai gane sunan abu ba, a cikin waya ta ke nuna masa hotunan su, bawan Allah Ruɗewa yayi saboda Ya razana da jin abubuwan da suka mallaka mashi, shi da ba kowan kowa ba arana daya sun maida shi billionaire.

Baisan sa'adda Hawaye suka Wanke fuskarsa ba saboda tsabar farin ciki, Yama kasa bude baki yayi musu godiya saboda farin ciki, hawayen shi da suka gani ya sa suka fahimci farin cikine Ya kashe mashi baki hakan ba ƙaramin faranta ransu ya yi ba dama sunyi ne saboda su faranta ransa kuma sun samu abun da suke so.

Agaban Kowa dake adakin taron prime minister da sheikha suka tambayesa ya faɗa musu me ya ke son su bashi a matsayin kyautarsu na iyayensa? Suna son suji komenene Karyaji shakku Ya faɗa musu in sha Allah zasuyi ma shi.

A lokacin bakomaine Ya faɗo masa aranshi ba face kalaman Unaisah, da su Ya ke kwana da su Ya ke tashi aran shi.

Cikin sanyin murya yace kyautar da ya ke so daga gare su itace su taimaka mashi, su bashi kwarin gwiwa da goyan baya don ya samu ilmi, kawai su wayar masa da kansa yanason Yasan komai Yana son ya goge ya koyi abubuwan da bai iya ba.... "

 ya karashe maganar da hawaye akan kuncinsa, gaba daya iyayen sa da sisters nasa saida suka zubar masa da ƙwalla, Tausayin shi ya kama su.

Anan take su ka yi mashi alkawarin za su yi iya kokarin su gurin cika mashi burin shi, kuma zasu canza mashi rayuwa su mantar da shi duk wata wahala daya ta6a sha abaya.

Ranar Omair ya ga tarin masoyan sa, mutane suka dinga daukar hotuna da shi, wasu ma video su ke yi, a karshe taro Ya tashi lafiya, kowa ya tafi da farin cikin ganin Omair.

Bayan kammaluwar Partyn, daga bisani Hateem ya tafi Da mutanansa Private resident dinsa na dubai, A Falo suka zauna cikin muryar lallashi suka fara zayyana masa dalilin daya kawosu Dubai, su ka ƙara da cewa Ya taimaka ya dawo kan mulkinsa, canada tana bukatar shi, su basu gaji da shi ba, suna son shi, suna son mulkin sa, ya janye maganar murabus dinsa, kar ya damu su ba zasu ta6a alaƙanta shi da laifin babansa ba, sun yarda da shi, sun san bashi da sa hannu, mutane suna ta ƙorafi akan murabus dinsa Ya taimaka kar ya karya zuciyar waɗanda suka aminta da shi.

Kalaman su sun so suyi tasiri a cikin zuciyarshi sai dai bayajin zai iya komawa ga mulkinsa.

Yace yaji dadin nuna damuwa akan shi da su ka yi, shima Yana son su Yana jin inama zai iya cigaba da ruƙe canada sai dai kash zuciyarsa ta yi raunin da ba zai iya ba, ayanzu yafison Ya koma kasarsa cikin Yan uwansa don ya ci gaba da rayuwa da su

Kamar zasu sanya mashi kuka, ba irin magiyar da basuyi mashi ba amma ya kafe akan bakansa, a karshe sukace zasu tafi masaukinsu amma ba zasu bar dubai ba, har sai sun yi nasarar shawo kan shi tukunna.

Bayan sunyi sallama da shi, Ya koma Ruler's resident Ya kira Mujeedat awaya, bayan ta same shi a part din ta, Suka zauna cike da damuwa ya fayyace mata komai da suka tattauna da bakinsa na canada.

Ta numfasa tace ita kanta bazata goyi bayan murabus dinsa ba, tuntuni taso tayi masa magana bata samu damar yi ba amma bataji dadin murabus din da yayi ba a live video din daya saki, meyasa zai sare saboda laifin da bashi ya aikata ba? mutanan canada suna son shi, kada Ya karya musu zuciya, tun da har su basu nemi Ya sauka daga kan mulkinsa ba why shi zai aje"?

Yace mata ta fahimce shi, ba zai iya ba, yayi rauni, mulkin ya fita aransa, dama siyasa ba ra'ayinsa bace, baban su ne Ya cusa masu ita, Yanzu kuma yaji ta fita aranshi, bayason komai daya shafi siyasa yafison Ya rayu tare da yan uwansa a Nigeria, tun da babu abun daya nema ya rasa, kuma abun da yafi damunshi lokacin da zai ba  Omair, Idan har ya koma kan mulkinsa tayaya Omair zai samu kulawar sa? Yana son ko da yaushe ya kasance a tare da shi.

Kalaman sa sun karya mata zuciya, ta fahimce shi sosai, ta kuma fahimci dalilin dayasa mulkin ya ƙara fita ran shi, amma tace yayi hakuri ya koma inyaso nan gaba kaɗan Sai Ya aje mulkin amma yanzu idan yayi murabus babu gaira ba dalili ga abun daya faru da mahaifinsa mutane zasu zargi wani abu.

Dakyar ta samu ta shawo kan shi har ya ce zaiyi shawara da Yan uwansa yaji ta bakin su.

Wata ɗaya su ka yi A Dubai ƙarƙashin kulawar dangin Mujeedat, daga bisani bayan daya gama yin shawara da yan uwansa gaba daya suka goyi bayan ya janye murabus din da ya yi har suka faɗa masa game da abun daya faru bayan zuwan dangin iyayensu mata, yayi farin ciki mara misaltuwa, ya kuma ƙara jin karfin gwiwa a tare da shi, su ka ce koda zaiyi murabus din kada yayi saurin yanke hukunci Ya bari sai nan gaba zuwa lokacin da ƙura ta lafa idan yaji baida ra'ayin ya cigaba sai ya yi murabus ɗin, suma sun nuna basu son mukamansu amma danginsu iyayensu mata  sun nuna rashin goyan bayan su su yi hakan sun kuma ƙarfafa masu gwiwar su cigaba.

haka kuwa akayi bayan ya gama yanke shawara da su, batare da 6ata lokaci ba su ka koma babban birnin Canada

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post