Ottawa, Ontario, Canada
A ranar da suka isa, Bayan da jirginsu yayi landing A airport, Yan jarida da Yan kasa suka cika makil domin tarbo sa sai farin ciki sukeyi da murnar dawowar Hateem da dansa Omair, dakyar Secuty details nasa suka yi masu ƙawanya har suka shiga cikin motocin escorts din da su ka zo ɗaukar su.
A washe garin ranar da suka koma Canada, har party governor general Yasa aka shiryama Hateem da Iyalinsa saboda murnar dawowarsa da kuma tayasa murnar ganin ɗansa Omair.
manyan ƙusoshin gwamnati da shahararrun ƴan jarida ne suka hallara domin tayasu murna.
Danish dai Yasha ruwan mamakin Ganin yadda Al'umma suke Girmama iyayen sa, shi kanshi dayake baƙo a family din nasa girmamasa su ke yi..
Anan ma Ya samu wasu ƙarin kyaututtukan na ban mamaki har baisan ma inda zai sanya kanshi ba saboda ruɗewar da ya yi duk da azahirin gaskiya Omair bai damu da abun duniya ba, hasalima ba kowani kyale kyale ke burgesa ba, amma idan aka basa kyauta yana jin dadi sosai saboda akwai wadanda ya ke da burin ya bama kyaututtukan.
Cikin ƙanƙanin lokaci rayuwar Omair ta sauya, musamman saboda ya samu gogewa ta bangaren ilmin addinin musulunci dana boko yasa Prime minister Ya ɗauki hayar private teachers din da zasu dinga zuwa har gida suna ilmantar da shi, bayan teachers din da Hateem Yasa suna koya masa karatu saida Gimbiya mujeedat ta dauki hayar therapist da Mentor saboda shi kawai, Albashi mai tsoka suke biyan su burinsu Omair Ya cika burinsa na samun ilmi, ya kuma manta da trauma din da ke damun shi.
Bayan haka sisters dinsa duk idan suka samu free time suna ilimantar da shi ta hanyar bashi lokacin su, su fita yawon shaƙatawa da shi, haka mom dinsa da daddynsa basu gajiya da 6ata lokaci gurin faranta masa rai, gata yayi masa yawa, jin dadi ta ko'ina, Ya rasa gane waya fi son shi tsakanin iyayensa da sisters dinsa? Kowa burinsa ya faranta masa rai, basu san 6acin ranshi, Ko jinjiri bai kaishi samun kulawa ba, ko sautin tarinsa ya sauya sai sun kira doc dinsa ya duba lafiyar sa.
Baida lokacin komai saina karatu, su kansu suna mamakin yadda yaba karatu muhimmanci fiye da komai in ka cire ibadarsa.
Baya gajiya da yin karatu, idan kana nemansa, Ka duba cikin bedroom dinsa a saman kujerar study table dinsa, idan baka same shi anan ba, to ka duba a home library, In nan ma baka gan shi ba ka duba garden, ko Classroom dinsa Inda teachers dinsa ke koya masa karatu.
Bawan Allah, kullum Yana a rungume da books yana karatu, sometimes da su ya ke kwana rungume a kirjin sa, yasa naci da dagiya, Ya sadaukar da ƙwaƙwalwarsa ga karatu, ko bacci ya ke yi ya dinga sambatun karatun da akayi masa.
Abun dayafi basu al'ajabi game
da shi kaifin basirar da ke gashi da saurin hadda ce karatu, he was gifted and a genus, masu wuyar samu a duniya, su kansu malamansa Yabon shi su ke yi suna al'ajabin irin hazaƙar sa.
Malamansa har fita sukeyi da shi Yawon buɗe ido badan komaiba sai don su wayar mashi da kan shi ya kuma ƙara ilmi.
Iyayensa sun ɗaura burin duniya akan shi, son shi su ke yi da zuciya ɗaya, Komai nasa mai tsada ne, suturarsa, takalmansa, turarensa, abincin sa, basu wasa da komai na shi, musamman su ka ware masa bodyguards masu kula da shi.
Cikin shekara ɗaya kacal su ka yi nasarar goge masa trauma din Suka wanke masa ƙwaƙwalwar sa da jin dadin rayuwa, Ya sauya gaba ɗaya, Ya zama wayayye mai tsantsar ilmi, ya goge ta fannin rubutu da karatu, haddar al'qur'ani dayafi bada himma akanta, Har yayi izuf talatin a cikin shekara ɗaya da watanni, tsabar wayewarsa ko magana yayi sai yaja hankalin mutun saboda komai nasa cikin qasaita da aji yakeyin sa, hatta salon tafiyarsa ta sauya, idan yayi dressing Ya fito outing gaba daya idanun mutane ke dawowa kansa.
Yan matan dake hauka kan soyayyar shi basu ƙirguwa.
shafukansa na social media miliyoyin mutanene ke following dinsa.
A cikin shekara ta biyu ne da iyayensa suka tabbatar Ya samu wayewa da gogewa ta fannin ilmi sanan suka fara tunanin sanya shi school, dama abun daya hana su sanya shi tun farko abu biyu ne! Saboda basu san ya fara zuwa makaranta a matsayin jahili wanda baisan komai ba, saboda gudun kada students su dinga tsokanarsa, dama ga baƙin tabon da kakansa Yabar masa dole asamu wadanda zasuyi bullying din shi akan abun da kakansa ya yi, shiyasa sukaji shakkar su sanya shi amma yanzu sun samu ƙwarin gwiwar kaisa school da zumar zasu baza guards dinsa har cikin Class din da zai zauna saboda tsaro.
malaman sa na gida ma sun goyi bayan su kaishi school saboda zaifi samun ilmin zamantakewa da mutane idan yana mu'amala da su, dama dole sai kana tare da mutane ka ke iya koyan zama da su.
Ko da suka tambaye shi me ya ke da burin ya zama nan gaba? yace baida burin daya wuce ya zama jami'in Isod saboda yana son aikin da zai taimaki rayukan Al'umma da kuma kawar da mugun iri a cikin su.
Sun yi farin ciki da jin hakan sosai, duk da za6in nasa bai kwanta aran su ba, saboda basu san yayi aikin da zai iya jefa rayuwarsa a haɗari amma saboda jin kyakkyawar manufarsa yasa basu nuna ƙin amincewar su ba, bayan haka suna son abun daya ke so, dan kuma saboda Owais.
Bayan Prime minister ya kira Owais awaya ya faɗa masa abun da suka tattauna da Omair, Owais yayi farin ciki sosai da jin burin da ya ke da shi na zama jami'in isod, dama ya dade yana yi masa sha'awar ya zama Jami'in Isod, tun lokacin daya ga irin ƙarfin da Allah yayi masa Yasan cewa zai iya! Nan ta ke ya shawarci prime minister da su sanya shi jami'a ya karanci cybersecurity, prime minister yace ya gode da shawarar da ya ba shi.
Batare da 6ata Lokaci ba suka aiwatar da hakan.
a wani zuwa da Owais yayi nan Canada, har bugun cikin shi yayi kamar yadda ya sabayi duk inyazo don yaji idan Yana tunawa da su Unaisah saboda iyayensa sun faɗa masa baya maganar kowa nasa, suna tunanin yayi loosing wani bangare na memory dinsa.
yace masa ba zai iya tuna su wanene su ba, baisan su ba, lamarinsa ba ƙaramin ɗaurewa Owais kai ya ke yi ba, zai iya tunawa da wani bangare na rayuwarsa a kurkukun ƙaddara amma kwata kwata bai iya tunawa da yan uwansa fursinoni ba, bai matsa masa akan ya tuna ba.
daga bisani suka tattauna fira kamar yadda suka saba duk idan yazo, kuma yana jin dadin Sauyin rayuwar daya samu ya zama cikakken mutum mai hankali da nutsuwa.
Gaba ɗaya komai dake faruwa yan uwansa ex-prisoners basu san Yana araye ba, an 6oye masu komai game da shi, saboda abu uku, na farko saboda rayuwarsa tana a cikin haɗari yasa suka 6oye kasantuwarsa araye! Bayan da shari'ar Elders ta ƙare babu sauran tashin hankali, still basu baiyana ba, saboda yayi loosing memory dinsa, ko da sun fada mashi game da yan uwansa ba lallai ya kula su ba, za su ji ba dadi, kuma zuciyar su zata karaya, ace ga garkuwansu amma bazai iya tuna ko su wanene su ba.
duk da unforgettable life din da sukayi a prison, duk da irin farin jinin da yayi a media basu taba cin karo dashi ba dan da yawansu ba ma'abota social media bane, tun bayan shari'ar su baba obie, amfani da social media ya gagare su, saboda wasu jahilan mutane da ke yi masu comment na cin zarafi ahlin su, a kan laifin da basu suka aikata ba yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa wasu suka daina hawa kwata kwata, kuma sunayin life dinsu a wuri guda ne daga gida sai school sai kuwa in za suje shopping ko yawon buɗe idanu shima din tare da rakiyar bodyguards din su, saboda su ba su kariya.
Abu na biyu dayasa basu san su matsa masa akan ya tuna da yan uwansa saboda idan memory dinsa ya dawo a tunanin Owais zai iya katse karatunsa ya tafo Nigeria saboda su, Wanda shi a yadda ya shirya sai ya gama zama cikakken mutum ya samu ilimin rayuwa yadda ya kamata sannan ya gabatar da Danish ga yan uwansa, waɗannan ƙwararan dalilan ne yasa bai faɗa ma su ba, ya bari har zuwa lokacin da ya tuna su da kan shi, kuma hada ƙarin yaga yan uwansa a lokacin sun jure rashin shi azaton su ya mutu shiyasa suka fidda rai da shi, suna ta yin rayuwarsu cikin jin daɗi.
daga cikin waɗanda suka san yana araye bayan yan uwan daddynsa sai kuma Taj da Salsabeel da big guy, da kuma Sheikh imam malik, Owais ne ya faɗa masu tuntuni, a ranar da sukaji yana araye sunyi farin ciki mara misaltuwa.
Yan uwan daddynsa suna zuwa kawo mashi ziyara nan Canada, musamman Chief Owais baya gajiya da zuwa Canada saboda yaga beloved cousin dinsa, ko ba su a tare Yafi kowa kiran sa video Call, Taj kuma yana samun labarinsa a wurin owais kuma bai taba nunama Angel Danish yana a raye ba, ya barshi a matsayin sirri kamar yadda suka tsara.
Abun da basu sani ba, Omair Yana sane ya ke yin pretending kamar yayi loosing memory din sa, idan Chief Ya tambayesa game da yan uwansa, ba dan Komai ba sai don bayason su san Yana araye, saboda Alwashi ne Ya ɗaukarwa kansa bazai ta6a komawa gurin Unaisah ba har sai Ya samu ilmi da wayewa ba dan Ya dauki fansar kalaman da tayi masa ba duk da Yaji zafin su kamar ta goranta masa ne amma shi a wurinshi ta taimaka masane gurin farfado masa da tunaninsa, ta sanya mashi buri a rayuwar sa, kuma komai da yayi yayi ne saboda ita, saboda yana son su rayu cikin jin dadin rayuwa batare da jahilcinsa ko evils dinsa sun cutar da ita ba, yana son tayi alfahari da shi aranar daya koma mata a matsayin mai ilmi da wayewa me kuma cikakken Asali dan babban gida, kuma Alhamdulillah Allah Ya cika masa burinsa duk da Yasha baƙar wahala na rashin Unaisah a tare da shi, ba ƙaramin azabtuwa ya ke yi da sonta ba, idan jarabar sonta ta motsa mashi kulle kanshi ya ke yi a daki ya dinga zuba karatun al'kur'ani, sometimes Shower Ya ke sakarwa kansa ko Ya sha sedative har sai ya samu sassauci tukunna ya ke lafawa.
har rokon Allah ya ke yi daya rage mashi sonta saboda ya samu Ya ci ka burin shi, baya son duk wani abu da zai kawo masa cikas a karatun sa.
A cikin shekara ta huɗu ne, wata rana Sheikha Mujeedat ta shiga bedroom dinsa don tayi masa sannu da dawowa daga school, ta iske ya shiga bathroom, taji bazata Iya fita batare data sanya shi a idanunta ba.
Ta nufi Study desk dinsa inda Laptop dinsa da kayan karatun sa suke, Anan taci karo da Diary dinsa daya manta bai kulle shi ba, hakanan taji tana son ta buɗe taga menene a ciki.
Tun a shafin farko ta fara cin karo da Destinyshield da ya rubuta tare da zanan Love.
Aranta ta ayyana Omair ya fara soyayya ne? Da fara'a akan fuskarta ta buɗe shafi na gaba ta soma karantawa, nan take ta fahimci bai yi loosing memory dinsa ba, tun da gayanan Ya rubuta gaba ɗaya labarin soyayyar sa da Destiny ɗinsa, labarin rayuwarsu a prison yayi mata dadi sosai taji dadin karanta shi, sai dai akwai kalaman da tagani wadanda suka ɗan ta6a mata zuciya har ta fahimci cewa ya ta6a samun sa6ani da destiny ɗinsa, a cikin zuciyarta ta shiga maimaita maganganun daya rubuta.
"Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai kuɗi mai asali ɗan babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?
"Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"
"Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaƙi? Ko arne mara addini? Ko kuwa jahili da baisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"!
Nan take ta fahimci destiny din nan itace silar da yayi pretending yayi loosing memory din yan uwansa, kuma kalamantane suka zaburar da shi harya sa dagiya da naci don ya samu ilmi, lallai ba ƙaramin so ya ke yi mata ba.
Wani shafin ta buɗo ta shiga karantawa kamar haka..
_"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_
Ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta a sa'ilin da ta kare karantawa.
Rufe diary din tayi, cikin sanɗa ta fuce daga dakin, bayan ta koma part dinta ta fara safa da marwa tana tunanin tayaya zata san wacece destiny dinsa"?
saboda tana son taci ka mashi burin shi na ganin ya mallake ta, saboda yarinyar ta kwanta mata aranta tun da ta karanta irin kyautatawar da tayi masa ta fahimci tana son ɗanta kamar ranta.
Layin Owais ta kira after yayi picking ta tambayesa wacece destiny? Taga sunan a diary din Omair harma da Takaitaccen tarihin alaƙar su.
Owais yasha ruwan mamakin yadda Danish ya ke masa pretending ya manta da yan uwansa ashe yana sane da su, kuma a labarin da mujeedat ta fada masa ta karanta a diary dinsa, yasa shima ya fahimci saboda kalaman Unaisah ya nisanta kan shi da su amma yana da burin ya dawo gare su wata rana.
nan ta ke Ya labarta mata komai daya sani game da alaƙar Danish da Unaisah harma da halin da ta shiga bayan da taji ya rasu.
Ta tausaya mata sosai, Tace tana son hotunan Yarinyar Ya tura mata a whatsapp, sannan tana son Ya taimaka mata su nema masa auranta, saboda batason Ya rasa ta, zata iyayin komai don ta cika mashi burin shi.
A lokacin da tayi maganar Owais baiji komai ba, saboda ya riga daya hakura da soyayyar Unaisah dama alkawarine Ya daukarwa kansa in har Danish yana araye shi kuma ya haramtawa kansa auran Unaisah, saboda yafi shi cancanta ya aureta, kuma bazai iya raba soyayyar su ba, tun lokacin daya gano akwai soyayya mai karfi a tsakanin su tun a Prison irin soyayyar da zasu iya rasa rayukansu akan Juna, ba zai ta6a mantawa da ranar da ya riske shi a cikin toilet yana bubbuga kanshi jikin sink saboda sun samu sabani da Unaisah, tun anan Jikin shi yayi sanyi.
Nan ta ke ya goyi bayanta, Yace shima zai bada gudummuwa ta hanyar yi masu jagora gurin nema mashi auran ta, taji daɗi sosai ta dinga masa godiya.
Bayan da suka gama yin wayar, ya tura mata hotunan Unaisah ta whatsapp hada videos dinta nan take ta gane fuskarta cikin yaran da yazo da su aranar farewall dinner na hateem, dama ta daɗe da siye zuciyarta, tayi farin ciki da kasantuwarta yarinyar da Omair dinta ya ke so.
Kwata kwata bata nuna ma Omair tasan sirrin soyayyarsa ba, saboda batason Yaga kamar tayi masa leƙen asiri, tafi son ta bashi mamaki.
daga baya Owais ya kira shi awaya, bayan sun gaisa cikin mutunta juna, yace mashi yadaina boye mashi, ya riga da yasan baiyi loosing memory nasa ba, kuma har yanzu yana son Unaisah!.
A lokacin ya za6i daya bayyana masa gaskiya tun da ya riga daya gano sa, bayan daya faɗa masa dalilan dayasa bayason ya koma gare su.
Owais ya fahimce shi, yace tun da yanzu ya cika burin shi, Yana da asali, Yana da dukiya, yana da ilmi da wayewa me zai hana Ya fara soyayya da Unaisah"?
cikin sauri yace bayason Tasan Yana araye yanzu har sai ranar da ya ƙarasa haddace alqur'ani mai girma da kuma degree dinsa tukunna.
Owais yace duk da haka zai taimaka masa yayi soyayya da ita batare da ta Iya gane shine ba.
daƙyar ya samu ya shawo kanshi har ya amince.......