Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 96 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 96 Complete

Takun Ƙarshe

Unaisah batasan komai ba, babu wanda Ya fada mata, wata rana Owais Ya kirata awaya bayan da suka gaisa Ya fada mata ya canza sim din da zasu dinga yin waya saboda su kawai.

Bayan daya tura mata new number dinsa tayi saving, ashe tsawon lokacin da ta ke yin chatting da Chief Owais a whatsapp ba shi bane Danish ne ya ke kiranta video call yayi hidding front camera don karta gan shi, sometimes tasha taji muryarsa tanayi mata kama data Danish amma saboda sanin baya araye yasa bata gaskata hakan ba saita barshi amatsayi gizau da muryar take mata a lokuta da dama.

Sometimes Raba dare sukeyi suna yin video call, taita fama da shi akan Ya daina boye kansa tana son ta dinga ganinshi amma sai yaƙiya.

Saida takaiga Wallpaper din wayarsa Hotonta ne, Haka gallery dinsa hotunan Unaisah ne da videos dinta da ya ke sanyawa ta tura masa.

baya gajiya da kallon ta, a ranar data fara tura masa hotonta Ya razana da ganin kyawun da tayi, kamar ba Unaisa ba, mamaki ne ya kamashi sosai ganin Abin da ya ke tsokanar ta akan bata dashi yanzu sun girma irin yadda ya ke so, wata irin kewarta ya ke ji da kuma San kasancewa tare da ita, baya gajiya da kallon pictures dinta ko dan ɗebe ma kanshi kewa.

Gimbiya Mujeedat ce ta fada ma abie dinsa da Sisters dinsa game da soyayyar Omair,  ta kuma nuna masu hoton Unaisah, Prime minister yayi murna sosai saboda shima Ya shaida soyayyarsu musamman daya tuna ranar da suka kamata a ɗakinsa ta la6e cikin labule.

Nazli data ga hoton Unaisah nan take ta tuna ta wato yarinyar da faryat ta kulle a cikin restroom saboda ita.

 tayi mamakin jin hakan, azaton ta soyayya ta ke yi da Owais sai kuma taji labarin soyayyarta da Kaninta, batare da sanin Kowa ba, Ta kira Owais awaya ta tambayesa tayaya akai yarinyar da ya ke so ta koma soyayya da kanin ta? Ko dama ba son ta ya ke yi ba"?

Yace mata ya ta6a sonta abaya amma ya hakura da ita tun lokacin daya gano alakar dake a tsakaninta da Omair, amma ba hakan na nufin ita kaɗai zai aura ba, a yanzu haka Ya samu wadda zata maye masa gurbin Unaisah daya rasa.

Daya faɗa mata hakan taji kishi har tayi danasanin kiran shi cikin 6acin rai tace meyasa bazai aureta ita kaɗai ba? me Allah ya rage ta da shi? ya fada mata ko tana da makusa ne"?

Cikin lallashi yace tayi haƙuri daga zuciyar shi ne, bazai iya hana kanshi son wata ƴa mace ba, amma ta sani har abada itace mace ta farko daya fara yi ma son da bai ta6a yi ma wata ƴa mace ba, kuma har a wannan lokacin babu abun daya sauya na daga son da ya ke yi mata, shiyasa ma zai fara auranta, ita kuma Yarinyar da ya ke so ya aura Allah ne ya jarabce shi da sonta bayan daya rasa yar uwarta Unaisah.

kalamansa sun tausasa zuciyarta, cikin sanyin murya ta tambayesa wacece yarinyar? tana so ta san ta.

A takaice Ya bata labarin Batool, nan take Taji tausayinta ya kamata, har taji zata iya amincewa Ya aure ta, duk izzar Nazli tana da zuciyar imani.

Nan take tace mashi ta amince saboda ta yarda da shi, ta yarda da son da ya ke yi mata kuma tasan shi din adaline zai kula da su.

ya yi farin ciki da jin hakan daga gare ta cikin ruwan sanyi ba tare da yasha wahala ba.

Bayan auran Owais da Nazli, a lokacin da suka dawo daga honey moon, da zai dawo Nigeria Prime minister Hateem ya biyo shi donsu zo nema ma Omair auran Unaisah, bayan da suka zo nigeria, Chief Owais Ya fada ma Iyayensa game da fasa auran Unaisah da yayi da kuma wanda ya bama ita, sun dan nuna rashin jin dadinsu saboda sunsan irin kaunar da yakeyi mata tun da daɗewa tunkan Yasan wacece ita, amma daya fada masu dalilansa da kuma alakar dake atsakanin Unaisah da Danish sai sukaji dadi aransu, suka kuma goyi bayan bar mashi ita din tun da har yaji zai iya jurewa kuma su ba zasu hana shi yin aikin alheri ba kuma kamar yayi ma zumunci ne.

Ranar da suka shirya zuwa Neman auran Unaisah, kafin zuwan su saida Chief ya saisaici lokacin da Benazir da Unaisah basa agidan, Unaisah ta tafi School, Benazir ta tafi gurin aikin ta, sannan ya kira Taj ya faɗa masa game da batun zuwan magabatansa, yayi farin ciki sosai yace Allah ya kawo su lafiya.

Kafin su ƙaraso gidan, Taj ya kira Danejo ya fada mata game da zuwan magabatan Owais, yace ta shirya masu abun da zasu ci, cike da farin ciki ta amsa mashi da toh, ya kuma kira dr shureim da Uncle abdallah, Hada Alhaji Ubaid duk ya sanar da su za'a zo neman auran Yar su Unaisah, kafin su ƙaraso gaba ɗayansu su ka hallara agidan.

Hateem da ƴan uwansa ne su ka zo neman auranta tare da Owais da Omar, a main falo suka zazzauna kan sofas, gaba dayan su, sunyi masu kyakkyawar tarba cikin girmamawa suka gaggaysa da su.

Danejo ta kawo masu abincin da ta girka masu tare da soft drinks, bayan ta gaishesu daga bisani ta fuce ta basu wuri, kafin suka fara tattauna batun daya kawo su.

daga bisani bayan sun gama gaisawa, Owais ya soma magana cikin nutsuwa yace ma Taj ya yi hakuri da abinda zai ji daga gare shi, yasan burinshi ne Ya kyautata masa shiyasa ya bashi auran Unaisah, amma Allah bai kaddara shine zai zama mijin Unaisah ba, shima Yaso Ya auri Unaisah amma bazai Iya raba soyayyar Unaisah da Danish ba, In yayi hakan baiyi masu adalci ba, sannan Idan harya ba Omair auran Unaisah to kamar ya bashi ne, zai yi farin ciki fiye da shi ne zai aureta, still zai zama surukin su, don haka yana rokon alfarma agurinsa ya maida auran shi da Unaisah akan Omair, kar ya ji komai, tun da shi yaba ita shi kuma ya hakura yabarwa dan uwansa kar yaji ba daɗi, da shi da Omair abu ɗaya ne.." 

zuciyar Taj ta karaya da jin maganar Owais, Hawaye suka cika idanun shi, kwata kwata baiji baƙin cikin abun da ya faɗa ba saboda shima yana son Omair yana kuma son abun da yar sa take so, duk da ba haka yaso ba, yaso Ya cika burinsa na ganin Owais Ya auri Unaisah saboda halaccin da yayi musu arayuwa, Yana son Owais Yana son ya auri Yarsa amma Allah bai nufa shine zai zama mijinta ba, dama can rubutacciyar kaddarace! Wadda babu wanda Ya isa Ya sauyata! In har mutun ba kaddararka bane bazai taba zama kaddararka ba, Owais shiya fara sanin Unaisah, Amma Allah bai kaddara Unaisah zata san da zamanshi ba har saida ta fada kurkukun ƙaddara ta haɗu da Omair, gaba daya dai rayuwarmu abisa mizanin ƙaddara take, kana naka Allah na nashi, duk abun da kaga baka samu ba dama can ba rabon ka bane 💔  Ubangiji Allah Ya zaba mana mafi alkhairi arayuwar mu.

Kowa da ke agurin saida ya lura da halin daya shiga, cikin sanyin murya yace tun da har shi da kan shi ya nemi alfarmar ya bar masa, shima ya amince ma auran su.

Sunyi murnar da bazata misaltu ba, suka dinga yi masa godiya yace su daina sunfi karfin komai agurin sa, sune sukayi masa halacci da har suka nuna suna son yarsa ta auri dan su.

daga bisani su ka ce basu san bikin ya ɗauki lokaci, Sati uku kacal Ya ishe su, Uncle Abdallah Yace su ɗan ƙara lokaci saboda suna son su shirya ma bikin.

Su ka ce karya damu, sun san me su ke jimawa, Su kawai Unaisah suke so Abasu, basu bukatar komai daga gare su, ko tsinke basu son akawo ta da shi gidan ɗan su.

Gaba ɗaya sunyi murna da jin hakan daga gare su.

Duk a zaman Chief Ya bayyana masu game da son da ya ke yi ma Batool, harya nemi da su nema masa auranta tun da ga Mahaifinta akusa, kowa dake a gurin yayi mamaki, Musamman Dr shureim tsantsar rudu da farin ciki ne ya cika zuciyar shi, sai yaji ma kamar kunnansa ne suke jiye masa ba dai dai ba, Alhaji Ubaid yace shikenan faɗuwa tazo daidai da zama, wannan ai yar gida ce, sai ayi tuwo na maina, gaba ɗaya suka sanya dariya.

Omar yace dama yana son Batool bai ta6a fada masu ba, yana murmushi yace ''itama batool din batasan yana son ta ba, amma shi yasan tana son shi, tsabar farin ciki yasa Dr shureim jin kwalla ta cika idanun shi, gani yake kamar Owais yafi karfin Batool, bayan yasan ta hanyar da suka same ta, amma ya za6i daya aure ta saboda Yana son ta, Allah abun godiya, kowa dake agurin saida ya fahimci farin cikin da ya ke a ciki,  bawan Allah, dama yana ta zullumin wanene zai auri Batool ya zauna da ita lafiya batare daya goranta mata ba? Kullum in yayi sallah sai yayi addu'a akan Allah ya bata miji na gari wanda zai so ta, batare daya goranta mata ba, sai gashi Allah ya kar6i addu'arsa a lokacin da bai zata ba.

Sa'ilin da hawayen da ya ke dannewa suka soma kokarin gangarowa daga cikin idanunsa, taj daya lura cikin sauri ya zaro hanky daga aljihu Ya mika masa ya kar6a tare da rufe idanunsa da shi, gaba ɗaya sun fahimci dalilin shigar shi halin da ya ke a ciki, haɗuwa su ka yi gurin lallashin shi don ya daina zubar da hawayen sa, Chief yafi kowa farin ciki da ganin yadda Dr. Shureim ya nuna jin dadin sa.

Bayan da suka shawo kan dr shurem, Prime minister yace"yana neman alfarma agurin su da su bar komai a sirrin ce, baya son Unaisah tasan Omair yana araye koshi zata aura, kuma baya san kowa ya sani har sai ranar ɗaurin auran saboda mommynsa tana son ta bata mamaki" basu musa ba suka amince masa..

Chief Owais yace"shima yana neman alfarmar kada abari Batool tasan zatayi aure har sai bayan ɗaurin auren nasu, saboda yana son ya bata mamaki"

Gaba ɗaya sun goyi bayan maganar sa saboda suma suna son su faranta masu.

Bayan komawar prime minister Canada, Ya labarta ma sheikha game da sanya auran Omair, taji dadi sosai, aranar da zasu faɗa masa bazata sukayi masa saida suka saisaici ranar daya gama degree dinsa na farko kuma duk aranar ya gama haddar alqur'ani mai girma.

 A gurin walimar safkar alqur'anin sa, suka bashi gift box daya buɗe akwatin Unexpected Ya tsinci Invitation card na auransa da Unaisah a ciki, tsabar farin ciki bakinsa kasa rufuwa ya yi.

yadinga yi masu godiya kamar zai yi musu kuka, farin cikin da suka gani akan fuskarsa ba ƙaramin biyansu yayi ba sunji daɗin faranta masa da su kayi.

Cikin shesshakar kuka yace ashe haka iyaye suke da daɗi? burin su su farantawa dansu rai da iyakar iyawarsu koda su zasu rasa jin daɗin su ne, ba abun da zai ce sai dai yayi godiya ga Allah da irin ni'imomin da yayi masa arayuwa, daga jahili zuwa mai ilmi daga mara asali zuwa mai cikakken asali, daga talaka zuwa hamshakin mai kudi, Allah Ya dawo masa da dukkan Hakkinsa da Elders suka tauye masa, a lokacin fa kwata kwata baya son tunawa da kurkukun kaddara, tun daya hadu da mommynsa Ya shafe babin su a memory din sa, a ranar da Yaji labarin farmaki na biyu da su Owais sukai da kuma nasarar da sukayi harma da shari'ar da akayi Ya ji komai abakin Owais ya kuma gani a labarai, Ya yi farin cikin kawo ƙarshen Gidan Kurkukun ƙaddara da Elders.

A ranar ɗaurin aurenshi, sukazo Nigeria a privet jet din daddyn sa, a gidan su na estate din suka sauka, Yana ta zumudin ganin yan uwansa da yayi kewa tsawon shekaru, musamman babban amininsa Haris na amana.

Bai tashi haɗuwa da su ba, sai a wurin ɗaurin aure, a masallacin imam malik, kwatsam ba zato ba tsammani sukaga Danish kamar a mafarki Ya zo, suka kasa tunkararshi saboda ruɗun da suka shiga, zullumin su kar ace bashi bane wanine mai bala'en kama da shi sai suka dinga satar kallon shi, Dayaga kamar suna kokwanto akansa Saiya nufe su da fara'a ya fada musu cewa shine Danish dinsu bai mutu ba, suka ki yarda har saida Ya labarta musu tukunna suka fashe da kukan farin ciki, Haris Ya rufe shi da fada akan don me ya nisanta kanshi dasu? Meyasa ya tafi yabarsu? Meyasa zai boye musu yana araye? Yasan kuwa halin da suka shiga lokacin da sukaji baya araye"?

Murmushi yadinga sakar musu yana lallashin su dakyar ya shawo kan su suka daina kuka. Kafin ya soma bin su daya bayan daya ya rungume su sunata santin shi badan anyi rayuwar wahala atare ba da ba abunda zai hana su ji shakkar sake mashi saboda da kallo daya suka fahimci Danish din yanzu yafi ƙarfin su, yana magana zaka fahimci ilmi ya shige shi ga hutu daya zauna a fatar sa, kamar yadda suke mamakin sauyawar da yayi shima haka yake mamakin sauyawarsu, yaji daɗin canjin da kowan nansu ya samu, har yanzu yana son yan uwansa, musamman da suka kara samun kusanci na yan uwantaka ta jini da wasu daga cikin su.

Abun da yafi faranta ran su jin cewa shi ne zai auri Unaisah, yaya Owais kuma zai auri Batool sunyi murna kamar kamar me amma yace masu bayason ta sani su yi shiru karsu fada mata har sai bayan an kaita gidan shi  sannan zai bayyana mata kan shi, suma sun goyi bayan ya ba ta mamaki saboda suna son farin cikin ta.

zan iya cewa Salsabeel yafi kowa murnar ganin Danish a lokacin da su ka haɗu a masallaci, yaji daɗin sauyin rayuwar daya samu, ya kuma ji dadin jin cewa shine zai auri Unaisah, burin sa ya cika, bakinsa ya ƙi rufuwa saboda farin ciki, daya rungume shi har saida ƙwalla ta cika idanun shi, shima Danish din duk sai yaji ba daɗi daya nisanta kan shi da su, sun yi kewar juna, hakuri ya dinga bashi yana lallashin shi har saida ya shawo kan shi.

 Sheikh imam already yasan shine zai Auri Unaisah tun a ranar da Taj ya kirasa ya sanar da shi komai, amma bai samu halartar gidan ba saboda baya agari, gaba daga a masallaci suka haɗu da shi kafin daurin auren.

Bayan kammala ɗaurin auren, al'ummar Annabi suka dinga taya angwaye murna tare da yi masu fatan Alkhairi.

Daga masallacin gaba daya suka wuce Reception, cikin farin ciki da ɗokinsa su ke ta bashi labarin abubuwan da suka faru bayan da babu shi, Yaji dadi sosai harya taya Sajeed murnar ganin yar uwarsa Sajeeda, daya tambayi haris Ya labarin deejan sa? Har yanzu suna son juna? Zai aureta? dariya yayi tare da girgiza kai yace hmmm ai zance Ya 6aci, aurensa da Deeja haramun, saboda uwar su ɗaya ubansu ɗaya".

Danish ya yi mamakin jin cewa shaƙiƙai ne, duk agurinsu Yaji labarin Unaizah yar gidan daddy da Unaisah yan uwane da kuma alakar su, haka sajeed ma ya'yan kawunta ne jan wuya, ga kuma Cousin dinsa, Yaji daɗin kasantuwarsu Ya'yan wa da ƙani,dayake duk bai bibiyi wadannan labaran ba yasan dai kowa an mikashi ga iyayensa, a yadda ya samu labari but baisan su waye iyayensu ba,sai Yan zu ya gane dalilin dayasa su ke bala'en son juna ashe soyayyar su ta jini ce.

Bayan da suka gama shagalin su Tare da Yan uwansa daga Reception suka tafi gidan daddynsa na estate din sunki rabuwa da juna, an dade ba'a haɗu ba, wuni yayi tare da su har saida lokacin daukar amarya yayi tukunna sukayi masa sallama kamar karsu rabu suka tafi dauko masa amaryarsa kamar yadda suka tsara.

Kamar Yadda Iyayen Unaisah sukayi mata nasiha akan zamantakewar aure shima haka Iyayen sa su ka yi masa, a ƙarshe suka sanya mashi albarka tare da fatan alkhairi arayuwar auran sa.

Daga baya ne Sheikha mujeedat ta shiga gidansu Owais donsu tarbi amarya idan danginta sun kawo ta, dama anan suka nemi alfarmar suna son su fara kawo ta, in yaso daga bisani sai ta kaita gidan angonta da kanta, sunyi hakanne saboda sunfi son Unaisah ta fara ganin sa a matsayin angon ta don su bata mamaki, kafin sauran su san yana araye kuma shi ta aura, haka Batool ma sun boye duk wani abu da zaisa tasan cewa anyi auranta da Owais.

Daddynta bai sanar da su ba, saboda Sun tsara sai daga baya zasu sanar da ita.

Shiyasa suka ɗage date din Dinnern Auran su zuwa bayan biki da sati.

Gaba ɗaya komai daya faru a cikin shekarun da suka gabata ne zuwa yanzu

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post