Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 97 Complete

Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe Page 97 Complete

Takun Ƙarshe

Gaba ɗaya babu annuri akan fuskarsa, tamkar bai ta6a yin dariya ba, ba haka ya zata daga gare ta ba, ta 6ata masa rai ta kuma karya masa zuciya, kwata kwata baiga alamun tayi farin ciki da dawowarshi araye ba, batayi murnar sauyawar shi ba! Bayan saboda ita yayi komai? Anya Unaisah tana son shi har yanzu? Tana kuwa son cigaban shi"?

Sam ya kasa furta kalma, ta kashe mashi baki, sai yaji dama bai dawo ba gaba ɗaya!.

Jinjina kan shi ya ɗanyi cikin fushi yace "Tell me, how can I make you understand? What's wrong with you? kin sauya min! that's not what I expected from you, You weren't happy about my return at all, ba ki taya ni farin cikin samu asalina da kuma cigaban dana samu ba arayuwana ba"! 

 wani irin faɗuwar gaba da sarewar gwiwa taji a lokaci ɗaya!

"Ina kokwanton in har yanzu kina sona! may be kin samu wanda ya maye maki gurbinane! kamar bakison cigabana! bayan ke da kanki kika furta bani da komai da zakiyi alfahari da ni ban da kyan da Allah yayi mini, Unaisah you're the one who inspired me to achieve those goals! I followed your orders and did everything for you! Why can't you see"? 

Daƙyar ya ke yin maganar saboda bai saba yin surutu mai tsayi ba, wahala ya ke sha.

"kin sauya magana Unaisah! Bakisan cigabana Unaisa! If not, why aren't you happy for me as Omair? You know I can never go back to being the Danish you knew, I regret coming back to you, I won't force you to stay with me If you can't live with me as Omair, you can choose to break up with me"

yadda yayi maganar da tsawa yasa ta gigice, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya sara mata nan ta ke jiri ya kwasheta agalabaice ta yi taga taga zata faɗi batasan sa'adda ta durƙushe ƙasa ba, duk akan idanunsa ko gizau baiyi ba, balle tasa ran zai taimaka mata.

Bai aune ba yaji ta rungume kafafun sa da hannayenta, jikinta na kerma ta rasa me ke mata daɗi duniyar nan! cikin shaƙaƙƙar murya ta furta Ina son Danish ɗina ya dawo gare ni, ka koma Danish dan Allah! shi kawai nakeson gani, Danish dina ba haka ya ke min ba, baya fushi dani, baya son 6acin raina, yana fahimtana, baya min magana da tsawa, bamu iya rayu nesa da juna, amma kai ba kamar shi ka ke ba, tayaya zan ji ka a matsayin shi? Bayan ka sauya gaba ɗaya.."

zuciyarsa ta karaya da jin kalamanta, jikinshi yayi sanyi laƙwas kamar babu laka, baisan meyasa yayi mata haka ba? Meke damun shi ne, duk da itama da laifinta ta kasa fahimtarshi duk kokarin dayake Dan ta fahimce shi Abu yaci tura.

 Tsantsar tausayinta ne ya mamaye zuciyarshi har yaji kamar bai kyauta mata ba, bai san ya zaiyi da ita bane! Baisan me ta ke so ya yi mata wanda zaisa taji shi a matsayin Danish!

Tayaya zasu samu fahimtar juna a daren farko na ranar auran su? Bayan sa6ani ya shiga tsakanin su? Bayin Allah har alkawarin ciyar da juna su ka yi💔

kwatsam Yaga ta kife kan floor babu numfashi, Tashin hankali, gabansa Ya faɗi rass! arazane Ya zube kan gwiwowinsa Ya tallabo kanta da tafukan sa.

 kyawawan idanunsa a kan fuskarta data jike sharkaf da hawaye kamar ba A.c a dakin gumi duk ya wanke ta, cikin karyayyar murya ya furta

"Ya rouhi! My Angel! Habib albi! Wake up pls, Ni ban dawo don na 6ata maki rai ba, har yanzu ni danish ɗinki ne ban sauya ba, Ina sonki, bazan ta6a canza maki ba..."

 Cak ya tsaya da yin maganar sa'ilin daya fahimce suma tayi.

Cuccu6arta yayi saman kafaɗarshi ya miƙe da ita Ya nufi katafaren Gadon su.

A hankali Ya kwantar da ita,  ya juya jikinshi na bari ya nufi minibar din ɗakin Ya dauko bottle water, ya dawo daga gefen gadon ya zauna tare da buɗe robar ruwan ya tarfa a tafun sa ya soma yayyafa mata ruwan saman fuskarta.

Nan take taja dogon numfashi har saida kirjinta yayi sama tukunna a hankali ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sam takasa buɗe idanunta sai jan numfashi ta ke yi daƙyar daƙyar, ga dukkan alamu bata a hayyacin ta.

Damuwa ce tsantsa kan fuskarsa ganin yadda ya jefa ta a mawuyacin hali.

a hankali ya ɗaura yatsunsa saman wuyanta har saida gabanshi ya fadi jin yadda jikin ta yayi zafi rau da alamun zazza6i a tare da ita.

"Rouhi! Are you Okay? meke damunki? Ko baki da lafiya"?

 ya faɗa yana kallon fuskarta kwata kwata bata fahimtar komai.

Sumar data yarfo saman fuskarta Ya shiga kawar mata da ita da hannunsa don ya samu damar da zai ƙare mata kallo

tun a karo na farko daya fara yin tozali da ita face to face saida ya razana da sauyawarta, tama fiyi masa kyau azahiri akan hoton ta da ya ke kallo, ta zama dirarran mace mai kyawu abar tunkaho ga Wanda ya mallaketa.

"malak albi na! kina jina? faɗamin meke damunki? Ni ne na 6ata maki rai... " shiru babu alamun zata furta kalma, ko idanunta ta kasa buɗewa.

Ganin yadda take zubar da zufa yasa ya fahimci zafin jikinta ne ya jawo hakan.

Tunanin rage mata kayan jikin ta ya yi,

A hankali cikin nutsuwa ya ruƙo hannayenta ya nutsu Yana kallon zanen lallen da akayi mata akan glowing skin ɗinta, lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su akan kyawawan hannunta ji yake kamar ya haɗiye su tsabar kyan da sukai masa.

 awarwaron ta ya zamiye daga hands din ta, a hankali ya ɗaurasu kan mattress.

Baisan sa'adda ya tsinci kan shi da shafa lallausar fatar hannun ta yayin da ya ke tariyo rayuwarsu ta baya a prison.

 Sakin hannunta yayi ya ɗan matsa Ya ruƙo kafafunta ya daura su akan Laps dinsa cikin nutsuwa ya soma cire mata takalman dakyar ya zame su, bai ji daɗin ganin yadda suka raunata kafafunta ba, sun yi jawur kamar na jarirai a tsaftacen su, baisan sa'adda Ya sumbaci foots din ta ba, a ƙasa Ya ɗaura takalman, bayan ya cire leg chain ɗin ta, Ya matso daidai saitin kanta, gently ya tallabe shoulders dinta da hannun shi, Ya ɗago da ita tare da kwantar mata da kanta saman kafaɗarsa, shu'umin kamshin turarenta ne Ya daki hancin shi wani irin kamshi mai rikita shauƙin bawa.

Zare sarkar wuyanta yayi cikin nutsuwa Ya cillar da ita ta faɗa kan mattress, kafin ya cire mata earrings dinta Ya watsar da su.

Numfashi yaja Tare da furzar da shi saman fatar wuyanta, a hankali ya dinga goga tsinin hancin shi saman skin din ta.

Ƙara haɗe jikinsa ya yi da nata a matse sa'ilin daya fara jin wani irin yanayi daya haifar masa da jarababbiyar kasala a jikin shi.

Tun da ya cusa hancinsa a tsakankanin wuyanta da kafaɗarta ya nemi nutsuwarsa ya rasa, bugun zuciyarsa ya tsananta, bakomai ne ke fusgarsa ba face shu'umin ƙamshin jikin ta da laushin fatarta.

tsawon mintuna bai motsa ba ya yi shiru yana jin yadda jikin shi ke tsuma.

dakyar ya iya tattara sauran kuzarin daya rage masa a jikinsa, ya sanya hannu ya Cire mata head pies din da ke a kan sumarta 

baisan lokacin da ya soma shafa sumar Yana liliyata a hankali a hankali almost mins, Yana jin fitar numfashinta a jikin shi, ta narke masa a kirjinsa babu alamun tana a hayyacin ta.

ya daɗe yana kwaɗayin Unaisah kamar zai rasa ransa bai ta6a nuna mata ba bai kuma ta6a neman ta bashi haɗin kai suyi ba.

_saboda yasan bazaiyi mata da kyau ba, baya son ya cutar da ita, a lokacin da suke a prison ko harararsa tayi ko ta murguɗa masa baki nan ta ke ya ke jin tsananin sha'awarta, yaji kamar Ya afka mata, tun bai gane me ya ke ji agame da ita ba, amma ko time da take ganinsa a toilet da biyu ya ke shiga saboda ya samu sassaucin azabtuwar da ya ke ji agame da ita, amma yayi hakuri ya jure saboda bayason ya cutar da ita, kuma baya son ya yi batare da amincewarta ba,sonta da kaunarta da yakeyi da zuciya daya bazai bari ya iya aikata mata hakan ba._

Ya ja numfashi da karfi yana jin zafin jikin ta a fatar sa

Dakyar ya iya motsa fingers dinsa gently cike da lalaci ya soma warware straps din rigarta, before he slid the straps off her shoulders..

Cikin muryar raɗa mai cike da shauƙi Ya furta"malak albi na! Are you awake? Kina ji na? Can I remove your gown? It's tight and causing you pain" 

shiru bata furta kalma ba, kuma bata buɗe idanunta ba, ya rasa gane meyasa ta fita hayyacin ta, amma yana ji aransa kalamansa ne suka jefa ta a halin da ta ke a ciki, bazai iya bar mata rigarba saboda yadda tayi tighly dinta, ga zufar da ta ke fitarwa, yasan tsiwar Unaisah kan tsiraicinta amma dole ya cire mata kuma ko ba komai muharramarsa.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post