Lumshe idanun shi yayi a hankali ya sake buɗe su kan fuskarta, da wata irin kasalalliyar murya taji ya furta"ki cigaba da yi min abun da kikeyi min, inajin daɗi sosai" gabantane Ya faɗi tana zare ido tace"am sorry.. bansan meke damuna ba, na ruɗe.." bata kare maganarba ya katse ta da cewa"karki ji kunyar nuna min soyayya, ni mijin ki ne, muharraminki.." lumshe idanunta tayi taji dadin furucin da yayi, yanzu ta fahimci shima yana jin abun da ta ke ji a game da shi..
Da kanshi ya soma yin undressing ɗinta, bayan daya kammala Ya tu6e kayan jikin shi, Ya janyo duvet Ya lullu6e su a ciki, gaba daya ta nemi kunyarsa da ta ke ji ta rasa, gaba ɗaya suka tsunduma cikin faranta ran junan su, almost Hour basu rabu da juna ba.
A ranar Dinner din auran su anyi gagarumin Shagalin da ba'a ta6a yin makamancin shi a ƙasar ba, dangin Amare da dangin angwaye gaba daya suka hallara kwansu da kwarkwatarta su a cikin Event hall din domin tayasu murnar auransu, a dakin Taron Omair yayi abun daya ba kowa mamaki, gaba ɗaya Ya bi yan uwansa Ex-prisoners Ya basu kyautar key din mota, tare da Gift cards na Hajjin bana, sunyi murnar da bazata misaltu ba, surukan sa ya gwangwaje su da kyautar Motoci tare da Gift cards na hajj, Ummi da Aneelerh da dr shureim harma da Danejo duk saida Ya basu kyautar motoci tare da Albishir din Hajjin bana, saboda Yasan Alkhairin Da Aunty Aneelerh tayiwa Angel dinsa tun da tana ƙarama, itama Danejo tun a prison Yasan da ita, lokacin da Unaisah take basu labarin taimakon da tayi mata, ita kuma Ummi mahaifiyar aminiyarsa ta kuruciya ce wato Batool, bazai ta6a manta kyautatawar da tayi masa musamman a lokacin da ya ke fama da lalurarsa ta rashin son haniya.
aikuwa gaba ɗaya suka dinga yi mashi godiya tare da addu'o'in fatan Alkhairi shida amaryarsa, Sun yi Murnar da bazata misaltu ba, musamman yan uwansa prisoners sun yi mamakin arziƙin Omair din su, ba komai yafi masu dadi ba kamar kasantuwarshi a raye especially matan da sai a lokacin suka ganshi sunji dadi mara misaltuwa, lokacin da yake basu car keys din, fashe wa sukayi da kukan farin ciki saboda ba su zata ba, duk wanda ya ta6a taimakon Unaisah saida Omair Ya bashi kyautar Mota da hajj, kuma babu abun daya ragu na daga arzikin da Allah yayi ma shi, gaba daya kyauttukan daya basu cikin wadanda ya samu ne agurin Partyn da Emir Ya shirya mashi, bayan tarin kyaututtukan daya ba su, saida ya ƙara ma Taj da kyautar Private Villa anan cikin Abuja tare da Diamond cufflinks, na lu'u lu'un gaske, Gaba daya Ya kashe surukin nasa da farin Ciki, Taj har kusan Zubar da ƙwalla ya yi saboda dadin da yaji na yadda Danish Ya girmama shi fiye da kowa, Unaisah Taji dadin kyautatawar da yayi wa Family dinta, sai taji ta ƙara ƙaunarsa fiye da komai a duniyar nan.
Bayan dinner din auransu da sati ɗaya, su ka fara shirye shiryen tafiya Honeymoon, su biyar suka tafi, Omair da amaryarsa Unaisah, Chief da amaryarsa Batool tare da Uwar gidansa Nazli, tun da suka tafi sai da suka shafe Watanni uku suna zagaye kasashe, daga cikin kasashen da suke je yawon buɗe ido ya haɗa da Canada, Korea, China, UK, daga bisani suka ziyarci saudi arab, sunyi rayuwar farin ciki da jin daɗi, sun more lokacin su, abubuwa da dama sun faru wanda ba zasu ta6a mantawa ba.
kafin dawowar su Nigeria, wasu masoyan sun yi Aure, Arana ɗaya aka ɗaura auran, Sajeeda da zaid, dr Jazz da Faryat, Zeenatu da Mahboob, a inda sheikh imam Malik ya auri Hajiya sarah Kowa yayi mamakin yadda har suka fada tarkon son Juna, ikon Allah kenan Musa Ya saka masa da sharri yayin da shi kuma ya saka mashi da alkhairi, Ya aure matar sa, bayan haka Abie Ya auri Ummi mahaifiyar su Zahra, da amincewar Mamie, itace ma ta bashi shawarar ya aureta in dai yana son ta saboda su rufawa juna asiri, ba iya nan ba ma'auratan suka tsaya ba, shima sir mubarak ya auri Hajjaty, a inda Hajiya saratu ta amince da auran dan Uwanta kanin Sarauta dan sarkin Yarbawa wanda yasota tun da daɗewa tunma kafin ta auri Praven amma saboda batason shi a lokacin shiyasa bata amince masa ba amma bayan shari'ar Elders ya bayyana mata cewa har yanzu yana son ta, kuma ashirye yake daya aureta, in har ta bashi dama, da farko ta nuna kin amincewarta saboda aure ya fita aranta, tana da ciwon abin da praveen yayi mata, amma daga bisani da yayyanta suka shawarce ta akan ta aure shi tunda yana son, kuma bafa lallai ta samu wanda zai so ta tsakani da Allah ya rufa mata asiri kamar shi ba, dama tunfil azal shine za6in su, shi sukaso ta aura amma ta bijire masu a lokacin ta kawo nata za6in, A yanzu da suka nuna suna son ta auri dan uwan ta bata musa masu ba, ta daina kin bin umarnin su, bayan data amince akayi auren su, ta zama second wife dinsa.
duk a cikin shekarar Ahlin Elders Suka aurar da mafi rinjayen matasan family ɗin, Kuma auren zumunci su ke yi a tsakanin su, saboda su rufawa kansu asiri don kuma su ƙarfafa zumuncin su, Alhamdulillah Allah ya azurta wasu ma'auratan da samun ƙaruwa, ta bangaren Chief Owais Uwargidansa Nazli ta haifa masa kyawawan Twins mace da namiji masu bala'in kama da shi, kamar yayi kakin Su, ya yin da Batool ta ke ɗauke da cikin sa.
Zaki Ya samu ƙaruwa tare da Aneelerh ta Haifa masa kyakkyawar Jinjirarta mace, a inda Zahra Ta haifi kyawawan Twins maza, Zayn da Yan uwansa sunyi farin ciki sosai, Salsabeel da Matar shi Dr Yusrah suma sun ƙara samun ƙaruwar Ƴa mace, Cikin Ikon Allah Danejo da bata ta6a haihuwa ba tsawon shekaru abun na damunta, a lokacin baya har asibiti Taj ya ke kaita in ta matsa mashi akan tana son ta haihu, amma ko sunje likita ya bincika ta kamar kullum sakamakon ɗayane bata da matsalar Haihuwa, Taj yasha ya kwantar mata da hankali yace tayi hakuri suci gaba da yin addu'a in Allah ya nufa tana da rabon samun ya'ya, zata haihu ne in da rai da lafiya, a lokacin kwata kwata baya nuna damuwa akan rashin haihuwarta, saboda damuwar rashin ƴar shi Unaisah, Danejo tun tana damuwa har ta cire rai, sai da ga Bisani a ranar da Imam Ya kawo masu ziyara gidan, suna tsaka da yin fira a falon Danejo su biyu Shi da Taj, lokacin da Danejo ta shigo kawo mashi Abinci, Bayan ta gaishe da shi ta ajiye masu kayan abincin, cikin jin kunyar Imam ta nemi daya taya ta da addu'a tana fama da matsalar haihuwa, Kallon ɗaya sheikh Imam yayi mata ya fahimci tana da evil jins a jikin ta, wanda ita kanta bata sani ba, Taj ma bai ta6a sani ba saboda basu ta6a tashi a jikin ta, Bayan da yayi mata tambayoyi a amsoshin da ta bashi ya fahimci Aljanun sun daɗe a jikin ta, tun tana a rigarsu ta daji, kuma sune suka haddasa mata rashin haihuwa, nan take ya yi mata alƙawarin in sha Allah zai tayata da addu'a, sannan zai aiko mata da ruwan addu'a da magunguna, ya kuma rubuta mata addu'o'in da zata dinga yi, sannan ya gargaɗeta akan ta daina sakaci gurin neman tsarin Allah.
bayan da Sheikh imam malik Ya kawo mata magungunan ta fara amfani da su ta kuma dage da yin addu'o'in daya rubuta mata, Cikin Ikon Allah ta samu warakar lalurarta, salin alin Iskar suka fita daga jikin ta, sai gashi ta samu ciki, har kukan farin ciki sai da ta yi, tsawon wata tara cuff Ta haifi Twins ɗinta mata masu kyan gaske kamar indiyawa, kamannin su sak da ita kamar tayi kakin su, Taj ya yi farin cikin da bazai misaltu ba, haka Benazir da Unaisah sunfi kowa ɗokin ya'yan Danejo, Suna son su sosai.
qarin abin farin ciki! Benazir da ummi suma daga baya ba zato ba tsammani suka samu ƙaruwa kusan a lokaci daya Dan har sun fidda rai da qara haihuwa musamman Ummi saboda ita da kanta ta dinga shan kwayoyin da zasu hana ta daukar ciki tun lokacin da take karuwanci, sune suka jaza mata matsalar rashin haihuwa, amma daga bisani sai gashi cikin ikon Allah sun sake samun qaruwa, gaba dayansu ya'ya maza suka haifa, murna a wurin Unaisah da Batool kamar su zuba ruwa qasa susha suma sun samu ƙanne shaƙiƙai, Cikin yan shekaru albarkar ƴa'ƴa ta yaɗu a zuri'ar Elders sun ƙara yawa sun bunƙasa, ga arziki ta ko ina.
__________________________
EVIL FOREST🔥
Wata irin ni'imtacciyar iskace ke kaɗawa acikin dajin mai dadin gaske.
baka jin sautin komai saina kukan tsintsaye dana namun dawa dake hargowa daga can cikin dokar dajin.
mata da maza na hango sanye da shiga ta fararen kaya a jikin su, cikin Dajin Evil forest, Suna a zazzaune saman korayen ciyayi, sun kewaye ƙabari da ke agaban bishiya, yayin da suka ɗaga tafukan hannayen su Sama suna yiwa mamacin da ke a cikin ƙabarin addu'a, idanun su cike tab da ƙwalla.
daga bayansu, Isod Soldiers ne sanye cikin Combat Uniform dinsu, Hannayen su ruke da bindigu, sun kewaye masu yiwa mamacin addu'a domin basu kariya.
Bakowa bane wadannan bayin Allahn face ex-prisoners da kuka sani, gaba dayansune suka ziyarci kabarin tsohuwa tamira wadda duniya ta naɗa mata suna( Mother of the prisoners) Salsabeel ne Ya jagoran ce su zuwa kabarin nata, bazai taba mantawa da inda ya binne mahaifiyarsa ba, da taimakon shaidar da yayi ma kabarin ya ci sa'ar gano shi, bayan da suka kammala yi mata addu'o'in, suka yanke shawarar shiga cikin dajin don su yi yawon buɗe ido, babu tsoro ko fargaba atare da su, saboda akwai sojojin dake tsaron su, su kansu suna da bindigunsu na kansu da suka mallaka bayan sun zama jami'an Isod, cikin nishadi suke kutsawa cikin dajin suna tafiya sunayin fira yayin da su ke tuna rayuwar da su ka ta6a yi a cikin shi saida su ka yi nisa a tafiyar tasu suka lura babu Mutun biyu a cikin su, aruɗe suka ci burki hankulan su atashe suka soma ƙwala masu kira da karfi"Sister Unaisah! Big bro! Garkuwa! Kuna ina ne! ina ku ka shiga ne"? Yadda suke ƙwala masu kira kamar maƙoshinsu zai 6alle, raba kansu sukayi gida uku wasu suka miƙi hannun dama wasu sukayi hagu yayin da wasu suka miki hanya, Gaba ɗaya suka bazama neman su a cikin dajin..
Duk Kiran da suke ƙwala masu kwata kwata ba su ji ba, suna acan saman Wata gabjejiyar Bishiya mai girma da faɗi, tana da yalwar rassa da Ganyayyakin da su ka yi mata rumfa, ba zaka taba gane akwai mutane asamanta ba, saboda rassan bishiyar da ganyayyakinta sun lullu6e su hasken rana ne kadai ya ke hasko su, wata irin ni'imtacciyar iskace ke ratsa fatarsu mai dadin gaske.
yana a kishingiɗe saman wani ƙaton reshe na bishiyar mai faɗi, yayin da ta ke akwance saman jikin shi, ta ɗaura kanta a kirjin shi.
Gaba daya tafukan hannayensa suna a daddafe da matashin cikin ta, wanda baifi wata biyar ba, sunyi kyau a cikin fararen kayan su fiye da ko da yaushe ga dukkan alamu bacci ne ya yi awon gaba da su, sunyi nisan kiwon da basa jin kira a cikin kunnan su.
kwatsam wani giant snake Ya biyo jikin reshen da suke a kai, Ya durfafe su gadan gadan, Yana gab da zai hau kafar Unaisah, Omair ya farka daga bacci, nan take idanunsa suka gane mashi macijin, wani irin faduwar gaba Yaji, Yasan muddin Ya hau jikin Unaisah zata iya firgitar da zaisa ta fado daga kan reshen.
Yana tsaka da tunanin yadda zaiyi da macijin, Yaji ta ambaci sunan shi "My Man.." hankali atashe ya dubeta a lokacin da take kokarin buɗe idanunta, kaitsaye suka shiga cikin nashi, murmushi tasakar mashi, kwata kwata bata lura da halin da yake a ciki ba, abun dayake ma zullumi kartayi motsin da zaisa macijin Ya sareta, Hamma tayi kafin ta rufe bakin yayi saurin hade bakinta da nashi, gaba daya ya kashe mata jiki ta kasa motsawa, kissing dinta ya shiga yi yayin da yake zare pistol daga waist dinsa a hankali, idanunsa akan macijin Ya saita kanshi, Ya daddage Ya sakar mashi alburushi a tsakiyar kan shi, ji ka ke daramm!!! Tsabar firgitar da ƙarar harbin da kunnuwana suka jiyo min ne yasa na gigice har bansan sa'adda Na saki alƙalamin da nake rubutu da shi ba.
Alhamdulillah 🤩 🥳🥳subhanallah🤩, Masha'Allah🤩 La'ilaha Ilallah🤲, Allahu Akhbar 💖
THIS IS THE END OF KURKUKUN ƘADDARA 😭😭😭
All praise is due to Allah, the Most Merciful and Benevolent, for granting me the strength and perseverance to complete my novel, "THE PRISON OF DESTINY"
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai rahama mai jin kai, Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)
Ina Godiya ga Ubangijinmu Allah subhanahu wata'ala, da ya bani tsawaicin kwana da lafiya da karfin gwiwa da juriyar kammala rubuta littafina na biyu mai suna 'KURKUKUN ƘADDARA" wanda na shafe tsawon shekara ɗaya da watanni ina rubuta shi, da daɗi da ba daɗi amma Alhamdulillah yanzu komai ya wuce, na ƙara shaidawa cewa sannu bata hana zuwa, kuma komai mai wuce wa ne arayuwar mu indai mu ka yi hakuri, Tabbas Ina Alfahari da baiwar da Allah ya bani ta rubuta littafin kurkukun kaddara fiye da littafina na farko kuma fiye da sauran littattafan da zanyi agaba saboda ya fita daban babu tamkar shi ko dan darussan dake a cikin labarin wanda ni kaina dana rubuta shi, na ilmantu, na fadakantu, na kuma nishadantu, nayi kuka tamkar raina zai bar gangar jikina saboda yadda labarin ya ta6a zuciyata inajin shi kamar True life story, bani ba hatta makarantar littafin sun shaida hakan.
Ina fata littafin Kurkukun ƙaddara Ya zama Alkhairi a gare ni, Allah Yasa kowa ya amfana da littafin Kurkukun ƙaddara burina ne, 😍Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da yan'uwana da dukkan masoyana a duk inda suke a faɗin duniya🥰 kura kuren ciki Allah ubangiji ya yafe man🙏_
_*Gaisuwar ban girma da karramawa ga mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya, she is my first luv and my everything, kin gama min komai arayuwa, Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana, bazan iya misalta kyautatawar da kikayi min ba, Allah ne kaɗai zai iya biyanki, kin gama min komai, Allah yasa Aljanna ta zama makoma agare ki💘, 🤲✍️*_
_*Jinjina Ta Musamman Da Ban Girma Ga Uwar Masu Uba Hadda Marayu, HAJIYA KUBRAH, kada Ku manta gaba ɗaya Littafin Kurkukun Ƙaddara tun daga farko har ƙarshen shi sadaukarwa ne ga Mommy Kubra, Jarumar mace, mai daraja da ƙima, saboda Ita yasa na jajirce na tsara labarin ya yi daɗi yayi ma'ana saboda inaso ya zama abun tunawa da ni da alfahari a gare ta, kin gama min komai arayuwa Mommy, goyan bayanki, tallafawarki, shawarwarin ki, da ƙwarin gwiwar da kike bani sun kasance ƙarfin kuzari na, Ina alfahari dake a koda yaushe kuma bazan ta6a mantawa da halaccin da kika yi mana arayuwa ba, Allah ya Kara Daukaka Darajarki Fiye Da Tunanin Mai Tunani da ke da Ahlin ku, Allah Ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada, Allah ya shirya maki zuri'a, Allah yasa ku gama da duniya lafiya Allahumma Amin 🤲*_
YABON GWANAYE YA ZAMA DOLE🤩JINJINA TA MUSAMMAN DA BAN GIRMA A GAREKU YAYYE NA NA KAINA DA BABU KAMARKU, ABUN ALFAHARI NA 🥺🥳🤩
AUNTY ZEE DA MUNAH BATURE MY P.E.
haƙiƙa kunyi namijin ƙoƙari gurin gyaramin rubutuna tun daga farko har ƙarshe baku ta6a gajiyawa ba, kun nuna min kauna, kun bani goyan bayanku da karfafamin gwiwa aduk lokacin dana nuna na sare, kun bani shawarwari masu muhimmanci da suka amfane ni agurin rubuta littafina, Kun tsaya min tsayin daka don ganin rubutuna ya yi kyau, wallahi ni bazan iya biyanku kokarin da ku ka yi min ba, sai dai in cigaba da yi ma ku addu'a Ina son ku ina kaunar ku 🥺🤲
JINJINA DA BAN GIRMA 🤩🥳😍 ga masoyana na asali masu sayan book dina, Dumbin gaisuwa da fatan Alkhairi zuwa gareku a duk inda kuke a fadin duniya, members Na Paid grps ɗina
Kurkukun Ƙaddara paid
Takun Karshe Posting section
Prison Of Destiny
kurkukun Kaddara Facebook
Prisoners Posting section
bayin Allahn nan kunyi hakuri dani, kun jure bibiyana har zuwa karshen littafina, kun jure kar6ar uzururrukana, nasan kun wahaltu gurin bibiyar littafina musamman wadanda na fara da su tun farko, don haka ina mai ƙara baku hakuri ga duk wanda na 6ata ma rai yayi haƙuri ya dubi girman Allah da manzonsa ya ya fe mun, badan komai ba sai don mu rabu lafiya, ba lallai mu sa ke haɗuwa a wani littafin ba, tun da rayuwar mu a hannun Allah ta ke, bansan ko zan kai lokacin da zan ƙara rubuta wani littafin ba, ina sonku ina kaunarku, ina jin dadin Comments dinku, ina rokon Allah daya saka maku da mafificin Alkhairinsa, Allah Ya sada fuskokin mu gaba daya agidan Aljanna, Alfarmar Annabi Muhammad SAW🤲✍️
Special Thanks To My Teammates
Aunty Zee Lalu, the Writer Of Asanadin Makwabtaka
Oum Arwan, Writer Of Auren Katin ƙasa and Matar Taj
Hafsat Amjad writer of Captain Janan da sauran su
Karku bari abaku labari, ga wadanda basu karanta books dinsu ba, Ina baku shawarar ku hanzarta mallakar naku, saboda Labaraine da babu kamar su, kunsan Team dinmu akwai baiwar tsara labari, kuma salon mu na daban ne, we're new writers but da ƙwarewar mu muka fara rubutu, Readers sun shida hakan 🤩🔥✍️
_*DAGA ALƘALAMIN HAFSAT BATURE MUHAMMAD (BOSS BATURE) WRITER OF ABBAN SOJOJI AND KURKUKUN ƘADDARA🔥✍️*_
*SINCE 2023 TO MON, JAN 20, 2025*