Yana ta satar kallon ta, yaga ta soma sanya kayan baccin ta, lura da rubutun da ke a gaban rigar yasa takai idanunta akai, My Shield taga an rubuta da wani irin salon rubutu mai jan hankali.
murmushi ne ya su6uce mata, juyawar da zatayi keda wuya idanunta suka sauka cikin nashi, da yatsan shi ya nuna mata rubutun dake agaban rigarsa, waro idanu waje tayi yayin da ta ke karanta rubutun a fili ta furta My Destiny,
Gaba ɗayansu suna da tambayoyin da su ke so suyi ma junan su musamman ita, tana son taji komai da komai game da Omair don bata gamsu da labarin daya bata ba, tana bukatar kari.
Bayan ta ɗauko hijab ta zura a jikinta, Yace tabiyo bayanshi, suka fito daga dressing room suka shiga Prayer room, a tare su ka yi sallah, yayi masu addu'o'i suka shafa, basu wani jima ba saboda yunwar da suke ji ga bacci cike da idanun su, ya riga ta fita daga dakin bayan sun gama yin sallar.
Daga bisani ta miƙe tare da cire hijab din, ta maida ta cikin closet, Ta dan tsaya tare da ruke qugunta tana tariyo komai daya faruwa a tsakanin su, fatanta Allah Yasa ba mafarki takeyi ba, don har yanzu ta gaza yarda mafarkin da ta dade tanayi ne Ya zamana gaskiya, can kuma ta kama tunanin wani irin arziki Danish yayi? Komai na shi ya sauya ya koma na hamshakan masu kudi, duk da dama ta dade tana ji aranta Danish jinin arziƙi ne amma gaba daya yafi karfin hasashenta musamman data lura katafaren gidan nan da suke a ciki mallakinsa ne.
Abun dayafi daure mata kai yadda Allah ya juye al'amarin tun tana karama tana da burin ta auri attajirin mai kudi, amma lokacin da tafara ganin danish sai ta kamu da sonshi a yadda yake har taji zata rayu da shi har karshen rayuwar ta sai gashi Allah ya juye al'amarin shima ya zama Hamshakin Mai kudi kuma ya aureta.
DESTINYSHIELD
Fitowa tayi daga dressing room din, A hankali take tafiya tana yan waige waige kamar mara gaskiya, ganin babu shi a bedroom din yasa ta tunanin Ina ya shige ne? Ita fa bata son kona minti daya yayi nesa da ita gudun kada Ya zamana mafarki ne komai daya faru..
Ɗaga murya tayi da karfi ta furta My Man, kana Ina"?
Neman shi ta farayi saida tagama zagaye bedroom din babu shi, Ta fuce daga ɗakin tana tsaka da neman shi.
Unexpected Ta hango shi A dining room ta cikin glass Yana a zaune kan dining mat ya tattara hankalinsa akan wayarsa da ya ke pressing, Nannauyar zuciyar ta sauke, Ta nufi Dining room din, ta tsaya daga bakin kofar tana ƙare mashi kallo mai cike da shaukin shi, pyjamas din jikinshi sunyi mashi kyau sosai sun kara fito da hasken fatarshi fara sol.
Ya nutsu abunsa, bai lura da zuwanta ba, dadin kallonshi ta ke ji cike da ɗokinsa kamar ta haɗiye shi ta ke ji, Aranta ta ayyana wai yanzu nan mijinta ne Uban ya'yanta nan gaba? Wonders shall neva end, Allah ya za6e ta a cikin dubunnan mata ita ɗaya Ya mallaka mata shi! Ya Allah, kamshin Jikintane Ya ziyarci hancinsa, nan take ransa Ya bashi tana a tare da shi, a hankali Ya ɗago da sleepy eyes dinsa Ya dube ta da su, gaba ɗayansu akwai gajiya da bacci acikin idanun su ga yunwar da suke fama da ita wuni guda baci ba sha.
"Ke nake jira, Kizo muyi dinner nasan kina jin yunwa"
ya faɗa yana nuna mata kayan abincin dake shake akan mat din, nufo shi tayi kamar wadda aka zarewa Laka, daga bayan shi ta tsaya tana kallon dinner din, arabian dishes ne a cikin Silver platters and Coffer, aroma dinsu ne Ya fara dakar hancinta ta fara hadiyar yawu, tana leken abincin, Ganin bata da niyar zama ta tsaya bayan shi, yasa shi yi mata gyaran murya, dakyar ta motsa ta zagaya zata zauna daga karshen Dinner mat din, Tana satar kallonshi suka hada idanunsu cikin na Juna, girgiza mata kai yayi"kinyi min nisa, ba haka nakeso mu dinga cin abinci ba.. " dan zare ido tayi, tare da jinjina kai, ta dawo zata zauna tana facing nasa, still ya girgiza mata kai, Ta rasa gane me yake nufi, ganin ta toge yasa shi mika mata hannu"zonan"!
Yadda ya kirata kamar ƙaramar yarinya, ya zatayi tun da karkashinshi take, Wuka da nama suna a hannunsa, sai yadda ya ga dama..
Matsawa tayi daga gaban shi, harta yunkura zata zauna agefen shi, Ya janyo hannunta gaba ɗaya ta rubzo saman laps dinsa,daidaita zamansa yayi yadda zataji dadin zama, kuma yana kallon face dinta.
Wani shock taji kamar electric current Ya ta6ata.
Saboda kunyar shi yasa ta rufe idanunta.
Kallon fuskarta yayi kamar zaiyi murmushi, har cikin ranshi daɗi ya ke ji na kasantuwar su ma'aurata, yana mai mamakin kunyarsa da ta ke ji bai dauka angel dinshi zataji kunyarshi irin haka ba.
"Haka nakeso mu dinga zama idan zamuci abinci" can kasan makoshi ta furta"toh"
"Tayaya zamu iya ciyar da junan mu bayan kin rufe idanunki"?
dakyar ta ɗan bude su batare data dube shi ba.
A hankali ya dauko tea put me dauke da gahwa (Arabic coffee) Ya tsiyaya masu a cikin Silver cups, Ya ruko cup daya ya miƙa mata, hannunta na kerma ta kar6a ta kanga abaki, kamshin tea din ne Ya ratsa hancinta har batasan sa'adda ta kur6e shi duka ba, tana so ta dan ja aji kar yaga hadamarta amma takasa, sau uku yana ƙara mata coffee tana shanyewa, yayin da shi ko rabin cup dinsa baiyi ba, ta ƙosa su fara cin abinci yunwa ta ke ji kamar kamar me.
Silver platter ya buɗe mai ɗauke da Chicken machboos
(Abincin gulf ne, wanda aka yi da shinkafa da nama,)
tuni taji miyanta yatsinke, sam ta shafa'a ta tsoma hannu batare data sanya spoon ba, ta fara duma loma abaki tana ci, kasa ci yayi ya nutsu yana kallon ta gwanin ban sha'awa, tana tsaka da cizgar cinyar kaza ta ƙware, da sauri Ya dauko glass of zamzam Ya miƙa mata, arazane ta dube shi bakinta dama dama da maiko, ɗaga mata gira yayi da sauri ta sunkuyar da kanta kasa cike da jin kunyarshi, ta bude baki ya kwafa mata bakin cup din tasha ruwan mai sanyi da dadi.
"Kin tuna ranar da yunwa ta farkar damu tsakar dare agidan kurkukun ƙaddara, muna laluban kwandon abinci muka hada hannu atare muke ruke kwandon.."
batasan sa'adda ta fashe da dariya ba, Murmushi yayi idanunsa akan white teeth dinta, dimple dinta yafi komai tafiya da shi.
Ta shagala tana ta dariya har ta dan kwantar da kanta saman kirjin shi.
Dama da biyu ya tuna mata ranar, saboda yana son ta daina jin kunyar cin abinci agaban shi, yafi son ta saki jiki da shi suyi rayuwar farin ciki.
Tsagaitawa tayi da yin dariyar tana fadin"na Tuna ranar, idan bazan manta ba, dana hana ka har kayi zuciya ka ki ci ko"?
Ta faɗa tare da kallon shi kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, dage mata gira yai alamar eh, da sauri ta kawar da idanunta gefe ɗaya, cikin nishaɗi suka cigaba da cin abincin, tun tuna jin kunyar shi harya fara bata abaki itama ta soma bashi, saida sukaci suka ƙoshi, a lokacin dare ya ritsa sosai, Suna kammala Cin abincin ya dauko mata pain reliever ya bata tasha saboda ta kara jin sauƙin jikin ta.
Daga bisani ya sa6eta da hannayensa biyu Ya nufi Bedroom da ita, Asaman gado Ya shimfiɗar da ita kamar new born baby, tayi lamo tana bin shi da kallo,Addu'a yace suyi sannan, ya kashe hasken dakin, Ya Hau kan gadon daga bayanta, Ya Janyo duvet din Ya lullu6e masu rabin jikin su, kwata kwata bai matsa kusa da ita ba da akwai tazara a tsakanin su.
Ji tayi bazata iya jirewa ba gudun kada ta juya taga babu shi yasa tayi tunanin ta ɗan juya ta saci kallon shi, A hankali Ta dan juya ta dube shi, ya lumshe idanun shi kamar maiyin bacci.
Nutsuwa tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa yayin da take tuna komai daya faru a tsakanin su yau, kafin ta sauya a kalar tunanin nata zuwa kalmomin daya furta mata kafin tafiyarsu kai farmaki, taso ayau dinnan ta cika mashi burin shi amma tsoro ya hana ta, da dabara ta mirgina kamar irin cikin magagin bacci ta matsa kusa da shi, ta haɗe jikinta da nashi, da sauri ya tallabe bayanta da hannayen shi tare da cusa hancinshi tsakankanin wuyanta har wani sautin shakar kamshin ta yake fitarwa, a hankali itama ta cusa hannayenta a cikin sumar shi tana shafawa kamar tanayi mashi susa, tun sunayi cikin hankalinsu har bacci ya fara fisgar su cikin shauƙin juna, in a short time bacci mai nauyi yayi awon gaba da su, yadda suka ƙanƙame juna kamar zasu dawwama a haka.
Tun ƙarfe 2 da rabi na dare suka fara sharar bacci, Har wuraren ƙarfe goma na safe ba su farka ba, Tsawon Awanni takwas Cuff.
Lokacin daya farka daga bacci, Unaisah ko motsawa batayi ba, tayi nisan kiwo a cikin baccin ta kamar matatta, ta haura kafarta daya asaman waist dinsa.
Abu na farko daya farayin tozali da shi sa'ilin daya buɗe idanun shi itace kyakkyawar fuskarta, Akan ta ya sauke eyes dinshi, yadda take fitar da numfashi kamar wata jinjira cikin natsuwa da kwanciyar hankali,murmushi ne ya subuce mashi Dan kadan kafin a hankali yayi kasa da idonshi ajikinta,yadda take numfashi a hankali haka kirjinta ke hawa da sauka ba karamin jan hankalin shi su ka yi ba, bakomai ya ke tunawa ba face time din da babu albarkatu a kirjinta, kamar na namiji saboda shafewar su, bai ta6a tunanin wannan ranar zatazo ba, kamar zaiyi murmushi ya dan ta6e red lips dinta.
Fuskarta Yabi da kallo tana bacci kamar jinjira.
Ya gaza yarda Ya mallaki Unaisah, Yanzu tashi ce ita, matar shi, uwar ya'yanshi masu zuwa, ta zama a karkashin ikon shi, Nauyin komai nata na akan shi, Allah ne kadai Yasan farin cikin da ya ke ji.
a cikin zuciyarshi ya karanta addu'ar tashi daga bacci, A tsanake Yake sake bin eye lashes dinta da kallo, a hankali Ya Daura yatsunsa asaman sumar kanta Yana dan shafa mata ita kamar jinjira, kwata kwata bai lura da lokaci ba, saboda shagalar da yayi gurin kallonta.
Kamar ance Ya dubi agogo, arude Ya zare eyes dinsa ganin karfe goma na safe, Bacci Ya shagalar da su har asuba ta wuce ba su yi Ibada ba.
Tunani ya somayi tayaya zai tayar da ita daga bacci batare daya takura mata ba! Badan sallah ba da ba abun da zaisa ya farkar da ita.
Saitin kunnanta ya kai labbansa cikin muryar raɗa ya furta........