"ya rouhi, Tashi muje muyi sallah, mun makara"
shiru bata farka ba.
Sau uku yanayi mata raɗa kamar wanda zai tayar da jinjira.
Yasan ta da nauyin bacci wani lokaci,balle jiya data jigata.
Qira'ar Alqur'ani ya soma yi mata cikin nutsatstsiyar muryarsa, Unexpected cikin bacci ta tsinkayi ƙira'arsa mai dadin sauraro irin ta Larabawa.
Tana buɗe idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi, ta ƙura mashi idanu tana kallon yadda ya ke motsa labbansa yana qira'a tayi mamaki sosai, jin surar da yake Karanta mata da kai batare daya duba al'qur'ani ba, Saida ya kai aya tukunna ya dakata yana lumshe idanun shi yace"barka da safiya ya malak albi, kin tashi lafiya" lumshe idanunta tayi tana jin ta awata duniyar nishaɗi.
Saida ta fara karanta addu'ar tashi daga bacci duk yana kallon ta daga bisani tace
"My man In har zaka dinga tada ni daga bacci irin haka zanfi kowa more tashi daga bacci, zanji dadi idan ka zama mutun na farko da zan fara yin tozali da shi a duk lokacin dana farka daga bacci.
Murmushi yayi wanda bai wuci fatar labbansa ba.
"Mun makara bamuyi sallah ba"
da sauri ta dubi agogo, zare idanu tayi, tare da yin saurin miƙewa, Batai aune ba, Taji Ya cuccu6eta ya sauko da ita daga kan gadon, A saman kafadarshi Ya sa6e ta, Babu alamun Yana jin nauyinta, Ji ya ke kamar ya ɗauki jinjira, Toilet Ya shige da ita.
Bayan sunyi alwala, suka fito Coset room suka shige don su shirya kan su, jim kaɗan suka fito cikin shigar larabawa hannunsu ruke cikin na juna suka nufi prayer room wanda komai na cikinsa na yin ibada ne.
Asaman wata dankareriyar prayer mat, suka tsaya tana gaba Yana abayanta, Shi yaja su sallar, dakyar ta samu nutsuwar daina kallon bayan shi ta maida natsuwarta kan sallar da suke..
A tsanake suka yi sallar, Bayan da suka kammala, suka zauna ya mika hannu Ya janyo prayer beads Biyu Ya mika mata daya ta kar6i, ya ruƙe ɗaya a hannun sa, suka soma yin tasbihi, tsawon mintina, ganin yayi mata nisa yasa ta ja jiki ta dawo gefen shi don taji dadin kallon shi.
Tana jan Cazbaha tana satar kallon red lips dinsa, Dadi takeji Man dinta ya Musulunta Ya iya karatun al'qur'ani da komai ma,komai sabo yake zo mata a tare dashi tabbas wannan omair ne ba danish din da ba sauyin rayuwa ta ko ina,ransa ne ya bashi tana kallon shi, da zarar yayi kamar zai juyo sai tayi saurin sadda kanta kasa taci gaba da jan casbaha.
Murmushin gefen fuska ya saki, shi kanshi yasan dole Unaisah ta susuce akan shi.
Qur'ani ya buɗe masu akan wooden qur'anic stand.
Muraja'a suka yi atare idan ta karanta aya sai ya karanta ayar gaba, Sura Uku suka karanta kafin Ya rufe al'qur'anin.
A lokacin da bata zata ba, Taji Ya janyo hannayenta a cikin nashi ya shiga murza ziraran yatsunta yana kallon zanan kunshin ta.
ta ɗago da farare idanunta ta dube shi.
Yayin da ya saka idanunsa a cikin nata.
"Jiya bayan ɗaurin aurenmu, daddynki Ya kira ni gefe daya ya faɗa mun wasu maganganu da suka karya zuciyata... " gabanta ne ya fadi aruɗe take duban shi.
Numfasawa yadanyi before ya daura da cewa"ya yarda dani dari bisa dari, kuma yasan cewa babu namijin da zai iya sarrafaki bayan shi sai kuma Ni saboda ya shaida tsantsar son da kike min, Ya bani amanarki, rukon ki ya dawo gurina, da dukkan dawainiyarki, ya bani ke badan ya gaji dake ba, sai don yana son kema ki raya sunnar Manzon Allah SAW kamar Yarda kowani uba nagari yake fatan yayanshi sukasance sunyi koyi da wannan sunna, ya kuma rokeni akan na kula masa dake kamar yadda ya kula dake tun kina jinjira har ya labarta min zaman da kukayi ya kara da cewa yasan wani lokaci baki jin magana kina da saurin fushi amma inyi hakuri da ke, idan kikai min badaidai ba, kada in ƙwaurace maki, in zaunar dake inyi maki nasiha, zaki gyara, saboda ni kadaine kusa dake, ayanzu zanfisu sanin me kike a ciki, idan na juya maki baya zaki kuntata, kuma bai yarda son da muke wa juna ya rufe mana ido mu kasa ganin laifin junan mu ba, mu ji tsoron Allah mu tafiyar da rayuwar aurenmu bisa tafarkin addininmu, mu kuma yi koyi da rayuwar manzon Allah da matayensa, lokacin daya ke fada min maganganun nan abun dayafi karya min zuciyata, dayace yasan bazai hana ki fuskanci jarabawar rayuwar aure ba da kowace mace take fuskanta agidan ta, amma koda nan gaba naji kin fita araina kada in tsangwameki, In dawo mashi da ke bazai taba gajiya da yar sa ba kuma bazai ji haushi na ba, Unaisah yana magana hada kwalla ya zubar min wai ni... " ya faɗa tamkar zai fashe da kuka saboda abun ya ta6a zuciyar shi.
tunkan ya karashe labarta ma, Idanunta suka cuccuko tab da ƙwalla, a hankali zafafan hawaye suka soma gangarowa saman kuncin ta, ta ƙarajin kaunar daddynta da tausayin shi yana sonta fiye da komai na duniyar nan tun tana kankanuwarta take azabtar da shi daidai da rana daya bawan Allahn nan bai ta6a tsanarta ba, hasalima sai dai Yaja ta a jiki in ta yi badaidai ba..
Batasan sa'adda ta fashe mashi da kuka ba kamar jinjira, da sauri Ya janyota jikin shi Ya rungumeta a kirjinshi, Ya daura hannayensa bayanta Yana lallashin ta dakyar ya samu ta dakata tana shessheka.
"Ni ban fada maki don na sanya ki kuka ba, sai dan Inaso ki taimaka min Unaisah ki bani hadin kai, mu zauna lafiya da juna, inajin tsoron na gaza ruke amanarki yadda ya kamata, amma nasan son da nake maki bazai bari ni in cutar da ke ba ko da ni zan cutu, a shirye nake dana baki dukkan kulawata da soyayyata, da lokacina"!
Ya ɗan dakata da yin maganar kafin ya daura da cewa..
"jiya bayan daurin aurenmu naji dadin da bazan iya misalta shi ba, saboda farin cikin kin zama tawa, zaki rayu agidana a karkashin ikona da kulawata, gaba daya dawainiyarki ta dawo kaina, komai ni zanyi maki Unaisah, Ina da halin da zan tafiyar da rayuwarmu harma data ya'yan mu batare dana gaza ba.. " yayin da ta ke sauraron daɗaɗan kalamansa wani sanyi da daɗi ne ke ratsa zuciyarta..
"Nasan dole wata rana mu samu sa6ani a rayuwar auran mu, amma in har muka yarda da junanmu, muka zama masu hakuri da juriya, mu ka kuma ruƙe addu'a, batare da sonkai ko son zuciya ba, In sha Allah zamu zauna lafiya, Aure yana bukatar fahimtar juna da soyayya, uwa uba hakuri shine jigon zaman aure gaba daya ma, kuma ni nayi imanin akwai fahimta a tsakanin mu... "
ya faɗa yana duban fuskarta, kanta na akan kafadardarsa bata motsa ba, hawayen dake tsiyayowa ta cikin idanunta ya bi da kallon ji yayi bazai juri kallon su ba, tana kokarin buɗe idanunta Batai auneba taji ya sanya red tongue dinsa akan fuskarta a hankali ya shiga lashe hawayen ta.
A lokaci ɗaya ta dinga jin wutar kaunar shi na ruruwa a cikin zuciyarta, fiye dana kowani lokaci.
Ɗaura idanunsa yayi acikin nata suka ƙurawa juna ido kamar yau ne rana ta farko da suka fara ganin juna, tun fil azal Allah ya jarabce su da kaunar juna, yadda kasan tushen soyayyar su a jikin ransu take saboda yadda su ke mutuwar son kansu.
sunkuyar da kanta ƙasa tayi cikin sanyin murya ta soma magana yayi shiru yana sauraron ta.
"In sha Allah zanyi iya kokarina gurin taimaka maka na ganin ka sauke nauyin dake akanka, zan dage da tayamu addu'a Allah ya tayaka ruƙona My man, Nima ka tayani da addu'a Allah Ya bani ikon sauke hakkinka da ke akaina, Allah ya bani ikon yi maka biyayya sau da kafa... "
har cikin ranshi yaji dadin maganarta, a hankali yake amsawa da ameen yana kallon lips din ta still kanta na kallon kasa.
"Allah ya bamu hakuri da juriyar da zamu rayu cikin farin cike da jin dadi batare da mun samu sa6ani ba, kuma koda zamu samu sa6anin in dai mun kasance munayi wa juna addu'a in sha Allahu shaidan ko zuciya ba zasu rinjaye mu ba balle wani, sai dai mu mu rinjaye su,sai kaga cikin kankanin lokaci mun shirya kanmu..."
dakatawa ta danyi tana kallon Yatsunsu dake harɗe cikin na juna..
"My man, ji nake kamar nafi kowace mace a duniya, bazan iya godewa ni'imar da Allah yayi min ba, daya za6eni cikin matayen duniya ya mallaka min kai a matsayin mijina, kai din burin kowace ya mace ne, son kowa kin wadda ta rasa, namiji mai tsada da wuyar samu afadin duniya, Allah ya kar6i koken da nake masa Ya dawo min dakai, Tun da na mallake ka ji nake babu abun daya rage ban mallaka aduniya ba, Allah ya gama min komai atanan saura fatan cikawa da kyau da imani..."
baisan sa'a murmushi ya subuce masa ba Yabon Unaisah agaresa kamar an masa albishir da gidan Aljanna ne.
"Ina matuƙar alfahari da ke! Nima bazan iya godewa ni'imar da yayi minba Daya mallakamin mace mai tsada mai wuyar samu a duniyar nan ni daya ya zabeni ciki mazan duniya, Kinfiye min komai Unaisah, in babu ke babu ni, kece ni Unaisah, Inason ki, Ina son mu rayu har karshen nunfashinmu..
daɗaɗan kalamai suke ta gayawa junan su.
Daga bisani Suka ɗaga hannayen su sama suna yiwa kan su addu'oi cikin harshen larabci.
Atakaice Cikin kwanakin nan shaƙuwa mai karfi da zazzafar soyayyace a tsakanin ma'auratan nan, zan iya cewa ban ta6a ganin masoyan da suke masifar son juna da zuciya ɗaya irin su ba, tsantsar kulawa suke bawa junansu, tattalin juna sukeyi da tarairaya, sallah kadai ke fitar da shi daga gidansa kasantuwar bai fara zuwa Office ba,dayake a nan Nigeria ya zabi zaiyi aiki, hutunsa Yake sha agidansa tare da hurul aininsa, Basa gajiya da faranta ran junansu, kullum suna a manne da juna, Wanka atare suke yin shi, sanya sutura a tare, Cin abincin a tare, bacci a rungume da juna, su yi gym a tare, su yi karatun al'qur'ani a tare, ranar da zata fara yin girki a tare su ka yi shi, Musamman saboda ita Ya ko yi girki agurin mommynsa, shi ya ke zama Ya gyara mata sumar kanta idan Ya hargitsa mata ita gurin kwanciya, idan ya gama itama ta gyara mashi tashi sumar, a tare suke zagaye bangarorin shaƙatawar dake a cikin gidan, duk idan zasuyi fira saita tambaye shi ya bata labarin rayuwarsa agidan iyayensa baya gajiya da labarta mata, dadi takeji idan yana faɗa mata irin