Muhimman abubuwa 12 da ya kamata ka sani game da maɗiga domin ceto jarirai

Muhimman abubuwa 12 da ya kamata ka sani game da maɗiga domin ceto jarirai

Maɗiga

Muhimman abubuwa 12 da ya kamata ka sani game da maɗiga domin ceto jarirai

1. Bayan haihuwa, ƙashin ƙoƙon kan jarirai a rarrabe yake kuma ya ƙunshi ƙasusuwa guda biyar ne: biyu a gaba, biyu a tsakiya, sannan ɗaya a ƙeya. Maɗiga wani gurbi ne mai taushi daga gurunguntsi da tantani, saɓanin ƙashi, a mahaɗar waɗannan ƙasusuwa.

2.Hikimar kasancewar ƙashin ƙoƙon kan jarirai a rarrabe shi ne domin kan ya sami sauƙin fitowa daga ƙugun uwa yayin haihuwa. Bugu da ƙari, kasancewar ƙoƙon kan a rarrabe zai bai wa ƙwaƙwalwa damar girma kafin ƙasusuwan su haɗe.

3. Bayan haihuwar jarirai, akwai maɗigai har guda shida a ƙoƙon kai. Sai dai, an fi lura da maɗigar tsakiyar kai, wato ta saman goshi, da kuma ta ƙeya. 

4. Maɗigar tsakiyar kai, ita ce maɗigar gaba, wato 'anterior fontanelle' a turancin likita. Kuma wannan maɗiga ita ce mafi girma kuma wace aka fi lura da ita cikin maɗigai shida da ke ƙoƙon kan jarirai. Sauran maɗigan biyar suna rufewa da wuri tun a makonni zuwa watannin farko na rayuwar jarirai.

5. Maɗigar tsakiyar kai tana da kusurwa huɗu kuma tana da sifar daimon. Matsakaicin faɗinta ya kai santimita 2.1. Sai dai, akwai wasu larurori da ke janyo buɗewar maɗigar fiye da ƙima.

6. A yayin da jariri yake cikin ƙoshin lafiya, maɗigar tsakiyar kai akasari a shafe take ko kuma ta ɗan lotsa kaɗan. Amma ana iya ganin ta ɗan ɗago sama yayin da yaro ke kuka, amai ko kuma yayin da yake kwance. Har wa yau, maɗigar tana kasancewa cikin harbawa ne a kowane lokaci kamar harbawar zuciya.

7. To ko yaushe maɗigar tsakiyar kan ya kamata ta rufe? Maɗigar tsakiyar kai tana rufewa tsakanin watanni 13 zuwa 24 bayan haihuwa. Amma akwai larurorin da ke shafar ginin ƙasusuwan fuska da ƙoƙon kai waɗanda ke haddasa rufewar maɗigar da wuri. Haka nan, rufewar maɗigar da wuri na iya janyo dakushewar girman ƙoƙon kai da kuma ƙwaƙwalwa. 

8. Jariran da maɗigarsu ta rufe da wuri suna da haɗarin samun ƙaramin kai da kuma dakushewar aikin ƙwaƙwalwa. Hakan kuma na iya kawo jinkiri ga matakan girmansu, misali, gaza iya riƙe wuya, zama, tsaiwa ko tafiya a watannin da aka saba gani.

9. Kamar yadda aka ambata a sama, cewa akasari maɗiga a shafe take, Sai dai ana iya ganin faɗawar maɗigar , wato ta rufta ciki, musamman idan ruwan jikin jariri ya yi ƙasa sakamakon wata larura ko kuma ƙaranci ko rashin ingancin ruwan nonon uwa ko abinci.

10. Kamar yadda maɗiga za ta iya faɗawa ciki, haka kuma za ta iya bulli waje yayin da jariri ke fama da cutukan da ke haddasa batsewar ƙoƙon kai sakamakon wani kumburi, taruwar ruwa ko jini a cikin ƙoƙon kai.

11. Rufewar maɗigar tsakiya kai ƙasa da watanni 13 tare da bayyanar jinkirin matakan girman yaro ko kuma bayyanar alamomi kamar jijjiga, rirriƙewar gaɓoɓi, dalalar da yawu ko gani hararagarke duk na nufin a gaggauta ganin likita.

12. Bugu da ƙari, faɗawar maɗiga ko kumburowarta waje tare da alamomi kamar yawan kuka, zazzaɓi, shawara da sauransu duk na nufin gaggauta ganin likita.

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post