Rainonta Zanyi page 1 Complete by Maman Teddy

Rainonta Zanyi page 1 Complete by Maman Teddy

 

Abokiyar Hira Novels

Story and written by:

Ayshatou maman teddy

Free page 1

Zaku sami wannan littafi tun daga 1-5 pages a ƙyauta sauran kuma pages nashi na kuɗi ne sai anyi payment  Ga masu buƙatar fara payment Regular payment₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ta Wannan number 08081202932.ko katin MTN ta Wannan number 07037236845.

________________________

_Bismillahir rahmanur Raheeem_


Wani irin ƙauye ne da ya amsa sunan shi ƙauye , Garin shiru tamkar babu Al'umma a cikin ta , duk inda ka kalla babu abin gani sai Tumakai da zabbi da Sauran dabbobi na mutanen ƙauyen, haka zalika ko ina Jar ƙasa ne (Taɓalɓali) ta ko ina kai da gani kasan ƙauye ne da ake tsananin Rashi yawancin su manoma ne sai Makiyaya”. 


“Wani irin gida ne na hango mai gajeriyar katanga wanda dashi da babu Duka Ɗaya , amma ciki sai uban fatsamin ƴaƴa da zamu iya cewa yawancin mutanen ƙauyen a wannan Gidan suke Rayuwa ”.  Hadari ne ya taso tare da iska mai Ƙarfi Wannan yasa Wata matashiya wacce ba zata Haura shekaru 25 ba saurin buɗe Ƙatuwar Tukunya wacce aka cika da Tuwon dawa daaamm tana faɗin Ku kawo kwanoni jama'a hadari ya taso”. Kamin kace mene tuni Yaran gidan sun rufe ta munana gaje gaje dasu wannan hanci na zubar majina wannan haƙora babu ƙyawun Gani ”.


“Haka Wannan matashiyar da tsohon ciki take Aikin zuba masu Tuwon da ko miya babu a haka ake cin shi a cikin wannan ƙauye , gumi kam tsiyaya mata yake ta ko ina”. 


Gigeef Aleena tayi tana Saurin tashi daga Ƙwancen da take tana janye jikin ta daga lallausar blanket ɗin data rufa jikin ta Da shi ”. Hasbunnallah Ta Furta da Ƙarfi tana Mai kai Shimfida²n yatsun ta tare da Ɗaurawa bisa Goshin ta tana furta “ Oh  God! Meke faruwa ne? , Rufe lulun idanunta tayi tana buɗe su a hankali ta tuno da Wannan ƙatuwar baƙar tukunya da tuwo da ta gani a wannan barcin nata , Ni dai Gani nayi Kawai ta zabura tayi na Privacy tana Fara sheƙa lafiyayyun Amai , da ta Rufe idanun ta ta buɗe sai ta hango fuskar Yaran Gidan da ta gani suna Washe mata Dafaffafun haƙoran su wanda ko a labari bata taɓa jin irin wannan ba , Wannan yake sata ƙara yin sabon kakarin Aman tana yi tare da Kama ciki tana Wani jaaa baya don ji take kamar za'a cafko ta ”. 

 

A hankali ta Murɗa Handle Door Ɗin bedroom na Aleena duka don kar ta tashe ta Daga Barcin ta domin kuwa Sanin hali yafi Sanin kama , Ɗaga idanun ta tayi tana bin Bangon Ɗakin da aka bishi da Hotunan Aleena ta ko ina tun tana Jaririya har zuwa yanzu da ta kai kusan shekaru 10 . Murmushi Hajiya Nadiya tayi tana nufo toilet Din kanta Tsaye tare da Furta “ Good morning my Dear ”. 


Shigan ta yayi dai dai da Ɗagowan Aleena tana Goge Fuskar ta da Towel , Ba tare da ta ba Hajiya Nadiya Amsa ba ta kai duban ta zuwa Agogon dake privacyn niko mamaki ne ma ya ka Mani ace Lokaci har a toilet 😂 ”. 


Cikin zazzaƙar Muryar ta ta furta “ What did I told you yesterday's night Mom? , Cewa fa nayi kar Ki tashe Ni sai Ƙarfe 10:00am na safe , just because of the school mutum ya tashi da sanyin safe , da mene zamuji it's raining season nd makarantar nan Na Uncle Ɗina ne , Zanje duk lokacin da naga dama Haka zan dawo duk lokacin da na So . 


“Cike da Rashin damuwa bisa Kalamanta ta kai Hannu tana Gyara mata Gashin ta da ya barbazo mata yana taɓa mata ido don masifa ”.  Come on my baby it's Ok! Muje ki ƙwanta ki koma Barcin....No ” . Ta katse ta tare da Janye jikin ta tana ɗaukar brush ɗin ta tare da fara wanke fararen haƙoranta wanda Wushirya suka raba daga tsakiya . 


Da taimakon Hajiya Nadiya Aleena ta yi wanka sannan ta ɗaura mata Rigar Wanka tare da Ƙaramin Towel tana tsane Ruwan Kan ta kana su fito zuwa bedroom ɗin nata ”.


*

Khairy Khairyya! 


Muryar Doctor Bilki ya katse Khairiyya dake can Ɗakin ta , wannan yasa ta amsawa da Yes Mom”. Time For School , Doctor Bilkisu ta Furta cikin sauri tana cigaba da Haɗa mata lunching box . Daga Saman up stairs Ne Khairiyya ta leƙo da kanta inda na ganta sanye cikin Shigar Ƙananun kaya Riga da Wando mai kamewa rigar mai kauri sakamakon yanayin Garin ,Saman kan ta Head Phone ne tana jin Waƙoƙinta Doctor ta katse mata ”. Hannun ta Riƙe da Wayar ta Samsung mai bala'in tsada baka ce yarinya ce ƴar 11 yrs take Riƙewa ba . 


Tsayawa tayi tana bin Mahaifiyar nata da kallon burgewa don tayi shigar ta tsaf na tafiya wurin Aikin ta cikin suit riga da wando baƙaƙe sai Mini hijab Fari , ƙafarta cikin hill mai ƙyan gaske . Wow Mum kin yi ƙyau sosai . 


Ɗagowa tayi tana Sakin baki tare da cewa “ Ohhh wai dama kina tsaye ne anan Khairy? Lokaci da zai tafi Quarter to eight. 


Ɗan caɓe baki Khairy tayi kana tace “ Momy ki daina Damuwa fa ko 11 naje makaranta babu Wanda zai tambayeni dalili saboda Ƙawata Uncle Ɗin ta ne mai makarantar . 


Sakin baki Doctor tayi kana tace “ Uhhmnn Ohk shine Dalili? Shi Uncle Ɗin nata ne ya goya maku bayan ku rinƙa zuwa a ko wani lokaci kuka So?.


A'a Ai Bama ya ƙasar nan Mummy nima a hoto na san shi , Mummy yanda kika san balarabe ko don a ƙasar larabawa yake ne yasa ya zama haka , cox tace kaman a labenun yake ko Egypt ne Na dai manta . 



Hmmm Ni ban tambaye ki ba , ga Lunching box din ki nan idan Talatu ta shirya ki sai Auta Driver ya kai ki , Ni ina da Surgery da Ƙarfe 9:00 yanzu zan tafi Asibiti . 


Ohk Bye Bye ”.

*



Kai ne wane? Nifa malamin ki ne tun daga can Egypt kawun ki ya wakilta Ni akan na kula da ilimin ki na Addini.... Malam Abdullahi yana Maganar yana Gogar Asuwaki  tare da tofar da Tuƙar ”. 


Matsawa Aleena tayi Saurin yi baya tana bin Malam Abdullahi da Wani irin wulaƙantaccen kallo kana tace “ Ya isa Haka bawan Allah”. 


A Gaskiya tun da nake ban taɓa ganin kazami irin ka ba , ko brush baka yi bakin wari yake yi😳😂 Fiddo ido Waje malam Abdullahi yayi cike da mamakin rashin kunya irin na Wannan yarinya ƙarama , kana ya girgiza kai yana bin tanfatstsen gidan da kallo a hankali ya furta Dama Ƴaƴan Gata haka suke , shi kuma Ɗan Gata Ɗan banza . 


Ba tare da Aleena ta saurara taji mene yace ba ta miƙe tana barin shi da Littafi a hannu . 


A falon tsakiya ta tadda Hajiya Nadiya Zaune cikin shiga ta Alfarma cikin wata dandatsatsen Abaya da ya karɓi jikin ta ƙwarai hannayen ta sun sha manyan zabban Zinarai suna walwali. Tun daga Yanda Aleena ta Hango Hajiya Nadiya cikin Rufe jikin ta da Wani Zabgegen Mayafi irin ta alfarma yasa ta fahimtar da Uncle take Video call.  Haɗa ido suka yi da Hajiya Nadiya wannan yasa Aleena saurin Nufar ciki . 


Wucewar Aleena ya bani damar Kallon Fuskar Wannan wanda suke kira da Uncle , Ya subhnallh, tabbas da ba don na samu tabbacin Hajiya Nadiya ce mahaifiyar sa da to babu shakka nace daga ƙasar larabawa ya fito , don har sajen sa shigar sa kyawunsa hasken sa ga manyan idanu tare da Ɗan Dogon hanci mai sauka ”. 


Motsin dawowan Aleena ne ya sani saurin kallon ta tare da mamakin ganin ta da nayi da Hijabi kamar ba itace ta baro Malam Abdullahi ko ɗan ƙwali babu ba...” 

Cike da fara'a ta ,ta zauna gyefen Hajiya Nadiya tana kallon fuskar Uncle Afeef kana ta ɗaga masa hannu tana furta “ Hi Good Day Uncle ”. 

Kallon Mahaifiyar sa yayi yana mata kallon ya naji haka ? , Turanci akasin yaji larabci ,RAINON ta sa kenan?  . Lumshe Sexy eyes ɗin sa yayi yana motsa laɓɓansa a matuƙar miskilance fuska babu wasa yace“ Assalamu alaikum ”.  

Kallon Hajiya Nadiya Aleena tayi kana ta kalli Uncle Afeef tana cewa “ Sorry Uncle”. Ƙurrr yayi mata tsawon lokaci fiye da Mintuna Goma idanun sa na akan Aleeena ba tare da yace komai ba ”. Sai kuma suka ji ya sauke numfashi yana furta “masha'allah zan Dawo nan sati Daya ”. Kamin Hajiya Nadiya tace wani Abu tuni ya datse ,wannan yasa Aleena kallon Hajiya tare da cewa “ Mummy wai shi Ya Afeef baya turanci ne , komai nasa da tsauri, sai kaji yana wani mashaallh, Alhmdlh ko fa Hi baya cewa sai Assalamu alaikum...” mu tara a next page💃🏻💃🏻

Wannan somun taɓi ne a cikin littafin RAINONTA ZANYI 

Wai shin waye Wannan Uncle Afeef? 

Sannan wani irin rayuwa Aleena da ƙawayen ta suke gudanarwa a makaranta . 

Jaruman mu suna gaba💃🏻💃🏻 Na tashi don Shiga kitchen ne kuyi manage 

*Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post