Rainonta Zanyi page 2 Complete by Maman Teddy

Rainonta Zanyi page 2 Complete by Maman Teddy

Abokiyar Hira Novels

 *Story and written by:*

*Ayshatou maman teddy*

*Free page 2*

*Zaku sami wannan littafi tun daga 1-5 pages a ƙyauta sauran kuma pages nashi na kuɗi ne sai anyi payment  Ga masu buƙatar fara payment Regular payment₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank shaidar biya ta Wannan number 08081202932.ko katin MTN ta Wannan number 07037236845.*

________________________

*Ga masu buƙatar a Tallah ta masu hajar su zasu biya 2k kacal inshallah*

*For those who interested you can join us*

*https://chat.whatsapp.com/GAKVOq0DCaA6Vicx9saIrj*

Ba tare da Wani dogon tunani ba jin yayi mashaallh Alhmdlh tasan dama maganar tasu ce tazo ƙarshe don haka Cikin Sauri Aleena ta miƙe tana barin inda Hajiya Nadiya ke zaune ....Nufar Resting room ɗin Mummy tayi tana fiddo da Wayar ta tare da Shiga WhatsApp tana fara Chat da Aminiyar nata Wato Khairy “Hi shine Kalmar data turo mata tare da Emoji 🙋🏻‍♀️ 

Dawo mata da massage Khairy tayi kaman haka “ Hi biebie ya mummy? She's pretty Good Alhmdllh ”. 



Wani irin dariya Khairy ta fashe dashi jin amsar Pretty Good Alhmdllh don tabbas yau tasan sun yi call da Uncle Mutumin Larabawa”. 


Meke faruwa biebie? Ya Uncle Afeef ɗin? 


Kallon ta Aleenah tayi tana caɓe bakin ta kana tace “ Wai zai dawo nan da Two weeks”. 


That's a Good news 🤩 Wallahi duk na ƙosa naga dawowan sa naga wannan Uncle Ɗin namu”. Saurin kallon Khairy Aleenah tayi tare da jefa mata kallon baki san shi bane ,da kin san tsaurin sa tabbas da baki ce haka ba . Ke Khairy zaki dakata da Wannan shashancin naki ko kuwa? Ni ce Miki nayi inaso ya dawo? Ke da ganin yanayin sa kin san bashi da kirki nifa banyi wayo dashi ba, tun ban fi shekara Ɗaya ba yabar ƙasar nan , kinga ko kusan shekaran sa Goma kenan babu shi , Da ya tashi tafiya sai ya faɗa ƙasar larabawa duk ɗabi'un sa irin na malam Abdullahi mai hular taɓani kaji hadisi sai suyi ta......Katse Aleenah Khairy tayi ta hanyar cewa “ Kar ki damu , sai fa kiga yazo Miki kamar bashi ba yanda muke expecting ganin sa ba , kar fa ki manta Yanda Uncle Afeef yake , Bama anan ƙasar shi aka haife shi ba , lokacin Mummy tana zaman London can fa ya taso har ya gama secondary sannan suka dawo Nigeria bai yi shekara Uku ba ya koma Egypt shine ya zama haka , So cool ur mind Aleena , Zaki mamakin ganin Uncle Afeef shima zaki gane he's such an amazing en...... Stop Khairy Stop please....!!


“Aleenah ta katse ta cikin fushi da tsawa tana mai tura mata emojin angry😡 tare da cilli da Wayar nata gyefe....sam bana expecting ganin sa kaman Daddy da Mummy tabbas idan ya dawo ban san ya gidan nan zai komar mun ba hmmmmn”.  


Ya za'a yi nasa Daddy ya dakatar da Wannan dawowan nasa i most find a way to stop him . 


Ƙiririn💃🏻Sabon saƙo ya shigo Wayar ta wannnan ya sata a kasalance kai hannun ta tana ɗagawa... group ɗin su ta gani An ƙuƙe ana zuba zance wanda babu shakka ko bata shiga ba tasan Khairy ne ta kai masu labarin Uncle Afeef zai dawo . Rintse idanunta tayi tana furta “ Wai a hakan shi fa Doctor ne surgeon,hmmmm ƙila haka isar patient ɗin sa da Mashaallh Alhmdlh da iyayin larabcin sa , Ni Abin damuwa na ya dawo ya fahimci ko zo dauko mun cup da Larabci ban sani ba tabbas na shiga uku! 


Bude idanunta tayi tana kallon Sunan group din nasu wanda su ne yasu yasu ƴaƴan gata masu fahari da Naira marasaa ji fahari da ɗagawa ga rashin kunya”. Wanda suka yi ma Group ɗin Suna da ALEENKHAIR DELIGENCY 

ALEEN -Aleenah

KHAIR -Khairy

D- Deeja

I- Intysar 

L-Leemat 

I-Ihasaan

G- G Yasmeen 

E-Elvin Teeemah

N-Nusy

C-Chronicle Hauwa 

Y-Yusrah

Dukan su idan kana neman yara tsagera danger marasa kirki to ku sami waɗannan yaran , kuma ko wannen su da Dalilan da yasa suke kiran su da sunan shi ...” 


Numfasawa Aleena tayi tana kai hannun ta tare da taɓa group ɗin tana ganin Wainar da ake toya “ Su duka sun ƙofe suna farin ciki da jin dawowan Uncle Afeef, Abin Ni kai na har mamaki yake bani yara ƙanana Wanda dukan su babu wanda ya haura shekaru shi biyu a duniya ,amma idan ka gansu ƙaɓa kaɓa barin Aleenah da kuma ta kasance duk ciki itace ƙarama ,amma controlling din su take ita ga Queen ba” .  Ganin haka yanda suke ta farin ciki ita kuwa tana Akasin haka yasa Aleeena jan dogon tsaki tana Ajiye wayar nata a gyefe ”.


A wannan Rana sam Aleena ta ƙi fitowa ko falo ,don ɗakinta ta shige tana jin motsin Mummy sai ta rufe ido tayi kaman mai barci har yamma sannan ta miƙe ”. Kai tsaye bathroom ta shiga tana Watsa ruwa tare da zaman durshaan Ita dai kawai taji bata farin ciki da dawowan wannan mutumi . Lumshe lulun idanunta ta yi tare da miƙewa tana nufo bedroom ɗin ta , dressing mirror ta nufa tana taje gashin ta mai cika da tsawo ga tsantsi kana ta kame da Ribon tana rabasa gida biyu kaman yanda Mom ke yi mata ”.  


Miƙewa tayi tana saka takalmin ta mai rufi tare da yowa falon Hajiya Nadiya ”. Turusss tayi Hango Mummyn nata tana baimawa ƴan Aiki umarni alamu tun yanzu an fara shirin tarbar mutumin da taji yace kaman saura Sati biyu ya dawo ”. 


U wake up? Hajiya Nadiya ta furta tana kallon fuskar Aleena tare da murmushi tana mai takowa zuwa inda Aleena take”. Cike da jin kan nan nata ta rufe idanun ta tana gyaɗa mata kai tare da cewa “ mum meye naga ana kaiwa da dawowa all this is for What Mum? ,Ta Ƙare maganar ta na nuna Wata Ma'aikaciyar gidan da ta wuce da Turare a hannu tana Nufar Ɓangaren Uncle Afeef . 


Cike da Son Muryar tausasawa Mummy ta kai hannu tana ƙoƙarin jawo ta jikin ta amma sai ta janye tana wuce ta cikin sauri gudu gudu na ɓacin Rai tana furta “ No! Kar Wanda yazo inda nake yau bana buƙatar ganin kowa , Sannan zan kira Daddy ya dawo daga Abroad shi zai mun maganin Uncle Afeef ba zan bari ya dawo ba ”. 

*


9:30am. 

Alarm ne ya buga mata wannan yasa Aleeena fahimtar lokacin tashin ta yayi don zuwa makaranta . A natse take shirin ta hankalin ta kwance kana ta saɓo school Bag ɗin ta hannun ta riƙe da hular Barrett da suke sanyawa ”.  Yanayin shigar ta zuwa makarantar ka Ɗauka ba a Nigeria makarantar yake ba. Cike da mulki take saukowa daga Stairs tare da nufo dirning area ”.  Wani Ɗauke Wuta tayi tare da tsayawa turusss kurum jikin ta taji yana rawa kar² sakamakon tozali da idanun ta suka yi da fuskar Afeef yana daga can sofa cushine dake gyefe sanye cikin Boxer da Rigar sanyi mai kauri ya ɗaura hular ta yanda yayi mata a yau kamar baƙon Bature akasin yanda ta saba ganin shi yana mshallah .  Ƙirjinta na dukan uku³ ta nufi dirning tana zama yayin da nan masu girke ² suka fara gaishe ta tana amsawa cike da izza, don kuwa ita bata gaishe da babba sai dai a gaisheta tarbiyyar da ta samu kenan . 


Ba tare da Afeef ya kalli inda suke ta zuba mata gaisuwar ba amma kuma kunnen shi na wurin yana mamakin wannan RAINON TASA kenan? ”. Muryar Mummy yaji tana cewa “ Good morning my Dear ” . Kissing din Mummy tayi tana furta “ Morning mummy ”. A sace Mummy ta kalli inda Afeef yake idanun shi na kan Laptop din dake gaban sa , a hankali ta furta “ Je ki wurin Uncle Afeef ya dawo jiya da dare ”. Caɓe Baki Aleenah tayi tana kallon Lunching box ɗin ta tare da Kai hannu tana dauka tana miƙewa tare da cewa “ No need for breakfast mum , bye bye”. Tana furtawa ta miƙe ta fice ”.  


Kallon Afeef Hajiya Nadiya tayi tana rasa me ma zata ce mishi ,don tafi kowa sanin tsaurin shi da kuma waye Afeef da jan Ran sa ”.


*

Ɓangaren Aleenah kuwa tun da ta fita sunan Driver na jan ne amma sam bata sanin inda suka nufa Tunanin Afeef ya cika mata Ƙwanya, wani Mai mashin ne yazo wucewa da Yarinyar sa yana gudu alama yana cikin wani uzuri ba tare da ya sani ba idanun sa ya hadu dana Aleenah suka zo suna gogar ya windown motar yana ƙoƙarin wucewa , shidai kawai yaji saukar yawu ne a gyefen fuskar sa , tana furta stupid, kamin ya yi wata wata yaji ta balle murfin ruwa tana shako masa wannan yasa shi kusan sakin burki da sauri yayi Gyefe don ta kusa saka shi yayi hatsari ”.  


Ita dai taga moton su ne yana slow da reverse drivern na baya . 


Are You pool ? Meye nakq na tsayawa? Tayi ma drivern magana a tsawace , Wanda jin hakan yasa Drivern cewa “ Yi hakuri hjy Me Gida ne Alhaji yace na juya ”. Da Sauri ta kalli drivern tana juyawa ɓangaren mai zaman banza inda taga Afeef zaune wanda sam bata lura dashi ba tun shigowar ta😳”. 


To ko wani mataki Afeef zai ɗauka? 


Kuna ganin Aleenah ta cancanci hukunci kuwa akan Abin da ta Aikata tabbas littafin akwai badakala a gaba💃🏻💃🏻 da Alama Mummy ta lalata RAINON nasa amma ga shi ya dawo ai .



Shin kuna ganin Afeef ya karɓe Rainon sa ya ya raine ta da kansa yanda yake so ko kuwa? Abar ma Mummy? 


*Hmmm mu tara page na gaba inshallah naji sharhin ku ina matuƙar godiya masoya MAMAN TEDDY 🧸 🥰💃

Post a Comment

Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.

Previous Post Next Post

Sponsored Link

Sponsored Post